Complete Hausa Novels

Aindo Part One Complete Hausa Novel

Reading file: Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part One Complete Hausa Novel.txt

Chapter 33 of 44

*Page 65-66*

Ihu take tana ya bud'e mata anma ina ko sauraran ta baya yi,ficewar sa yayi daga gidan ya nufi wajen Salman........

Salman na zaune a office dinsa Bashir ya Shigo rai a bace ya zauna .

"kaiko lfy kake?
Ka shigo ba ko salama."

"Ruwa Bashir ya d'auko a firge yasha ,sanan ya furzar da iskar bakin sa,yace"wai yar rainin hankalin yarinyar nan ni zata yaudara,taje can wani kato yayi mata ciki wai tazo tace ni na mata ciki ta ya ma za'ace ciki nawa ne bayan ina bata maganin hana d'aukar ciki kullum idan zan sadu da ita."

Salman yace"ban gane ba,dama Matar ka ba a budurwa ka same ta ba?

"A budurwa na same ta mana."

"To cik'in wata nawa ne da ita" ?
Salman ya jefo masa tambaya .

"Doctor yace cik'in wata biyu ne,kuma auren mu wata biyu ne da kwana uku a yanzu."

Salman yace "tun yaushe ka fara bata magani kafin ka sadu da ita."?

" Bayan kwana uku da auren mu."Bashir ya basa amsa kuma nan take ya tsaya cak da zancan sa yace" kenan a cik'in kwana ukun nan ta d'auki ciki na,tab wallahi bazata sabu ba,kodai ta zubar da cikin nan ko mu rabu,ni bazan iya zama da ita ba har na haihu da ita ba,kai wallahi a ma fida mahaifar gaba-daya yafi,zan bata duk wani kwanciyar hankali,da duk wani gata da take so ."

Salman zaiyi magana Bashir ya tashi ya bar Office din ya shiga motar sa yajata da gudu yabar wurin,gidan sa ya nufa,ya nufi d'akin da ya kulle ta dazu ya bud'e,kwance ya same ta ,kallon ta yayi ta dan basa tausayi yanzu yace"ki fito zamuyi magana ne."

Batada k'arfin jiki anma haka ta tashi ta fito,nesa da inda yake zaune kadan ta zauna,kallonta yayi da kyau,sanan yace"Aisha idan kina son farin ciki a gidan nan da kwanciyar hankali mu koma tamkar lokacin muna saurayi da budurwa,ki yarda mu zubda cik'in nan."

Share hawaye A'indo tayi tace"indai zan samu farin ciki daga wajen ka na yarda a zubda,in har ka yarda yanzu naka ne."

Murmushi yayi yace"haba ko ke fa masoyiyar ,ai haka ake so anma da kin tsaya taurin kai, yanzu shirya kici abinci
Akoi inda zamu inda za'a zubda."

Murmushi tayi tace"Bashir dagaske zaka koma kamar da idan aka zubar."

Murmushi yayi yace"fiye da da ma."

B'ANGARENTA ta nufa tana murmushi tayi wanka,ta sa doguwar riga wace take iya gwiwa,wani irin sha'awa take ji , wajen yanzu wata daya kenan tunda ta saba da sex yanzu take jin matukar sha'awa saide abun bakin ciki sam Bashir baya gushe mata sha'awar ta,baya tambayar ta tana gamsuwa ko kuwa,kawai shi in ya gamsu shikenan,a yanzu haka ma duk da tanajin yunwa,ga raunin dake jikin ta anma bata jinsa tafi jin sha'awar mijin ta.

Zuwa tayi ta zuba abincin taci ta k'oshi, sanan ta wanke bakin ta ta bare bonbon mai kamshi tasa a bakin ta.

Wajen sa ta nufa ta zauna kusa dashi tare da shafa jikin sa tana masa wani salo mai nuni da tana bukatar sa.

"a'a lfy dai kuwa keeee."

"Plz Bashir sau daya dai ka taimaka ka biya min bukata ta,wallahi ina cik'in bukata,kuma kai daga kayi kake tashi."

"Me kike nufi da hakan,kinga malama bana son rainin hankali,me kika d'auke ni,kije ki shirya muje nace miki bana ciki da rainin sense din ki ,in mun dawo na baki duk ma abinda kike so ."

Ba yanda ta iya haka ta hakura ta tashi ta shirya ta fito.

Katon hijabi tasa,dan tasan jarabar kishin sa wani private asibiti suka nufa,dama ya san doctor din abokin sa ne.

Suna zuwa Office dinsa sukaje direct ,bayan sun gaisa Doctor ya gaisa da A'INDO,nan suka dan taba yar fira,sanan daga bisani Bashir yayi ma Doctor signe da su dan tashi zasuyi magana ne .

Ganin Yanayin Bashir Wanda bata yarda dashi ba sai wani zargi ya tsargu a ran A'INDO ,Dan haka suna fita ta tashi itama ta bisu.wani Office na kusa da wanan suka shiga.
Ita kuma sai ta labe daga k'ofa
Suna zama Doctor din yace"haba Bashir me yasa kake son a juya mahaifar ,ai ka bari koda da daya ku samu da ita ko."

"Bashir yace"Abokina nifa ba haihuwar ce bana so ba a'a daga ita din ne dai bana son haihuwar,soboda bazan haihu da wace batada cikak'en asali ba,kuma wace batada cikak'en dangi ba,in ma akoi su yan kauye ne,kawai ka cire mata cik'in sai a juge mahaifar,inason yara anma ba daga gareta ba,zan auri wata wace take yar wani kusa wada kowa ya sani akasan asalin ta a birni ba a kauye ba,,yar masu kudi kamar ni."

"anma Bashir idan kayi haka baka kyauta ba,yanzu sai ka zabi juya mahaifar baiwar Allah,haba Bashir ai rashin imanin yayi yawa,ga cire ciki ga kuma juya mahaifa.

Gaba-daya wanan abu a kunnuwan A'indo,tabas yau ta shaida cewar Bashir baya sonta tabas yau tagane cewar Bashir ba masoyi bane makiyi ne,tabas yau tasan cewar Bashir shine asalin mugu ba Alhassan ba.
Share hawayen ta tayi tabar asibitin.

Keke napep ta tara ta fada masa unguwar da zai kaita,direct ya kaita gidan ta,ta shiga ta fido kudi ta fito ta basa .

Zama tayi falo ta hada Kai da gwiwa tana kuka kamar ranta zai fita,Bashir ba irin dubawar da basuyi ba basu ganta ba,sai mai gadi suka tambaya suka kwatanta masa mai kaya kala kaza, yace musu ta fito ta tari adaidaita.

Ran Bashir idan yayi dubu to ya baci dan haka bai ma tsaya sauraran doctor ba ya shiga mota ya fice daga asibitin,gidan sa ya nufa,tun a waje yake ihun kiranta,falo ya iske ta ta takure waje daya tana zabga kuka,.

Yana zuwa ya ganta baiyi wata-wata ba ya zuba mata naushi,Wanda ya sata kara sautin kukan ta,yace"dan ubanki Raina ni kikayi da zamuje wuri ki gudo ki barni.

"Allah ya isa tsakani na da kai Bashir ,kuma bazan zubar da cikin nan ba mugu."

"Ke ni kike ma wanan banzar maganar?

"An maka Bashir kayi abinda zakayi."

A'indo ta fada cik'in hargagowa da bakin ciki.

Belt din wondon sa ya zare nan ya fara lafta mata ,ba k'ak'autawa,"zaki bari a cire ko kuwa.?

"Wallahi saide ka kashe ni bazan yarda ba."

"Good good Aisha to bara kiji wallahi ko ki yarda ki tashi muje a zubar da cikin nan ko kuma na yanke igiyoyi uku dake tsakani na dake."

Duk da bala'in da take ji a marar ta Saida ta bud'e baki tace"na k'wanmace ka sake ni zanfi jin dadi,."

Zuciya na dibar sa,ransa a bace ba ko tsayawa tunanin yaje ya d'auko biro da takarda,yazo ya tsaya kusa da ita yace"damar ki ta k'arshe ko ki tashi muje a zubar ko na baki takardar sakin ki."

"Na fada ma ba inda zani kuma wallahi bazan zubar da cikin nan ba."

_Rubutu yayi kamar haka ni Bashir na saki Hassana matata saki uku,saboda na kama ta tana zina da wani namijin Wanda ba ni ba,kuma tayi cikin shege Wanda ba nawa ba._

Yana gamawa ya jefa mata takardar yace"ki tatara inaki inaki kafin na dawo ki barmin gida."

A kwance take da k'yar ta bud'e takardar ta karanta abinda ta gani yayi bala'in girgiza ta,waro idanu tayi a matukar razane tace"Bashir ni kayi ma shairin zina,kuma ka rasa abinda zakayi dogoro dashi sai zina."

Ko sauraran ta baiyi ba ya jata kiiiii sai waje ya yar daidai shigowar Husseina gidan,yayyin da jini ya balle ma A'indo anan take.....

Kuyi hakuri bana Jin dadin jiki na har yanzu kawai Ina dai muku ne hakanan da Babu gwanda kadan...
[04/11 à 19:38] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨

*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋

*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚

*DAGA ALKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
_and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*

_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.