Facala Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Facala Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 15 of 26
_*page*_*29-30*
A Sannu cikin aminci a ka fad'a cikin watan Ramadana, a lokacin kuma ayyuka sun gama shan kan Khaleelee, duk da yana k'ok'ari wajan ganin ya bawa Su'ada lokacinta don kar ya shiga hak'k'inta,hakan yasa ya tsara lokutansa na dawowa gida. K'arfe goma na safe zai fita,ba zai dawo ba sai gab da shan ruwa,to in yasha ruwa ya d'an huta, da an kira asham in yaje yai salla ya dawo gida zai yo,to duk lokacin nan nata ne,sai wajan sha d'aya na dare zai koma shago,ba zai dawo ba sai yayi sallar asuba.
Sosai su ka tsara abubuwansu don kaucewa shiga shingen Allah, sabida Khaleelee ya saba mata matuk'ar ya na gida to ko yaushe tana jikinsa, shi kanshi ya saba bai so ya ganta nesa dashi,to da Allah ya taimakesu da rana duka yana shago,lokacin da zai dawo kuma kad'an ya rage asha ruwa,kafin yai wanka ya shirya an kira salla,sauran lokutan kuma duk nasu ne,anan suke more soyayyarsu su maida tsinkakken yawu.😝
Da asuba kuwa in ya dawo ya taro gajiya da bacci yana shigowa sai bacci, yana kwance ma take shiryawa ta tafi aiki.
Wai wani aiki sai FACALA wai wannan dawowar ma da yake gida na dare sai da ya zama abun k'orafi a gun Sakeena, sabida rannan ya dawo su Baby sun shigo kallon (dad'in kowa) yace su je bacci zai yi ya kashe kayan kallon,to da su ka je su ka fad'a mata da safe tai ta yada magana.
Su'ada na jinta tana fad'in "Mace me jarabar namiji dai bata wani lasting, ko yaushe miji manne da kai kamar fata, da azuminma ba za'a hak'ura ba Allah dai ya kyauta."
Sosai Abun ya bawa Su'ada dariya tana ayyukanta tana dariya,don ita yanzu abun Sakeena ba kowanne ke damunta ba,duk da ma yanzu an d'an sami sauk'i tun da a Kai case d'in d'aki bata k'ara tado wata ba,sai dai habaici kam Su'ada na shanshi.
Sati guda da d'aukar azumi Abban su Su'ada ya dawo,nan ya aiko mata da k'wai cikin wani dogon farin boket,Su'ada ta kira Abbanta tai ta mai godiya, da Khaleelee ma ya dawo ya gani ya kira waya yai godiya,bayan an sha ruwa Su'ada tai maganar "Khaleelee kaga nace kaga muna da k'wan da ka siyo daman,kuma yanzu ana zafi sosai tunda k'wan da yawa zai iya lalacewa kafin wani lokaci,nace me zai hana mu raba uku a bawa Maman Abba kaso d'aya a aikawa Zakiyya kaso d'aya?'
Idanuwansa da ke lumshe ya bud'e a kanta yana mata kallon shiga rai,sannan a hankali yace " Duk yanda ki kai ya yi my world, komai kika tsara banda ja a kai don duk shawarar da ki ka kawo me kyauce,ki basun Allah yayi miki albarka ya baki babban rabo a duniya da lahira matar rufin asiri."
Cikin farin ciki ta fara godiya "Nima na gode mijin wuce sa'a, ko yaushe 'karfafa min gwiwa ka ke akan duk abunda nazo da shi,ina jin dad'in hakan kuma ina alfahari da kai a kowane lokaci."
Washe gari da safe Su'ada ta raba k'wan ta kawowa Sakeena, kadaran kadahan ta amsa tai godiya, sannan Su'ada tace "Don Allah Maman Abba zan aiki Abba gidan Zakiyya ya kai mata sa'ko in ba inda za ki aikeshi."
"Ba inda zan aikeshi,sai dai kin San dake ya na azumi kuma da gani yana bashi wahla."
Da sauri yaron yace "A'a Mama ni dai zance don Allah, ba wani wuya da azumin ke bani,kuma ai a napep zan je ko Aunty?"
Gyad'a mai kai Su'ada tai da fad'in "Eh zan baka kud'in mota wanda za'a kaika har k'ofar gidan in ma jiranka zai ka kai ka fito Ku dawo duk zan bada."
Bai k'ara bi ta kan uwar ba ya shiga cire kayan jikinsa don sauya wasu.
Ita kam Su'ada komawa tai d'akin ta sami bokiti me murfi zuba k'wan a ciki,da kansa ya biyo ta d'aki ya amsa sak'on.
*Manege plss*🥰
*Taku ce*
*Yar mutan Jaoji*🙋
[2/23, 11:58 PM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭
*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*
👩🏻💻👨🏻💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_
_ALLAH KAI MANA MAGANIN DAMUWARMU_🙏🙏🙏
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.