Complete Hausa Novels

Aindo Part One Complete Hausa Novel

Reading file: Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part One Complete Hausa Novel.txt

Chapter 36 of 44

*Page 71-72*

Murmushi Bashir yayi ,tare da kokarin matsowa kusa da ita,da sauri ta kara ja baya tayi tuntunbe da wani dutse ta Fadi a gurin k'afar ta ta fashe.

Anma sam bataji zafin ciwon ba saboda a yanzu ji take wanda ke gabanta yafi zafin ciwon sau dubu.

Dukawa yayi tare da sakin murmushin sa ,yace"welcome baby nayi kewar ki."

Ya fada tare da shafa fuskar ta,runtse idanu A'INDO tayi tare da fadin"karka kara sa wanan banzan hannun naka ya taba min jiki na fada ma mugu."

Gashin kanta ya kama ya jata kiiiiii har saida ya isa da ita k'ofar falo sanan ya sabe ta da k'arfi ya shigo da ita.

Ihu A'INDO take dan neman agaji anma ina ba Hali.

"Bashir kai wani irin mugu ne dan iska,wanda baisan darajar dan Adam ba,kai bunsurun ina ne,to bara kaji na rantse da Allah tun muna shaidar juna ka bani hanya na tafi idan ba haka ba kuma wallahi lahira zatayi bako."

"Hahaha , yarinya kinada abin Dariya,sai ya marairaice fuska kuma yace"haba Aïsha na kira

ki baki d'auka ba nayi miki message bakiyi reply ba, a k'arshe ma kika sa ni a black liss,haba dan Allah Aisha kizo muyi zaman mu,nan Kinga ke ba wani dangi ne dake ba bare a wani damu da bacewar ki,kizo mu zauna na Miki Alkawarin zaman farin ciki a gidan nan kiyi yanda kike so."

Murmushi A'INDO tayi,ta tashi kamar ba ita ba ,tayi dariya tace" Allah ko karka damu anma bara na dan sama mana abinda zamuci yunwa nake ji."

Washe baki yayi yace"Alhamdulillah kin hakura kenan."

"☺me zai hana kuwa Bashir bara dai yanzu na dafa wani abu idan na koshi sai muyi maganar."

Kitchen ta nufa,yayyin da shi kuma yayi wani tsale ya haye saman kujera yana tsalen murna tare da kecewa da dariya yace"ai dole ta so ni kodan kyau na,wly zaman mu zamuyi ba ubanda ya isa ya raba mu.

A'indo ko tana shiga da ma rigar ta doguwa tanada aljihu koda taga yanda mai Adaidaita ya rugo da ita ta d'auki wayar tasa a aljihun rigar ta ,a lokacin da ta shiga kitchen kuka ne ya kusa kufce mata, tayi sauri tayi shiru ta kama bakin ta,sai ta fido wayar daga Aljihu numbers Al'Hassan tasa har mamaki tayi ya akayi ta hadace ta haka.

Kira daya biyu Al'Hassan ya d'auka bayan ya samu gefen titi ya tsaida motar sa dan tunda ya rasa inda A'INDO take yaketa yawon garari Yana neman ta kamar mahaukaci.

Number ta ya gani wace dama yanada ita
Yayi saving dinta,da sauri ya d'auka har bakin sa na rawa wajen magana "hello!

Aisha kina ina kin tada min hankali."

"Yaya Al'Hassan plz kazo ka raba ni da wanan mugun Bashir shine yasa a sato ni gani nan gidan sa ina kitchen plz kazo ka d'auke ni."😭

Idan ran Alhassan yayi yayi dubu to a lokacin ya baci, gaba-daya kansa hayaki ma yake masa, jijiyoyin kansa har tashi suke,Kiran Idrissa yayi bayan idrissa ya d'auka yace"maza ka bani adreshin wanan dan inskan tsohon mijin Aisha."

"Yaya lfy?"

"Kaga nace ka bani ko."
Saurin basa yayi Yana basa ya Kira Hajiya yace"Hajiya maza kije gidan tsohon mijin Aisha dan inaga brother yau Zuciyar sa ta tashi Kar ayi kisan Kai ba alamun lafiya."

"Ya Salam Hajiya tace ta tashi ta hau sama dan d'aukan hijabin ta.
Shi ko Alhassan a dari ya ja motar kamar zai tashi sama,sai gashi a unguwar, k'wank'wasa gidan yayi sai ga Mai gadi ya bud'e ,bindiga ya dungura ma mai gadi ba shiri yayi mazan bashi hanya yana rawar jiki,yana shigowa Mai gadi ya arta a guje yabar gidan.

Shikuwa Al'Hassan da sauri ya karasa falon
Yana zuwa" ya daga murya Aisha kina ina ."

Bashir dake zaune saida gaban sa ya fadi anma ya dake yace " kai Malam lfy zaka shigo min gida ba'a koya maka salama ne ba"

Wani mugun kallon Alhassan ya wurgo Masa Wanda ya kadar da Yan hanjin Bashir,da gudu A'indo ta fito ta nufi Alhassan da gudu ta rungume sa tana kuka.

Tace"kaga wanan mugun ne ya sato ni,kara rungume ta yayi yana shafa kanta alamar rarashi, Bashir ya waro idanu waje yace "dama ke Yar iska ce,shine kika Kira kwarton ki to da yazo me zaiyi wallahi A"indo sai na baki mamaki."

A wani irin k'arfi Al'Hassan ya janye A'indo daga jikin sa ya nufi Bashir baiyi wata wata ba yakai ma bakin sa naushi,ba shiri Bashir ya rike Baki Dan tuni hakorin sa daya ya fita baki ya fara jini,cakumo wuyan sa yayi ya makure Al'Hassan yace"kai dan gidan uban waye ? Wane ganganci yakai ka taba min mata,dan uwarka dama inada haushin ka kyale ka nayi in banda akuyanci ka saki mata sanan ka dinga bibiyar ta,to uwar me zakayi mata ,,Bashir zai kuma magana Al'Hassan ya kuma naushin sa,anan ya makure sa ya fara sakar masa duka tako ina nausan sa yake tun Bashir na iya ramawa har yakai ya kasa,jina-jina da jini Al'Hassan ya Masa,yaji haushi ko gani bayayi aikin dukan sa kawai yake,tuni Bashir ya sume anma Alhassan yaki saurara Masa,A'indo ko kadan bata ji tausayin Bashir ba,illa ma wani so da take ji nasa yana mamaye Zuciyar ta,a yau duk wata kiyaya da take masa ta kawar,ta maye gurbi da so ,Hajiya ce ta shigo gidan ita da idrissa abinda ta iske ne ya tsorata ta,da sauri taje ta ririke Alhassan shima Idrissa haka ya rirke Al'Hassan Hajiya tace"kai wai meye haka?
Kashe dan mutane kake son yi ne Bashir ya debo ruwa ya watsa ma Bashir ya dawo hayacin sa,Hajiya ranta a bace ta tambayi Al'Hassan da har yanzu jikin sa ke rawa gaba-daya baya cik'in hayacin sa,ji yake kamar ya kashe Bashir.

A'INDO ta rugo ta rungume Hajiya tana kuka tace"Hajiya sato ni yasa akayi shine na Kira Yaya Alhassan,dama yana Kira na tare da yi min test akan wai nayi hakuri na dawo gidan sa,ganin ya takura min shine nasa number sa a black liss,shine
Yau yasa aka sato ni lokacin da mukaje wajen siyen ice cream,na fito ina jiran yaya Al'Hassan yasa wani mai Adaidaita ya sato ni ."

Su A'indo harda karya wai ta fito tana jiran Al'Hassan🙄

Ran Hajiya kanta ya baci kallon Al'Hassan tayi tace"kayi min dai-dai,sanan takai kallon ta ga Bashir Wanda ya farfado anma idanu kawai yake binsu dashi dan baida ko k'arfin motsa yatsar sa .

"Bashir ada nayi tunanin Kai dan mutunci ne a yanda ka yaudare mu kaje mana da mayaudariyar fuskar ka,wada tasa muka baka yarinya,Ashe ba haka kake ba,munyi nadamar aura maka Aisha da mukayi tun farko, kai ko tausayin maraicin ka baka yi, gargadi zanyi maka Wanda na farko kuma na k'arshe tun farko yara na sun so rufe ka na hana su dan tausayin maraicin ka duk da abinda kayi ma yarinya ta,ka sani Aisha ya ta ce,wallahi Allah duk ranar da ka kara kokarin koda Kallon banza wa Aisha wallahi Allah kaji na rantse sai ka raina kanka ku fice muje."

Hajiya taja A'indo shima idrissa yaja Al'Hassan suka bar Bashir kwance tamkar gawa.

Bayan sunje gida gaba-daya Alhassan yaki sakar ma A'indo fuska domin cewar sa laifin ta ne da tayi hakuri suka tafi bata fito ba da duk hakan bata faru ba....

Aci gaba da gashi🍇
Maimou love😘
[15/11 à 20:06] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨

*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋

*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚

*DAGA ALKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
_and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*

_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_

*🏵 HAPPY JUMA'A🏵*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.