Aindo Part One Complete Hausa Novel
Reading file: Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part One Complete Hausa Novel.txt
Chapter 16 of 44
*Page 31 -32*
,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,Alhassan doctor yasa ta duba hannun Linda,tace gocewa ne tayi,nan aka gyara hannun Linda,sanan aka bata magani.
Ranar anan tare sukayi barci Alhassan da Linda,yayyin da A'indo ke can d'akin kare,wahala da zafi ya ishe ta,domin kuwa Alhassan da kansa ya hana a kunna A.C sanan yace kar a saki a kunna mata panka,idan kaga yanda A'indo ke kuka sai ka tausaya mata,tsabar wahala,in banda sunan Mahaifin ta ba abinda take kira,ita kam yanzu ba abinda tafi bukata kamar ta koma wajen mahaifan ta.
Washe gari Abass ne yazo gidan cik'in shirin sa shima na sojoji,a falo ya tarar da Alhassan zaune yana kalon Tv yana shan coffee.
Ko kalon inda Abass yake baiyi ba,zama Abass yayi yana dariya.yace
"Haba abokina me yayi zafi haka,har kazo gari ba tare da ka sanar min ba,saide naji a bakin wasu,gaskiya banji dadin hakan ba,me yasa baka sanar dani ba"?
"Saboda na tsane ka"
Alhassan ya basa amsa .
Zaro idanu Abass yayi cik'e da mamaki ,yace"Alhassan ni ka tsana bisa kan wane dalili"?
" Wani kallo Alhassan ya watsa ma Abass yace"saboda a ranar da kayi min baki a ranar ya kama ni,yanzu kamar ni ace an aura min yar kauye ,kauyen ma kauyen kayyau,jahila,munana , marar aji jaka,tunkiya,ai wly Abass Allah ya isa tsakani na da kai,saboda na tabata bakin ka ne, anma ba matsala,ni bazan iya zama da ita ba zan barta ne ta wahala,da kanta zata gudu,kowa ma ya huta."
Sake da baki Abass yayi yana kallon Alhassan sanan daga bisani yace"kai ni fa ban gane abinda kake nufi ba,kana nufin aure aka maka"?
"Dan Allah malam bana son munafurci baka saniba,tun a ranar da kayi min baki a ranar Daddy ya sanar min wai ya aura min yar aiki kuma yar kauye jahila."
Me ko Abass zaiyi baicin dariya, dariya yake kamar Allah ya kawo,abinda ya kara kullar da Alhassan kenan,tsaki yayi ya tashi ya bar falon,Abass saida yasha dariyar sa sosai tukon ya tsagaita,yace"tab anma wallahi Daddy ya burge ni,ai Alhassan anyi maganin ka,ace mutum bai d'auki dan kasar sa a bakin komai ba, ace ka raina matan hausawa,bayan taka mahaifiyar bahausa ce,ai wallahi zaka gane."
Abass yana gama fadar haka ya tashi ya fita motar sa ya shiga yayi compagni na sojoji.
Alhassan ma kayan sa yasa na sojoji sunyi matukar kama sa sun masa kyau,dogon mutum,mai kyan sura,a gaskiya kakin ba karamin kyau suke masa ba,ko mazan idan suka gansa burge su yake,bare kuma mata da suke haukan sa.
Shiryawa yayi ko takan A'indo baibi ba ya nufi wajen aikin sa.
A takaice dai A'indo saida tayi sati a wanan d'akin ba tare da wani abincin kirki ba,saboda abinci ma sau daya take ci a rana, gaba-daya zafi ya feso mata da kuraje a jiki,tayi baki ta rame,ga dauda ta kara rine ta.
A yau ne Alhassan yace a fito masa da ita,fido ta akayi duk tayi yaushi ta rame, wulak'antacan kallo ya watsa mata, sakamokon wani wari da yaji tanayi,saboda rashin wanka,done hanci yayi ya nuna ta da yatsa yace"abinda zan fada miki shine daga yau wanan d'akin da kika fito nan ne d'akin ki,na yarda ki dinga amfani da panka,anma banda A.C, kuma duk wani aiki da kika sani kama daga gyaran falo,wankin b'andakin gidan nan gaba-daya har na waje,sanan motocin gidan nan da fulawoyin gidan nan ke zaki dinga wankewa,kiba fulawa ruwa,wankin motoci ko baki iya zaki dinga wankewa ,sanan wankin kayana,akoi mashine a gidan nan anma da hannu zaki dinga wankewa, kuskure daya kikayi sai na saba miki,sanan abinci sau biyu zaki dinga ci a gidan nan,kamar yanda a kauye nasan ance kuna cin rama da tuwo,to akoi su a d'akin da zaki zauna,naso ma ace kin aza a itace,anma bana son a bata min gida shi yasa ga resho can ke zaki dinga yin abincin ki ke kadai,sanan wly wly naji kin bud'e bakin ki kince ma wani ke matata ce to wallahi sai na saba miki,wancan karon sati daya kikayi a duhu da zafi da yunwa ko,to wanan karon wata zakiyi har sai kin mutu an bine ki."kararawa ya danna,sai ga mai wanke motoci da mai ba fulawa ruwa,da mai wankin bayin gidan sunzo,nan ya umarce su da kowanne ya koya ma A'indo aikin sa,idan ta koya su bar mata ita zata dinga yin ayukan,sanan su zai basu wasu ayukan."
Godiya sukayi suka tafi,kallon sa na tsanar ta ya watsa ma A'indo yace"kuma bara kiji b'andakin gidan nan na waje wanda maza suke wanka suyi komai a ciki,to kema can zaki dinga wankan da komai ma,sanan naji ance kin kula wata hallaka da mace ko namiji a gidan nan to wly sai kin azabtu,babu fita,ke ko magana Kar na Kara jin kinyi a gidan nan,kin fahimta"!
Ya daka mata tsawa,a matukar tsorace A'INDO ta kada kai tace "eh" cik'in rudu. domin kuwa yanzu A'indo tayi matukar tsorata,ko kallon sa bata son yi,domin kuwa ya zame mata wani dodo....
Cik'in ranta take ayyana ranshin tausayi da rashin mutunci irin na Alhassan,yanzu ita da karayar ta a hannu yake son tayi wa'inan ayukan,wasu hawayen tausayin kanta suka zubo mata,korar ta yayi daga falon,wai ta bar gurin wari take,har done hanci yake,yana kwagirar ta,tare da kyama,tashi A'indo tayi tabar falon,haka ta tafi b'andakin tasa soso da sabulu na b'andakin da hannu daya ta fara wanka,a haka ta samu ta gurza jikin ta tayi wanka,ta sake kayan da ta taho dasu,na kauye duk da tana jin zugin da hannun ta yake mata haka ta fito,sai ta koma tamkar ba A'indo ba Tantagariyar Yar Aiki,sai ta zama A'indo abun tausayi....
D'akin ta ta zauna ,tayi tagumi,gari rogo ta gani kusan rabin buhu,nan ta ga suga,da garin tuwo,komai dai irin na karkara akoi a gurin,diba tayi ta jika garin tasa suga ta motse ta fara sha,saida taji cik'in ta ya cika tukon ta dan kwanta,kwancin ta keda wuya aka buga k'ofa,a matukar gajiye ta tashi ta fito ,"yauwa oga yace kizo a fara koya miki ayukan da akace ."
Murguda masa baki tayi,tace"hum wly bakuda tausayi,da hannun daya zanyi aiki."
"Ok bari na fada masa."
"a'a yi hakuri muje ."
binsa tayi,ya nuna mata yanda ake wanke motoci,ya kuma nuna mata kowace mota da fanar da ake shigar ta,kuma tun k'arfe shida na safe ake tashi a wanke ma oga motar da zaya fita da ita,ya nuna mata duk sabulan da klin din da ake wankewa ,da kuma yanda ake wankewa....
Saida ya tabatar ta gane,ya nuna mata wace za'a wanke yanzu,tausayi ta basa yace"hannun ki daya bayada lfy ne?
Kai ta kada masa tare da cewa"karaya ce."
Tausayi ta basa yace"kuma a haka zakiyi wankin."
Marairaicewa A'indo tayi tace"to ya na iya."
"Ok karki damu bara na miki,tunda oga yanzu yana wurin aiki,ke kuma ga ayuka sun miki yauwa."
Godiya sosai A'indo tayi,nan mai wankin bayi yazo shikam ba tausayi ya nuna mata komai nan ta fara wankin da k'yar,har saida ta wanke b'andakin gidan kusan guda shida. Sanan ta bawa fulawa ruwa,duk da hannu daya,kuka kam tasha yinsa,wanan bauta ita A'indo take yi duk wani shirme da wawanci ta aje su gefe,nace hum ashe shirme ma wuri garesa,idan kaga yanda A'indo ta dahe ta lalace tayi baki,ko kai waye sai ka tausaya mata,hannun ta kam kullum sai tayi kuka akan sa,saboda badan Allah yana tsarewa ba,da tuni gyaran ya lalace,abinci ko batada wani abinci sai garin rogo,shi take ci tasha.
*Bayan sati biyu*
Alhassan ne yake horn a bakin k'ofa aka bud'e masa A'indo ya hango tana wanke motar sa,take yaji duk wani farin cikin sa ya gushe,motar ya kara ma wuta da gudu yayo kanta, ganin haka da gudu A'indo ta gusa, cik'e da tsoron abinda taga yana shirin mata jikin ta na rawa.
Parking din motar sa yayi ya fito fuskar nan kicin-kicin, gadan gadan ya nufo ta,bai wani tsaya komai ba ya wanka mata mari yace"jahila baki ganin mota ne kika wani tsaya dan kin raina ni."
Hawaye ne suka zubo mata a kunci itakam bataga abun bugu ba ,kuma ai ta kauce kawai yana son cin zalinta ne."
Share hawayen ta tayi tace"yi hakuri."
Murmushi yayi na gefen baki,dan ga dukan Alamun horon da yake mata tana horuwa duba ga yanda ta lalace,ficewa yayi tare da bangaje ta,ta fadi akan hanun da ta karye,ta saki wata Kara saboda azaba,tsaki yayi ya kara wurgo mata kalon tsana yayi gaba, cik'e da farin cik'in yanda yaga ya kuntata mata....
Yau Mari itace da aiki a gidan,dan haka da gudu tazo ta kama A'indo ,tana hawayen tausayin ta,tace"haba,meyasa oga yake miki haka me Kika masa ne?
Share hawaye A'indo tayi tace"wallahi ban masa komai ."
"Ok to tashi muje d'akin ki,Kama ta tayi ta kaita d'akin A'indo ta duba hannun taga kamar ya dan gota kadan,ita ta kara gyara ma A'indo,saida tayi kuka kamar na fitar rai.
Yau Mina ce tazo gidan Alhassan,dan yau da kansa ya gayato ta,nan sukayi iskancin su,bayan sun gama suka fito falo,Mina tace"Alhassan wai dagaske kake zaka aureni"?
"Mina ina sonki zan aureki,zamuyi aure a boye,kaf Yan mata da suke so na kece nake jin zan iya aura,saboda ilimin ki,wayewa ga class ,inason mace haka,dan haka in ba damuwa inason auren ki,yau sati daya kenan da nayima iyayena magana akan auren anma sunki yarda,inaga kawai muyi auren mu ,daga baya sun huce."
Wani dadi Mina taji burinta zai cika,rungume sa tayi tare da cewa ta amince."
Tace"my Man zanje wajen wankin kafa."
"No karki damu bara akoi yarinya anan ta wanke miki k'afar tunda akoi komai na wankin ."
Sa wa yayi aka kira masa A'indo,da kyar A'indo ta tashi saboda zazabin da ya kamata ,jikin ta kamar garwashin wuta,haka ta tashi Idanun ta tuni suka canza kala,zuwa tayi ta duka tare da sunne kai tace"ranka ya dade gani."
Harara ya wurga mata,sanan ya kalli Mimi yace"tashi muje ta wanke miki k'afar ,tashi sukayi a wulak'ance ya kalli A'indo yace"ke!!!
Taso ,binsu tayi,wani baban d'aki ne sukaje ya tsaru gurin,d'akin gaba-daya duk wani abu da ya danganci wankin kai wankin k'afa,gyaran jiki irin na mata akoi sa,mayuka,turaruka,abun wankin kai ,kask komai dai na Salon na gyaran jiki akoi,nan yayi ma Mina kiss a baki sannan yace"yauwa nuna mata duk abinda zata d'auko ta wanke miki k'afar,wanan baiwar ki ce."
Cik'in kyama Mina tace "gaskiya wanan kazama ce ,anma zanyi maneji....
Aci gaba da gashi🍇
Maimou love😘
[10/10 à 17:34] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨
✨
*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋
*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚
*DAGA AKALAMIN MARUBUCIYAR*
👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
_and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*
_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.