Facala Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Facala Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 13 of 26
_*page*_*25-26*
Rayuwa taci gaba da garawa Su'ada a gidan Khaleelee, bayan matsalar matar wan miji (FACALA) Su'ada bata da wata damuwa,mijinta yana bata kulawa d'ari bisa d'ari, uban mijinta yana mu'amulantarta tamkar y'ar cikinsa,haka y'an uwan mijinta su ke zaune da ita lafiya lafiya,kowa Son barka,don haka mafi yawan lokaci in tasa damuwar halin Sakeena aranta kuma ta tuna alkairan sauran mazauna gidan sai ta gode Allah taji komai ya fice a ranta.
Yanzu kuma wani sabon balli da Sakeena ta sako a gidan shine, wai dole Jabir ya koma d'akin Baba da kwana don tun bayan bikin su Su'ada tare su ke kwana da Abba a d'akin sa, to Jabeer baya shigowa gida da wuri sai sha d'aya, shi kuma Abba ga baccin wuri, ko yaushe sai dai ya kwanta a falo don Jabir baya barin key tun randa ya lalata mishi wayarsa da ya barta jikin charge yaje bacci yai danne danne ya lalata mishi,shi kuwa yace ya daina barin key d'insa,sai dai in ya shigo a tashe shi yaje ya kwanta, yanzu kam ta mirje idanuwanta tace sam bazai yuyu ba,d'aki dai cikin kason mijinta yake, don haka ita me 'Ya'ya hud'u an had'ata da d'aki biyu,sauran dakunanta biyu kuma uban miji da k'anin miji sun gaje, ga amarya ma da bata da kowa an shatar mata waje ita guda ko don ita an san y'ar masu dashi ce.
Tun safe yau take mita,kasancewar week end ne,Su'ada na gida, tana ta y'an gyare gyaran ta, haka ma Jabir Yau ya tashi da wanki kuma yana ta kwalemar d'akinsa.
Duk yarda maganar da take Jabeer yana jinta sarai amma sai ya kauda kai,uzirin da su kewa Sakeena ko yaushe shine, da can ba haka take musu ba,in ka d'auke k'azanta da rashin son gyara gida bata da wata matsala,amma tun auro Su'ada gaba d'aya ta firgice ta zama wata fitinanniya,ko hira ka fiye yi da Su'ada sai ta fara had'ema rai.
Bayan ya gama wankinsa ya fito da kayan gadon ya ke ta gogesu,da sauran tarkacen d'akin, can ya jiyo muryarta tana magana.
"Wallahi Allah cutar da ake min a gidannan ta isheni, gashi yanzu ina ji a radio wani malami yana fad'i cewa da yaro namiji ya tasa a raba shi da 'Ya'ya mata,to sabida ni bani da gata cikin gidan nan,yaro d'an shekara goma sha an barshi yana raba dare cikin mata,yo kullum yaro sai yayi barcin farko cikin mata sannan a tashe shi,kuma yanzu ga faruk ma ya fara girma shekara shida ai shima ya dace ace na cireshi a d'akin nan,ya dace ace Baby kad'ai ke kwana a falo ita da Islam amma da nai magana sai ace na fiye k'orafi da rashin son zaman lafiya,wallahi dole asan abun yi,tunda dai duk d'akunan nan sun zama mallakin ubansu,ya dace a barsu su wayata kuma,yo in banda ma lalura ace mutum ya zauna gida tun da k'uruciyarsa cikin garadan maza kuma har yanzu ba canji, tunda dai shima mutum an bashi matsugunni sai ya koma can da zama in an taki gaskiya fa."
Iya k'uluwa Jabir ya gama k'uluwa, duk sanyi irin na y'an gidan shi kam babu shi ciki,don sam baida hak'uri don haka bai son shiga sabgar mutane.
Yanzu d'in ma wani k'ululun bak'in ciki ne ya turnik'eshi,sam Sakeena bata gane dalilin da yasa yake mata kara,ta d'auka isarta ne ko wani abu,amma bari yau ya nuna mata shima d'an zamani ne.
Fitowa tsakar gidan yai ya tsaya cikin b'acin rai ya ke fad'in "Ke malama wai me ki ke son cewa? Fad'i abunda ke bakinki kai tsaye ki daina kwana kwana hakan zai sa nafi saurin d'aukan haske."
To daman me neman abokin tayi,nan da nan Sakeena ta shiga ruwan bala'i.
"Kar kai min rashin kunya kaji ko,kuma duk maganar da nake ai kaji kuma kasan Inda ta dosa,don haka d'aki nake son a bani guda zan had'a 'ya'ya na maza a can,kuma ba zan yarda da wani cewa ku rink'a had'uwa tare ba,yaro yayi barci tun sallar isha'i sannan sai bayan shad'aya a tashe shi, don haka naje karshe,hak'urina ya k'are wallahi dole a san abun yi."
Cikin fishi ya fara maida mata martani yace "Fad'a min cikin gidannan bulo nawa kika kawo da za'a gina?har kike ikirarin dole sai an baki d'aki kinsa 'yay'anki maza,to baza'a bayar ba k'arfinki ya k'watar miki, don tsabagen rashin mutunci har kina fad'ar wai sauran d'akunanku guda biyu uban miji da k'anin miji sun gaje, wallahi Allah Maman Abba ki gyara halinki sam wannan halin da kika samo ba d'abiar arzik'i bace,kuma ki shiga taitayinki kan yin duk furucin da ya fito a bakinki don wata rana zakiyi furucin da zai zame miki danasani."
Bambami fa Sakeena tai tayi kamar ta ari baki,ganin abun yak'i k'arewa ya sa Su'ada fitowa daga b'angarenta,hak'uri take ta bata,sannan taiwa Jabeer magana kan yayi shiru haka nan.amma me sai abun yake neman komawa kanta,ganin haka yasa ta koma b'angarenta taci gaba da ayyukanta.
Cikin ikon Allah sai ga Ibrahim, yana shigowa yaji yanda Jabeer ya ya ke caccakawa Sakeena magana,cikin tsawa yace "Kai Jabeer meye haka? baka da hankali ne? rufewa mutane baki dalla."
Cikin bala'i da masifa Sakeena tace "A'a ka barshi dai ai d'aurin gindi ya samu,in ba rashin mutunci ba yaron da na raina a hannuna cikin gidan nan amma shine yake k'ok'arin zagina."
Hak'uri Ibrahim ya fara bata yana fad'in "Meya faru ne haka? Me yai miki don Allah?"
"Ka tambayeshi mana,ka tambayeshi wace rashin kunya yake min."
Ibrahim ya juya ga Jabeer yana Tambayar sa meya had'a su.
Bai rage komai ba,ya fad'a mai duk maganganun da tai mai da Wanda shima ya maida mata.
Fad'a Ibrahim ya shiga mai yana fad'in "Kai zafin kanka har a cikin gida,Sa'arka ce,duk abunda tai maka bazaka iya kai k'ararta ba sai ka zauna kana cacar baki da ita.karka bari na k'ara jiyo muryarka wallahi."
Daga haka ya juya ya shige b'angaransa.ita kuwa Sakeena an samu yanda ake so nan ta k'ara bud'e wuta da yara maganganu.
Shi kam Jabeer kamar zuciyarsa zata fito haka yake ji,yanzu duk abunda Sakeena ta fad'a bai zama laifi ba sai nashi ne laifi,cikin fishi ya fice cikin gidan.
Ibrahim kam yana shiga ya zauna falo dafe da kansa,Sam shi bai son hayaniya a rayuwarsa, matsalolin gidan nam sun fara mai yawa.
Hannun Su'ada yaji a cikin nashi ta zauna jikinsa tana magana "My Choice sannu da zuwa,daina tagumi kaji don Allah."
Ta janye mai hannayensa daya dafe Kai.
Zuba mata ido yai ransa a b'ace yace " kina ji Suna rigima amma kika kasa kirana a waya ki sanar min."
D'an lumshe ido tai tana k'ara matsa hannunsa e cikin nata tace "Me yasa zan kiraka kana wajan sana'arka na tashi hankalinka, na fita na bata hak'uri bata jiba don haka na barta, tun d'azu nake fatan Allah ya dawo da Baba ko Yaya Muktar d'in, sai kuma ga ka Allah ya kawoka,matsalar nan abun dubawa ce my Choice, wani sashin Maman Abba tana da gaskiya,kawai yanda zata kai kokenta ne bata iya ba,a k'aidar musulunci daman Abba da Faruk bai dace su na kwana cikin su Baby ba,in ba da wata babbar lalura ba,kawai rashin iya magana ne yasa ba za'a fahimceta ba."
Lumshe idanuwansa yai yana d'an cizon lips d'in sa yace " Su'ada ba wannan dalilin ne yasa Sakeena take wannan borin ba,kishi ke damunta, tun lokacin da Baba yace ya bar mana gidan nan ni da yaya Muktar kuma ya kasafta ya bawa kowa rabonsa take bori,borin kuma taga duk d'akunan da take wadak'arta dasu sun shigo rabona,taga na ware sashi na na keb'ence shi,tun sannan taga gidan ya tsuke mata ta shiga masifar d'akuna biyu sun mata kad'an da y'ay'anta, wannan dalilin yasa nace Abba ya rink'a kwana tare da Jabeer tunda ni na bar d'akin, to bayan wannan me Sakeena ke nema kuma Su'ada? "
Tsam tai da ranta tana nazari can tace "D'aki d'aya take so a k'ara mata."
"To wane d'akin za'a bata? Na Baba ko na Jabeer?"
Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace " Na Jabeer take hari,da akwai shago a k'ofar gida da ya koma ya bar Mata."
Zamewa kawai yai ya kwanta bai k'ara magana ba.
Ganin haka yasa Su'ada ta tashi ta ci gaba da ayyukanta.
Jabeer kam yana k'ofar gida zaune shi kad'ai sai huci yake,a lokacin su Baba su ka dawo daga d'aurin Auran da su ka je, ganin Jabeer d'in dafe da kai fuska d'aure tamau yasa Baba saurin tambayar sa me ya faru. Cikin k'unar rai ya juyewa Baban komai har fad'an da Ibrahim yai ta mai kuma akan gaskiyarsa.
Shiru Baba yayi na d'an lokaci sannan yace " Tashi muje ciki."
D'akin Baban su ka shiga,bayan ya rage kayan jikinsa ya dubeshi da kyau yace "Jabeer! abunda kai Sam baka kyauta ba,shin ka manta Sakeena matsayin uwa take gareka,shekaru goma sha fa tana rainonka,sauyin halin da tai bashi zai sa kuma Ku sauya ba,duk rashin mutuncin mutum karka manta alkairin da ya tab'a yi maka, kishin matar k'anin miji (FACALA) ke cin Sakeena, kuma ba akanta aka fara ba,sai dai kuma shi kishin jahilci ne,ba wani dalili da zaisa kai kishin matar da baku had'a miji da ita ba,a da can mata sun maida kishin FACALA abun yi,har sai kaga wata macen bata kishin kishiyarta kamar yanda take na FACALA, amma a yanzu da ilimi ya wadata wayewa tai yawa duk an zubar da wannan abun,sai dai dai daikun mata ne irin Sakeena basu gane hakan ba,abunda nake jan hankalinka Kai tai mata uziri karka bari wannan halin yasa ta zama abokiyar fadanka,sannan kamar yanda kowa ya sani wannan gida a da can ne yake nawa,yanzu kuwa ya zama mallakin Ibrahima da Muktar don haka matansu nada iko dashi, ni da kai duk cin arzik'i muke na d'an lokaci, kwanaki kad'an su ka rage min a duniyar,yayin da kai kuma lokaci na zuwa kaima za kai auranka ka zauna a naka gidan, don haka yanzu kana ji ko,ka had'a kayanka tsaf ka dawo d'akin nan muyi zamanmu mu biyu,daman d'akin yamin girma ai,kaga ko cikin dare ka rink'a taimakona in ciwo ya tayar min."
Tofa Baba ya gama kulle Jabeer, banda tsananin biyayyarsu da mahaifnsu ba abunda zai sa bai musawa Baba ba,amma ba yanda ya iya,haka ya amsa ya tashi ya fice.
Ibrahim ya fito sallar azahar Baba yake sanar dashi shawarar daya yanke ta dawowar Jabeer d'akin sa,bai so amma bai nuna ba yacewa Baba Allah yasa hakan yafi alkairi, nan ya zage ya taimakawa Jabeer d'in su ka kwashe duk kayan su ka dawo dashi d'akin Baba, gefe duk ya jera kayansa,sai dai gado bazai samu waje ba duk da k'arami ne,Baba yace ba komai nashi ya ishesu su biyun ai,yace ya bar gadon a d'akin su Abban sai su rink'a kwana,habawa bak'in ciki kamar ya kashe Jabeer ya kasa dannewa har Baban ya gane ya sassauta murya da fad'in " Ashe ba zaka iya yiwa y'ay'an d'an uwanka hidima ba? Shin me Sunana da faruku da zasu rink'a kwana a d'akin akan gadonka shi kakewa bak'in ciki,ko ba ran Muktar Kai me rik'e mai y'ay'a ne don haka karka sa b'acin ran uwarsu a ranka har ya shafesu,kayi mu'amala dasu kamar y'ay'an cikinka kaji ko?"
Gyad'a kai kawai yayi yaci gaba da jera kayansa,da yawan wasu abubuwan dole ya barsu a d'akin don ba wajan ajiyar su.
05/12/2019
*TAKU CE*
*Y'AR MUTAN JA'OJI*🙋
[2/24, 12:05 AM] LAYUZA KABIR: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
👭 *FACALA* 👭
*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*
👩🏻💻👨🏻💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_
*Sadaukarwar gareku D'alibai masu albarka*
*'Daliban makarantar Intisharul Qur'anil Kareem*
*Da 'Daliban Nusratul Aulad Islamiyya*
*Allah yai muku albarka ya sawa iliminku albarka,ya sa musulunci yai alfahari da ku,Al'umma su amfana da ku*🙏🙏 *Kuna cikin raina ina sonku sosai duk da irin charger min k'wak'walwa da Ku ke*😕
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.