Complete Hausa Novels

Facala Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Facala Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 20 of 26

_*page*_*39-40*

Innaro ce ta Fara d'aukan Babyn tana fad'in "Madalla da hikimar ubangiji,wannan kama ta b'aci."

Mik'awa Mama Babyn tai fad'in "Duba min wannan kama ki gani don Allah."

Sosai mama ke kallon yarinyar, cikin memory d'in ra take tuno ranar data haifi Su'ada, babu wani abu daya banbanta fuskarsu, lalle yarinyar na tsananin kama da mahaifiyarta.
Rungumeta tai cikin jikinta tana mata addu'a da jin tsantsar k'aunar y'ar ba ratsata.

Cikin tsokana ta Mama tace "Wannan y'a da kalen kama kike,ki rasa kamar wa zakiyo sai ta mijina to ahir d'inki, mijina ba tsaranki bane(dake Su'ada kamarta d'aya sak da mahaifinta)

Dariya innaro tasa tana fad'in" To me ma zatai da mijinki fata duk tai laushi,ita kam Wannan d'iya mijinta ma na Saudi yana karatu."

Dariya suka sa gaba d'aya, sai a sannan Mama ta k'arasa ga Su'ada dake kwance, gaba d'aya kunya ta rufeta,yau kam ji take har Maman kunyarta take,tunda ya haihu ta kasa had'a ido da kowa.
Mama tace "Sannu Su'ada, yanzu me kike ji a jikin naki?"

Girgiza kai tai idonta b kallon gefe tace"Ba komai Mama."
"To Alhamdulillah, an gode Allah, haihuwa tai kyau ai,tunda an haihu lafiya ."

A lokacin Khaleelee ya shigo daga gun doctor, da sauri ya tsugunna yana gaidasu,su ka amsa suna mai barka, kansa a k'asa yake amsawa, sannan yace "Mama zan d'an je gida na dawo,don sun ce sai k'arfe goma zasu sallamemu,to Sakeena ma yanzu nace taje gida sabida yara,nima zanje na dawo."

Innaro ce ta amsa da fad'in "Jeka ai ba damuwa,muna nan,kamar yanzu goman za tai."

Mik'ewa yai yana musu sallama ya fice.

*******
Wajan k'arfe goma da rabi likita ya bawa Khaleelee takardar sallama,Wanda ya dawo tun tuni daman wanka yaje yai.
A motar Mama su ka wuce gidan,shi kuma Khaleelee ya biyosu a mashing d'in sa.
To fa yau dai ga jika taja Baba har d'akin Su'ada, duk da baida lafiya,amma haka ya sa sandansa ya dogara zuwa d'akin, Khaleelee yana fad'in "Baba ka bari a kawo ma ita d'aki."

Yace "A'a miji ai shi ke tarar matarsa,barni naje na ganta."

Cikin mutunci su ka gaisa dasu Mama,suna mai sannu da jiki,bayan ya d'auki y'ar yai mata addu'a sosai,sannan ya dubi Su'ada da ke zaune kan filo kanta a k'asa yace"Sannu Su'ada kinji, Allah ya k'ara lafiya,abunda nake son sanar dake shine, yanzu Allah ya d'ora miki wani nauyi ne me girma,rayuwarki data baya ba d'aya ba,kin zama uwa,don haka duk abinda zaki aikata yanzu to karatu ne ga yarki,duk abunda za kiyi na kirki ko akasin haka to nad'ewa za ta rink'a yi,kece makarantarta,don haka kiyi k'ok'ari ki zama malama me koyar da ita karatun sanin Allah da manzansa, kiyi mata tarbiyar da duniya zatai alfahari da ita,kar kiyi wani abu na Allah wadarai gaban y'ar ki,kina jina ko Su'ada? "

Gyad'a kai Su'ada tai da fad'in "Eh Baba ina ji."

Yace "To masha Allah, Allah yai muku albarka ya baki lafiyar shayarwa,kai kuma ya baka arzik'in kare duk buk'atun iyalinka."

Su Innaro ne su ke amsawa da Amin amin.

Sosai Mama taji Dattijon ya k'ara birgeta,ta k'ara tabbatarwa y'arta tayi aure gidan tarbiyar.

***********
Ba jimawa Mama ta koma gida aka bar Innaro me zaman dab'aro.

Sakeena kam yau ba kyashi ta zage taiwa Su'ada hidima,kama daga ruwan wankanta zuwa na Baby, gyaran gida duk ita tayi.

Sai da Zakiyya tazo ne ma ta amsheta,da yamma kuma su Jidda su ka zo,su sukai girkin dare su ka k'ara gyara gidan.Khaleelee ya takura sai da aka bar Husna,me bin Jiddda, yace ta zauna sabida girki kar aikin yayiwa Innaro yawa ga girma.

*********
Kowa yazo barka sai ya jinjina kamar da Baby ke yi da mamanta,in ka d'auke tsayi da yarinyar ta debo na Khaleelee don doguwa ce sosai masha Allah, to babu abunda ya rabata da uwarta.

Ranar kwana biyu da haihuwa Su'ada ta shiga bedroom kaiwa Khaleelee wayarsa data gama kira da ita,tana mik'a mishi ya jawota jikinsa yana fad'in "Sai wani baya baya ake dani me nayi wai?"

Janyewa take son yi daga jikinsa yak'i,ta d'an turo baki tana fad'in"Ba wani baya baya da ake da kai fa,kawai jego ne."

Kamo fuskarta yai yana k'ok'ari kissing d'in ta tai baya da sauri tana zare ido, Y'ar dariya yai yana gyara tsaiwarta a jikinsa yace "Kin min wayo pretty, kowa sai ya gano kamar da Babyna ke yi dake,kin cini wasa a wancan karon amma a gaba zan bud'e wuta,nan da wata goma zaki bani me kama dani."

Zaro ido ta k'ara yi,tana dafe k'irji tace "Don Allah ka rufamin asiri,wane wata goma kamar tattabara,sai na huta fa,shekara uku ko hud'u."

Hararanta yai cikin wasa yace "Shekara uku lokacin kin haifi uku."

Da k'arfinta ta tureshi ta fice da sauri.
Dariya yasa ya koma gado ya kwanta.

************
Aunty Bilkisu wato babbar Yayar su Su'ada dake aure a katsina tun kwana d'aya da haihuwa tazo, daman kullum jiran sak'on haihuwa take.tun zuwanta kullum gidan take yini sai yamma ta koma gidansu ta kwana.

Shirye shiryen suna ake sosai,daga b'angaran gidansu Su'ada da kuma b'angaran Khaleelee.

Ranar kwana biyar da haihuwa aka kawo kayan barka daga gidansu Su'ada, kaya ne na alfarma Abbansu sa Mama sukai rawar gani wajan had'awa,don tunda Jidda ta turawa Abban su pic d'in Baby ya gani yace wannan ta dabance don dashi take kama bama da Su'ada ba,don haka ya sakarwa Mommy kud'i sosai tai siyayya.kansa kayan Babyn abun kallo ne,riguna zafafa masu d'aukar hankali da tsada, haka ma akwatin Su'ada damkam da kaya,sannu Khaleelee shaddarsa shima yadi biyar kusa biyu da hula,sai dank'areriyar atamfa da Mama ta aikowa Sakeena sabida hidimar da tai a asibiti.

Ranar kam Sakeena ta k'ara tabbatar da Iyayen Su'ada masu zuciya ne,don komai a wadace su ke mata shi.

Washe gari ma kayan da Khaleelee ya had'a aka fito dashi,shima yayi k'ok'ari matsayinsa na me k'aramin k'arfi,yaiwa Baby riguna guda goma,mamanta kayan fitar suna ma guda bakwai,kuma kaya masu tsada.

Ana gobe suna fa gidan yai damk'an da alumma,dangin su Su'ada na darki duk sunzo wai haka ma da yawa suna gidan mama,way'anda zasu yi aiki kad'ai suka zo kwana anan.

********Ranar suna yarinya taci sunan kakarta mahaifiyar Khaleelee wato Aminatu, anma za'a mata lak'abi da (Nusrat)

Sosai fa taron suna yayi taro,gida tamkar ana biki ba suna ba,kasancewar Su'ada y'ar dangi kuma me mutane da yawa yasa gidan ba masakar tsinke,k'arshe dai Khaleelee Canopy yayi ranting da kujeru aka sa k'ofar gida duk jama'a su ka zauna,a sannan aka samu sukuni cikin gidan.

Su'ada a b'angaranta bata da abun siya da kud'inta komai n mata mijinta ya tsare mata komai haka iyayenta,don da tacewa ma Khaleelee tana son badawa ai mata jaka da calanda na Baby yace ya bayar ayi jaka,sannan Jabeer yayi kalanda stickers.daga haka bata kara magana tana ta tunanin me zatai itama da kud'in dake cikin account d'inta, don albashinta ba wani abun take dashi ba sai abunda ba'a rasa ba.bayan tai dogon nazari ta yanke hukuncin siyawa yarinyar d'an kunnan gold,don haka tasa a ranta da an gama hidimar suna zata siya mata.

Taro yayi kyau kowa sai fad'i yake masha Allah, ko a b'angaran abincin suna da lemuka kowa ya shaida Khaleelee gwarzon namiji ne,ga ragunansa manya guda biyu daya yanka na hakika.

******da daddare taro ya watse ya rage mutum uku a gun Su'ada, Innaro da Aunty Bilkisu sai k'anwar mamansu Aunty iyami.

Ruwa me zafi aka had'awa Su'ada tai wanka sannan a kaiwa Baby Nusrat,ta fito a wankan tana zaune bakin gado tana shafa turare a jikinta kasancewar tsananin zafin da ake yasa ko mai bata shafa ba,ko wankan ma badan jikin jego ba ba zata iya sa ruwan zafi a jikinta ba.su Aunty Bilkisu nata gyarana gida da wanke tsakar gidan da akai kaca kaca dashi,ita d'aya ce a d'akin ya shigo da sallama,kallonsa tai tana mirmishi don sosai taga kyansa cikin idonta.yana sanye da Sabuwar shaddarsa gak light blue an mata aiki da dark blue d'in zare,haka hular kansa da takalmi duk kalar aikin rigar.ganin kallon da take masa me nuna tsantsar birgentan da yai yasa yaja ya tsaya jikin k'ofar shima yana kallonta fuskarsa wadace da mirmishin.

Kauda kai gefe tai tana d'an dariya tace "Wannan kallon kamar za'a siyeni ."

Lumshe ido yai ya bud'e yana y'ar dariyar shima ya bata amsa da "Hhhmmmm siya kuma na nawa? An siya an biya har an jujjuya an sami ribar farko gata a kwance."

Mik'ewa tai tana saka doguwar rigar data d'auko mara nauyi kuma bata da Babban hannu,yana tsaye yana kallo ta gama sawa sannan ya k'araso cikin d'akin sosai yana k'arasawa ga bakin gadon yanawa Nusrat wasa da wak'a. "Mamana tafi ta kowa, Mamana sarkin kuka,amma kukan ma da dalili,Mamana y'ar albarka,Mamana Ummyn Abba."

Juyowa tai da mamaki tana kallonasa kafin tace "yaushe ka fara wak'a?"

Dariya yai bayan ya zauna sosai ya d'auki Nusrat Sannan yace "Tun ranar da na zama Abba."

Jijjiga kai tai da d'an mirmishi tace "Ba ruwana, Allah yasa wani ya jika kanaiwa y'ar fari wak'a."

Sosai maganar ta bashi dariya,sai da yai mai isarsa sannan yace"Ke in bakiyi ni bani waje,ko a gaban Baba zan mata wak'a da rawa."

Zaro ido tai da fad'in "La' ni kam ba ruwana Wallahi, ni ka fita ma kar aga kazo ka dad'e a d'akin ayi wani tunanin."

Bai kara tanka mata ba ya ci gaba da yiwa yarinyarsa wasa harda kwanciya kan gadon, ita kam Su'ada data gaji da magiyar ya fita yak'i sai ra fito ta bar mai d'akin. A falo a tadda Aunty Bulkisu na ta sharewa su kam su Innaro na tsakar gida.tace Aunty sannunku da aiki,da kun huta ma da safe ai kwayi."

"A'a k'ara mu rage yanzu, kuma shara ma ai ba'a barta ta kwana ba,kina ganin fa yanda duk wajan ya jagale,ki koma d'aki don moping zan yi."

"To sannunku da aiki" ta fad'a tana komawa d'akin.

Jan stool tai ta zauna bakin gadon tana kallonsa na d'an lokaci sannan ta lumshe ido. Shima kallontan yai ya kauda kai da fad'in "da ganin Wannan kallon na kewa ta ne."

Turo baki tai kamar zatai kuka tace "Ni bance ba,gaskiya ka bari,kawai don na kalleka sai ya zama abun fassara."

Ajiye Nusrat yai ya taso zuwa Inda take,d'an rank'wafowa yai saitin fuskarta yana magana can k'asa "Ko baki fad'a ba yarinya na gani cikin idonki, kuma duk abunda ido ya nuna gaskiya ne."

Yana fad'i ya mik'ar da ita tsaye tare da rungumeta,maimakon ta tureshi yanda take mai tunda akai haihuwar sai yaga sab'anin haka,don lif tai a k'irjinsa tana sauke tagwagen ajiyar zuciya.

Shafa bayanta ya ke a hankali yana jin wani bala'in bukatarta na taso mai,idonsa a lumshe yake ta sansana gashin kanta dayasha gyara yana bada k'amshi.

Sun dad'e a haka,maganganun su Innaro da sukaji a falon yasa su sakin juna a d'an hanzarce,Innaro da bata San Khaleelee yana wannan d'akin ba don tasan bai shigowa yana can dayan d'akin, ta turo k'ofa da sallama,ganin Khaleelee tsaye Su'ada zaune kan stool a gabansa yasa da sauri ta juya.

Shima da saurin ya d'auki Nusrat ya biyo bayanta,a d'an kunyace yace "Inna sannunku,ya gajiyar taro data aiki?.

Cikin kulawa ta amsa mai da " Alhamdulillah. "

Dayan d'akin da ya zama makwancinsa yanzu ya shige,bayan ya ajiye Babyn a gado ya cire kayan jikinsa tare da kwanciya ya d'ora ta a cikinsa yana d'an shafa bayanta don bacci take.

A d'aki kam cikin hikima Innaro ke k'ara jawa Su'ada kunne kan kame jikinta daga Miji,a dabara take ta bata labarin rayuwar su ta da,yanda mace ke gujewa miji a duk sanda take jego har sai tai arba'in ko dama da haka ma.duk da bata bayyana zancen akan Su'adan ba amma ita tasan da ita take,sabida yanayin data riskesu d'azu duk wanda ya gansu yasan da magana.

********Washe garin suna y'an uwan Su'ada suka gyara nama suka soyeshi,bayan sun gama suka rarraba shi kamar yanda akeyi,kowa dake da hakki aka fidda mishi rabonsa.
A ranar su Aunty Bilkisu duk suka tafi,gida ya koma daga Su'ada sai Innaro.

********Jego me tsafta Su'ada keyi da Babyn ta,ba zaka taba shigowa wajanta ka sami wani abu na k'i ba,kullum cikin ado take da k'amshi, haka ma Nusrat, Baby kam ta zama y'ar raino,data dawo makaranta take yada zango taita fama da goyo.

Bayan Su'ada tai shawara da Khaleelee ta had'a kud'ad'an data samu na barka dubu 700 tacewa mai tana son siyawa Nusrat d'an kunne,bai k'i ta tata ba amma yace tasa dubu hamsin a account d'inta, dubu ashirin kuma tasai mata k'arami,a gaba in ta k'ara girma sai tasai mata babba. ba gaddama ta yarda da shawararsa,ta aikawa mama kud'in aka siyowa Nusrat d'an k'aramin d'an kunne.

*******A yanzu kam Sakeena sai dai ace Masha Allah, don tunda akai haihuwar nan bata nuna wani halinta ba,ta nutsu tai komai kamar yanda ya kamata,duk da dai abubuwa da yawa a lokacin sun sosa ranta,yanda akai komai kamar sunan wata y'ar attajirai.
Su'ada a ranta take fad'in Ashe duk mugun halin FACALA tana da rana,ita kam taga ranar FACALA a lokacin da haihuwa tazo mata,don Sakeena ta taimaka mata sosai,har addu'a Su'ada keyi Allah yasa Sakeena ta gyara halinta kenan, zasu zauna kamar yanda sauran facaloli je zama da junansu.

*Taku ce*
*Y'ar mutan Ja'oji*🙋
[2/24, 12:03 AM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭

*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*

👩🏻‍💻👨🏻‍💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.