Complete Hausa Novels

Facala Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Facala Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 7 of 26

_*page*_*13-14*

Mama na lura da duk sabgar da Su'ada ke yi,kuma ta fahimci da Ibrahim ta ke yawon yin wannan wayar,don haka ta k'ara bata lokaci su fahimci juna tunda ta lura soyayyar tasu sabuwa ce. wani sa'in ta na ji in suna waya zata Kira Khaleelee tace yazo ya gaisa da takwaransa,ko kuma su jidda su amsa su yi ta hira har su Sajida ma. yanda Mama ta lura Ibrahim na jan y'an uwan Su'ada a jiki ya sa ta k'ara nutsuwa da lamarin sa,duk da dai Su'ada bata fad'a mata abunda ke tsakanin su ba amma ita uwa me kula ai bata buk'atar bayani da ga halin da y'ay'anta ke ciki.

*********
K'arfe tara na dare Ibrahim na zaune cikin gidan su,abinci ya ke ci a tsakar gida suna hira da matar yayansa Sakeena. rabin hankalinsa na ga wayarsa,ihsan k'aramar y'arta tazo ta dafashi tana mai surutun su na yara,dariya yai yana nuna mata hoton da ke kan wayarsa,yace "Ihsan kin ga Auntyn ki ko?"

Da sauri Sakeena ta mik'a wuya da ga inda take tana son hango hoton, ganin me ta ke yasa Ibrahim shiga cikin gallery ya fiddo hoton Su'ada guda d'aya ya mik'awa Sakeena wayar yana fad'in " Maman Abbah ga k'anwar ki insha Allah very soon tana tan tafe."

Da hanzari ta amshi wayar tana k'arewa hoton kallo "Kai Ibrahim ina ka samo wannan bafulatanar haka?"

Y'ar dariya yayi yace "Costumer ta ce a da,amma a yanzu matar da nake son aura ce insha Allah."

"Gaskiya masha Allah da ita. amma da gani ba ta jin hausa ko?"

Wata dariyar yai sosai yace hausa iya hausa kuwa,Mamanta bahaushiya ce, Babanta ne bafulatani kuma ko jin filatancin ma basa yi. bari na kirata Ku gaisa."

Amsar wayar yayi daga hannunta ya fara danna kiran number d'in Su'ada, bugu biyu ta d'auka cikin shagwab'ar da ta saba mai tace "Yau an manta dani tun k'arfe d'aya na rana."

"Ayya, Yi hakuri aiki ne ya rik'e ni sosai sai yanzu ma na shigo gida,ya kike ya kowa?"

"Kowa lafiya amma ni dai ba lafiya ba."

"Subhanallah me ya sameki?"
Ya fad'a cikin fad'uwar gaba.

"Rashin ka tare dani mana,yau haka na yini ba sukuni."

Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace,
"Kiyi hak'uri kinji,kinsan yanayin sana'ar ta mu wani lokacin sai godiyar Allah.ga Matar Yaya muktar zaku gaisa."

Dai daita muryar ta tai ta dawo normal, Sakeena ta amshi wayar da sallama,itama ta amsa mata su ka gaisa cikin girmama juna ta tambaye ta yara,ta amsa mata da duk suna lafiya,daga nan su kai sallama.amsa yayi ya mik'awa Ihsan da ke ta mik'a hannu tana son ya bata, Cikin maganar ta ta yara suka gaisa tana ta mata shirme,ita kam ta biye mata ta na ta dariya. k'arb'a yai duk ya bawa yaran suka gaishe ta sannan ya tashi ya shige d'akin sa. Nan ya narke mata cikin soyayya duk yanda Su'ada take mishi shagwab'a In ya fara mata tashi dariya kawai take mai. don Ibrahim irin mazan nan ne masu bala'i bala'in iya soyayya, cikin d'an lokaci ya ke haukata Su'ada da kalamai, wani lokaci in tai fishi har kuka zata ji yana mata cikin waya wai duk na rarrashi ne,nan da nan zata rikice ta dawo rarrashin sa ita ma. To yanzu ma haka ya kashe ta da kalamai ya kawai da k'orafin da ta ke. juyi kawai take kan gado tana lumshe ido don yanda kalaman sa ke ratsa dukkan zuciya da gangar jikin ta.

*********
Wannan karon Abbansu Su'ada wata biyu yayi a gida sannan ya koma sari.
kwanansa biyu da tafiya Mama ta kira Su'ada d'aki,bayan ta zauna tace "Mama ga ni."

Kallonta mama tai na d'an lokaci sannan ta gyara zama ta fara magana,"Su'ada ya maganar da mukai da ke tun watanni biyu ko uku da su ka wuce?"

D'agowa tai ta kalli Maman kamar ba ta gane inda ta dosa ba.

"Eh maganar Fitar da mijin aure da nace kiyi cikin masu son ki."

K'ara k'asa tai da idonta tana wasa da gefen rigarta, jin tai shiru ya sa maman fad'in "Ina sauraran ki Su'ada maza fad'a min wa ki ka fitar cikin su?"

Karon farko da taji tana kunyar mahaifiyar ta wajan sanar da ita wata magana,amma ba yanda ta iya haka ta daure ta fara magana,"Mama daman Ibrahim ne yanzu dai . ."
sai kuma tai shiru.

"Um hmm ina jinki,wane Ibrahim d'in?"

Daurewa tai tace
"Khaleelee tela."

"Ok shima son naki ya ke?"

Gyad'a kai tai idonta a k'asa.

Numfashi Mama ta sauke tare da fad'in
"Su'ada ban son ki yi gaggawa cikin zab'in ki shi yasa na k'ara miki dogon lokaci don ki k'ara nazartar wanda ya fi kwanta miki a rai kuma ki ka yarda da ingancin sa,shin Kin tabbatar Ibrahim d'in ya miki kuma shima d'in da gaske ya ke?"

Muryar ta a sanyaye tace
"Eh Mama da gaske ya ke,ya ce duk sanda aka min magana zai turo manyan sa."

"To masha Allah, Allah ya sanya alkairi. Tabbas nima na aminta da d'abiun Ibrahim da tarbiyar sa,Allah ya sa abokin rufin asirin ki ne."

D'an mirmishi tai amma kanta a k'asa ta kasa amsawa da Ameen.
cikin zolaya Maman tace "Wai yau kunya ta ki ke ji ne Su'ada? Sai sunne Kai ki ke kamar kina gaban surukar ki."

Dariya tai tana d'ora hannayen ta a fuska.Maman ma darawa tai sosai cikin farin ciki, don ita farin cikin y'ay'anta shine nata. musamman yanda ta lura Su'ada na son Ibrahim matuk'a.

"Shi kenan za muyi magana da Abbanku insha Allah, in yaso sai manya su shiga cikin maganar,tashi ki je Allah ya yi muku albarka."

Mik'ewa tai tana fad'in "Ameen,muna godiya,Allah ya ja da rai."

Wannan addu'ar su ga Mahaifiyar su ce ko yaushe.

Allah Allah take Ibrahim ya kira waya tai mishi albishir, ai kuwa da ya kira ta sanar dashi kamar an ce mai an tsaida ranar auran su haka ya ji. ya sanar da ita zai fad'awa mahaifin sa kome ake ciki.

*********
Ibrahim ya yi magana da yaya Muktar sannan su ka sanar da mahaifin su,yaji dad'i kuma ya yi farin ciki don kullum mita ya ke Kan rashin auran na sa.nan dai ya tura y'an uwansa guda biyu su kai mai binciken gidan su Su'ada, komai an same shi yanda ake fata, sannan ya ce ya sanar da Su'ada ta fad'a a gida za'a zo kawo kud'in aure.

Su'ada kam Lokacin daya sanar da ita za'a kawo kud'in aure tamkar ranar ce ma tazo haka ta ji, duk yanda ta danne murnarta sai da ya gane don haka dariya kawai yai ta mata ya na tsokanar ta.

Bayan ta sanar da Mama itama ta sanar da mahaifin Su,ya kira danginsa can Darki da kuma amininsa da ke nan cikin gari, ya ce su yi bincike kan Ibrahim duk da an sanar dashi halin kwarai gareshi,amma su k'ara bincikawa in an samu komai yanda ya dace to su tsayar musu da ranar da zasu kawo kud'in auran.

Bayan dogon bincike kan Ibrahim Manyan Su'ada basu sami komai ba sai shedar arzik'i daga kowa.hakan yasa ba Jan lokaci aka basu damar su kawo kud'in auran.

Sun kawo kud'in su dubu talatin na aure kasancewar sa me k'aramin k'arfi. Akai fatan Allah ya sanya alkairi da albarka.

To fa Su'ada da Ibrahim an yi baiko nan magana ta yad'u kowa ya ji, ciki harda samarinta da yanzu su ka fahimci daman ba sonsu take ba.Jameel ya yi takaici kamar kamar me amma ya hak'ura ya san ba matar sa bace daman can.

Ita kam Su'ada ko a kwalar rigar ta farin cikin ta kawai ta ke sha,ta fara shanshano auranta da burin ranta.

*********
Lokacin azumi ke tunkarowa da gaske wanda ya rage kwanaki goma a d'auka,zuwa lokacin Sam Ibrahim ba shi da wadataccen lokacin kansa bare na soyayya, don kullum cikin aiki su ke,kaya kamar zasu tsaga shagon su,tunda ya San hidimar da ke tunkaro shi yanzu ta aure yasa ya k'ara himma wajan tara kud'i,ahi ya sa ya ke d'inkin sa ba kasala.Su'ada ta San yanda ya ke shiga busy lokacin azumi tun asali don haka bata damu da rashin nemanta da ba ya yi sosai ba,a haka watan ya kama komai ya kara cab'ewa,ko yaushe dai in ansha ruwa zata kirashi ta mai barka da shan ruwa,to a wannan d'an tsakanin ne kawai su ke samun yin waya kafin a kira isha'i a hakam ma hankalin sa duk a rabe ya ke yi,ya na fama da jama'a, ya na waya.To in sun yi Sallama daga nan kuma sai washe gari.

Wannan karon Mama ta hana kowa kaiwa su Ibrahim d'inkin Salla,ta ce yanzu ya zama suruki ba zai yuyu a tara mai d'inki sama da goma ba kuma ya ga ya k'i amsar kud'in,Wannan ba girma bane.
Badan sun so ba su ka kai wani shagon don duk basu saba da kai d'inki wani wajan ba.

Da kansa ya ke tambayar ta ba zasu kawo dinkunan su ba,ta sanar da shi Mama ta hana, da ya tambayi dalilin ta fad'a mai, ya nuna rashin jin dad'in sa a zahiri,amma ba yanda zai yi tunda an riga ma an kai su wani wajan ba damar amsowa.

***********
Ranar da azumi ya yi sha biyar a ranar Ibrahim ya yiwa Su'ada zuwan bazata,don su na idar da sallar Asham ta ji kiran wayar sa,da zumud'i ta d'auka don daman yau ko barka da shan ruwa ba ta mai ba,wayar sa a kashe take, d'agawa tai tare da sallama. Bayan ya amsa kafin tace komai yace "Ina k'ofar gida yanzu ."

Mirmishi tai tace,
"Hhhmmmm tsokana ta ko?don kaga na matsu da son ganin ka."

"Da gaske fa ina bakin gate."

Da sauri ta mik'e ta na fad'in "Bari a shigo da Kai to."

Kashe wayar tai da murna ta ke kiran Sajida, "Sajida maza je waje Khaleelee na nan ki shigo dashi sitting room,ki kai mishi ruwa da lemo in ya shigo."

Juyawa tai cikin d'aki da sauri ta cire kayan jikinta zuwa Riga da siket na atamfa sannan ta duba fuskarta ba komai jiki kasancewar bayan shan ruwa tai wanka,powder ta goga kawai ta gyara gashin idonta da maskara,sannan ta gyara girarta,bakinta ta d'an gogawa jan baki me saukin k'ala,ba ta sa d'an kwali ba sai mayafin kayan da ta rufa tare da fesa turare me saukin k'amshi, plat d'in takalmi ta saka ta fito zuwa d'akin Mama don ta sanar da ita zuwan Ibrahim d'in, Mama tace to sannun shi da zuwa,a kai mai ko fruits ne da lemo.
Amsawa tai ta fito cikin zumud'i.

Da siririyar sallama ta shiga,kansa na ga TV d'in da ke ta aiki, a hankali ya d'ago ya zuba mata ido cikin mayataccen kallon sa me narkar da ita.

Ji tai wata kunya ta lullub'eta ta da su ka had'a ido,ta sa hannayen ta biyu akan fuskarta bayan ta lallab'a ta zauna kan kujerar da ke farko.

Cikin shauki ya ke kallonta, gaba d'aya sai ya ga ta canja mai,yanda ta rufe fuska ma sai ta bashi sha'awa, k'asa sosai ya yi da murya yana fad'in " To tunda ni ba'a min barka da zuwa ba ni bari in miki barka da gida, Allah ya taimaki Gimbiyar mata zak'in zuciyar Ibrahimal Khaleel, ina fatan na same ki cikin koshin lafiya."

A hankali ta zame hannayen ta amma idonta a k'asa tace "Sannu da zuwa ya Ibada ya aiki?"

Y'ar dariya yai yace "Ni ba'a amsa gaisuwar da nai ba an min wata,to Sannunki, Ibada Alhamdulillah, aiki kuma gashi muna fama kullum ba sauk'i. Ya Mama da sauran y'an gidan?"

"Duk su na lafiya qlau,Ya jikin Baba?"

"Baba jiki da sauk'i Alhamdulillah."

Shiru ne ya d'an biyo baya,shi ya k'ara kauda shurun da fad'in "Kin rame Su'ada ko azumin ne?"

d'agowa tai karo na biyu su ka had'a ido,ya k'ara narkar da idanuwansa cikin nata, kauda kai ta d'an yi cikin kaucewa kallon tace"Kowa haka ya ke fad'a, amma ni banga ramar da nai ba."

"Hhhmmmm ko kowa ma bai gani ba ni zan gani ai,kinga alamun ci gareki yanzu ba'a samun yanda ake so shine aka rame haka."

Da sauri ta kalleshi da fad'in "A'a fa, Allah ni banda ci,kawai ulcer ta tayar min ne jiya da yau,amma ba azumi bane."

Mirmishi yai yana kallonta sosai,don ta mishi kyau k'warai da gaske.ganin kallon ya yi yawa yasa cikin Shagwab'a tace "Oh Khaleelee kallo haka."

Kwaikwayon muryar ta shima yai yace "Oh Su'ada kyau iya kyau haka."

A tare suka saki dariya, daga nan kuma suka shiga hira me gardi irin ta Masoya.

Awa guda cif ya yi ya ga goma ta yi,kallonta yai tare da kallon agogo yace "Hajjaju dare ya yi ko?"

D'an turo baki tai kalar na shagwab'a tana girgiza kai tare da marairaicewa.

"Wasssh Allah wannan salon fa zai iya hanani tafiya don Allah a barni in tafi kinji."

Juyar da kai gefe tai tana buga k'afa alamar tak'i yarda d'in.

Gaba d'aya abunda take k'ara narka Ibrahim take,yama rasa me zaice don ta wullashi duniyar shauk'i sosai,daurewa ya yi ya sauko da ga kujerar sa ya tsugunna gaban ta yana had'a hannaye alamar ban hak'uri, "Zan tafi ne badan na so ko na gaji ba,sai don lokaci ya nuna kamatar in tafi,sannan kin ga akwai tarin ayyuka agaba na, zan je in d'ora inda na tsaya,in harhad'a musu d'unkunan su su harhad'a min kud'ad'e na in samu in yi aure, kullum in ta zama tare da shagwab'ab'b'iyar mata ta."

Bata San sanda ta sa dariya ba har duka hak'oran ta su ka bayyana.
Ya na ganin haka ya mik'e shi ma ya na dariyar, ita ma mik'ewar tai tare da hard'e hannayen ta a k'irji ta tsare shi da lumsassun idanuwan ta,sosai shima ta narkar da nasa su ka sark'e idanuwan junan su cikin mayen so.

Ita ta fara janye nata a kasalance tace "Sai kuma yaushe Khaleelee?"

Sauke ajiyar zuciya yai Sannan yace " Sai zuwan Salla kuma,in na samu kaina zanzo in miki awa uku cikakku kinji."

D'aga mai kai tai cikin gamsuwa. Shi kuma ya saki mirmishi ya na nuna mata ledojin da su ke gefe, "Su'ada ga wannan ba yawa kin san mijin naki me k'aramin k'arfi ne."

" Don Allah me yasa ka wahalar min da kanka wajan siyayya,Allah da ka barshi amma har wannan uban kayan."

Zare ido ya yi ya na d'ora hannunshi kan lips d'in sa kamar ya na tsoratar da yaro.

"Kin san me ye a ciki kike cewa da yawa? Kuma ban wahalar miki da kaina ba wajan siyayya ba wani abu ne me yawa ba fatana kawai su yi miki."

Annuri ne ya k'ara k'aruwa a kan fuskarta tace "To na gode Khaleelee, Allah ya k'ara bud'i da arzik'i me amfani,Allah ya tsare min kai."

Sosai ya ji dad'in addu'ar ta cikin fara'a matuk'a yace"Ameen Ameen Sweet Su'ada. in kin shiga ki gaida min Mama ki yi mata barka da shan ruwa, ki gaida Takwara me baccin wuri."

"Ok duk za su ji insha Allah."

Rakiya tai mai gate ya fidda mashin d'in sa da ya zo da shi, cikin kewar juna su kai sallama ya tafi.

Da ta dawo ta d'auki ledojin manya guda biyu ta shiga dasu gida,a falo ta samu kowa duk su na kallo,ajiye ledojin tai gaban Mama tana fad'a mata sak'on gaisuwar sa,Mama ta amsa cikin jin dad'i.

Ita dai wucewa tai d'aki don cire kayan jikin ta.Jidda ce ta bud'e ledojin, ta farko Atamfa ce me kyan gaske, d'inkin riga da siket abunka da masu abu,an tsantsara d'inki, sai material royal blue me laushi an mai d'inkin doguwar riga, yaji stone work, sannan takalmi kamfanin Vinci, da mayafi kalar takalmin.
D'aya ledar kuma kayan ciye ciye ne fal su cake da su ice cream da lemuka.

K'alawa Su'ada kira Mama tai, ta fito da ga d'aki, kallon tuhuma ta kafe ta dashi,a sanyaye ta k'araso ta zauna kusa da ita.

"Su'ada wannan kayan fa?"

"Mama shi ne ya kawo min." Ta amsa mata.

"Na San shi ya kawo miki ai,ina miki maganar sun yi yawa ne,ban son kina takurawa bawan Allah fa,Su'ada a rayuwa kin san kowa da yanayin k'arfin sa, Ibrahim akwai hidima a gaban sa, bai kamata ya sawa kansa damuwa a ire iren wannan hidimar da samari ke yiwa y'an mata ba, aure ne a gaban sa,fata na ki samu kwanciyar hankali a gidan auran ki ba wani k'yale k'yale ba. Su'ada karki rink'a nuna mai ki na son ya miki wata hidima kinji ko,duk da na san ba halinku bane son abun wani,amma ki k'ara kiyayewa kinji."

Jiki a mace ta gyad'a kai da fad'in "To Mama insha Allah zan k'ara kiyayewa."

Bayan Jidda ta shigo mata da kayan sawar dak'i ta bubbud'e su tana dubawa,mirmishi kawai ta ke, a ranta ta ke cewa 'Allah sarki Khaleelee na,Allah ka k'ara bud'a mishi ka dafa mishi cikin sana'ar sa."

*28/10/2019*

*Taku ce*
*Y'ar mutan Ja'oji*🙋
[2/23, 11:53 PM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭

*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*

👩🏻‍💻👨🏻‍💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_

*Dedicated 2*

*Aunty Maimuna OG* *malamata ta adabi . . .*
*Maryam Obama*🤭🤣🤣🤣

*Hassan and Hussain 80k*

*Alherin Allah ya kai muku har gadon barcinku*💃

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.