Aindo Part One Complete Hausa Novel
Reading file: Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part One Complete Hausa Novel.txt
Chapter 19 of 44
*Page 37-38*
Doctor yace" yace a gaskiya a yanda ta bugu munyi tunanin ma zata samu matsala a k'wak'walwar ta ,anma kuma sai muka samu akasin hakan,saide inda matsalar take shine idan har ba'a bar yi mata abinda bata soba Zuciyar ta na gap da kamuwa da ciwon zuciya ,dan haka a kiyaye abinda zai dinga bata mata rai."
Sauke ajiyar zuciya Hajiya tayi dan a yanda taji doctor ya fara magana tayi tunanin wani mumunan abun ne ya kuma samun A'indo.
Duk a fransanci doctor ke musu bayani suma a yaren suka maida masa cewar yaushe za'a salame su yace yau ma zasu iya tafiya."
A gadon asibiti Hajiya zaune A'indo na kusan ta cik'e da kukan farin ciki,yayyin da Mari ke b'angare daya a tsaye, A'INDO ta tashi ta dan dafa goshin ta da ya dan sara Mata gurin har ya dan kumbura,Hajiya ce ta taimaka mata ta zauna A'INDO rungume Hajiya tayi ta fara kuka tana fadin hajiya dan Allah ki taimaka ki rabani da danki,wly kasheni zaiyi bana son sa,a raba auren😭😭."
Tausayi taba hajiiya ganin yanda A'indo ta lalace ta rame,share mata hawaye Hajiya tayi tace"naji A'indo anma sai kinyi min Alkawarin zakiyi duk abinda nace kiyi,sanan zaki natsu kiyi hankali."
Saurin daga kai A'indo tayi tace"Hajiya wallahi na yarda zan natsu,ai na ma nutsu kuma wly Hajiya zanyi duk abinda kikace ."
"Good yayi kyau ,zan sa Alhassan ya sake ki anma sai kinyi karatu anma idan ba haka to saide na maidoki gidan sa."
"Wallahi Hajiya zanyi ko wane irin karatu ne,indai zaki rabani dashi."
Hajiya takai kallonta ga Mari tace"to Mari ba abinda zance dake sai Allah ya miki Albarka,kuma aikin da kikayi nagode sosai da kika sa min Ido a kansu kamar yanda na sa ki,yanzu zamuje gidan Alhaji da yake anan zamu kwana acan washe gari zamu koma Niger."
Murmushi Mari tayi tace"ba komai Hajiya aike uwa ce,dan haka karki damu."
Murmushi Hajiya tayi tana yaba halin Mari.
Mari dai yar kawarta ce da ta rasu shekaru biyu da suka huce,Yar gidan Alhaji Usman ce,mai Kudi ne a a Niger garin Zinder,Mari zawara ce ,dan ta taba aure,shine lokacin da zataje Karin ilimi akan aikinta na soja sai kuma akayi sa'a Alhassan ne zai kara bata horo hakan yasa Hajiya ta kira ta ,tace"ta kullar mata da A'indo duk da bata fada mata cewar matar Alhassan bace,anma tace yarinyar yar uwarta ce ,
Wanan dalilin yasa duk motsin A'indo a idanun Mari .
To Hajiya ni zan koma bakin aiki insha Allah nima a satin nan zan koma Niger,idan naje zanje can Hajiya saboda akoi magana mai mahinmanci,sannan ta dafa A'indo tace"to kanwata Allah ya baki lafiya sai mun hadu a Niger idan Allah ya kaimu."
Murmushi A'INDO tayi sanan suka rungume juna Mari ta tafi takai bakin k'ofa A'indo tace"Anty ya zancan mu da fa gaske nake,dan a yanzu burina kenan😊."
Murmushi itama Mari tayi tace "karki damu insha Allah burinki zai cika,kiyi kokari ki warke,kuma ki dage ki samu ilimi tukon."
Mari na gama fadar haka ta fita, A'indo kara rungume Hajiya tayi tana sauke ajiyar zuciya,koda doctor yazo ya dudubata sannan ya salameta tare da rubuta mata wasu maganun nuka.
A gidan Alhaji dake garin suka kwana washe gari jirgin su ya daga zuwa Niger.
Gaba-daya Alhassan ya rude ,ya razana ya rasa abinda ke masa dadi,farin cik'in sa guda ne idan ya tuna cewa yanzu fa ya rabu da wanan jakar kuma jahila ,yanzu burinsa daya ne shine ya shawo kan iyayen sa su yafe masa sanan su aura masa Mina ,wanan ne kadai matsalar sa.
Bayan su hajiya sun sauka akazo d'aukan su da mota,abun mamakin da A'indo ta iske bai huce yanda ta tarar da yar uwarta Husseina ba ta fito daga islamiya,ta fara nutsuwa,ita kanta Husseina da gudu tazo ta tarbi A'indo tana murna da farin ciki tare da mamakin ramar da A'indo ,anma jin Hajiya tace "Yi a hankali husseina A'indo karaya ke gareta."sai taja baya ta tsaya,hawaye ne suka fara zuba a idanun ta tace"meye haka hassana ya akayi kika karye,me ya sameki haka"?
Dafata Hajiya tayi tace "Husseina ki barta mana ta huta daga baya kunyi magana."
Kama hanun A'indo hussaeina tayi suka fice d'akin su na da Wanda a yanzu aka kara gyara sa komai akoi,su din tamkar ya gida aka d'auke su ba yan aiki ba,dan haka harda A.C aka sa musu a d'akin su.
Komai akoi,Hajiya ta kalli A'indo tace"A'indo je ki huta har a jima.
A d'akin su zaune A'indo ke tambayar Rabi'u daudu ,Husseina tace"ya tafi hutu ."
Husseina matsa ma A'indo tayi ta fada mata abinda ke Faruwa da ita ta koma haka ,A'indo bata boye mata komai ba ta fada mata duk wahalar da tasha a gidan Alhassan."
Kuka Husseina keyi harda shasheka ,tana tsine ma Al'Hassan,sannan daga baya ta share hawayen ta tace"A'indo shi yasa na nutsu na shiga islamiya,a yanzu haka Hajiya har Makaranta ta sa ni, wallahi na tsaya nayi tunanin ba komai ke damunmu ba illa jahilci,dan wallahi da ace a waye muke babu wace ta isa ko wanda ya isa ya wulakanta mu,A'indo a tafiyar ku na hadu da Mansoor ganin sa na farko da nayi , naji ina bala'in son sa, anma sai me ranar na fito domin a yanzu kusan kullum sai na zauna k'ofar wanan gidan dan na gansa naji dadi,saboda dan wanan gidan ne na gaba damu kadan,anma sai me ranar na gansa shida wata yarinya,a tunanina kanwar sa ce ,a nawa jahilcin sai naje na tare sa nace Ina son sa dan Allah ya so ni ,anma sai me,ji nayi ya kwada min mari,tare da zagi na uwa uba,tare da cewa mai zaiyi da irina yar kauye kuma jahila,marar aji, ya nuna min budurwar sa wada daga ganin Yar masu kudi ce kuma wayaya mai ilimi ,yace itace matar da zai aura,dan haka bashi ba, ko mai gadin gidan su ya huce ajina."
A ranar nayi kuka, hankali na ya tashi,sanan a ranar na tsani kaina,da ban tsaya na nemi ilimi ba,bayan shirme da jahilci da na zuba,wallahi a yanzu karkiso kiji yanda nutsuwa ke zo min,dan Allah A'indo kema ki nutsu mu nemi ilimi mu huce takaici ."
Rungume juna sukayi suna kuka A'indo tace "insha Allah na miki Alkawarin neman ilimi nima,sai mun zama wa'inda Al'umma zasuyi Alfahari dasu.
Husseina ni dama tun kafin kimin maganar ilimi nayima kaina karatun ta nutsu, Husseina a yau burina bai huce na zama nima wata babar soja ba."
Waro idanu Husseina tayi tace"ke A'indo ki rufa ma kanki asiri Ina ke ina wani zama soja,aikin soja ai na maza ne,ina laifin ma kice likita kamar yanda nakeda buri."
"zakiyi mamaki kuwa anma Alkawari na d'auka insha Allah sai nayi soja."
Murmushi sukayi sanan suka hada hannuwan juna saka fara magana a tare kamar haka cewar "munyi Alkawari,sai mun cika burin mu insha Allah."
Alhaji zaune shida Hajiya ransa a bace jin abinda Alhassan yayi ma A'indo,Alhaji yace"kinyi min daidai abinda kikayi,kamar yanda yace yana son ya auri wanan yarinyar da yace zan aura masa ita,duk da ba yar gidan tarbiya bace,tunda nayi bincik'e,zamu aura masa ita ,tunda yace zabin sa ce."
"Kwarai Alhaji Nima na goyi bayan ka Masa auran,dan idan ma bakayi ba zai iya ja mana abin kumya,ni yanzu kawai abinda nake so gobe aje a saka A'indo itama islamiya da kuma Makarantar boko,sanan a d'auko musu Wanda zai dinga zuwa nan gidan yana kara koya musu lesson."
Aci gaba da gashi😘
Maimou love🍇
[12/10 à 20:42] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨
✨
*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋
*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚
*DAGA AKALAMIN MARUBUCIYAR*
👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
_and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*
_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.