Aindo Part One Complete Hausa Novel
Reading file: Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part One Complete Hausa Novel.txt
Chapter 26 of 44
*PAGE 51-52*
Murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo,alhakikanin gaskiya wani irin tararin bala'in sonta yakeji ,wanda shi kansa abin tsoro ya fara basa,bai taba son wata mace ba haka,sanan baisan lokacin da son ya shige sa ba,tafin hannun sa yasa zai janyo ta ,itako idanu a rufe ta yarfar da hanunsa,a inda tsotsayi yaja ta yanka tafin hannun nasa,take jini ya fara zuba, bud'e idanu tayi jin yayi yar karamar kara,jini taga yana zuba a hanun sa,duk da bataji dadiba a k'asan zuciyar ta,saboda har ga Allah bataji dadin abinda tayi ba,saboda ita ba irin sa bace,d'aurewa tayi ta dake,tare da cin fuska ,tace"Wallahi kadan ka gani ma ,idan ka kara gangancin koda taba hannuna ne to wallahi abinda zan maka sai ka kwanmace baka doron duniyar nan."
Mamaki ne fal a idanun sa,kwayar idanun ta ya duba yaga kiyayyar sa fal a idanun ta,gashi har zata iya fido masa da jini,ganin yayi sanyi yasa A'indo yin tsaki tare da buge sa ta bud'e k'ofa tabar wurin.
Doctor ya kira yazo ya duba masa hannun ,akayi bandeji tare da basa maganunnuka,tunda A'indo tasa kai ta fita,hankalin sa ya kara tashi,sam duk zugin da hannun sa ke masa bayaji,domin kuwa a cewar sa baikai zugin da zuciyar sa ke masa ba.
Tunani yake ,yanzu wai cik'in maza zataje ta shiga suyi cudanya dasu,kuma ma wai namiji ne zai kaisu wanda yake tunanin saurayin ta ne,😳waro idanu yayi da ya tuna maganar ta ,ta dazu wai ko mijin da zata aura,to waye wanan kuma?
Gaban sa ke bala'in faduwa,ji yake kamar ya kwala ihu a hankali yake jin kansa na sara masa,tsabar kishin bala'i maganin barci ya balla yasha.
Anma abun mamaki barci yaki d'aukan sa,hanun da akayi ma bandeji ya jimke waje daya,nan take jini ya kuma balewa,anma ina ko ta hannun baibi ba,wani iri yake ji,idrissa ne ya shigo yanata salama yaji kamar ana nishi, sama-sama dan haka da sauri ya karasa d'akin, Al'Hassan ya iske a tsaye,idanu sunyi masa jawur,yayyin da hannun sa ke tsiyayar jini.
"Ya Salam bro meye haka me ya sameka?
Da sauri Alhassan ya karaso ya rike hannun sa yana dubawa,saurin komawa yayi ya d'auko kayan aikin sa yayi dressing din gurin,sanan ya kara nada masa wani bandejin,dago kai yayi zaiyima Al'Hassan magana,kawai sai yaga har barci ya d'auki yayan nasa,gyara masa kwanciya yayi tare da barin d'akin,yana mamakin abinda ya samu dan uwan sa
.
A'indo ko fita sukayi,Bashir ya kaisu,akayi reunion,tsakanin yan matan amarya da samarin ango,duk da Bashir ya hana A'INDO fita daga motar.
Suna zaune a mota suna fira Bashir yace "baby nifa so nake daga an gama auren sisin mu nima na turo,kuma gaskiya bana son asa dogon lokaci wata daya nake son asa ,dan gaskiya bikin bazai d'auki lokaci ba."
Murmushi A'indo tayi tace"ka ganka ko,to naji kai baka ma barin nan da ko shekara ne."
"Kiyi hakuri baby zancan hakuri bai taso ba,naji ance tsohon mijin ki ya dawo,ni kuma a kowace rana cik'in zulumi nake kar ku koma tare,shi yasa nafi son ayi komai a gama."
Nan take annurin fuskar A'INDO ya d'auke ,ranta ya baci,zuciyar ta tayi zafi a k'ankance ta kalli Bashir tace"bash kasan tunda nake dakai baka taba bata min rai irin na yau ba?
Wallahi ka batan rai ,ta ya ma kake tunanin zan koma gidan sa ,Allah ya kiyaye,dan Allah kabar wanan maganar."
Ganin da yayi ranta ya baci yaji shima baiji dadin abun ba,kallonta yayi yace"plz my princess kiyi hakuri,wallahi kishi ne yasa nayi wanan maganar kiyi hakuri bazan kuma ba na miki Alkawari."
"Is ok karka damu,zaka iya turowa da zaran anyi auren Yar uwata."..
Murmushi yayi yace"nagode sosai my princess.
Al'Hassan bai tashi ba sai bayan sallah la'asar,anma kuma koda ya tashi ya tambaya yaji su A'indo sun dawo aka tabatar masa da sun dawo sanan hankalin sa ya kwanta.
Duk wani shirye-shirye anyi,yayin da dangi sukayita zuwa wanan sabga Mina matar A'lhassan kuwa ana saura sati daya tazo biki,da saura sati daya amarya ta shiga lale,
Su A'indo ansha gyara,kamar amarya,domin ta fada ma Hajiya da zaran an gama bikin Husseina Bashir zai turo kuma baza'a a d'auki dogon lokaci ba a cewar sa,Hajiya tace "Masha Allah muma abinda muke jira kenan ,a shirye muke,dan haka tasa har A'indo ayi mata gyaran amare waw idan kunga kyan da A'indo ta Kara ba'a magana,da misalin k'arfe biyar aka fara fulani day,a inda kowa ya halarci gurin,akayi decoration din gurin abin gwanin sha'awa,kowa yayi shirin fulani,hata abokan ango wasu sunzo,yayyin da Alhassan ke rabewa waje daya inda yasan A'indo na bi yana kallon ta,a yanzu bayada aiki daga kallon photon ta a waya sai tunanin ta,yau ma kamar kullum yana daga lungun sa,ya hango suna rawa, Zuciyar sa yake jin tana masa zafi ganin gaban maza ne suke wanan abun,kowa na kallon ta.zai tashi kenan sai ga Mina da yar iskar shigar ta,zaro idanu Alhassan yayi 😳a matukar tsorace yace"ke wai kinada hankali kuwa?
A gidan surukan ki kika fito haka daga ke sai wondo,Wai Mina yaushe zakiyi hankali."
Tsaki Mina tayi tace"kaga Malam wallahi bazan iya ba,dama ka gayatoni nan ne dan ka wulakanta ni,to bara kaji yanda nake shiga ta acan haka zanyita anan ba Wanda ya isa ya hanani,haba dan Allah meye haka, mtsss."
Da sauri tabar wajen zataje wajen wasan da akeyi,har taci rabin tafiya,domin ta kusa kawo gunsu,da gudu Alhassan ya taso yazo ya taro ta,baiyi wata-wata ba ya kwashe ta da mari,bata tsaya tunani ba itama ta kwashe sa da mari a daidai idanun hajiya da A'indo da Hajiya ta fito kiran ta dan ta raraba abinci ......
Kuyi hakuri da wanan oga ya dawo ,banida lokacin baku yanda kuke so
🥰😍😘
[24/10 à 21:29] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨
✨
*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋
*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚
*DAGA AKALAMIN MARUBUCIYAR*
👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
_and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*
_DEDICATED TO My Kawa Mrs Adam (yar Mutan kagara),&My dota Aisha A Bagudo_
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.