Complete Hausa Novels

Facala Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Facala Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 24 of 26

_*page*_ *47-48*

Kula sosai Mama take bawa Su'ada a zaman jegonta,sati guda da suna Abbansu ya tafi legos, kwana uku da tafiyarsa ya turowa Khaleelee dubu d'ari wai ya k'arasa shirya shagonsa.lokacin da wannan sak'on yazo ga Khaleelee ji yai ya rasa ma da wane baki zai yi godiya, sabida alkairan Su'ada da iyayenta gareshi sun yi yawa,shi ya kamata yayi dawainiya da iyayen matarsa,amma gashi sune suka bashi ya kuma suke dawainiya dashi, lalle samun surukai irin wannan sai an tona.

Kiran Abban yayi a waya yana mai godiya, Abba kam ya kamashi da fad'a kan cewa shi uba ne a gareshi, duk abunda yai masa bai buk'atar godiyarsa,don haka ya daina godiya a tsakaninsu.

Da Khaleelee ya fad'awa Baba shima godiyar yai tayi,yanawa iyayen Su'ada addu'ar alkairi.

Da sallar isha ma da suka had'u da yaya Muktar a masallaci yakw fad'a mishi bayan keke ga dubu D'ari Abban Su'ada ya k'ara mai,godiya shima yayi,har suka shigo gida suna maganar, Sakeena dake tsakar gida tana d'aura alwala tana jin me suke tattaunawa,jin abunda Abban Su'ada ya yiwa Khaleelee ya sa jikinta mutuwa murus,,ta san ita kam in mijinta ne ya samu wannan jarabtar Babanta bashi da ko dubu goman da zai iya tallafa mai,tunda gobarar nan ta afku ko yaushe cikin hidima yake da su, ga keken daya siya mishi industrer iyayen dubunnai ya fidda ya siya,ga hidimar suna da yai musu, sannan ga wannan kud'i ya bashi,eh Lalle Khaleelee auran jari kawai yayi.

Abunda tai ta maimaitawa a zuciyarta kenan jin wani d'acin Bak'in ciki na tasowa daga mak'ogaranta zuwa harshenta.

________Cikin ikon Allah Khaleelee ya shirya shagon sa kamar da,sai dai har zuwa yanzu kekuna basu k'aru ba,daga Wanda Su'ada ta bashi ya siya,sai Wanda Abbanta ya siya mai,sai kuma wata uwar d'akin sa ta bashi bashin keken surfani guda d'aya duk wata zai rink'a biya. Ai kuwa sai ga shago yayi ras.

************
Lokacin da Su'ada tai ar'bain ta rok'i Khaleelee ya barta taje garin Abban su wato Darki,da farko yaso yak'i yarda Amma tai tai mishi magiya, ba dan yaso ba ya barta.

Tare suka tafi da dukkan k'annanta,kwana biyu su kai suka dawo.
Washe garin dawowarta Ta koma gidan mijinta.

___________
Haka rayuwa taci gaba da garawa yau da dad'i gobe babu,fannin miji kam sai godiyar Allah,don Su'ada kullum cikin godewa Allah take,bata da wata damuwa tsakaninta da mijinta,ko yaushe cikin kyautatawa juna suke.
Fannin FACALA kuwa me hali bai fasa halinsa sai dai a samu sassauci wata rana,to haka Su'ada ke k'ara hak'uri kullum ga Sakeena,don bata fasa halinta na kishi da hassada.

*BAYAN Y'AN WATANNI*

*********
Wata ranar jumma'a Khairiyya tazo gidan Su'ada ta taho da Nusrat don har yanzu ba'a dawo da ita ba.

Kwalliyar kawai da akaiwa yarinyar abun kallo ce,ga tsananin kyawu da kullum take k'arawa, harma wasu na cewa duk kamarta da mamanta tafi maman nata kyau.
Masha Allah, dake kuma ta d'auko tsayin mahaifinta sai ake ganin saurin girmanta,duka lokacin shekarunta biyu,amma zaka ce tayi uku ko ma tafi haka,sanyin halinta sak na mahaifinta,duk da Su'ada ma akwai hak'uri to gado biyu tayi, zaka dad'e baka ji hayaniyar yarinyar ba,balle kaji kukanta,sam bata da rikici irin na yara da rigima,sosai zaka tabbatar da hak'urinta.

An mata kwalliya cikin riga da wando y'an kanti,wandon Jean's bak'i,sai wata riga me jikin santsi kalar ruwan madara me haske sosai,duka gaban rigar an sa stones me d'aukan ido,k'afar ta sanye da wani bak'in d'an ubansu takalmi sau ciki,kallo d'aya za kaiwa takalmin kasan da iyayen kud'i aka siye shi,kanta kuwa wani k'ananun kitso ne da aka sawa bit tako ina, ga wasu k'ananun ribbons an jera, dake Allah ya mata baiwar gashi me cika da tsayi tamkar mamanta,kai da kaga yarinyar kaga jinin fulanin asali.kuma dake akwai kula sosai da gata tare da ita sai kaganta tamkar d'iyar turawa.

A tsakar gida Kairiyya ta iske Sakeena na girki, bayan ta dire Nusrat da ga hannun ta zuwa k'asa ta gaida Sakeena cikin girmamawa, itama cikin fara'a ta amsa amma duk hankalinta na ga Nusrat,kallon yarinyar take tamkar bata santa ba,cikin d'an yak'e tace "A'a Nusrat y'an mata,yau an kawo mana ziyara kenan, zo in ga kwalliyar taki."

Tsayawa yarinyar tai tana mata kallon rashin sani,amma dake bata da k'iwa sai ta k'arasa gareta,Sakeena ba tai la'akari da bak'in gawayi da maikon dake hannunta ba ta Kai mata cacima tana d'orata a cinya,d'an wasa tai mata sannan ta sauketa ganin kairiyya ta ja ta tsaya tana jiran ta direta su k'arasa.

Su'ada da ta jiyo muryar khairiyya tun shigowarta amma taji shiru bata shigo ba,a ranta take fad'in'To Khairiyya da bata shiri da Maman Abba me ya tsaida ta a gunta'
Bata gama zancen zucin ba taji sallamarta ta shigo,da fara'a ta tare ta amma sai ta ga khairiyan ta turo baki gaba,alamar ranta a b'ace yake,dubanta tai tana fad'in "A'a ke kuma ke da wa naga kina kunkuni."

Wulla jakarta tai kan kujera gami da zama tana yatsina fuska tace "Kai Aunty Su'ada Wallahi matar nan ba ta da nutsuwa,fisabililla kallin abunda tai min." Ta k'arasa maganar tana nunawa mata gefe gefen rigar Nusrat.cikin rashin fahimta Su'ada tace "Meya faru ne ban gane ba,ke da waye?"

K'ara yatsina fuska tai cikin b'acin rai tace "Wannan Maman Abban mana,dubi yanda ta d'aukar min yarinya hannunta duk bak'i da maik'o, sabida k'azanta,in tasan hannunta bai da kyau ai sai ta hak'ura da d'aukan ta ba dole a Kai mata ba."

Dariya Su'ada tai tana rik'e baki tace"Kai!lalle ma,to don ta miki kara ta d'auke ta sai ya zama abun haushi. "

"To ni nace ta d'auke ta ne,jifa yanda ta b'ata mata riga,mutttttssss."
Ta k'arasa maganar d'auke da tsakin takaici.
Ita dai Su'ada dariya abun ya bata sosai,ko dake daman tasan Khairiyya sam ba hak'uri gareta ba,amma anan kam bata ga abun mita ba,kuma tasan sarai da Sakeena bata d'auki yarinyar ba hakan ma sai tai k'orafi tace ko kula Y'ar ba tai ba.

Kukan muklees da Su'ada ta jiyo a d'aki yasa ta shige da sauri,tana fad'in "Yauwa Babana sarkin kuka an farka da kukan kenan."

Khairiyya dai cirewa Nusrat kayan tai gaba d'aya, ta barta daga ita sai base da d'an pant,dake daman zafi ake sosai a lokacin.

Bayan Su'ada ta d'auko muklees ta zauna kusa da Khairiyyan tana fad'in "Uwar masifa ko gaisawa ba muyi ba fa."

Y'ar dariya Khairiyyan tai kafin ta gaida ta,tana tsokanar Muklees "Su Abbanmu sarkin kuka sarkin tsotso."

Harararta Su'ada tai da fad'in"Abban ake cewa sarkin kuka ko?"

Cikin dariya Khairiyya tace "To ai ba k'arya nai ba,jifa daga farkawa daga bacci ya cika gari da kuka,yasin yaron nan badan sunan Abbanmu gareshi ba bazan had'a jam'iyya dashi ba."

"To karki had'a mana,ni ina had'e da Abuna,kin fi son ki ganshi salo salo kamar y'arku,ah Allah ya kiyaye, Abbana namijin duniya ne me k'arfin sojoji."

Khairiyya na dariya ta d'ora Nusrat akan cinyarta tana fad'in "Ai Wallahi yarinyata bata da makusa, d'abiun ta kalar na mata,jan aji da nutsuwa ne yasa bata hayaniya tun tana jinjira, komai nata cikin class take,amma wannan Abban ai kalar garada ne."
Ta kai k'arshen zancen da dariya sosai.

Yatsina Fuska Su'ada tai tana kallon kayan da aka cirewa Nusrat d'in tace "Wai don wulak'ancinku kawai don ta d'an goga mata maik'o shine kuka cire kayan? Yasin baki da kara fa."

D'age gira Khairiyya tai da watsa hannu alamar ko a jikinta tace "To akan me zan barta da kaya me datti a jiki? Ah haba wai baki da labarin y'ata me tsada ce ne?"

Mik'ewa Su'ada tai tana dire muklees a kan cafet,ta wuce kitchen, don bata dad'e da dawowa daga makaranta ba,don ma yara exam's suke da wuri suke tashi

Girkin data d'ora taje ta duba,sannan ta dawo suka d'ora hira.
Sallamar Baby ce tasa su tsayawa da hirar suna amsa mata,da fara'arta ta k'araso tana fad'in "Yanzun nan ina shigowa Islam tace min Nusrat tazo."

Tsugunnawa tai tana kamo hannun yarinyar,tana gaida Khairiyya, sannan ta dauketa zasu fita Muklees yasa kuka yana mik'awa Babyn hannu.

Tafa hannu Su'ada tai da fad'in "Eh lalle Baby,sabida kinga Nusrat shine zaki wulak'anta min uba,to ai zata tafi ta barmu da ke ne."

Dariya Babyn tai tana jutowa ta d'auki muklees d'in a d'aya hannunta.

bayan Sun fita Khairiyya tace "Allah sarki Baby,Wallahi sam ba tai halin Uwarta ba,yarinyar na birgeni."

Gyad'a kai Su'ada tai tace "Ita kam halin Babanta tai,ba ruwanta,rayuwar ta komai da sauk'i take yinsa."

Daga wannan hirar suka koma hirar bikin Jiddah, Wanda ya rage wata biyu.

******
Baby dai na can d'akinsu tana ta fama da su Muklees, musamman Nusrat da take ta hannun damanta,sai ina naka sa ina naka aje take da yarinyar.

*********K'arfe daya da rabi Khaleelee ya dawo gida don yin shirin sallar jummaa,dake su masallacin murtala suke bi,kuma sai k'arfe biyu ake salla a masallacin.

A tsakar gida ya tarda Baby ta na goye da Muklees, tana bawa Nusrat abinci a baki,cikin mirmishi yake amsa sannu da zuwan da yaran ke masa.
Rik'o hannun Nusrat d'in ya yi yana fad'in "Mamana yau an waiwayomu kenan, ke da wa kuka zo?"

Cikin gwarancinta tace "Aunty Khairiyya ne."

Gyad'a kai ya yi yana mik'awa Islam hannu su ka tafa,yace "Maman mama me aka ci ne baki ke maik'o
"

Girgiza kai tai cikin dariya tace "Abinci muka ci fa me dad'i."

Yana y'ar dariya ya wuce ciki.

A falo ya same su suna cin abunci,Khairiyya ta gaisheshi ya amsa yana tsokanarta don Bayan Khaleelee cikin y'an gidan yafi wasa da Khairiyya.

Kad'an ya d'an zauna yana tambayarta gida dasu mama, sannan ya wuce d'aki.
Bin bayansa Su'ada tai zuwa d'akin, yana k'ok'arin rage kayan jikinsa yace "Madam a had'a min ruwa,ji nake kamar ban tab'a wanka ba,gaskiya yau ana zafi sosai."

Taimaka mishi tai ya cire kayan jikinsa zuwa jallabiya.sannu ta fito ta had'a mishi ruwan wanka.

Sai wajan k'arfe uku Khaleelee ya dawo gidan daga masallaci.

Khairiyya na d'aya d'aki tana bacci, yayin da Su'ada ke falo tana marking exam's d'in d'alibai, Muklees ma baccin yake sai Nusrat a gefenta tana mata hirarsu ta yara.

Zama ya yi kan kujera yana amsa sannu da zuwan Su'ada, idonsa naga Nusrat,sosai yake kallon yarinyar yana ganin kullum k'ara girma take,dukda yana wata guda ko giye bai ganta ba,amma duk sanda zai ganta sai yaga tai tsayi.

Yana wannan tunanin har Su'ada ta kawo mishi abinci.bayan ya sauko k'asa inda zai ci abincin yace "Mamana zo mu ci abincin ."

Girgiza Kai tai alamun ta k'oshi, mirmishi kan fuskarsa yace " Su'ada yarinyar nan ta kusa kamoki a tsayi fa."

Dariya Su'ada tai kafin tace "Tunda tai gadon tsayi ai in ma ta fini tsayin ba damuwa bace."

D'agata yai cas ya d'ora ta kan cinyarsa,wani k'aunar yarinyar yake ji na ratsa b'argo da jijiyarsa,tabbas kara da kawaici ne kawai ba za su barshi yace a dawo mai da y'arsa gida ba.ya San yanda ake kula da ita a can ko gidan ma sai haka,to amma fa shima ya na buk'atarta kusa da shi.

Wasa take tayi da gaban rigarsa ,yayin da idanuwansa ke tsaye a kanta,mirmishi yak'i barin fuskarsa,ko yaushe in yana tare da yarinyar sai ya riski kansa cikin farin ciki.

Su'ada idanuwanta a kansa ta san sarai tunanin da yake,ko yaushe bakinsa kan maganar Nusrat yake,tasan kara yake mata kawai,don kafin ta haihu yasha fad'a mata shi fa a rayuwa bai tab'a iya yin kyautar d'a, yanda yake da son y'ay'a ba zai rink'a barin d'ansa yayi nisa da shi ba ko na sati guda.to amma ga shi yau tsawon shekara guda tun daga yaye iyayen ta sun rik'e Nusrat,kuma ko ita akan kanta tana jin k'aunar kasancewa da yarinyar tare da ita,amma ba zata iya cewa zata karb'eta ba in ba su suka dawo da ita ba.

*******Ana kiran Sallar la'asar Khaleelee ya mik'e da Nusrat a jikinsa yana fad'in "Mamana bari naje salla."

Mak'ale kafad'a ta yi tana k'ara shegewa jikinsa.
Da yai zaton wasa ne abun,amma da ya fara k'ok'arin sauketa k'asa sai ta k'ara rik'eshi cikin b'ata fuska tace"Zanje fa."

Komawa ya yi ya zauna a kujera yana y'ar dariya yace"Zauna, in naje masallaci na dawo zan d'aukeki muje yawo."

Kuka ta fara yi sosai,abunda ya sa Khairiyya fitowa daga d'aki da sauri don cikin bacci ta jiyo kukanta.
"Me ya faru take wannan kukan?"

Su'ada dariya tace "wai masallaci zata bishi, kullum kuyi ta cewa y'ar Ku bata rigima to gashi tayi mun gani."

B'ata fuska Khairiyya tai kafin tace "wallahi ba ta rigima,in kinji Ku kanta da dalili,shi yasa da naji kukan na tashi da sauri."

Jin an fara tada sallar ya sa da sauri Khaleelee ya mik'e da ajiye ta kan kujera ya shige ban d'aki don d'aura alwala.

Sosai fa Nusrat take kuka,ita dole zata bi Abbanta.
Khairiyya ta d'auketa tana rarrashinta,ita kuwa Su'ada tashi tai don yin salla ta barsu wajan.

Har khaleelee ya dawo a salla tana kuka,hakan ya sa yace Khairiyya tasa mata kaya yaje da ita shagonsa,in ta fito sai ta tsaya ta karb'eta.

Jakarta ta bud'e ta d'auko mata wata y'ar doguwar riga Mara hannu.
Nan da nan tai mata y'ar kwalliya ta shafeta da farar powder sabida zafin da ake,sannan ta canja mata Pampers.

Yana d'aukan ta ta fara dariyar murna,shima dariyar ya yi,yana fad'in "Yau dai Mamana ta zama Muklees sarkin rigima."

Su'ada tace"Ah daman da kukanta,kawai tana dad'ewa ne batai ba,ba Muklees ne kad'ai akoke ba."

Fita yayi sab'e da ita yana dariya yace "Khairiyya sai kin fito."
Ta amsa mishi da to.

A tsakar gida Sakeena taga Khaleelee d'auke da Nusrat ta kalleta da sabuwar kwalliyar sa akai mata,ta had'iye wani yawu kafin tace "Nusrat kukan me take ne? Naji ihunta ina salla."

Khaleelee yana sa kai zai fita yace"Rigima take wai in fita da ita."

Daga haka ya fice.
Ita kuma ta tab'e baki cikin ranta take cewa 'To in banda ma abu yarinya da gidan ubanta amma an barta gidan kakanni,sabida son abun duniya da kwad'ayi kawai.'

Ba Wanda ya jita balle ya bata amsa,ita kad'ai take ta nunk'ufurcinta kamar y'arta.

***
Shi kuwa Khaleelee tunda yaje da Nusrat shago yaran shagon keta fad'in "kai masha Allah, wai haka ta girma."

Sosai ta ware dashi a shagon tana ta mai gwaranci.

Wani kanti Dan gefen shagonsu ya shiga yayi mata siyaugar biscuit da alawowi.ta sha kad'an bacci ya d'auketa. Ya kwantar da ita a cinyarsa yana d'an pitting bayanta.

Sai wajan k'arfe shida da mintina Khairiyya ra tsaya a adaidaita tanaiwa Khaleelee magana.

Tasowa yayi ya kawo mata Nusrat d'in yana fad'in "Khairi Wannan yarinyar taki yau ta had'a ni da aiki,kinga da zuwanmu fa tai bacci."

Dariya Khairiyya tai bayan ta gyara mata zama a jikinta tace"Um a bani abata,duk kunsa tai kuka da yawa daga zuwanmu gidanku."

Dariya yai lokacin da yake bata ledar da yayiwa Nusrat d'in siyayya,sannan ya d'aga mata hannu yana cewa ta gaida mama.

*****
Bayan sallar magriba a gudansu Su'ada, duk suna zaune falo don cin abincin dare,Mama ta dubi Khairiyya tana cewa "Wai ya akai Nuarat tai miki bacci a hanya ne yau?"

Gyad'a kai Khairiyya tai tana cewa"Kuka ta sha,shine kuma sai tai bacci."

"Wane irin kuka kuma?abunda ba cinikinta ba."
Cewar mama.

Nan Khairiyya ta basu labarin sanadin kukan.

Mama tace "Ai da kin barta ta kwana biyu,ko zuwa jibi sai a d'auko ta."

Zare ido Khairiyya tai da fad'in "Tab' d'in, haka kawai da ga nan suce sun rik'e ta."

Da mamaki maman ke kallonta tace "Ah to in sun raketa ma ba y'ar su bace, ko daman kunyi da su sun ce miki kyauta su ka bamu?"

Turo baki Khairiyya tai,don zancen bai mata ba,Jiddah dai kam sai dariya take,mamy me bin Khairiyya tace "A'a wallahi mama,ba mai d'auke mana ita,sai da ta shak'u da mu,muma muka shak'u da ita,sannan sai su d'auke ta,tab' d'in, ai Wallahi nasan Abba ma ba zai yarda ba."

Sosai mama ke mamakin yaran nata, cikin dariya tace "To shi Abban y'ar sa ce da zaki ce ba zai yarda ba,shi ba ga nashi nan ba birjik,wa ya tab'a baiwa ko aro bare kyauta,ko ni lokacin da Ku ke k'anan haka kowa ke son in bashi ko d'aya cikinku amma Abban naku ya yi k'irmishishi ya hana,duk da yawanku kuwa.
To Wallahi in ma zaku cire rai ga y'ar aro to ku cire,don na tabba ko yanzu ko nan gaba za su k'arb'i abarsu.kuma tunda ta nuna tana son zama gun mahaifinta daga yanzu duk jumma'a za'a rink'a kaita,lahadi sai a karb'ota,a haka ma za tafi sabawa."

*Taku ce*
*Y'ar mutan Ja'oji*🙋
[2/24, 10:54 AM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭

*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*

👩🏻‍💻👨🏻‍💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.