Aindo Part One Complete Hausa Novel
Reading file: Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part One Complete Hausa Novel.txt
Chapter 29 of 44
*Page 57-58*
A haka suka isa inda ake dinner ,gurin yayi bala'in haduwa, decoration din ja da fari ne,kai gurin ya tsaru iya tsaruwa,A'indo ta shigo da motar ta,inda Idanun mutane duka suka juyo kanta,babu.abinda kake ji illa waw da Masha Allah,tafiya take anma yawanci idanun mutane na kanta,har samarin wanda sukazo da yan matan su kallon ta suke,ita ko a kwalar rigar ta,daidai isowar su Alhassan,ko takan Mina baibi ba,ya fito daga motar ,yayin da take ta faman zagin sa...........
Fitowa yayi ya nufi inda yaga A'indo ta zauna wani saurayi yaga yazo zai zauna kujerar kusa da tata,da sauri Alhassan ya riga saurayin zama,da sauri A'INDO ta juyo sai ganin A'lhassan tayi zaune kusa da ita,ranta yayi bala'in baci zatayi magana kenan wayar ta tayi kara, kiran Husseina ne ya shigo,tasan me ke ma'anar kiran dan haka takai duban ta ga su Salma tace"ku tashi muje ga amarya da ango sun kusa isowa."
Tashi sukayi su shida,hakan ya kara ba Alhassan damar kara kallon surar ta,wanda yasa shi lumshe idanu, cik'e da shaukin ta,kamshin sanyayan turaren ta ya buge sa,a ransa yake yaba sura irin tata.
A k'ofar harabar filin sukaje suka jera,uku uku face to face, abin yayi bala'in yin kyau daga tsakiya inda zasu taka an shimfida dogon jan carpet, ba'a jima ba sai ga amarya da ango anzo,aka tarbo su,tare da musu feshin turare tare da watsa musu jar fulawa,hannun su sak'ale da juna suna murmushi sunyi kyau sosai,DJ ya saki kida mai dadi,mai cik'e da sanyaya Zuciyar Masoya, Alhassan na murmushi sai yake ganin tamkar shida A'indo ne ,fata yake Allah nuna masa shida A'indo ranar da zata amince masa,da ko a ranar yafi kowane da namiji farin ciki,a haka Amarya da ango suka zauna mazaunin su,nan DJ ya musu barka da zuwa tare da taya su farin ciki,sanan aka umarci da daya daga b'angaren ango da daya yazo ya bada takaitacen tarihin sa,inda aka tura Alhassan yaje yayi ,nan ya hau fili ya bada takaitacen tarihin kanin nasa tare da yabon k'yawawan halayan sa na gari cik'in harshen fransanci.
Bayan ya gama aka tatafa masa sanan aka umarci daya daga cik'in kawayen amarya wata tazo ta bada takaitacen tarihin amarya.
A'indo suka tura,da k'yar ta tafi gyaran murya tayi,tare da musu salama,nan ta fara bayanin ta da harshen fransanci Wanda yayi bala'in ba Alhassan mamaki yanda yaji tana francanci ba ko wani gargada cik'e da kwarewa,sanan bayan ta gama danan ta koma da turanci.kamar haka👉
_(My name is Hassana Adamu, popularly known as A'indo. I'm the brides maid, her sister and her_ birth twin._
_Hussaina is a very good person to live with, she respects her elders, she's jovial and lively. Sometimes she's troublesome, but whenever she sees something wrong, she tries to correct it. I'm not saying this because she's my sister, I'm saying it because that is just who she is. I wish them all the best in their marriage. My sincere appreciation to our invited guests, I wish them a safe trip back to their respectful destinations._)
Bayan ta gama aka mata tafi raf raf tare da burge dubunan mutane,hata amarya da ango ta burge su,sanan akayi mata tafi raf raf raf........yayyin da bashir ya shigo anma bata san yazo ba,shi kansa ta kara burge sa da shiga ransa.
A lokacin da ta gama,can ta hango sa nesa kadan yana mata murmushi wani farin ciki taji itama,yayin tayi gurin da yake direct, gaba-daya Alhassan duk wani motsin A'indo Yana ganin sa,har lokacin da ta isa wajen Bashir tana farin ciki,"la kalbi na
Yaushe ka dawo."
Murmushi yayi yace"my princess yanzun nan na dawo,na ganki.kinyi kyau princess anma gaskiya nayi kishi."
Dariya tayi ta jawo hannun sa sukazo suka zauna Wayyo Allah a lokacin idan kukaga yanda hankalin Alhassan yayi bala'in tashi ba'a magana,bare da yaga suna dariya cik'in farin ciki,wasu zazafan hawaye ne suka zubo masa,tashi yayi daga gurin ya d'auki motar sa da gudu yabar wurin gaba-daya shikam bai taba gaza d'auriya akan wani abu ba, kamar yanda ya kasa tsaida hawayen sa akan kishin A'INDO da sonta....
Lokacin da akazo za'ayi rawar bashir ya nuna bacin ransa tare da cewar bai yarda ba gaban wa'inan mazan A'indo tayi rawa ba,
Dan haka dole yasa ta hakura su sukayi rawar.
Mina kam ko a kwalar rigar ta da Alhassan ya tafi,ila ma wani abokin ango ta samu sukayi holewar su.
Masha Allah anyi taro lfy an watse lafiya,komai ya kayatar,washe gari misalin k'arfe takwas na safe dubunan jama'a suka shaida d'aurin auren Idrisa Alhaji sanmani da Husseina Adamu.
Bisa sadakin naira dubu dari biyu,hata yan kauyen su A'indo sunzo da Antyn su...
Masha Allah anyi taro lfy,an watse lfy inda aka kai husseina tangamemen gidan ta na gani na fada inda Alhaji da Hajiya sukayi musu Addou'a ,sai fatan Allah sanya Alherie.
Bayan sati daya da bikin su husseina ,a lokacin aka Kira Alhassan zuwa garin Niamey domin hada wasu takardu.
Kawun Bashir sukazo neman auren A'indo kuma an basu tare da sa ranar biki sati uku masu zuwa,cik'in farin ciki akaci gaba da gyaran A'indo,duk wani kaya da uwaye ke saye na diyan su sun saye duk wani kayan d'aki na kasar waje masu kyau da tsada,su hajiya sun sya Mata,yayin da yaran Hajiya suka koma Makaranta,saboda jarabawa ta kusa,ba kowa gidan,akwati goma sha biyu aka kawo ma A'inso bayan sati uku dubunan jama'a suka shaida d'aurin auren Bashir Al'Mansoor Kadafi da kuma A'INDO ,wato hassana Adamu.
Masha Allah d'aurin aure yayi jama'a,kasashe daban daban,yayyin da zukata biyu suke cik'in farin ciki, Anty da wasu daga cik'in yan uwan Hajiya su sukaje sukayi gyare gyaran d'akin A'indo,Masha Allah gidan yayi bala'in haduwa,ba yanda Bashir baiyi ba akan Kar akai A'indo da komai shi zaiyi,Alhaji da Hajiya sukace a'a su zasuyi ma Yar su komai,hakan ko akayi,harda Husseina a yan kai amarya,bayan Alhaji da Hajiya sunyi Mata Nasiha mai ratsa zuciya da shiga rai.
An kaita tangamemen gidan ta mai cik'e da kyau da kayan alatu.
Ayi hakuri da wannan
Kadan ne
Sorry time Al'Hassan😭
[27/10 à 20:39] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨
✨
*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋
*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚
*DAGA ALKALAMIN MARUBUCIYAR*
👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
_and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*
_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.