Complete Hausa Novels

Aindo Part One Complete Hausa Novel

Reading file: Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part One Complete Hausa Novel.txt

Chapter 12 of 44

*Page 25 _26*

,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,Sosai yan sandan suka hassala,sai ga Hajiya da Rabi'u daudu,Hajiya tace "ranka ya Dade lfy?

"Hajiya wanan ce da ita da wanan ya nuna Rabi'u sukazo office sukace damu barayi sun shigo gidan nan,shine yanzu muka shigo wanan take nuna mana kusaye wai sun sace Mata kudi,a gaskiya Hajiya sunyi wasa da hukuma dole a hukunta su."cewar daya dan sandar da ransa yafi baci ,kululu cik'in Rabi'u ya bada sauti,yayi bala'in tsorata,shikam ya ma fi A'indo hauka da ya biye mata,Sam ya manta ya tambayi A'INDO wane irin barayi ne.

"Anma A'indo Allah shi kwashe miki Albarka ,yanzu saboda Allah bazaki ce min kusaye ba,kisamu wahala a banza,ki tado bayin Allah nan daga aikin su,ke kinko san kwalawan nan basuda dadi fa aradun Allah🙄ranka ya dade wly ni dan rakiya ne ,da ta fadamin a tunani na barayin gaske ne,shi yasa na biye mata."

Cewar Rabi'u daudu."

"Yau ni naga ikon Allah yanzu saboda Allah ace k'asa ba'a son gaskiya,ba za'a ba mai gaskiya gakiyar sa ba ,a kwatar masa hakin sa,a kama azalumai ba,wai ace ba za'a kamasu ba,dan Allah ranka ya dade ka kama min wa'innan kusayen su fido min da kudi na,yau nake tunanin sayan rago na turka anma saboda Allah yanzu kudin nawa ace an sace min sanan nakai Kara ace ba za'a fida min hakina ba."😭wanan magana A'indo take fada, tsakani da Allah take kukan ta tuburan ,tana sai an bi mata hakkin ta ga kusaye."

Hajiya ganin da tayi yan sandan kamar sun d'au zafi,kuma komai zai iya faruwa,k'arshen ta ma su rufe A'INDO har Rabi'u, din , tace"dan Allah ranka ya dade kuyi hakuri,yaran nan har namijin basuda hankali ne,sun samu tabin k'wak'walwa ,dan Allah kuyi hakuri ba yinsu bane ,jakar ta aka d'auko mata taba yan sanda dubu hamsin ,tace susha Mai."

sai a lokacin yan sandan suka sauko suka amshi kudin suka fito,sun taho a daidai tsakiyar gida sai ga Husseina ta dawo daga yawon ta,irin kayan A'indo ne tasa komai iri daya,dan ko a kauye in za'a musu kaya komai iri daya ake musu,wa'inan yan Sandan ganin husseina ba karamin rudu da tsoro sukaji ba, domin kuwa daya daga ciki saida cik'in sa ya kirta,domin kuwa sudai sunsan da sun baro ta a cikin gidan,ashe suma yan sandan na waje tsaye sukayi a sankare saboda sudai sunsan yarinyar da suka zo da ita tana ciki to ya akayi haka ,kodai Aljana ce,shikam dan sandan na cikin gida Wanda suke tare da biyun wanda Hajiya ta ba kudi,kusan zawo ya kusa kufce masa,dan shi kansa da gudu ya fita daga gidan,su kansu biyun ta maza sukayi,dan Kar aga gazawar su.

Ita kam Husseina ko a kwalar rigar ta,harara ma ta bala musu,tayi gaba abunta tana yar wakarta.

Haka yan sandan nan suka koma wasu cik'e da tsoro,wasu kuma cik'e dajin haushin raina musu hankali da akayi,wasu kuma suna murnar samun kudin da sukayi.

A"indo tana ganin yan sanda sun tafi ta Fadi a gurin ta fara birgima tana kuka,sai an bi mata hakkin ta,Hajiya ta girgiza kai,tare da mata Addou'a shiriya, tayi gaba,Rabi'u ma barin gurin yayi bayan yaba Hajiya hakuri,aka bar A'indo tana kuka .

Husseina ta shigo ta iske A'indo na kuka,nan itama ta zauna ta mike k'afafuwa ta bud'e baki iya k'arfin ta itama ta fara zabga kuka kamar Allah ya aiko."

Tsayar da kukan A'indo tayi ta kalli Husseina tace" ke kuma lfy?

Murguda baki Husseina tayi,sanan taci gaba da kukan ta,itama A'indo da taga ba amsa itama ta juya taci gaba da kukan ta , haka sukayita kuka,har barci ya kwashi Husseina,itako A'indo tashi tayi tana tafiya tana kuka ta nufi kichen abincin ta loda a katon plat ,naman kaji da shinkafa da miya uban me yauwa, wanda mutum biyar zasu iya cin sa ,kuma su koshi,nan ta zauna falon Hajiya ,sai ta ciko hannu da katuwar loma ta zuba a baki,tana gama cinyewa,zata saki kuka ,kuma ta kuma kwasowa ta zuba a baki ta tsayar da kukan sai ta cinye na bakin kuma sai ta kece da kuka
Haka tayita kukan ta har Rabi'u daudu yazo ya iske ta a wanan yanayin,talabo harbar sa yayi da hannu ,ya fara salalami,yace"ni kam sai yau na taba ganin wanan ikon Allah,aradun Allah A'indo kina bukatar rukiya,dan wly inaga Alamun mutanen boye ne."

"Ai ba ma sai kayi magana ba,nasa a kirawo liman na wanan unguwar,kuma inaga har kai kana bukatar rukiyar,cewar Hajiya da take saukowa daga sama ,dan tuni tayi waya tace a Kira mata malam yayi ma A'indo rukiya,domin kuwa ita lamarin A'indo tanaga akoi mutanen boye a tare da ita,abun ya fara bata tsoro,tun yanzu gwara suyi maganin abun kafin su tafi.

Bata gama saukowa ba,sai ga daya daga cik'in masu aiki ta shigo tace"Ma ga malam yazo."

"Yauwa ce ya shigo cewar Hajiya,da take zaune a daya daga cik'in kujerun falon,ga A'indo tana cin abincin ta tana kuka , Rabi'u kusa da A'INDO yana tsokanar ta.

Malam ne ya shigo tare da salama ,Hajiya ta amsa,ta nuna masa guri ya zauna,aka kawo masa abun motsa baki,Nan Hajiya tace "yauwa malam yarinya ta ce gatanan,wly abubuwa take tamkar Mai mutanen boye,sam bataji."

"To Hajiya ba matsala zan mata yan tambayoyi,daganan za'ayi rukiya,mu gani,Nan malam ya fara ma A'indo tambayoyi,ta murguda masa baki taci gaba da cin abincin ta tana kuka,Malamin dama irin wa'inan malaman Nan ne,wato muna malamai,masu son banza,nan ya guso ya fara ma A'INDO rukiya, itako A'indo wani haushin sa take ji,ga takaicin an sace mata kudi ba'a biyata ba,kuma wanan yazo yana wai rukiya,.

Tsagaitawa Malam yayi,ya Umarci su hajiya da su tashi a barsa daga shi sai A'indo ,nan yayita karatun sa ko a kwalar rigar ta,can bayan dan wani lokaci yace su hajiya su fito, yace"da Hajiya ai Hajiya munsha daga da Aljannun ,guda shida ne a kanta."

Waro idanu A'indo tayi 😨tace"tab yekuwa jama'a ina makaryata suke,to kuzo ga uban ku ,kuma shugaban ku,anma wly ba'aji dadin dan Hali ba,yanzu kai Malam saboda Allah muna anan zaune kace ka fida Aljani shida,🙄 bayan ka cinye min tuwo na,tab zuki tamale,aradun Allah anji kumya,."

Cewar A'INDO.

Shikam malam kuri kuri yayi,dan yasan yarinya batada komai ,kawai yayi haka ne dan ya samu Yan kudi.

Hajiya ta gane dan haka ta d'au dubu goma ta basa tare da godiya,ai A'indo na ganin wanan kudin ta fadi kasa tana birgima tare da kuka,wai anba makaryaci kudi.....

Addou'a neman shiriya Hajiya tayi ma A'INDO.

A yan kwanakin nan hajiya dama taba antyn A'INDO duk wasu kudi Wanda akayi ma A'indo dinkuna ,kala kala,na kece raini ,masu yauwa da tsada,babu abinda ba'a mata ba,a kayan sawa,ko yayan masu kudi sai haka,sanan Antyn A'indo kulum zuwa take domin Kara ma A'indo fada,da nutsar da ita,haka Hajiya ma na iya kokarin ta,anma abun na A'indo sai abinda Allah yayi,hata shirin kauye anyi anyi ta daina ta Kiya,sai tasa bunguzuma banguzuman katuwar riguna da zani,tayita yawon ta,kayan da take sawa ko uwarta kuluwa sai tasa,anso kayan tasa anma ta kiya.

A yau ne tafiyar su A'INDO ta Kama,zasu shiga jirgin k'arfe bakway,sosai Alhaji da Hajiya suka yima Alhassan fada,A'indo ma haka,Husseina da A'indo sunsha kukan rabuwa, Rabi'u ma harda Yar kwalar sa,akayi filin jirgi,zo kuga yanda A'INDO taki shigar jirgi,tana kuwa,da abun ya ishi Alhassan ya faki Idanun ta ya hada wata alura ta barci ya mata,anan take barci ya d'auke ta bayan sun Shiga jirgin,Dan ihu ta dingayi wai an hada baki za'a kashe ta,shiko Alhassan cik'e da takaicin ta yake,yana ta tunanin irin akubar da zai dinga mata......

Ana tare muje zuwa🤝🏻
[10/10 à 17:34] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨

*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋

*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚

*DAGA AKALAMIN MARUBUCIYAR*

👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
Na yanzu👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*

*banza, jaki ,dan rainin sense yanzu Kai bakaji kumya ba,kuna d'aukan book din mutum kuna saidawa,ba tare da izinin mai litafi ba,wly ka sani ni Maimouna ban amince ba kuma ba da yawuna ba,idan ka kara saida min litafi Allah ya isa, ban yafe maka ba,idan kudi nake so nida kaina zan sayar,ko ka fini son kudi ne,to bara kaji wly na Kara jin ka d'auki ko/ kin d'auki litafina ko litatafai na an saida wly zanyi karan mutum,haba hinmu son kudi akayi ne dan zalunci mu da wahala wasu da cin wahalar mu*

*Sanan fans ku sani duk wanda ya kara ce muku Novels nawa na kudi ne yayi karya,duk mai son novels dina ta nemeni ta wananan number --------->+227 80229915*,
*Karku kara yarda a saida muku book,ga litatafan da na rubuta nan a sama duk maiso tamin magana inada dukan su zan bata, na fada da baban murya bana novels na* *kudi,sanan zan kara jadada masu fida sunana su canza suna a book din,harda sunan litafi,to wly karku Kara,dan wly zanyi shari'a da koma wacece,ko wanene,in kunne yaji jiki ya tsira*🤷‍♀

_DEDICATED TO Sadjida & Ummy Ontop_

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.