Aindo Part One Complete Hausa Novel
Reading file: Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part One Complete Hausa Novel.txt
Chapter 44 of 44
*PAGE 87-89*
Bashir ne zaune gaban Dr a rikice inda Bashir yaje Dan neman sanin meye matsalar sa da har yanzu kusan shekara daya da aure anma matar bata samu ciki ba,bayan tazo anyi musu duk gwajin da ya kamata yanzu results ne yazo amsa,Dr yace"Bashir kayi hakuri a gaskiya a yanzu ita Matar ka lafiya lau take kai daine dama a kashi dari kashi daya ne ake sa ran koin haihuwar sa zai iya samun d'aa,gaba-daya Kashi 99 din nan kwayoyin haihuwar sa bazasu iya Samar da ciki ba a mahaifar mace,dan haka dama tun can Allah ya nufa koin sa daya ne a duniya wanda ake sa ran zai iya haihuwa.
Nan Dr ya fara basa hakuri, gaba-daya hankalin Bashir ya tashi,kuka ne ya kufce masa yace"innalillahi wa'ina illaihi Raju'un Ya Salam,biyu biyu ya fara gani anan take ya suma taimakon gagawa aka basa,Saida yayi awa daya ya farko.
Kuka yake Yana fadin" na cuci kaina ,ya Allah, Allah ka yafe min,Aisha Ina zan ganki Aisha ki yafe min nasan Alhakin ki ne har yanzu ke bibiyata ,ya Allah ga shinan na zubar da dana dan Halak ban sani ba ashe shi kadai ne koi na a duniya Allah ka yafe min Aisha Ina zan ganki."
Kuka yake kamar ransa zai fita,kasa tafiya yayi dole sai kaisa gida akayi.
Acan ya kuma tarar da tashin hankalin da ya kara fitar dashi hayacin sa,wato Mai gadi ya iske yau a falo yana fasikanci da matar sa tsirara haihuwar uwar su."
Kusan faduwa yayi saboda wata muguwar juwa ce ta kusan kwashe sa,Rai a bace ya nufi kichen ruwan zafi ya dora duk da baya gani sosai saida suka tafasa sannan ya d'auko su,Mai gadi na sex da matar sa ya watsa musu ruwan wanda ya fida su hayacin su suka zuba wata irin kara mai rikitarwa,a take fatar jikin su ta fara sabewa.
Mina saboda bala'i Sam ta wani manta da d'aukan magani hakan yasa ta kwanta cik'in muguwar rashin lfy inda dama ba wani damuwa sukayi da ita ba ,ganin sai ramewa take abun ya basu tsoro suka kore ta,ta koma yawo lungu da sako yan iska na kwana da ita subata naira dari ko naira dari biyu,saboda bata shan magani kuma gashi bata samun taci abinci mai rai da lafiya da gina jiki,haka aka wayi gari aka iske ta a wani kwango bayan wasu yan daba sun cita aka iske ta mutu har ta fara kumbura,Allahu Akbar haka Allah ke Al'amarin sa,gadai yanda k'arshen Mina yazo .
Bashir bayan ya zuba musu ruwa ya fita neman inda zai samu Aisha ya neme ta gafara,anan ne akace masa suna asibiti dan yau ta haihu da asuba.
Ji yayi kamar ya mutu tsabar bakin ciki,da yanzu yana tare da matar sa da Yarsa ko dansa.
Yana kuka da k'yar ya samu ganin Hajiya ya roke ta gafara tare da masa Alfarmar ganin A'indo da A'lhassan ya neme su gafara,anan ne Hajiya tace ta yafe masa,da kanta ta jasa sukaje asibiti,a lokacin da yaga A'INDO da Alhassan kusan Suma yayi tsabar kyau da yaga ta Kara,ga kuma babyn su mai kyau,Dana sani Kam yayi sa,da kuka ya duka Yana neman su gafara, Al'Hassan so yayi ya kore sa Saida Hajiya ta tsawatar sanan A'INDO tace"ta yafe masa,yaje ya nemi gafarar Allah.
Yana kuka ya koma gidan sa Yana zuwa yan sanda suka damke sa.
Khalissa ta auri wani Abokin Alhassan suna zaune hankali kwance.
Inda Halissa ta koma ga mijin ta yanzu Kam ya nutsu Yana nuna mata tsantsar soyaya.
Lamarin soyayar A'INDO da Alhassan kullum saide ya karu baya raguwa, Al'Hassan yana son Matar sa da dansa Sosai shi abun har tsoro yake basa saboda son da yake musu,inda a yanzu ya kuma samun girma,yanzu baya zuwa daji saide ya tura wasu,dan ya dawo ma kasar sa da zama wato Niger.
Suna zaune lfy lau Hankali kwance zuciya zaune,inda aka gabatar da biki Wanda har kasashe maganar bikin ake tsabar haduwa.
Alhamdulillah
Masha Allah anan na kawo k'arshen wanan litafi Ina fatan kuskuren dake ciki Allah yafe min ,Ina matukar godiya ga masoyana Yan wattpad ,Yan WhatsApp ,Yan Facebook,Ina godiya ga yanda kuka bi labarin Nan nagode sosai Allah ya barmu tare 🥰😘
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.