Complete Hausa Novels

Aindo Part One Complete Hausa Novel

Reading file: Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part One Complete Hausa Novel.txt

Chapter 17 of 44

*Page 35-36*

Mari ce ta shigo dan ganin yanayin jikin A'indo duk da yau hutu take,anma ta kasa zama saboda itadai bata san me yasa ba A'indo ta shiga ranta,tana jinta tamkar yar uwarta dan haka ko breakfast batayi ba ta taho,a Lokacin tuni Alhassan yabar gidan,iske A'indo tayi rai hannun Allah numfashin ta na zuwa da dawowa,kamar mai asma,a rikice ta rugo da gudu ta iso ta talabo ta ta rungume,fadin take "Aisha Aisha mai ya sameki, innalillahi wa'ina illaihi Raju'un,aisha jini,kardai wanan mugun ya Kara miki wani abu,waya tayi mazan d'auka ta kira saurayin ta doctor,ce musu yayyi suyi mazan zuwa asibitin da yake,dan wanan abu dole sai anje asibiti,fita Mari tayi ta kirawo wata cik'in gards din tace su kama mata tasa A'indo motar da ta taho da ita ta kaita asibiti....

Mina ce ta fito,tana wani cin shuiwingwom tana harare harare, A'INDO taga an fito da ita ,zaro idanu Mina tayi tace"kai gidan uban wa zaku kaita,ku ajeta zan sata wani aiki ne."
Mari tace"kiyi hakuri madame zamu kaita asibiti ne batada lfy."
"🤨 Nace ku aje ta,baiwa dama tanada galihun da za'a kaita wani asibiti ne"?

Ku ajeta zan sata aiki ne."

Dayar ta saki A'INDO yayyin da Mari ta kara riketa gam,tare da cewa" Madame kiyi hakuri a yanzu wanan baiwar Allah tana bukatar ganin likita,idan ba haka ba komai zai iya faruwa."

"Ke har kin isa ina magana kina sa min baki,tare da yi min musu,to ki kiyaye ni, wallahi idan bakiyi abinda nace ba idan mai gidan nan yazo zaki iya rasa aikin ki."

"To sai me?
Ai indai dan zan ceci rai ne zai koreni a shirye nake,kuma ai Allah ba azalumin bawan sa bane,Nan ta fara jan A'INDO rai a hannun Allah,Mina idan ranta yayi dubu ya baci ,dan haka tayima gards din gidan maganar cewar karsu bari Mari ta fita da A'indo,aiko kata biyu suka tsaya a gaban Mari ,tare da maida hannuwa baya,sukaci fuska,dama Mari daga ita sai riga da wondo sanan kuma dama akoi bindiga karama a aljihun ta,fido ta tayi ta nuna su da bindigar tare da cewa "wallahi Allah idan har wani daga cik'in ku ya kuskura ya hanani fita to wly zan iya yin Ajalin sa,dan haka ku bani hanya."
Tabas sunsan Mari kwarara ce,kuma zata iya domin kuwa idan ranta ya baci babu wanda bai san halin ta ba,dan haka ba shiri suka gusa suka bata wuri."

Hucewa tayi tasa A'indo a mota suka bar gidan a guje a tsiyace,Mina kam tsiza yatsa tayi tare da jin haushin wanan Marin sanan ita kadai tasan shairin da makircin da zata kulla mata daga ita har A'indo.

Da gudu sosai suka isa Asibiti,bayan sunje doctor dama yayi komai taimakon gagawa aka ba A'INDO,wanda numfashin ta ma saida akasa mata Oxygen,da k'yar aka shawo kan matsalar ta,an gano cewar yunwa ta mata baban kamu,wanda a lokacin idan aka kara jan lokaci zata iya hadasa mata ciwon Ulcer,sanan kuma saida akayi mata karin jini,saboda gaba-daya jinin ta ya tsotse, kasancewar batacin wani abinci mai vitamin,da kara jini,sai ma gari rogo da take sha.

Dan haka karin jini aka mata, har leda hudu tasha,sanan kuma aka mata karin ruwa,Mari ke wurin ta tun dasafe har dare,ita ta koma gida ta dawo da abinci,da Alhassan ya dawo Mina bata nan tabar gidan saboda Kiran ta da samarin ta ya mata cewar akoi casu,dan haka a bakin masu gadin yaji cewar ankai A'INDO asibiti,bai ko damu ba,yayi gaba abunsa.....

Mari ce ta dawo dan d'aukan kayan A'INDO saboda sai an tsare su.

Ce mata akayi oga ya dawo, direct falon sa ta nufa yana danna computer,yana shan coffee,ba abunda ya sha masa kai,kamar ba shi ba yasa Yar mutane cik'in wani hali,salama tayi tare da sara masa ,tace"sa dama dan nace maka an rike A'INDO so zan kulla da ita a asibitin,dan haka ina bukatar adan bani hutu."

Wani matsiyacin kallo Alhassan yayyi mata yace" Mari kinsan cewar ba'a min katsa landan,dan me zaki d'auki yarinyar nan ki kaita asibiti?da izinin wa?
To bara kiji wallahi kika ja min magana sai na miki hukunci tsatsaura,sanan bayanin d'aukan hutu ruwan ki ne kizo ruwan ki ne ki tsaya,anma ki sani ki tabatar kin dawo da yarinyar nan dan tayi aikin ta ,tunda kinsan ba Wanda zaiyi mata aikinta."

Yana fadin haka yabar mata falon."

zagi ta bisa dashi a zuciya ta juya ta tafi.

Kaya ta duba taga Gaba-daya kayan sun tsufa,wani katon akwati ta duba anan taga sababin kayan ta su less atamfofin shadodi,duk dinkaku,kuma masu tsada,tayi mamaki sosai,zagar kala biyar tayi ,sanan ta d'auki mayuka da sabulu ta fito,masu aikin ada wanda A'INDO take aikin su yanzu wa'inda a yanzu suke wani aikin, su ta gani ta basu wasu yan kudi tace su dinga yima A'indo aikin da take ma oga kafin ta samu lfy."

ba matsala sukace, sanan tayi ficewar ta,tunda aka kai A'indo har yanzu bata farfado ba,nan Mari ta kwana a asibitin,sai dasafe A'indo ta farka,ras taji saukin jikin ta saide rashin kuzari .

Mari take dawainiya da A'indo,yau kwana uku kenan A'indo ta warke tana komai ,tagumi A'indo tayi tana kallon Mari,A'indo tace"nagode sosai Anty, Allah saka miki da Alherie,badan ke ba nasan da yanzu na wula,daga hannun mugun nan."
"Ehee dama ina cewa bara na tambayeki meye hadin ki da wanan azalumin."

"Mijina ne"
A'indo ta bata amsa.

"😱,Miji fa kikace"?
Cewar Mari cik'e da mamaki da kuma razana."

Murmushi A'indo tayi sanan ta ba Mari labarin ta,sosai Mari tayi dariya sanan ta tausaya ma A'indo dan tabas jahilci na dawainiya da ita,dan da ba jahilci ai A'indo mace ce ta nuna ma tsara,kuskure daya akayi da ba'a bata ilimi ba kafin a aurar da ita.

Tabas tanada bukatar taimako.

"Anty Mari wly na tsani soji,anma kuma ina sha'awar nima nayi wanan aikin,Anty inason ilimi ,ina sha'awar zama soja nima."

"To anma kin taba Makaranta kuwa"?
Mari ta tambaye ta .
"Eh nayi primary a kauyen mu."

"Aisha yanzu zaki iya aikin soja,aikin soja fa saida jarumta,kuma Kinga da ace ke ba matar aure bace zan iya taimaka miki,anma Kinga ke matar aure ce."

"Wallahi Anty dagaske nake, inason zama jaruma nima dan na dau fansa,wly Anty ni kaina wani abun idan inayi sai nayi tunanin kamar banida hankali,wallahi inason inyi hankali,nayi ilimi,nima fito soja."

Murmushi Mari tayi tace"kwanta ki huta..

Saida A'indo tayi kwana biyar aka Salamo ta,Sam Alhassan baiyi tunanin ba bata gidan,domin a tunanin sa ita ke aikin da ya bata,tunda ana yin aikin kafin ya fito ,wanan yasa baya sanin mai aikin....

A'indo tayi rama saide cimar da Mari ke kai mata a kwana biyar ta murmuje,kayan da Mari ta kawo mata ba karamin bala'in kyau suke mata ba,saide duk sai taji ta a takure ,batajin dadin sa su.

Taji k'arfin jikinta sosai hakan yasa suna dawowa gidan maida kayanta na da.

Kuma abun burgewa acikin wanan dan zaman da A'indo tayi a asibiti kwararun likitoci suka duba hannun ta inda aka maida mata shi daidai,hanun ta ya koma dai-dai,sanan suka kara bata wasu maganin nika wanda zata dinga sha zaiyi saurin warkewa,Masha Allah ba karamin godiya Mari tayima doctor ta ba,domin shine yayi wanan taimakon .

Mina ce a zaune saman k'afar Alhassan inda take fada masa abinda Mari tayi mata saboda A'indo ran Alhassan a bace yasa a Kira masa Mari da A'indo a tare sukazo ."

Kallon tsana yakai ga A'indo sanan ya juya ga Mari yace"ke har kin isa kina k'arkashi na ki nemi cima Matata mutunci,har ki fada mata magana saboda wanan jakar,wallahi kinci darajar tsohon ki badan haka a yau din nan sai na koreki,

kije kiyi abinda ya kawoki ki tatara tsuman rayuwar ki, ki barmin tawa karki kara shiga Al'amarin rayuwata zaki iya tafiya."

fita Mari tayi ranta ya baci anma ta danne.
Sanan yakai kallonsa ga A'indo yace "kije ki gyara min d'aki na, sanan inason ki sani kika saki kikayi kuskure sai kin gane shafi ruwa ne,sanan ki tabatar bakibar dati ko daya ba,ki gyara komai ,ki wanke na wankewa ,ki gyara na gyarawa.wly idan kikayi kuskure sai na lahira yafiki jin dadi,d'akin sa taje ,duk an birkita d'akin anma kuma tasan anyi haka ne dan ya wahalar da ita,gyaran d'akin ta fara da hannu daya,ta share da k'yar sanan ta dinga nade kayan. , b'andakin sa ta shiga b'andakin ma harda Tv ta bango b'angare guda, b'angare dayan kuma su cumputer ne,da wasu takardu, b'andakin ya hadu matuka ,gyara b'andakin tayi duk da ba wani dati tayi ba,sanan ta wanke , cumputer ta d'auka taga kamar ta danyi dauda sai ta hada ruwa da klin ta sa ta cik'in ruwan ta fara wanke ta,saida ta wanke computer da kyau sanan ta goge ta maida ma'ajin ta,sosai ta gyara ko ina.

Duk ta gaji , gashi dama bata ida warwarewa ba. Alhassan ne ya shigo d'akin ya huce b'andakin dan d'aukan computer sa,aiko sai yaga aika aikar da A'indo tayi masa,zaro idanu yayi yace"what cik'in razana da k'arfi,jiya ya sayo computer dan yasa wasu bayyanai anma sai gashi A'indo ta wanke Masa computer,Idanun sa suka rikida tsabar bacin rai,ita kam A'INDO tuni ta sure,dan tasan wata killa tayi laifi,itakam tasan yau kashe ta zaiyi,wuri daya ta tsamure, cik'e da tsoro abin tausayi,juyowa yayi ya kalleta tuni ya kara jin wata tsanar ta a ransa,"ke!! Wly na tsane ki ayau zanyi ajalin ki uban kowa ma ya huta nima na huta,wuyan ta ya kaima cabka ta baya,ya rikota,ya fara janta,har saida ya sauko falon da ita ya fara marin ta,sanan ya jefar da ita,Allah ya taimake ta ba bisa kararen hanun bane,kuka take sosai tana basa hakuri akan ya yafe mata, k'afafun sa ta rike da hannu daya,tace"dan Allah kayi min rai kayi hakuri idan na maka laifi."

"Dan ubanki har tambaya kike in kinmin laifi,agidan uban wa kika taba ganin an wanke computer."
Duk Mina na tsaye tana kallon su tana dariyar jin dadin bugun da yake ma A'indo,itakam A'indo neman gudu tayi dan ta ceci kanta ,ganin haka ran Alhassan ya kara tunzura,ya kara damko wuyanta ta baya da k'arfi ya buga kanta da bango wata irin razananar kara A'indo ta buga sai gata suuuuu ta fadi,jini ya fara zuba daga goshin ta,salati yaji an buga daga bayan sa,wanda yayyi matukar razana sa,juyawar da zaiyi aiko wa zai gani idan ba Hajiyar sa ba,wato Momyn sa,a matukar ruduwa da firgita ya zaro idanu,da gudu Hajiya ta karaso ita da Mari dan dama a tare suka shigo talabo A'indo Hajiya tayi,ta fara jijigata tana ambatar sunan ta anma ina A'indo ta suma.
"Mari taimaka mukaita asibiti.".

Hajiya tace da Mari,d'aukan A'indo sukayi,aka kaita wata asibiti daban,ba wacan ba,taimakon gagawa aka ba A'indo awa daya aka d'auka a kanta,sanan aka samu ta farfado,anma kuma ga dukan alamu akoi matsala a kanta,domin kuwa har k'wak'walwar ta likitoci suna tsoron idan bata samu matsala ba saboda buguwar da k'arfi ne akayi mata.hajiya na hawaye ta dafa Mari tace nagode ya ta,da Kika kirani,anma dan Allah ki fadamin gaskiyar duk abinda kika san ana mata a gidan,domin na tambayeki a waya kince sai nazo to ki fadamin yanzu."

Sauke ajiyar zuciya Mari tayi,ta fadama Hajiya duk wani abinda ta sani.

Goge hawaye Hajiya tayi,tabas sunyi kuskuren yin wanan hadin,ashe haka Alhassan yake bashida imani,tabas zai gane kuren sa,dafa Mari Hajiya tayi sanan tace "Mari ki kula min da A'INDO zanje na dawo fita Hajiya tayi,ta shiga taxi gidan Alhassan ta koma,yana falon har yanzu, yana nan inda yake, Mina kam ta gudu ta bar sa dan tsoro ,tunda ta fahimci Hajiyar sa ce tazo .

A tsaye Hajiya ta iske sa,bata ko masa magana ba ta basa takarda da biro tace"amshi ka saki A'indo a yanzun nan,idan ko kaki bin Umarni na zan iya tsine maka,hannu na rawa ya amsa ya rubuta ma A'indo saki daya,ya ba Hajiya takardar hannun sa na rawa,"Mom dan Allah tsaya kijiiiii."

"✋ya isa!!! tsayar dashi Hajiya tayi a tsawace,tace"a yau ka nuna mana mu bamu isa dakai ba,cewa nake ko Kashi muka aura ma ka zauna dashi ba tare da ka zalunce sa ba bare dan Adam,ni bazan maka baki ba,anma ka sani wallahi alhakin baiwar Allah nan kadai ya ishe ka,yanzu sai kayi abinda kaga dama ,A'indo insha Allah ta rabu dakai har abada."

Hajiya na gama fadar haka tabar gidan ta nufi asibiti,anma tana zuwa asibiti ta tarar da mumunan labari,zaune suke daga ita har Mari gaban doctor inda yake musu bayani game da matsalar A'indo kamar haka........

Aci gaba da gashi🍇
Maimou love😘
[10/10 à 17:34] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨

*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋

*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚

*DAGA AKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
_and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*

_kuyi hakuri na rubuta Latifa ina tsaka da editing ya goge_😢

_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.