Complete Hausa Novels

Aindo Part One Complete Hausa Novel

Reading file: Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part One Complete Hausa Novel.txt

Chapter 34 of 44

*Page -67-68*

ta sume,waro idanu Husseina tayi a razane idrissa da bai ida fita daga gidan ba ta madubi yaga abinda Bashir yayi ma A'indo ,da gudu ya fito daga motar ya nufo su husseina hankali a tashe ya shiga falon ya iske Bashir sai famar huci yake ba shiri yaji idrissa yakai ma Bashir duka a baki,waro idanu Bashir yayi yace"Kai dan uwarka ni zaka doka,
"an dokeka dan iska Wanda baisan darajar mace ba,dama dan ka halaka ta ne yasa ka aureta,dama tunda naji zuciya ta bata kwanta da kai ba nasan kanada wata boyayar fuska a tare dakai."

Dambe ne ya kaure a tsakanin su,inda idrissa ya samu Sa'a ya kayar da Bashir yanata jibga, Husseina ce ta kwala ihun kiran Idrissa tace"idrissa yanzu ba lokacin fada bane dan Allah kazo mu kaita asibiti kaga bata hayacin ta,ga jini da take zubarwa."

Saida idrissa yayi ma Bashir jina jina sanan ya sauka daga kansa ,da gudu suka talabo A'indo suka sata a motar su sukayi asibitin sa dashi da gudu, koda suka isa aka amshe ta ,akayi urgence da ita,nan aka hau kanta dan ganin an tsayar da jinin,anma ina saida ciki ya zube gaba-daya,da k'yar suka samu suka shawo kan matsalar.
Anma ciki kam ya zube,saida akayi Karin jini,da ruwa, gaba-daya ta rame ta fita hayacin ta.

Alhamdulillah Alhassan jiki yayi sauki inda a yau ne kuma aka Salamo sa,duka yan aikin sa da manyan mutane,hata shugaban kasar saida yazo ganin sa,anma banda Mina,a yau aka Salamo su,kuma a yau suka taso,dan takanas shugaban kasa ya bada jirgi aka taho dasu.

Masha Allah ,idan kaga Alhassan kamar ba majinyaci ba,yayi kyau yayi freshe,kawai ramar da yayi ce zaka tabatar da cewa yayi jinya.

A'INDO Saida tayi kwana biyu Husseina ke kulla da ita,anan Suma idrissa ya salamo ta,direct gidan Hajiya suka nufo wanda yayi daidai da shigowar motocin da sukaje tarbon su Hajiya da Alhassan.

Idrissa ne ke jan motar bayan motocin su Alhassan sun gama shiga shima sai ya danno da kan motar sa.,idrissa na murmushin jin dadi suka fito harda A'INDO wace duk ta rame da Husseina, Hajiya ma fitowa sukayi ita da Alhassan,kusan a tatare duk suka fito.

Duk yanda A'indo takai ga ramewa bai hana Al'Hassan ganeta ba ,sai yaji duk ba dadi ganin ta a haka,dan daga gani yasan batada lfy,saurin kawar da fuskar sa yayi sakamokon tunawa da yayi yanzu fa ita matar wani ce,juyawa yayi tare da fakar Idanun mutane yayi saurin goge yar kwalar da ta zubo masa, idrissa ne yaje ya rungume Alhassan yace"waw brother kunyi mana surprise,ya jikin."

"Alhamdulillah."
Alhassan yace tare da sakin Idrissa,ya kalli Hajiya yace"Mom zanje b'angare na na huta."

"To Hajiya" tace

shiko yace hakan ne dan Sam baya son yana ganin A'INDO,dan idan yana ganin ta wani sonta ke kara fizgar shi.

Hajiya ce ta kura ma A'INDO idanu,tare da jansu ita da Husseina,sukayi b'angaren su idrissa na biye dasu.
Halissa ce ke gidan wace har yanzu take zaune miji yaki sakin ta kuma yaki zuwa,dan Khalissa ita tana gidan idrissa yanzu haka ma.can ta koma da zama,saboda kumyar cik'in da tayi,idan ta zauna kusa da Hajiya kara mata damuwa take,yayyin da har yanzu ta kasa fadin waye ya mata cikin.

Bayan sun shiga sun zauna falo, Rabi'u daudu wanda ya dawo daga hutu,ya kawo musu juis da abin ciye ciye, yanata murna,sanan ya tashi domin komawa kitchen.

Hajiya ce tayi gyaran murya tace"Aisha meye ya faru Kika koma haka,Ina mijin naki?

Kecewa da kuka A'indo tayi,nan ta fara ba Hajiya Labarin abinda ya faru,tun da aka kaita tana amarya da yanda Bashir yaso juya Mata mahaifa,har dukan da yayi mata da kuma sakin da yayi mata ,tare da shairin zina .

Innalillahi wa'ina illaihi Raju'un kawai suke nanatawa,dukansu kowane saida ya zubar da kwala,Hajiya tace "Allah nagode ma Allah ka bani ikon cinye wanan jarabawar da take fadawa akan yara na,shairin zina ai ba karamin abu bane,idrissa yace"Mom wallahi sai naja dan iskan nan shari'a."

"a'a karkayi haka,ka barshi da Allah,shi yayi ma kansa,kuma kanshi ya cuta bamu ba,Allah yasa hakan shi yafi Alherie,Aisha kije wancan d'akin ku dinga zama keda Halissa tunda yanzu kamar mai jego kike sai an kulla dake.

Nan tace husseina ta kama ta takaita gatanan zuwa bara tasa a aza mata ruwan zafi.

Rai a matukar bace ya juya d'akin sa yana huci,duk abinda ya faru da A'indo Alhassan yaji,domin kuwa mantuwa yayi a jakar Hajiya shine yazo d'auka ,zai shigo ne yaji abinda A'indo ke fada shine ya tsaya yaji komai. wayar sa ya d'auka ya kira idrissa yace yazo d'akin sa zasuyi magana ,tashi idrissa yayi ya nufo d'akin nasa.

Alhassan ya daga kai ya dubi idrissa da ya shigo ,shi kansa idrissa saida gaban sa ya fadi dan daga gani kasan ransa ya baci,"Brother lfy? nagan ka haka."

"Idrissa Ina ne gidan wanan dan iskan da ya dake ta.?

Koda yace haka

Idrissa ya gano cewar lalai Alhassan yaji komai,zama idrissa yayi ya dafa dan uwan nasa yace"Yaya kayi hakuri ka bar zancan tunda kaji abinda Mom tace,dan ko ni nan kafin na fito daga gidan sa saida na bubuge sa,kayi hakuri,mubi umarnin mahaifiyar mu plz."

Sauke ajiyar zuciya Alhassan yayi yace" shikenan."

Dafa sa idrissa yayi yace"brother ka kwanta ka huta,bara na tafi wajen aiki."

Lumshe idanu Alhassan yayi tare da kada Kai.

Tunda idrissa ya fita Zuciyar Alhassan zafi kawai take masa, duk ji yake ba dadi,jin yake kamar shi akayi ma wanan wulak'anci ba A'INDO ba.

*Bayan sati biyu*

Duk wata kulawa da ta dace Hajiya tana ba A'INDO,tana kulla da ita tamkar mai jego,
Sanan duk wani gyara tana Mata,tuni A'indo ta dawo yanda take,ta warware ta cika tayi freshe,Sam ta fida damuwa daga ranta,dan dama zama a gidan Bashir tamkar cik'in kaya take,yanzu ko da suka rabu daidai take Jin kanta,abu guda ne idan ta tuna yake mata ciwo shine yaudarar da Bashir yayi mata,da kuma shairin zina da yayi mata.

A wanan lokacin kuma tuni Bashir ya fara raina kansa,domin kuwa ya saba da cin abincin A'INDO,ya saba da shiga cik'in kogin zumar ta mai dadi,ya saba da adon ta,da yanda take gyara masa gida yayita kamshi,gashi idan yana cinta wallahi wani bala'in dadi yake ji kawai baya Fadi ne,baya sambatu dan karta raina sa,a yanzu bayada aiki sai zama yana tunanin ta.

A yanzu Alhassan kullum yana tare da Halissa zaune idan ya gansu zaune itada A'INDO sai yazo shima ya zauna to daga A'indo taga haka sai ta tashi ta bar wurin abun baya masa dadi, hakuri kawai yake.

Yau ma kamar kullum yazo ya zauna falo suna hira,ita da Halissa.

Halissa ta tashi dan d'aukan wayar ta a d'aki zatayi waya ,itama A'indo tashi tayi zata bar wurin,sai jin muryar Alhassan tayi yace"haba Hassana ko ba komai ai ni matsayin yaya nake a gun ki,me yasa kullum idan nazo kike tashi daga gurin kina kyama ta tamkar kinga Kashi."

"Saboda banga abinda zan tsaya ma ba,me zan maka idan na tsaya,kaga Malam banida wata halaka da kai dan haka ka shafa min lfy."

"Haba Hassana me yasa kin kasa yafe min laifin da nayi miki,karki manta Allah mu ma muna masa laifi kuma yana yafe mana sai mu yan Adam, wallahi hassana na yarda zan d'auki k'addara a duk yanda tazo min anma bazan iya hakurin fushin ki a tare dani ba,Hassana Allah ya nuna min ishara tun daga Matar da nake aure yanzu,zuwa ga kannaina,ga wanan accident din da nayi duk hakkin kin ne ke dawainiya dani,kiwa girman Allah ki yafe min kura kurai na,wallahi Allah hassana tun daga gareki na daina wulak'anta duk wata ya mace,ki taimaki rayuwa ta ki yafe min."😔

Ko kallon sa batayi ba ta buga tsaki tabar wajen,dan ita yanzu kara jin tsanar maza ma tayi,duk da a yanzu bata ma Alhassan kiyayar da take masa ada,anma bata son basa fuska ne har wani shakuwa ya shiga tsakanin su,hakan yasa taki basa fuska ma.

anan tabar Alhassan,kansa na sara masa,ya rasa yanda zaiyi da rayuwar sa,ashe haka ciwon so yake,shikam ji yake da ma ba'a halace sa ba a duniya.

Alhassan sha'awa ta bala'in yi masa yawa,anma baisan yanda zaiyi ba,wanan wace iriyar rayuwa ce haka ace kanada mata anma sam da kaida wanda baida duk daya,shikam dole ya nemi daddy ya gaji da wanan auren .

Tashi yayi jikin sa a matukar sanyaye yabar falon d'akin sa ya nufa,ya d'auki wayar sa number Mina ya lalubo kira daya biyu ta d'auka,tana d'auka ba ko salama tace"ya akayi ."

Rai a bace Alhassan yace"idan kinga dama ki dawo Nigeria,dan na gaji da rainin hankalin ki,idan kuma can zaki zauna to Zan turo miki da takardar sakin ki."

Yana gama fadar haka ya kashe wayar sa.

Aci gaba da gashi🍇
Maimou love😘
[10/11 à 22:14] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨

*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋

*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚

*DAGA ALKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
_and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*

_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.