Facala Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Facala Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 3 of 26
_*page*_ *5-6*
Tunda ta sauka cikin adai daita sahu ya ke binta da kallo,ji yai kamar yayi watanni bai ganta ba, a sannu ta k'araso shagon da ledar kayan,Jabir ya fito ya k'arb'i kayan hannunta. A gajiye ta k'arasa ta zauna da fad'in "Ya Allah."
Cikin kulawa su ka gaisa da jama'ar shagon sannan a hankali ta juya gareshi yana amsa waya mirmishi ya sakar mata ita ma ta maida mai martanin mirmishin tana kauda kai gefe.
Bayan ya gama wayar ya juyo gareta da fadin"hajjaju kin karaso kenan ya exam d'in?"
"Hhhhhmmm gani na karaso Khaleelee amma kamar zan fad'i don gajiya."
"Ayya sannu,ai an kusa dai a huta gaba d'aya ko."
"Eh insha Allah nan da two weeks zamu k'are gaba d'aya."
"To Allah ya nuna mana."
"Ameen ya Allah, ga d'inku nan zuwa gobe zanzo ma awan wanda baka dashi da kudin ma gaba d'aya."
"Ok ba damuwa,ina godiya."
Mik'ewa tai tare da fad'in"na wuce sai goben."
"To Allah ya kaimu,ki gaida Mama da takwara."
"Ok zasu ji insha Allah." Ta fad'a tana fita a shagon.
***********
Da dare suna zaune a falo tare da mamansu kallo suke yayin da rabin hankalin Su'ada yana ga bitar karatun ta wani sashin na zuviyarta kuma na tsinkulin ta da maganar Khaleelee, a hankali ta zame ta kwanta kan kujerar da take zaune,lumshe idanuwa tai tana hasko fuskar Khaleelee d'auke da wannan k'ayataccan mirmishin nashi,ita ma ji tai mirmishin ya sib'ice mata.
Mama da ta juyo za tai mata magana ta ga ta rufe ido tana ta mirmishi ita kad'ai,zuba mata ido tai tana karantar yanayin da take ciki a hankali tace "Su'ada karatun kike ko bacci ko ko tunani."
Da sauri ta bud'e idonta tana d'an yak'e tace "Mama karatu fa tuni na gama dashi,kinga duk in da na duba cikin handout d'in ma sai naga na gama da wajan."
"Ok haka ake so, na ga kin kwanta ne kinata mirmishi ke kad'ai kamar an miki albishir da wani abu,ko akwai wata a k'asa ne bamu sani ba."
Ta k'arasa da d'an dariyar tsokana.
Langab'e kai Su'ada tai da fad'in "Mama meye a k'asa wanda zaku kasa sani,kawai dai tunanin duniya nake."
"Hhhhmmm ko tunanin surukina ake?"
Da sauri ta zaro ido tana fad'in "lah Mama wane suruki kuma,Allah ni dai a'a fa."
Dariya Mama tai da su jiddah ganin yanda ta wani rikice kamar bak'on abu ne a gurinta.
Husna tace "Aunty Su'ada kin san me? Jiya yaya Nazeef ke tambayata wai don Allah ko dai kina yin zance da wani ko dashi ne baki son tsayawa kullum yace zai zo sai ki ce karatu karatu."
Hararar ta Su'ada tai tana tab'e baki tace "ku kuka sani ke da shi,daman na san ke ce abokiyar gumata dashi."
"Aa fa ni tambaya ta kawai yayi na bashi amsa da cewa exam kike maybe in kin gama zaki bashi dama ya rink'a zuwa."
kafin Su'ada tai magana Jidda ta d'auka da fad'in "ke dilla k'yale shi,shi shegen tambaya gareshi kamar ya aje mutane."
Dak'uwa Mama tai Mata da fad'in "Dan gidanku yayan ki ne fa kike mai haka,to wai ma ke yace ya na so ne ko me da kike tada jijiyar wuya haka."
Su'ada ta ce " Mama fa ni wallahi ban sonsa ko kad'an shi kamar bai karatu ba,wallahi da a darkin ma ya ke da zama ban san irin gidahumancin da zai yi ba."
Fulon da ke kusa da Mama ta cillowa Su'ada tare da dak'uwa "Wallahi ku kiyayeni da wannan iya shegen,wai to ma in bi ki bawa masu sonki dama yanzu ba sai yaushe? Eh Su'ada nace sai yaushe? da karatu ya rik'eki mun goya miki baya yanzu kuma meye ya rik'e ki tunda dai karatun nan duka kwanaki ya rage a gama shi."
Sassauta murya ta k'ara yi taci gaba da fad'in " Su'ada ki tsaya ki nutsu cikin tarin samarinki ki fidda wanda ya fi kwanta miki a rai,kinga yanzu saura watanni ki cika shekaru ashirin, gashi saura sati biyu ki gama N.C.E d'inki,kinga aure shi yafi dacewa da ke yanzu,don haka na baki lokaci daga nan har zuwa wata guda ki nutsu ki fidda guda wanda hankalinki ya fi kwanciya dashi kinji."
D'aga kai nai a hankali nace "To mama insha Allah zan fidda."
Tun daga wannan lokacin ban k'ara cewa uffan ba har tsawon lokaci na mik'e zuwa d'aki ina cewa "Mama zan kwanta sai da safe."
"Allah ya tashemu lafiya."
Mama ta amsa Mata.
Tunda ta shiga d'aki ta fad'a gado k'irjinta na wani irin bugawa, rintse ido tai tana fad'i cikin ranta ' Allah ka dafa min Allah karka barni da zab'in raina kai min zab'inka,Allah dukkan abunda zai zama alkairi gareni da rayuwata Allah ka zab'a min shi,kai kasan halin da nake ciki kuma kai zaka min maganinsa."
Juyi take tayi tana rok'on Allah mafita, ba ita tai bacci ba sai k'arfe d'ayan dare.
Da safe haka ta tashi jiki ba k'arfi ta shirya ta tafi school.
Tun daga wannan ranar Abubuwa suka cakud'ewa Su'ada ga karatun exam ga tunanin wa zata zab'a cikin tarin samarinta, ga ciwon son Ibrahim dake k'ara azalzalar zuciyarta, nan da nan ta rame tai fiyau da ita.
**********
Ya rage kwanaki Biyar su zana final Pepper ranar basu da exam da yamma tace Jidda ta shirya ta rakata Wajan Khaleelee ta anso d'inkunan su,don da safe take son tafiya musu dashi school.
Tana sanye da doguwar riga marron colour me adon yello me duhu mayafin da tai Rollin kanta yellow sai plat shoe d'in ta shima yello wayarta kawai ta d'auka ban da jaka, tana tsaye cikin gate tana jiran Jidda ta fito su tafi taji tsayuwar mota a k'ofar gate d'in nasu,bata maida hankali ga gate d'inba don bata tunanin gidan nasu za'a shigo, a sannan Jiddah ta fito tana fad'in " Sorry sis na tsaya d'auko wannan material d'in nawa ne in bawa Khaleelee ya d'inka min na gaji da ajiyarsa a akwati.
Ita dai Su'ada bata amsa mata da komai ba illa sa kai da tai don fita a cikin gidan.
Kicib'us su kai da Jameel yana k'ok'arin shigowa,D'an jenyewa tai gefe tana fad'in "Oh soja kana gari Ashe? Zaka bigeni da k'arfin allurarka."
Dariya yai a taka'ice yace "ina zuwa haka na kawo muku ziyarar bazata.hajiya Jidda har dake za'ai tafiya ma?"
Cikin dariya Jiddah tace "Yaya Jameel ai bamu San kana tafe ba wallahi,zamu je zoo road ne mu amso d'inki."
"Ok to bari in shiga mu gaisa da Mama sai in fito in kaiku ko."
Da sauri Su'ada tace " A'a ba zamu wahalar da kai ba ka barshi kawai wlh zamu hau Napep ma."
D'ora hannunsa yai a baki alamar tai shiru daga haka ya wuce cikin gidan.
Cikin k'unk'uni Su'ada ta je ta tsaya jikin motar tasa tana fad'in "Wai ayi ta takurawa mutum haka kawai,ni nace ban son hawa motar amma ya wani zaro min ido kamar ubana,mutttsss."
Y'ar dariya Jidda tai tace "Kai Aunty Su'ada meye laifin yaya Jameel wai don Allah yanzu shima duk k'ok'arin sa kanki baki gani,duk sanda yazo garin nan yata nacin zuwa wajanki kina yarfa shi,ni kam wlh ban ga aibunsa ba Sam."
"Dallah malama rufemin baki ke me yasa bazaki soshi ba?"
"A'a ai ke yace yana so ba niba amma dai gaskiya Aunty Su'ada a shawarce karki wuce yaya Jameel a cikin zab'enki wlh don mutumin yayi fa."
Ta bud'e baki zata bata amsa ya fito don haka ta gintse kawai amma ta watsa mata harara."
Cikin fara'arsa ya k'araso yana fad'in " kuyi hak'uri na tsaida Ku ko? Ku shiga mu tafi."
Ya bud'ewa Su'ada gaba sannan ya zagaya ya zauna mazauninsa.
*Taku ce*
*y'ar mutan Ja'oji*🙋
[2/23, 11:51 PM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭
*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*
👩🏻💻👨🏻💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.