Facala Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Facala Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 18 of 26
_*page*_ *35-36*
Jidda kam tunda taji maganganun da Sakeena ke tayi duk akan abincinta ranta yai matu'kar baci,kallon Khaleelee tai da ke zaune dafe da kai,jin tsantsar tsanar Sakeena yake a cikin ransa,bai tunanin samun matsala ga Sakeena ba a rayuwa,yai tunanin matsayin da su ka d'auketa na uwa ko babbar yaya zai sa taci gaba da rungumarsu da kauda dukkan damuwarsu,amma sai gashi Sakeena ta zame mai matsala a rayuwar auransa.
Juyawa Jidda tau da sauri cikin d'akin ta jawo wayarta ta danna kiran mamansu, bugu d'aya Maman ta d'auka tana tambayarta ya jikin Su'ada, a gaggauce ta amsa sannan ta shiga fad'awa mama halin da ake ciki,sannan ta d'ora da fad'in "Mama me zai hana kiyiwa Yaya Khaleelee magana Kawai ya bari mu taho gida da Aunty Su'ada, halin da take ciki ba zata tab'a hak'ura da abincin Sakeena ba,ita kuma ba zata gaji da yi mata wulak'anci ba,tunda gashi akan abincin yanzu tana ta fad'a da mijinta,amma in muka dawo gida kinga zata hak'ura tunda tasan ba samu za tai ba,in Allah yasa hankalinta ya koma ga son wani abu sai ta dawo d'akin ta ko?"
Cikin gamsuwa da batun na Jidda mama ta kashe wayar,sannan ta kira number d'in Khaleelee, bayan sun gaisa cikin girmamawa tace "Ibrahim daman alfarma zan rok'a a gunka."
Cikin tsananin jin kunya da mamaki Khaleelee yace "Mama alfarma kuma? ai ke uwa ce kinfi 'karfin neman alfarma sai dai ki bada umarni,fad'i ko mene mama insha Allah za'a miki."
Cikin jin dad'in furucinsa mama tace "To Ibrahim daman don Allah so nake in ba takura ka dawo da Su'ada gida zuwa lokacin da Allah zai kawo mata sauk'i duk da irin Wannan lalura sai an rabu lafiya ke samuwa,amma yanda Jidda ke fad'a min halin da take ciki nake ganin in ta dawo kusa dani zan san irin taimakon da zan rink'a bata."
Shiru Khaleelee yai don bai zaton jin wannan daga mamanba,amma ba yanda zai yi,ba zai bijirewa umarnin mama ba sannan a halin ma da suke ciki yanzu k'ara tai nesa da gidan,don haka ya k'ara k'asa da murya yace "Ba komai Mama kin fi k'arfin komai ai, balle wannan. insha Allah da safe ko zan kawo ta."
Da fara'a sosai mama tace "To na gode,Allah yai maka albarka ya baku masu yi muku biyayya kuma."
Cike da kunya yake amsa mata har su kai sallama.
Kiran Jidda yai bayan ta fito yace "Jidda mun yi waya da mama,insha Allah da safe zaku koma gida har zuwa lokacin da Allah zai bawa Su'ada lafiya,yanzu ki had'a mata duk kayan da kike ganin zata buk'ata kema ki had'a naki,da safe zaku tafi."
Gyad'a kai tare da fad'in "Tom Yaya Allah, ya kaimu, bari na had'a kayan."
Ta shige bedroom d'in cikin ranta tana murna shawarar ta ta karb'u.
Tun sallar asuba Jidda bata koma ba,ta shiga kitchen ta shirya musu abun Karin kumallo,sannan ta d'ora girkin rana, ba dan wai su zasu cu ba,a'a sabida Baba da Jabeer,wajan k'arfe takwas ta kammala girkin,wanke wanke tai tare da gyara ko ina,bayan duk ta kammala sa gyaran gidan sai ta shiga wanka.tana fitowa a lokacin Su'ada ta tashi,itama ruwan wankan ta had'a mata tai,tana fitowa tace "Jidda d'umamamin guntun shinkafar nan ta jiya.kallon ta Jidda tai tana y'ar dariya tace " Na san zaki nema don haka tuni na d'umama,shirya ki fito kici."
Girgiza kai tai tana zama kan kujerar dake k'ofar toilet d'in tace "a'a kawo min yanzu na ci,da k'yar ma nai wankan nan don yunwa nake ji sosai.
Ita kam Jidda bayan ta kawo mata shinkafar wucewa d'aki tai don ta k'arasa shiryawa.
Nauyin bacci yau Khaleelee yai,don haka har Su'ada ta gama cin abincin ta koma d'aki sannan ta tadashi.
cikin mayen bacci ya ke kallon idanuwanta,itama shi d'in take kallo cikin d'an mirmishi tace " Ka tashi ka shirya karka makara a shago tara ta wuce tuni fa ."
Mik'a yai yana salati yace "Um nama manta,Wallahi yau dogon baccin na samu sosai."
Tashi yai ya zauna yana duba agogo yace "Pretty jiya fa mun yi waya da mama,zaki koma gida sabida jikin ki,in kin d'an k'ara warwarewa sai ki dawo."
Da murna ya kalleshi tace "Wayyo amma naji dad'i Wallahi, k'arfe nawa zamu tafi?"
Mik'ewa yai yana fad'in "Bari dai nai wanka tukun ."
Bayan Jidda da Khaleelee sun gama karyawa ya fita wajan Baba ya sanar dashi Su'ada zata koma gida.bai ce komai ba sai fatan samun lafiya da yayi mata.
Wajan sha d'aya su ka tsaya da keke napep a k'ofar gidansu Su'ada, shi da Jidda ne su ka d'auki jakan kayan nasu zuwa ciki.
Bai samu mama a gida ba tana wajan aiki don haka bai jima ba yai musu sallama ya tafi.
***********
K'arfe biyu ma rana mama ta dawo,cikin fara'a take amsa gaisuwar Su'ada tana fad'in " Maman biyu sannunki ya jikin ?"
Rufe ido Su'ada tai cikin jin kunya tace "Kai Mama ni dai fa."
Sai kuma tai shiru,maman ma dariya tau ta wuce d'akin ta.
Sai da tai wanka tai salla sannan ta fito falo,kowa nata cin abinci amma Su'ada ba kwance kan kujera,mama ta zauna tana cewa "Su'ada ke baki cin abincin ne kike kwance?"
D'an turo baki tai da fad'in " Ni mama ban son k'anshin abincin ma Wallahi. "
Cikin kwantar da murya mama tace "Eh daman yanzu kam ai sai kin yi hak'uri komai ba zaki ji dad'in sa ba,balle kin samu ciki me laulayi sosai,yanzu bari in dafa miki wani abu me dad'i nasan zakiji dad'insa sosai."
Kud'i mama ta bawa Khaleelee tace "Maza auta jeka k'ofar gida gun me kayan miya ka siyo min yakuwa."
Da kanta ta shiga kitchen d'in ta fara harhad'a kayan da zatai wa Su'ada fatan tsakin masara.
Zuwa k'arfe uku ta kammala, lokacin har bacci ya d'auketa ma,bata tasheta ba sai data farka da kanta sannan ta zubo mata faten yana ta turirin zafi.
Da fari kam Su'ada ca tai bata ci, sai da mama taita rarrashinta sannan ta d'ibi kad'an a cokali ta kai baki,Jim tai jin tsami tsamin ramar ya ratsa kanta,ta k'ara loma d'aya taji yai maya coy, ai sai ga Su'ada ta mik'e k'afa tana zuba loma,sai da ta cinye tas tasha ruwa,mama tai mirmishi tana cewa "Ko a karo wani?"
Girgiza Kai tai da fad'in "A'a mama yanzu na k'oshi, amma a ajiyemin anjima zan k'ara."
**********
Bayan sallar isha'i duk su na zaune su na ta hira, wayar Su'ada tai k'ara, mik'o mata mommy k'anwarta tai,bayan ta d'aga daga d'aya b'angaran Khaleelee ya amsa mata"Pretty ina hanyar zuwa gidan,me zan zo miki dashi?"
Jim tai tana tunani can tace "Kifi karfasa amma me zafi sosai,kuma a zuba yaji da yawa."
"Ok shi kenan ko da wani abun?"
"A'a ba komai shi kad'ai yayi."
Ba'a jima ba sai gashi ya zo,bayan sun gaisa da mama ya koma sitting room.
d'an kwalin kayanta ta yafa tabi bayan sa.tana shiga yaje kan cinyarsa ya zauna tana Rik'o hancinsa cikin tsokana tace "har na fara missing wannan dogon hancin fa."
Had'e fuskarsa da tata yai yana goga mata hancin kan nata,a hankali yake magana " shima zai yi ya fara kewan ki, ni fa da za'a ban wajan kwana nima had'o kayana zan yi mu dawo nan d'in gaba d'aya. "
Lumshe ido tai tana janye fuskarta ta kwanta a jikinsa sosai,sabida yanzu sam bata jin kwarin jikinta,yawon kasala da zafin jiki duk sun zame mata jiki.
Shafa fuskarta yake a hankali yace "Tashi ga kifin karya huce."
K'asa su ka sauka ya bud'e mata, a hankali take ci cikin jin dad'in sa,gashi sai nad'ar yaji take."
Kad'an ta rage ta nannad'e wai anjima kafin tai bacci zata ci,shi kam binta kawai yake da kallo yana mirmishi, gida ta shiga ta wanke hannayenta da bakinta,sannan ta ajiye d'aura kifin ta dawo wajan sa.
************
Kullum da dare sai Khaleelee yazo,kuma sai bayan goma yake tafiya. Zakiyya ma tazo gida ta dubata,Baba ma ya kirata a waya,haka ma yaya Muktar ya kikkirata ya mata Sannu, balle kuma d'an gidanta Jabeer, shi kam duk kwana biyu ma sai yazo sun sha hirar Sakeena kam sai da kunyar kanta ta isheta ganin yaya Muktar bai ce mata uffanba kan ta kira ko karta kira.gashi in dai Jabeer na gida zai kirata ya had'a ta da Islam, to da kanta ta gaji ta kirata tai mata sannu,daga ranar kuwa bata k'ara ba .
B'angaran Su'ada kuwa a gidansu ta sami lafiya masha Allah, tayi wani sharrr da ita ta k'ara fari da,har k'iba tai,sai dai fa zazzab'i kullum dashi take kwana,b'angaran abinci kuwa ta bud'ewa faten tsaki da alala wuta,in taci alala da safe to da rana zuwa dare fatan zatai ta sha,sai Zob'o wanda ta maidashi shine ruwan shanta.
**********
Yau sati uku da zuwanta gida,don haka ranar Mama tace ta shirya kayanta da dare in Khaleelee yazo ta bishi ta koma d'akin ta tunda lafiya ta samu.da ta fara rigimar ita ba zata koma ba,amma ganin mama ta had'e rai tasan ba wasa,don haka ta nutsu.ai kuwa nan da nan k'annanta su ka had'a mata kayanta waje guda,ita dai tana ta zumb'ure zumb'ure,mama tai kamar bata ganta ba.
********
Da dare kamar kullum Khaleelee yazo,yana zaune sitting room, Khaleelee yazo yana ta damunsa da surutu, sai biye mai yake suna shiririta,can Khaleelee yace "Yaya Khaleelee kasan me kuwa?"
Kai ya girgiza yana d'an mirmishi yace " ban San me ba sai ka fad'a my takwara."
Cikin y'ar dariya yai tsalle tare da gyara zama yace " Mama tacewa Aunty Su'ada yau d'in nan zata koma gida,yanzu ma tace kana zuwa zaku tafi tare."
Ware ido Khaleelee yai yace "Da gaske kake mutumina?"
Kafin yaron yai magana aka turo k'ofa aka shigo.
Ido ya d'ago yana kallonta,d'an mirmishi yai ganin yanda ta wani had'e rai ta kauda kai gefe.a hankali ya kalli Khaleelee yace "Takwara je kace ina gaida mama da Aunty Jidda."
Da gudu yaron ya fice.
A hankali ya dawo kusa da ita ya zauna tare da sakar mata wani numfashi a wuyanta,cikin k'asa da murya yace "Pretty yau ba'ai murna da ganina bane?"
D'an turo baki tai tana kauda kai gefe tace "um um ni ba Mama ce tace wai sai na koma yau ba,ni kuma ban son tafiya Allah."
Zuba mata ido yai na d'an lokaci, kafin ya fara magana "pretty na,me yasa baki son komawa? Ko bi kiyi kewana bane?"
K'ara turo baki tai cikin shagwab'a tace"To ai ni ban gama warkewa ba fa,kulleda zazzab'in nake kwana. "
Shafo gefan fuskarta yai yana k'ara shigewa jikinta sosai,hannunsa cikin nata yana k'ara matsa mata su,a sannu ya d'ora fuskarsa saman tata yana magana murya a mak'ogaro "kiyi hak'uri kinji sweetheart, ba zan iya ja da maganar mama ba amma da naje nace ta k'ara miki ko sati guda ne,amma ki yi hak'uri mu tafi,insha Allah zazzab'in zai daina ma gaba d'aya."
Yanda yake mata ne ya sa jikinta mutuwa tsikan jikinta ya fara tashi,rik'o hannayensa tai tana fad'in "A'a ka bari,ka cikani to."
Maimakon ya cikata kamar yanda tace Aa sai ya k'ara mak'ale mata yana mata cakulkuli,hakan yasa ta fara kyalkyala dariya tana tuttureshi.
K'wank'wasa k'ofa a kai,da sauri ya cikata ya koma wata kujerar ya zauna,sannan ya bada izinin shigowa,Mommy ce ta shigo tana gaidashi,bayan ya amsa ya d'an tsokaneta sannan tace"Yaya daman mama ce tace wai kazo."
Mik'ewa yai da sauri yana fad'in "To muje maza."
Itama Su'ada bin bayansa tai har zuwa cikin gidan,a falo ya samu Mama a mutunce kamar ko yaushe su ka gaisa,Mama tace"Ibrahim Allah yasa dai tama bayanin yau zaku tafi tare?don haka ba sai an zauna hira ba yanzu yanzu Ku wuce gidanku kwayi hiran a can."
K'asa yai da kai cikin jin kunya yace "To Mama mun gode,Allah ya k'ara girma ya k'ara lafiya, Allah ya ja da rai."
Amsawa Mama take tana k'ara sa mai albarka,sannan ta dubi Su'ada da ke gefe a tsaye ta harde tana ta turo
baki. 'dan mirmishi Maman tai sannan tace "To hajjaju je ki sako hijab Ku wuce ko? Mommy Ku rakata da jakar kayanta waje."
Har kwalla Su'ada tai don takaici, tabbas ba k'aramin jin dad'in zaman gidan tai ba,yanda kullum take rayuwa cikin y'an uwanta ga mamanta na ta shagwab'a ta,ita da za'a barta ma ta har ta haihu tai arba,in da taso hakan.
*Taku ce*
*'Yar mutan Ja'oji*🙋
[2/24, 12:02 AM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭
*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*
👩🏻💻👨🏻💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_
*Ina buk'atar addu'a daga bakunanku masu albarka*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.