Complete Hausa Novels

Facala Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Facala Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 19 of 26

_*page*_*37-38*

A hanya Khaleelee ya tsaya yaiwa Su'ada na kayan ciye ciye sosai,suna tafe yana mata hira amma tak'i tanka mai, don haka yaja bakinsa yai shiru, aransa ko fad'i yake ai 'Mama tai min gata, daman kwana biyun nan a d'ari nake jina,don haka yau hhhhmmmm'.

A k'ofar gida ta sauka a mashing d'in don bashi damar shigo dashi soro, k'ofar d'akin Baba ta tsaya da sallamarta,Jabeer ne ya amsa yana fad'in "Aunty kin dawo? Sannu da zuwa."
K'arasowa yai ya d'age labulan yana fad'a Mata Baba ya jima da yin bacci sabida bai jin dad'i. cikin damuwa tace "Ayya,Allah ya bashi lafiya, bari da safe ma gaisa,Ashe dole in ganka da wuri haka a gida."

Y'ar dariya yai yana shafa kai yace"Aunty ya jikin naki dai?"

"Alhamdulillah d'an uwa,jiki ya warware,bari in k'arasa kar mu tashi Baba."

A lokacin Khaleelee ya k'araso janye da akwatinta.
Tana sallama a tsakar gidan Baby da batai bacci ba da Abba su ka fito da gudu suna ihun murnar Aunty Amarya Oyo yoo,itama cikin fara'a ta tare su,tana fad'in"A'a banga mutuniyar ba ko tai bacci?"

Sakeena ce ta d'aga labulen d'akin ta ta fito,yau kam fuskarta da fara'a takewa Su'ada sannu da zuwa,itama cikin fara'ar ta amsa su ka gaisa,Yaya Muktar ma ya fito su ka gaisa tana k'ara tambayar ta jiki,ta amsa mai da sauk'i. K'arasawa tai wajanta da Khaleelee ya bud'e k'ofar,tana shiga ta cire hijab d'in ta ta wullar kan kujera,toilet ta shige tai brush ta wanke fuska,sannan tazo tai shirin bacci.

Yana kallon yanda take ta zumb'ure zumb'uren baki,amma sai ya kauda kai,shima shirin baccin yai ya kashe haske, a hankali ya fad'o kan gadon,ya na jawota jikinsa,k'ok'arin tureshi ta fara yi,amma yak'i bata damar hakan,a sannan yake sarrafata da hannu guda,tun tana ciccijewa da kauda kai har yai nasarar saka harshensa cikin nata, cikin salonsa na iya soyayya ya shiga juya harshensa cikin bakinta,Su'ada dai tun ba'a so har jikinta ya fara sauyawa,dole ta mik'a wuya.sun tabbatar sunyi kewar juna fa,don basu tab'a d'aukan wannan lolacin basu gamu ba tun auransu,amma gashi tunda ta fara laulayin nan kusan wata biyu basu had'u ba,duk suna buk'atar juna, dole su ka zage su ka more junan su.

Da safe Su'ada ta had'awa Khaleelee kayan break fast,sannan ta shiryawa Baba nashi,ita kam k'ullin k'osan data nik'a a blander shi ta d'iba ta d'aura alala guda biyu ta zabga attaruhu,sai kunun gyad'ar data damu musu ita ta zuba nono da yawa a cikin nata,don yanzu kullum wannan shine abun karyawarta,da rana kuma zuwa dare ayi ta shan faten tsaki.

Bayan tai wanka ta shirya Khaleelee daya taimaka mata wajan aikin shima ya shiga wanka bayan ya gyara d'an tsakar gidan nasu da ya b'aci da toka, dake har lokacin bata son warin gass a gawayi duk tai aikin.

Basu zauna karyawa ba Su'ada tace "Bari na duba Baba sai na karya."

Mik'ewa shima yai ya d'auki kayan break d'in Baban yabi bayanta.

Idon sa biyu yana zaune yana lazimi da carbi hannunsa.

Da sallama Su'ada ta shiga d'akin,cikin fara'a Baba ya d'ago ta kalleta,sannan ya Shafa addu'ar da ya ke,cikin sakin fuska sosai ta amsa sallamarta,bayan ta zauna ta gaidashi cikin girmamawa,kallo d'aya za kaiwa Baba kasan yaji dad'in dawowarta,don haka da Y'ar dariya yace"Ah masha Allah lafiya ta samu, sannu kinji,da asuba Jabeer ke fad'a min kin dawo jiya ina bacci,ya kika baro mutan gidan? "

Kanta a k'asa ta amsa da duk suna lafiya suna gaidashi,nan tai mai ya jiki ya amsa itama yana k'ara tambayarta ga nata jikin,bata iya amsawa ba don nauyi taje ji,Khaleelee ne ya matso kusa dashi sosai yana gaidashi da mai sannu sannan ya bud'e mai abincin yana fad'in "Baba ga girkin Y'arka ya dawo."

Dariya Baba yai yace "Su'ada daga dawowa sai d'ora tukunya? To sannu Allah ya k'ara afuwa da k'arfin jiki."

A zuciya ta amsa da amin,sai Khaleelee ne ya amsa a zahiri.sun d'an zauna su ka fito,nan Su'ada ta tsaya su ka gaisa da Sakeena shima Khaleelee ya gaidata sama sama,don yanzu Sam bata birgeshi a komai.

Bayan sun koma sashinsu su karya,su nayi suna hira,Khaleelee yau cir bai fita ba yana nanik'e da Su'ada,ita kanta Su'ada bata tabbatar tai kewar mijinta haka ba sai yanzu,don haka itama take ta mak'ale mai tana zuba shagwab'arta.

**************
Kwanaki na tafiya watanni sun yi nisa zuwa yanzu ga cikin Su'ada ya kai wata tara, haihuwa ake jira yau ko gobe da ikon Allah, batun kayan haihuwa fa ba abunda basu siya ba,Khaleelee yayi bajinta sosai,don ya had'a duk abunda ake buk'ata, koda Su'ada tace zata sai wani abu da kud'in ta sai yace A'a ta ajiye kud'in ta shi hakkinsa ne ya saiwa y'arsa komai,daman sun ui scanning an tabbatar musu da mace ce,don haka duk siyayyar su ta mace su kai.

Yayar Abbansu ce tazo daga can darki zata zauna da ita,amma bata zo gidan ba tana can gidan su Su'ada sai an yi haihuwar zata zo.

***********
Tun farkon wata suke sa rai da haihuwa,don abunda edd d'inta ya nuna farkon wata zata haihu amma gashi wata har ya kai kwana ashirin shiru,da farko Khaleelee ya tada hankalinsa amma a sanar da Mama sai tace ba komai daman yana haka ba lalle yanda edd ya nuna ake haihuwar ba hakan iko ne na Allah, amma dai su k'ara zuwa ga likita,to sun koma asibiti akai gwaje gwaje komai lafiya kawai lokacin fitar Babyn ne bai ba,sai a lokacin hankalinsu ya kwanta.

*******
Yau ashirin da bakwai ga wata, Su'ada na zaune Khaleelee nata matsa mata k'afa, don duk sun kumbura,duk da cikin bai wani k'ato ba amma ya kumburata,kallon Khaleelee tai idonta na cikowa da hawaye tace "Khalbee Wallahi cikin nan ya dameni,nauyinsa nake ji kamar kamar me."

Matsowa yai jikinta yana shafa kanta a hankali yake magana cikin kwantar da hankali yace"Ki daina cewa kin gaji dashi kinji pretty, ibada kike yi,kuma Allah yana baki ladan wannan wahalar da kike sha,sannan ki k'ara hak'uri kan wanda kikeyi,lokaci ne a sannu Allah zai kawo mana Babyn mu lafiya,fatanmu Allah ya rabaku lafiya,ki kwantar da hankakinki kinji."

Gyad'a kai tai tana maida hawayen daya cika idon.
Ci gaba yai da rarrashinta cikin kwantar da hankali yana shafa kanta,daga baya yaci gaba da mammatsa mata k'afar har ta fara gyangyad'i,kwantar da ita yai yana k'ara matsa mata jikin kafin shima baccin gaba dashi.

Can tsakiyar dare Khaleelee ya fara jin nishin Su'ada tana kiransa,kamar a mafarki yake jin ta,can yaji ta k'ara kiransa cikin muryar kuka,da sauri ya bud'e ido,amma dake d'akin sa duhu bai ganin komai don haka ya lalubo makunnar glop ya kunna,da sauri da diro a gadon hangota da yai a k'asa tana ta murk'ususu.rik'o ta yai yana salati da fad'in "Su'ada mene ne,me ya sameki ?"

Idonta a runtse tace "Marata ke ciwo, ka taimaka min don Allah."

Gaba d'aya ya rikice ya rasa me zai yi ma."

Rik'o hannunsa tai cikin dauriya tace"Ka bani wannan ruwan addu'ar da umma ta kawo,tace da naji ciwo in sha."

A rikice ya tashi ya d'auko mata gorar ruwan tare da d'ago kanta tai bisimilla tasha ruwan.

Tofa ciwo yace gashi zuwa,tun suna abu su biyu a d'aki har ya fita ya sanar da Yaya Muktar yace zaije ya taso wani abokinsa me adaidaita su wuce asibiti.

Yaya Muktar ya taso Sakeena yace taje wajanta,sannan yabi Khaleelee su ja fita zuwa k'asan layinsu,Usman abokin Khaleelee su ka taso a shagonsa,ba b'ata lokaci ya fitto adaidaitarsa daga garejin da yake ajiyarta,a ciki ya d'auko su suka k'araso k'ofar gidan.

Zuwa Lokacin Su'ada tai lak'was, da sauri Khaleelee ya ciccib'eta ya sata a daidaitan,sannan ya dawo ya d'auki akwatin da suka had'a kayan haihuwar, Ita da Sakeena a baya shi ya mak'ale a gefe su ja tafi yaya na mata addu'ar sauka lafiya,basu tashi Baba ba sabida jikin nasa ba dad'i, shi kuwa Jabeer uban y'an nauyin bacci duk bai ji abunda ake ba.

*********
Dake a asibitin gidan zoo take awo BA nisa tsakani su ja k'arasa, da gaggawa aka amsheta zuwa labour room,Sakeena da Khaleelee na zazzaune suna dako,Wanda zuwa lokacin ilahirin jikin Khaleelee ya gama yin sanyi,don sai yake jin kamar wani abune zai sami Su'ada, haihuwa na bashi tsoro, yanda yake ganin mata na matuk'ar shan wahaka.

Har aka kira salla shiru, yaje masallaci yai salla ya dawo,Sakeena ma cikin masallacin mata ta shiga tai sallar, har gari ya waye ba labari, yaya Muktar nata kiran waya amma sai suce shiru,wajan k'arfe bakwai Allah ta sauketa.

Khaleelee na can gefe a zaune ya dafe kai,cikin addu'a ya rasa wacce ma zai yi,yaji wata ma'aikaciyar asibitin ta fito tana fad'awa Sakeena ta sauka an sami y'a mace,ai a d'ari ya k'araso gareta yana fad'in "Da gaske ta haihu?na godewa Allah, amma ta take yanzu ya jikin nata ?"

Cikin kwantar da hankali tace mai "Eh ta haihu an sami mace,zamu gyarasu yanzu,anjima zaka gansu,duk suna cikin k'oshin lafiya.

Cikin murna yai taiwa Allah godiya,sai a sannan ya samu damar sanar da Mama, cikin farin ciki tace gata nan zuwa asibitin ita dame kula da Su'adan,bayan ya kashe ya kira Yaya Muktar ya sanar dashi,nan kuma ya shiga kiran y'an uwa da abokan arzik'i yana sanar dasu haihuwar,kowa murna yai ta tayashi da addu'ar Allah ya raya.

Kafin k'arfe takwas mama da Innaro su ka 'karaso asibitin.

*Taku ce*
*Y'ar mutan Ja'oji*
[2/24, 12:02 AM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭

*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*

👩🏻‍💻👨🏻‍💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_

*Ina barar addu'a daga bakunanku masu albarka*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.