Aindo Part One Complete Hausa Novel
Reading file: Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part One Complete Hausa Novel.txt
Chapter 11 of 44
*Page 21-22*
K'arfe biyu na rana jirgin su A'hassan ya sauka a garin Zinder,motoci ne guda shida ke jere suna jiran fitowar sa,yana fitowa da sauri sojawa suka tafo suka jera tare da sara masa,yayin da yan jarida suka fara cika gurin domin yi masa tambayoyi ,daga musu hannu yayi,Alamun ba zaiyi magana ba,nan body guards dinsa suka fara tatare sa,yana zuwa a mota ta tsaka suka bud'e masa ya shiga.
Nan aka tadi motoci sukayo gida,motocin su na shiga gida su A'indo suma suna shigowa gidan sun dawo daga yawan su,sai ciye ciyen gyada suke ,da suka k'wato ba tare da an basu ba,ido A'indo ta tsura ma motacin,har taga wanda zai fito,aiko tana ganin sa ta saki hannun Husseina ta ruga da gudu zata tarbo sa,fadi take weyy miji na ya dawo🏃♀🏃♀🏃♀💃,da sauri gards din suka tare mata hanya,shikam yana waya ya juyo yaji wace yar iskar ce.
tsayawa A'INDO tayi ganin sun rufe mata hanya,ta murguda musu baki tace"yau ni naga ikon Allah ,nida miji na zaku wani zo da bakin ku kamar bakin tukunya kun wani tare min hanya,yan bakin ciki to sai naga mijina eheee😏🤨.
Ta juya takai kalon ta ga Husseina da k'arfi tayi magana yanda Husseina zata jita,wada take tsaye cik'e da tsoro ,ganin sojawa,tace"Husseina zo kiga mijina yarinya Mai kyau kamar Aljani."
Alhassan gaba-daya sai ya d'auke ta a mahaukaciya dan shi a tunanin sa da mai gadi take ko wani,dan haka yaci gaba da wayar sa ya ficewar sa falo.
Da salama ya shigo,Hajiya na zaune ta tashi ta tarbe sa cik'e da farin ciki tace , welcome to home my Soja,tarbo sa tayi shi ko ya rungume ta, cik'e da shagwaba,suka zauna ,nan hajiya ta Kira Rabi'u a waya tare da cewa ya kawo juice mai sanyi,tashi Rabi'u yayi duk da har yanzu bayan sa na masa ciwo saboda faduwar da yayi,"anma wly A'indo Allah shi debe miki Albarka,ka duba shegiyar diya zata kasarani ko auren fari banyi ba ,mugunta kawai salon ta nakasa ni na rasa mijin aure,a da ma ya aka iya bare in ta nakasa ni."
Yana jera lemo a plat shi kadai yana masifa,a haka ya d'auko kugu a karkace,yanayi yana tafiyar mata,haka ya shigo falon yana mita,daga kai zaiyi ma hajiya magana Aiko carab suka hada idanu da Alhassan da tun shigowar sa yake kalon sa,a matukar razane, Rabi'u daudu ya fara Salati,Tare da fadin wa'innahu suleymana wa'innahu bisimillah kuke ganin mu ba mu ke ganin ku ba."
"Dan ubanka Aljani kagani da kake wanan abu."
Alhassan ya fada cik'in masifa.
A rikirkice Rabi'u ya gyara maganar sa sai gata ta koma sak ta namiji Kato ,yace"ai ranka ya dade ganin ku ba Alherie bane,sodji marmari daga nesa,a ganku daga nesa kumfi kyawan kalo,sai mazajen daga ,gaba salamun baya salamun,Allah ja da ranka 🙇."
"A'indo ce ta shigo d'akin tace "yauwa Hajiya dan Allah ki fada masa ya daina share ni,Ina matsayin Matar sa nazo zanyi masa oyoyo irin na Yan birni anma ya gwaleni😏."
,,,,,,,,,,,,"a rikice Alhassan ya juyo yace"ke wai dama dani kike?
dan ubanki nine mijin naki 😳?
ke dan uwarki kamar ni ki kalleni kice mijin ki,Alhassan ran maza ya bace duk yanda Hajiya takai ga ihun ya bar A'indo batada hankali Ina yau bai jita ba,domin ransa yayi matukar bala'in baci,damko ta yayi ya zage ceinture dake kugun sa,nan ya fara jibgar ta baji ba gani, Husseina uwar tsoro tuni ta labe bakin k'ofa tana kuka,A'indo ma kuka ta fara,dan ba karamin zafin bulalar take ji ba,ita a rayuwar ta ma ba'a taba bugun ta ba."
Hajiya ranta a bace ganin A'lhassan Zuciyar sa ta tashi kuma zai iya kashe yarinyar mutane,a tsawace tace"wly ka kara dukan yarinyar nan zan tsine maka ,cak ya tsaida dukan da yake,Ya yar da madakin Idanun sa har sun rikida tsabar bacin rai ya bar wurin,shiko Rabi'u tuni shima ya sume a gurin har da fitsarin sa,domin kuwa duk ya tsure yayi tunanin in an gama da A'indo kansa za'a koma."
Hajiya na share kwala ta tausayin A'indo ta kira gard dinta mata sukazo aka d'auki A'indo akayi da ita cik'in mota aka nufi asibiti ,a Asibiti ma dak'yar aka daidaita numfashin A'indo,dan har OXYGEN aka sa mata Husseina Kam kuka take tare da tsinema Alhhassan ."
Rabi'u ma ruwa aka zuba Masa yana farfadowa yayi d'akin sa a guje yasa sakata ya rukunkune cikin bargo ,yana karkarwa tsabar tsorata da firgita da yayi.
Bayan doctor sun cema Hajiya abar yarinyar tana hutu ne,sai Hajiya ta koma gida sakamokon Alhaji da yace mata yazo,dan ta Kira sa ta fada masa,shi yasa tace kawai yazo ayita ta Kare ,a fada ma Al'Hassan matsayin A'INDO a gurin sa.bayan tazo suka zauna ita da Alhaji a falo,ga Alhassan gefe da har yanzu yake huci ransa a bace ,ace in banda samun guri , yarinyar tana matsayin yar aiki kuma Yar kauye k'askantata,wai take ce masa mijin ta,anma ko wly da zai kara ganin yarinyar nan sai ya kara mata dukan.
Alhaji ne yayi gyaran murya,yace"to Alhassan kamar yanda ka sani na baka dama ba daya ba biyu ba,akan ka samo Matar aure anma ka ki samowa,kace bakada,to ni a matsayi na na uba kuma wanda nakeda iko da kai inaso na shaida maka cewar na d'aura maka Aure da Aisha wato hassana A'indo,yarinyar da take aiki gidan nan.,!
Wada naji ance yau ka daka,saboda bakasan daraja da tausayin mace ba,kamar ka samu kato.
A matukar razane da kidima, Alhassan ya tashi zurmut yana kalon dad din nasa ,bakin sa na rawa,yayyin da hankalin sa ya tashi, Zuciyar sa ta fara barazanar kai kawo, nutsuwar sa yabar gangar jikinsa, idanun sa suka rikida zuwa ja, cik'in i'ina yace"Dad anya kuwa ka gane abinda kace,uhum dad cewa fa kayi Yar kauyen nan, kazama,jahila mumuna,itace ni Alhassan danka ka aura min,Daddy nifa danka ne ba makiyin ka ba."
Ji yayi an basa pauuuu yaji mari a kumatun sa,Dad dinsa ne,dafe kumatu yayi,yayyin da ya zaro idanu,yace "Dad yau ni ka mara akan wanan yar kauyen."
"An mareka ko zaka rama ne?
Cewar dad da ransa yayi matukar baci akan maganar sa.
Cik'in bacin rai Dad yace "Alhassan ina matsayin uban ka ko Kashi na aura ma inajin Kai mai k'arba ne hannu biyu biyu,kuma ka gode,dama sau nawa na baka?
To bara kaji bazaka maida ni karamin mutum ba,kuma aure na maka,abinda zance dakai anan shine wly wly naji ka muzguna ma yarinyar nan dani da kaine,
sanan kafin kace komai inaso ka sani idan zaka tafi dole ka tafi da matar ka,kayi mata duk wani abinda ya kamata na zuwa K'asar waje France (Paris) inda kake aiki,dan k'afar ka k'afarta,sanan naji ance ka kara dukan ta irin wanan wly zan tsine maka."
dago da idanun sa yayi tamkar zaiyi hawaye, gaba-daya ya kasa magana,domin ji yake tamkar an kulle masa jijiyoyin jikin sa,Dad na gama bayani yabar falon....
Alhassan yaji kansa yayi masa bala'in nauhi ,yana mugu mugun sara masa,domin har jijiyoyin kan nasa sun tashi,tsabar ruduwa da rudani da ya shiga tare da tashin hankali,dago kai yayi ya kalli mahaifiyar sa yace"Mom dama baku so na ,ashe mahaifi zai iya haifar abu a cikin sa kuma ya ki sa,Mom mai na muku da kuka nemi hanyar mutuwa ta,domin auren wanan yarinyar tabas zan iya haduwa da ciwon zuciya,dan wly Mom matsawar zan zauna da wanan yarinyar wai a matsawar mata to tabas zan iya rasa rayuwata,dan wly ganinta kadai nayi sai naji kamar zanyi amai ,wly na tsaneta,tsana mafi muni a rayuwata,Mom ki taimaka dan Allah kiyi ma Dad magana yayi hakuri ya raba wanan auren."
Ya gama maganar sa tare da dafe daidai Zuciyar sa yana dan tari,saboda wani daci yakeji a Zuciyar sa,shafa kansa Hajiya tayi dan itama ya bata tausayi, tace"kayi hakuri Son wanan k'addarar ka ce,iyaye basa taba zaba ma ya'yayansu abinda zai cuce su,kayi hakuri ka amshi k'addarar ka,haka Allah ya rubuta,kaida kanka kasan Mahaifin ka,saida ya baka dama anma kayi wasa da ita ni yanzu ba abinda zance saide nace Allah ya sanya Alherie."
Tana gama fadar haka itama ta tashi tabar wurin taje wurin Alhaji.
shikam kansa yayita bugawa har saida ya fara jini, tsabar bakin ciki,"Abass na tsaneka ,Allah ya Isa tsakani na dakai,na tabata kaine kayi min bakin nan."
Shi kadai yake wanan sabatun tare da tsine ma Abass abokin sa,da kara jin tsanar A'indo da duk wani wanda ya shafe ta,ace kamar shi ya auri yar aiki jahila,bakauya,kuma ma dakikiya,mumuna,kuma bahaushiya,.
""Kai!!!!!!!
Ina sam bazaiyu ba wly,dole ma na rabu da wanan yarinyar,inko an matsa zan tafi da ita anma a matsayin Yar Aiki.
A'indo ta farfado,yayyin da Husseina ta karasa wajen ta,tunda ita ke tare da ita,hanun ta ta rike tana zubar da hawaye ,tace"A'indo dama da wanan mugun aka d'aura miki aure?
Gaskiya ki tashi mu gudu mu koma kauye dan wanan ai zai iya kashe ki."
Murmushi A'indo tayi tace"haba Husseina,ke yanzu duk da banida cikak'en hankali ai bazan bar wanan sumbulelen saurayin ba,ke yanzu idan na barsa wa kiki tunanin zai aure mu,a kauye ba'a d'auke mu a bakin komai ba,idan nace ban son auren sa wa zai aureni ,ai kawai ki barni dani da shine,wly tunda ya min haka sai na rama."🤨
Murmushi husseina tayi suka rungume juna, Alhamdulillah jiki kam na A'indo yayi sauki ta koma Normal,dama Hajiya ke zuwa kula da ita har ta samu sauki,aka salame ta,tuni A'indo ta koma A'indo ta ta da .
Rabi'u daudu dai ba karamar tsorata yayi ba,dan har Saida yaga yana neman kashe kansa ya fito daga cik'in bargon .haka ya mike ya koma namiji sak,bayan an salamo A'indo,shirme da kiririta,da wawancin ba abinda ya ragu .
Daddy ya kara kiran Alhassan ya tuntube sa da zancan maganar passport din A'indo,dan yaji ance ya kusa tafiya,kuma matsawar bai tafi da A'indo ba tofa suda su gansa,sai bayan wani dogon lokaci.
"Dad dama dama Alhassan ya fara wanan maganar.
"Ya isa haka✋"
Daddy ya tsayar dashi ya sa masa birki,ya isa Alhassan inaso ka sani nasan cewar kanada iko da kuma halin da zakasa ayima matar ka passport dinta a kwana biyu anma ka tsaya kana jan lokaci,to a yau na baka umarnin da kaje kayi duk abinda ya dace game da ita nan da kwana biyu naga komai nata."
Alhaji na gama fadar haka yabar falon, gaba-daya .
Alhassan fadar irin tashin hankalin da yake shiga kwanan nan game da A'indo abin ba kadan bane.
Tashi yayi ya fito falo baba,runwan sanyi masu sanyi ya fido a firje ya fara sha, A'indo ce ta shigo kamar kulum cik'in shirin ta tazo ta zauna Dan nesa kadan dashi,ta zuba masa ido tana kalo,duk da rashin hankalin ta tasan tana son mijin ta ,nisawa tayi can tace"kato dakai kuma wai Soja ka tsaya kana dukan mace,ai ba'a nuna jarumta akan mace malam kaje ka samu irin su idi Kato acan zaka nuna jarumta anma kawai dan an rainani azo ana duka na,to wly ni A'indo gani nan bari dan waken iyaka 😗 kuma dole a zauna dani."
Idanu ya kura mata cik'e da takaici,tabas da ba dan Mahaifin sa yace idan ya kara bugun ta bai yafe ba,to da yau din nan sai an d'auki gawarta."
Cik'e da bakin ciki yake kalon ta,tashi A'indo tayi ta kara d'aure kugu ta fara rawa,sai ta juya masa baya sai ta dan duka tace" kagani ka gani kwalelen ka,Allah ya yarda kagani ka gani kwalelen ka😝."
Kasa jurar bakin cikin yayi ya tashi yabar falon, kicibis sukayi da Rabi'u ai Rabi'u na ganin sa ya saki salati,tare da Addou'a neman tsari dashi ,Kai kace yaga Aljani da gudu ya koma ya sake hanya saida yaga Alhassan ya fice sanan ya dawo yabi hanyar falo ya iske A'indo nata gwatso tana fadin ka gani ka gani kwalelen ka,ta bada baya can bata ma san Alhassan baya wurin ba."
"Mtsss ke kam wly Allah shi shirye ki,to uwar wa kike ma wanan abu haka sai kace zarara."
Juyowa A'indo tayi tace" au ya tafi kenan mtss."
" Hajiya!!
Hajiya!
Hajiya!
A'indo keta kwala ma hajiya kira,hangame baki Rabi'u yayi yace "nikam yau zanga abinda yafi k'arfi na,wai an d'aura ma tsohuwa aure tace "duniya sabuwa,wai ke A'indo hajiyar nan ba surukar ki bace.""""""""""
Muje zuwa dai muga ya zata kasance,shin A'INDO zata tafi wanan K'asar wajen ko kuwa?
Ya zata kasance a a gidan Hajiya ?🤔
[10/10 à 17:34] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨
✨
*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋
*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚
_ba wai na daina typing din Latifa sabon salo bane,a'a ban rubuta bane,wanan ma da kuke gani a aje yake,an rubuta sa ne Yana aje so kuyi hakuri zaku ga Latifa kwanan nan insha Allah_
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.