Aindo Part One Complete Hausa Novel
Reading file: Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part One Complete Hausa Novel.txt
Chapter 39 of 44
*Page -77-78*
Bata gama maganar ba ya d'auke ta da mari,ya kara sharara mata wani,babu wanda yayi kokarin hana sa, kwalar sa taci tace"dan iska idan ka cika dan halak ka sake ni,yarfe ta yayi daga jikin sa Jin kake tim ta fadi kasa,nan ya dinga ball da ita,ya kwalo,saida mahaifan sa suka rike sa saboda ransa yayi bala'in bacewa,nan yace",wallahi daddy ku yafe min bazan kuma iya zama da wanan jahilar matar ba,Mina kije ni Al'Hassan na sake ki saki uku."
"Alhamdulillah Allah nagode ma,dama na jima ina jiran wanan ranar,acan ma na barka da ita ne saboda kaga ishara,saboda bijire ma zabin mu,anma yanzu da Allah ya ganar da kai nafi kowa farin cik'in rabuwar da kayi da ita,ke kuma idan Halin ki ne yima manya rashin kumya kije kin hadu da daidai ke."
Hajiya ce ke wanan bayanin Zuciyar ta fess,shi kansa Alhaji abun ya masa dadi ,domin tun can dama yarinyar ko kadan tarbiyar ta da ta ubanta bai mishi ba.
Mina tana kuka.
Ta tashi ta duka ta fara rokon Alhassan domin yanzu take kara Jin wani son sa na kara shigar ta.
"Dan Allah kayi hakuri karka rabu Dani ina son ka,wallahi bazan Kara ba."
"Kinga malama yanzu babu auren ki a kaina ki tatara inaki inaki ki barmin gida."
Haka ta tashi ta fita jiki ba kwarin gwiwa, A'indo da take labe wace da shigowa zatayi taji wanan abun,da gudu ta koma b'angaren ta,wani b'angaren na Zuciyar ta bataji dadin sakin ba,saboda koba komai mace ce Yar uwar ta,anma kuma wani b'angaren taji dadi koba komai abinda A'lhassan yayi ya burge ta,tunda dai batada mutunci har take zagar mata mutanen da take kallo a matsayin iyaye,bayan hakan yanzu zasu zauna hankali kwance suci soyayar su ita da mijin ta ba fargabar zata raba kwana da wata,har rawa tayi ranar,Mina kam Alhaji ya cirar mata ticket na jirgi dan komawa, shirye-shiryen biki sai kankama yake,inda Hajiya ke gyara A'INDO da ingantatun maganunnuka na mata masu inganci da kyau ,tare da d'auko mai gyaran jiki,inda take Kara koya ma A'indo kisoshin kala kala na zama da miji ,da kuma yanda zata saye zuciyar sa,da koya mata kalolin kwanciya,yayin da ta kara amsar number wayar ta tasa ta a group group nata wanda take wayar ma da mata kai yanda zasu kula da mazajen su,tana koya mata tsarin iya kwanciya,da inda zata kulla da jikin ta ta sanya turaruka
Lungu da sako da kuma kalolin turarukan da ya kamata tayi amfani dasu.
Yau ma kamar kullum A'INDO na zaune bayan an gama mata wankan turaruka,da kuma abubuwan da take sha, na Karin ni'ima da ciciko gaba da dadi.
Tana zaune da book dinta wanda take d'aukan note na abubuwan da zata dinga gyara jiki dasu,,
Ladi Mai gyaran jiki tace"Aisha maganin mata ga mace yanada matukar mahinmanci a jikin mace ,rayuwa ce yanzu ta lalace zakiga mata sun haukace shan maganunnuka wa'inda basuda inganci bare kuma kyau,to shan maganin mata ba laifi bane,anma shi ba'a maida shansa ya zama kullum.
Zakiga wasu matan na cewa maganin mata bai dame su ba,wata ma kusan shekara goma zakiji tace tun na auren ta rabon da tasha, ko kuma basu ma taba sha ba,haba a matsayin ki na mace ace shekaru kusan sama da goma baki taba shan maganin mata ba,sai ya miki kishiya yazo yana ihu a gado kiji ance ai asiri ne,ko daya tsabar gyara ne,wacan ta fiki iyawa,a koi mata yanzu mafi yawa suna tsoron maganin mata saboda yanda duniya ta lalace,ko kasa yanzu mace sai ta saida tace maganin mata ne,hakan ta faru ne yanda mata ke haukar neman maganin mata, zakaga ko bazawara na Saida maganin mata,to in fitsari banza ne kaza ma tayi mana, tana Saida maganin mata ne mijin ya koro ta,dan me bai zauna da ita ba ko dan dadin ta dan haka mata mu farka,mu daina dura ma cik'in mu tarkace,ku sani amfani da tarkacen maganin mata marar inganci yana kawo infection,yana taushe mahaifa,yana hana haihuwa,sanan yana bata ma mace test dinta na dadi, akoi ingatatun maganin mata wanda ya kamata mata su dinga amfani dasu,su ma kuma ba kullum ba,a wanan zamanin na yanzu zakaga mace tanada dubu daya ta sayan maganin mata anma batada dari biyun sayen sabulu dan tsabtace suturar ta da ta yaran ta da kuma gidan ta,wata yanda taba maganin mata mahinmanci bata ba addinin ta ba.ba fa maganin mata kadai bane zaman aure,yake yar uwa idan kika rike Sallah,karatun Alkur'ani ,ladabi da biyaya,tsabta,tarbiyar yaran ki,kula
Da mijin ki sanan ki kulla da kasan ki,wurare hudu karki yarda mijin ki yaga gazawar ki a kansu ,tsabtar farjin ki, tsabtar bakin ki, tsabtar hamatar ki,sai kasan nonon ki,wa'innan wurare idan ba'a yawan kulla dasu miji zai raina mace,mata ku saki jikin ku yayin da akaje shimfidar mai gida a dage a koyi salo-salo na rikitar da miji,karki yarda kullum miji ne zai hau kanki kamar doki,a'a kema ki dinga hawa kansa kina nuna masa salo naki,girki kala-kala mu dage mu koya kar a barmu a baya,duk abinda kikaga ya fito na zamani Wanda ya danganci girke-girke ,kwaliya ce muyi kokarin iyawa,akoi matan da ko fowder wanan basu iya shafawa ba,jagira ta zamani basu iya ba,jan baki ma basu san yanda zasu daidaita su shafa a bakin su ya fito yayi kyau ba,a'a wata zakiga ta shafa har saman lebo,wata fowder zakaga tayi mata furu-furu kamar an fito da ita daga kabari,ko kuma a shafa iya fuska kawai banda wuya,a bar wuya bakikirin.sai ace ba'a iya kwaliya ba,duk macen da tace bata iya kwaliya ba to Bata koya ba ,kuma bata sa kanta ba,ba fa sai kinje koyo ba,a'a a waya ma sai ki koya,dayawan mazajen mu wanan k'waliyar ta zamani da Yan mata suka iya duk idan za'a unguwa sai suyi su fita shi ke janye hanakalin mazajen mu,ko kuma susa turare mai kamshi wanan shine fa,to mai zai hana muma matan auren muda mukeda garantyn auren mu koya,anma ace munyi dabas komai sai muce mun barma Yan mata mu yanzu mun tsufa,wanan ai abun takaici ne.
Wasu basusan Shirin da ya kamata suyi ma mazajen su ba daga safiya zuwa dare,da farko idan mace ta tashi tun asuba tayi sallah ta aza breakfast,sai taje tayi wanka ta shafa mai ta dan shafa fowder da lips,sai kwali ,ba sai tayi jagira ba,ta shafa turare ,ga mai hali ya zamana tana shafa turare kowane da lokacin da ake shafa sa, ma'ana,na safe daban na rana daban na dare daban,ga mai hali ya kamata ace dasafe tasa doguwar rigar abaya mai kyau ,da rana tasa atamfa ko less ko shada,da dare kuma tasa kananan kaya riga da wondo masu fito da surar jiki,ko kuma riga da siket kanana, ko kuma riga iya gwiwa,ko kuma wondo daidai cinya ko siket,riga marar hannu,mai fito da kirji,duk dai kaya kanana sune na dare,wajen barci kuma asa kayan barci masu fito da surar jiki da kyau.....
Cin Aya,kwakwa,dabino, kankana,gujiya,madara,
Rake,gurji,koncumber, idan mace na yawan cinsu suna kara ni'ima da dadi,tsuguno a karamfani yana matse mace,akoi abubuwa diyawa wa'inda ya kamata mu mata mu rike,bara na barki anan sauran zamu karasa daga baya......
Sosai A'INDO ta koyi abubuwa,Idanun ta suka bud'e bisa kan kulla da miji,ko a wathapp tana karuwa da abubuwa sosai...
Biki ya matso dan yau saura kwana uku a d'aura aure ,Yan uwa na nesa da na kusa duk zunzo,abokan Alhassan duk sunzo,hada na Paris duk suna Hotel,A'indo dai cewa tayi babu kawayen da zata gayata,ita da yan gidan ma ya isa, duk wasu dinkuna tayi .
Yayin da aka hado Mata lefe akwati goma sha biyu
A yau ne katuwar mota ta tsaya a k'ofar gidan Bashir,Anty ce ta shiga yana ciki zaune yayi tagumi yana tunanin A'indo,da kuma auren da yaji zatayi a TV abun yayi bala'in taba sa kamar mahaukaci ya koma,domin sai a lokacin yake jin wata guguwar sonta na tunkaro sa......
Anty ce tayi salama ta shiga falon ya amsa a sanyaye ,a shekeke Anty ta kalle sa tace"munzo d'aukan kayan Yar mu ne,Wayyo Allah Bashir karamin hauka yayi ,Anty ko a jikin ta nan tasa kata su shiga su fara fitowa da kayan .,aiko nan aka fito komai ko tsinke ba'a bar masa ba,anan ya kara rudewa,hauka yayita yi a gidan.
Suna isa gidan A'lhassan ya fito zai tafi Hotel ya kalli motar kayan bayan sun gaisa da Anty yake tambayar kayan meye wanan?
Nan Anty tace masa na A'INDO ne da aka d'auko daga gidan tsohon mijin ta."
Ransa ne yayi wani irin bacewa,yace"duk abinda aka fido daga gidan Bashir Anty ta rike dan ba abu daya da za'a shigar Masa dashi a gida.
Godiya Anty tayita yi,ta shiga gida ta fada ma Hajiya abinda A'lhassan yace,Hajiya tayi murmushi tace"Soja rikici,kawai kije dasu ki tambayi ita Aisha idan da abinda take so sai ta d'auka ."godiya sosai Anty tayi ta nufi b'angaren A'INDO.
Bayan kwana uku dubunan jama'a suka shaida d'aurin auren hassana Adamu ,da Alhassan Alhaji Sanmani,kazo kaga farin ciki da kuma washe hakora da Alhassan yaji an d'aura,anan naga yan groupe A'INDO & LATIFA SABON SALO group sun tafo da kayan su aka kawa Mrs Adam ce ke gaba tana janye dasu sai masifa take musu wai suna kauyenci🙄 su Zainab,Mrs Abubacar,Ummu Muhammad , Murjanatu ,Manman Adnan,kausar da sauran Yan group din group yancin ki su jikar kulu,Maryam ,da sauran su, group Yar Mutan kagara &Matar Abdoul duk an garzayo dan taya Alhassan da A'INDO murna, da cin shinkafa kazat 🤪harda masu tsine Masa ko kumya basuji ba🙄🤣.
*Masoyan A'INDO musanman yan group A'INDO and Latifa sabon salo,ina matukar yabawa da comment din ku, group Yar Mutan kagara &Matar Abdoul , group yancinki fans, group ana tare fans,da sauran wa'inda ban fada ba wallahi ina matukar jin dadin comment din ku,yana sa ni nishadi,duk ina lura daku, kuyi hakuri idan kunga bana maida muku hakan yana faruwa ne saboda ayukan da suke Shan kaina,sanan wa'inda suke min magana pc idan sunga bana dubawa kuyi hakuri ba shariya bace ko cin fuska,abubuwa ne sukayi bala'in yi min yauwa shi yasa ,plz wa'inda suke a group din da nake idan an tambayi A'INDO ku bada ku rage min abubuwa plz.*
[21/11 à 20:23] Mai Waina: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨
✨
*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋
*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚
*DAGA ALKALAMIN MARUBUCIYAR*
👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
_and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*
_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_
*My Maryam Obam ina tayaki murnar Kamala Litafin ki Najeeb, ubangiji yasa muyi aiki da darasin dake ciki,Allah baki ladan dake ciki kuskuren ciki kuma Allah yafe Miki sai mun ji ki a sabo mai dadi kamar na sauran litatafan masu dadi*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.