Aindo Part One Complete Hausa Novel
Reading file: Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part One Complete Hausa Novel.txt
Chapter 13 of 44
*Page 23-24*
Juyowa A'indo tayi ta murguda masa baki, sanan tace"wai kai ni ba matar ogan ka bace da zakana takura min."
"Uhum su mata manya,adai yi mu gani idan tusa zata hura wuta."cewar Rabi'u
"Tsab ma kuwa zata hura,ba kamar idan mai kara ce irin daidai tasu hajiya🙄."
"Au na manta sarakuwa ta ce🙊."
"Nikam naga ranar da zaki natsu kinata kwala min kira, sai kace kin biyoni bashi"
Cewar Hajiya da take saukowa daga saman bene,"yauwa Hajiya so nake ki ranto min naira dari zan sayi dan ta matsitsi ,da agwalima,da gyada,sanan canjin zan karo dusa saboda dan taren da nake😁 ."
"Shine kike famar kwala min kira haka,Allah ya shirya ki,baga mijin ki ba can kije ki tambaye sa mana."
Cewar Hajiya,ta fada ne Dan tasan bazata iya zuwa ba,zataji tsoron sa,anma ga mamakin ta sai taga A'indo ta fita da gudu tayi b'angaren Alhassan
A falon sa ta same sa zaune,har yanzu ya kasa tashi ,ga kup din juis wanda yake Sha an akawo masa mai sanyi anma ya kasa sha saboda damuwa,shigowa falon A'indo tayi ,daga k'ofa ta tsaya,kafa daya a cik'in falo daya a k'ofa,tace"soja nazo ka bani kudin dan tamatsitsi, Hajiya tace nazo na amsa gun ka dan Kaine miji na🙈"
Dago da kai yayi yana kalon ta kuma yaji sarai abinda tace banza yayi da ita dan ya d'auke ta mahaukaciya,wata dabara ta fado masa yace mata "zo ki amsa."
Make kafada tayi tace"jeho dai ni ai ba A'indon mahaukata bace da zanje salon ka kuma jibga ta ."🙄
"Ke ina wasa dake ne,idan bugun ki zanyi kin isa ki tsere min ne,kizo magana zamuyi idan ba haka ba wly idan na tashi sai dukan yanzu yafi na ranar."
Da gudu ta karaso kusa dashi kadan ta dan tsaya tace"gani."
"Yauwa ai kudi kike so ko,zan baki masu yauwa sosai,wanda zakiyi ta ci har k'arshen rayuwar ki,anma da sharadi daya,shine kije wurin mahaifi na ki aza kuka kice a raba auren mu susa na sake ki."
Dariya A'INDO ta kece da ita tace"hahhh idan wanan ne ai mai sauki ne,yanzu dai na fara jin dumus,ta fada tare da Tara masa hannu,ta hada yawu ,saboda juis din da ta gani ,zama tayi ta d'auki na cup din ta shanye tas,shiko tsabar farin ciki bai hana ta sha ba.
"Tab aradun Allah Aljannar duniya na ga masu kudi,yau wanan irin dadi haka,dan Allah dan Karo min tace😁😋,kara mata yayi tunda shi ke nema,tana shanyewa zatace a karo mata,saida ta shanye juis din baki daya tayi gyatsa,sanan tace"yauwa,to bani kudin,cikin farin ciki zai rabu da kaya ya fido dubu biyar ya bata,amsa tayi tace"wo kai wo kai,😁yanzu ko zan fada ma su hajiya,."
"Yauwa yar kirki maza je kice baki so na ,in ta kama ma kiyi musu kuka."
"🤔 Kuma fa kana da gaskiya,bari kaga na tafi."
Da gudu tabar falon,yayyin da shi kuma yaji wani sanyi a ransa,zai rabu da jangwam ."
A'indo saida takai bakin kofa ta juyo ta duka ta juya baya tace" soja soja saida ya daga kai yana kalon ta ,ta duka tana karya kugu fadi take ka gani ka gani kwalelen ka,sanan ta tashi ta murguda baki 😗 tare da masa gwalo 😝ululu ululu tace" kuma wly bazan rabu dakai ba mutu ka raba takalmin kaza ,kuma bazan ce bana sonka ba,an fada ma ni A'indo mahaukaciya ce,nace banson saurayi kamar ka,dan subulbuli tab aradun Allah ina sonka,salon kamin asarar k'yawawan yara🙈,to inason ka 🙄."
Tana gama fadar haka ta arta a guje tabar wurin,shikam takaici ya hana sa tashi daga gurin,zuwa tayi ta adana kudin ta, a d'akin ta sanan tayi falon hajiya.
Da gudu,Hajiya na falo tace"Hajiya ya fa bani kudin,in fada miki hajiya har fa cewa yayi yana so na 🙈."
"Tab kaji karya ,a mafarki ba."
Rabi'u yace tare da tabe baki.
"Kuma Hajiya ya bani kudi yace nayi sayaya saboda banida kaya."
" Tab a gidan mahaukata ba"
Rabi'u ya kuma fada,
"😏wai kai Rabi'u ni ba uwargidan ka bace,me yasa ka Raina ni"
"Ta mahaukata ba "
Wacece ta mahaukata?
Ta kuma tambayar sa."
"Uwar gidan mana,kince ke uwargida na ce naga ke kam ai saide uwar gidan mahaukata anma ba ta mutane ba."
Rabi'u yace cik'in maganar mata.
Hajiya tashi tayi tabar masu wurin dan tasan idan suka fara ba mai tsayar dasu.
Bayan kwana biyu,dole tasa Alhassan yin abinda Mahaifin sa yace,wato nema ma A'indo passport da duk wani abun bukata,ya rage saura kwana biyar su tafi.
A'indo ta tashi yau dan d'aukan kudin ta ta nema ta rasa su,can ta hango wani dan lungu a d'akin ta kusaye suna ida jan sauran kudin ta suna sawa a lungu."
Tafowa tayi lungun taga kusaye ne suka d'auke mata kudi, sukasa a lungun,kuma duk sun cicire kudin."
🙆hannu ta aza bisa kai tare da fadin "kut ,yara yau aradu kun taro fada,sai kunsan kun sace kudin A'INDO Tantagariyar Yar Aiki,wly da masu kama mutane zan hada ku dasu."
wajen Rabi'u daudu ta nufa,da gudu yana falo zaune yana kalo,Husseina kuma ta fita yawan ta ,tunda ta san idan ta fita zata gane hanyar gidan shi yasa yanzu sai ta fita yawan ta ko ita kadai ce in ta gama ta dawo,to yau ma hakane,Zuwa A'indo tayi tace"dan Allah Rabi'a ki taimaka ki rakani wani waje."
Sakaka da baki Rabi'u yayi ,yace"yau naga abin mamaki 🙄keda Kika canza min suna Kika maida ni jinsin maza yanzu shine dan dibar Albarka taki ta kawoki zaki wani mak'e min murya kice"wai Rabi'a,to fada min meye ne?
"Dan Allah kiyi hakuri,haba Rabi'a, dan Allah kiyi hakuri ki rakani,kar su hajiya suji,dan aradun Allah idan taji bazata bari a kama azalumai ba,kai barayi keda koi a gidan nan kuma manya manya ."
"Ke dan Allah a Ina kika gansu,😨?
Rabi'u yace cik'e da tsoro.
A'indo tace"shi yasa nace maka muje ka rakani tun kafin
su ganmu.
Tashi Rabi'u yayi ya kara d'aure zanin dake kirjin sa,ya kama haba,yace" a lale abun ba na zama bane muje,fita sukayi daga gidan, Rabi'u ya tsaya yace"yanzu ina zamu fake,har su gama hatsaniyar su sai mu koma."
"A'a
" Yanzu Ina ne ya kamata muje mu samo wa'inda zasu kama su kaga sai muyi maganin su "cewar A'INDO
"a kinada gaskiya,muje police station,muzo dan yan sanda su kawai zasu kama su,kinga dadin sodja a gida da ace yana garin da shi zamu fada ma yasa sojawa su kama su."
Cewar Rabi'u."
"A Kai manya manya ne fa😨"cewar A'INDO."
A haka suka isa police station dake kusa dasu,suna zuwa A'INDO tace"yauwa ranka ya dade wly barayi ne suka shigo gidan har d'aki sukayi sata idan suka gama kuma d'akin Hajiya zasu haura,dan Allah kuzo muje a kama su."
Dan sandan da suka fada ma yace"kun tabatar da barayin suna Nan, A'INDO tace"kwarai ma kuwa,yauwa ku fada ma A,S,P ,cewar akoi wasu barayi a gidan wa dan sandan ya tambayi Rabi'u,
Rabi'u yace"Ranka ya Dade a gidan Alhaji Sanmani ne."
Waro idanu yan sandan sukayi sukace a 'a dole aje da mota biyu,dan duk barawon da zai shiga gidan ba karamin barawo bane,kuma darana.
Nan aka hada mota biyu tare da yan sanda suka tafi gidan,A'indo ce tayima dayan magana tace "yauwa ranka ya dade ni nasan inda suke muje na nuna muku,suna cik'in d'aki na,nan yan sanda suka fara bazuwa a gidan suna fakewa,hata body gards din Saida aka fada musu wai su ankare akoi barayi a gidan,A'indo tace"yauwa ranka ya dade zo ka gansu,su uku suka nufo d'akin nata rike da bindiga a hanun su,suka bankado d'akin "yauwa ranka ya dade ga lungun nan nasu ta nuna lungun da kusaye ke gurin,taga naira dari biyar dinta da kusaye suka cicinye suka fito dasu
Tace"la ranka ya dade kaga sauran kudin,wly ban yarda ba a biyani haki na,ka kama su su fido min kudi na,😭
"Ke shut up,karki maida mu kananan yara ina barayin suke?,daya daga cik'in yan sandan ya buga mata tsawa."
"🙄 Kaji ranka ya dade in banda abunku,mutum ya kawo ku wurin barayi kuma kuce ya nuna muku su,to baga lungun su ba ku kama su mana,Dan wly sai sun biyani kudi na🤨
Aci gaba da gashi🍇
Maimou love😘
[10/10 à 17:34] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨
✨
*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋
*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚
*DAGA AKALAMIN MARUBUCIYAR*
👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*
_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_
_Masoya na asali kuma magoya bayan mu,ni Maimouna Matar_ _Abdoulahi ina nan tafe tare da baban kuma mashahurin litafi na Mai suna *YAN GATA NE*,wanda yake d'auke da abubuwa mai matukar amfani garemu_ _Mata,litafi ne mai cik'e da abubuwa,wanan litafi ya kunshi abubuwa kamar haka ,👉iya kwanciya a gidan auren ki,iya kula da mijin ki,kissa,kishi cik'in ilimi,ba tare da mace ta maida kanta_ _mahaukaciya ba saboda kishi,magance matsalar da ta adabe ki ta namiji,kama da komai ma da Mata ke fuskanta a wanan zamanin,a gaskiya tsayawa zana abinda wanan litafi ya kunsa bata lokaci ne,shi yasa na baku kadan daga ciki,duba ga yanda idan har na fara rubutasa a_ _Free to nasan abinda zai biyo baya,dan nasan za'ace ina rashin kumya,nayi batsa,hakan yasa duk wada take son karanta wanan litafin zata biya Naira dari biyu,sanan wanan litafi na matan_ _aure ne kadai,dan Allah duk wace tasan budurwa ce bana gayatar ta ,sanan bana bukatar kudin ta ko shigar ta wanan group din,in ko kika shiga ba ruwa na🤷♀ Allah yana gani na fita hakkin ki,domin wanan litafin ,na karuwar matan aure ne kawai sai kuma wa'inda zasu shiga daga ciki ma'ana wa'inda aka kusa auren su,karku bari a baku labari,Naira dari biyu kacal zaki biya ki more rayuwa tare da_ _gyara halakarki gami da zamantakewar auren ki,Litafin_ _*YAN GATA NE*_
_Yana nan tafe_💃💃💃
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.