Aindo Part One Complete Hausa Novel
Reading file: Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part One Complete Hausa Novel.txt
Chapter 28 of 44
*Page -55-56*
Halissa ce ta shigo falon,ta ga yayanta a haka,a tsorace ta karaso inda yake,tana jijiga sa,tare da fadin" Yaya yaya plz ka tashi ,me ya same ka?
Wayyo Allah ,da gudu taje ta d'auko ruwa a firge ta yayafa masa,nan take numfashin sa ya dawo,a hankali ya fara bud'e idanun sa,har ya sauke su akan kanwar sa, murmushi yayi wanda yayi nuni da iya lebo kawai ya tsaya,ya tashi da k'yar da taimakon Halissa ta taimaka masa suka idasa saman kujera,tace"yaya bakada lfy me ya fito da kai haka"?
"Oh kanwata na gaji da zama d'aki ni kadai ne,kuma kinga bikin dan uwana ake."
Mina ce ta shigo falon sanye da riga da dogon wondo,tasha Attachment na gashi,ga farata zako-zako da tasa,tasa yar karamar hula,ga uwayen takalma dogaye masu tsini da tasa,da alamun fita zatayi.
Tana cin shuiwingwom irin na yan duniya,tsohin karuwan nan wanda suka shahara a bariki,kallon sa tayi shekeke,tace"key zaka bani na motar ka,dan ita nake son shiga yau zanje salon."
Daga kai yayi ya kalleta,ya girgiza kai cik'e da takaici,yace"fita da zakiyi kin tambaye ni ne?,sanan kina yar musulmi zaki fita haka bugu da kari da auren ki,wai Mina me kika d'auke ni ne?
Ina matsayin mijin ki ina kwance ba lfy anma ko kije ki duba ni ,babu abinda kike min na matsayina na mijin ki,sai abinda kika dama kike yi,wallahi nayi dana sanin auren ki,kaicon Rayuwa ta,nayi watsi da zabin iyayena, wallahi Mina matsayin baki canza ba bazaki ga da kyau ba"!
"Hum au kace malam ka koma ban sani ba,to bara kaji rayuwa ta ce,a haka ka ganni sanan a haka ka auro ni,Dan haka
Kaide baka isa kace zaka hanani abinda nake so ba, duniya ta canza yanzu kuma kowa yanada incin yin abinda yaga dama,dan haka Kai baka isa ba ka hanani abinda nake so ba,kudi nake so naira milions daya zanyi hidimar biki dan haka kai nake jira."
Zaiyi magana tari ya turnike sa, Halissa ce tashi rai a bace tace"ke ko wace irin jakar mace ce?
Mijin ki baida lfy anma ko a kanki,so kike ki kashe mana dan uwa,to wallahi ahir din ki ,ki kiyaye ni."
"Keko asu wa karan kada miya,wa ya tsoma bakin ki aciki?
Wanan maganar da yayan ki nake yi ba ke ba,domin ke baki isa ba ina musayar yawu dake,saide shi da yake sa'a na dashi nake.
Murmushi Alhassan yayi wanda yafi kuka ciwo yace da Halissa,"kanwata barta kyale ta tayi abinda taga dama ita da Allah."
Hararar juna sukayi tsakanin Mina da Halissa,sannan Mina tayi tsaki tayi ficewar ta, b'angaren Alhassan ta nufa,wata bakar jakarsa ta gani ta bud'e,dolar na kudi ta gani,tasan su dan haka ta debi iya daidai millions daya,ta duba key din motar sa ta d'auka tayi ficewar ta,babu wanda zai ganta ya kira ta bahausa,kuma musulma,musulmar ma matar aure,mtssss Allah shi kyauta......
Bayan fitar Mina Halissa ta kalli Alhassan tace"yaya wai me ka gani a jikin wanan kwarangwal din ka aura,kuma yau wai kaine mace ke fada maka magana haka kaida suke bi ka so su,anma yau kaine wata kucakar mace ke ci maka mutunci,yaya me wanan zata gwada ma tsohuwar Matar ka A'INDO, ai wallahi wanan a komai tsohuwar Matar ka ta fita,aji class,kyau,nagarta,sura, ilimi,Kai komai tafi ta,nesa ba kusa ba.wallahi kayi sake yaya."
Zuciya Alhassan ya danne,tare da tari,yace"ya isa haka,halissa,karki kara min wani ciwon,ni kadai nasan abinda nake ji a zuciya na,ni kaina nasan cewar Alhakin Aïcha ne ke azabtar dani,dan Allah ki taimaka kema ki tayani neman gafarar ta."
Murmushi Halissa tayi tace"insha Allah yaya."
Shikam runtse idanu yayi,tabas ba karamin mugun so yake yima A'indo ba,so na Allah yake mata,domin kuwa Sam baya jin wai wata sha'awar ta,ko wani abu na jikin ta,a'a ita din zahirin ta yake so,tabas Koda ace a yau A'indo ta zama ba kafa ba hannu shikam zai iya auren ta,"ya ALLAH!"...
Ya fada lokacin da yaji wani sonta na kara ninkuwa a zuciyar sa.....
A'indo ko da fitar ta ranta a matukar bace ta Kira Bashir,yana Office yaga Kiran ta, murmushi yayi tare dajin wani sanyi a ransa,saida ya bari kiran ya tsinke tukon ya kira ta,d'auka yayi tace"idan kanada lokaci inason magana dakai."
Murmushi yayi yace"ran gimbiya ya dade gani nan zuwa insha Allah nan da minti talatin."
Kashewa tayi ta koma b'angaren su suka ci gaba da hidima,bayan minti talatin sai ga Bashir,ya kira ta yace ya iso.
Da yake gidan akoi mutane sosai dan haka tace dashi ya jira ta a mota gatanan fitowa,tana fitowa ta isko sa k'ofar gida,shiga motar tayi,shiko Bashir ya lumshe idanu,domin kuwa dama yanada kishirwar ganin ta.
Gaida sa tayi,bai amsa ba sai illa kallon ta da yake tayi yana murmushi,juyowa tayi taga ita yake kallo, zumburo baki tayi cik'in shagwaba tace "meye kuma ina gaida kai baka ma amsawa."
"Oh sorry princess kinsan idan ina ganin ki,bana gani bana ji,nayi kewar ki sosai anma fada min waye ya taba min ke? Dan naga yanayin fuskar ki ya canza."
Murmushi tayi sanan kuma tayi fuska,Alamun ba Wasa tace"bash so nake nan da sati ka turo iyayen ka neman aure na,sanan wata daya nake so kamar yanda kace,dan Allah
A yanzu ina bukatar nayi aure da wuri."
Ajiyar zuciya ya sauke tare dajin wani sanyi a ransa,yace"Alhamdulillah my princess wly dama ni abinda nake so kenan ya fito daga bakin ki,nagode Nagode sosai, wallahi Allah dama zasu yarda da anyi auren mu rana daya da kanwar mu."
Murmushi A'indo tayi tace"a'a idan mukayi haka da takura mudai yi kamar yanda nace din."
"An gama ranki ya dade."
Yace da ita tare dayin murmushi.
Fira sukayi sama sama,sanan ya fido kudi dubu dari biyu yace tayi hidimar biki,ta sayama Husseina gift na aure.
Murmushi A'indo tayi taki karba,da k'yar ya shawo kanta ta k'arba tare da godiya........
Cik'in farin ciki ta koma gida,yau ne kuma akayi indiya day,inda kowa yayi Shirin indiya,anma A'indo gaba-daya ita da amarya
Sunfi kowa kyau da haduwa,inda duk abokan ango suke hada ma A'indo yawu.
Masha Allah an gama sa lfy lau ,washe garin ranar za'ayi dinner,dan haka a washe gari dasasafe su A'indo suka tafi salon har amarya,inda aka musu gyaran kai,sanan aka tsantsara masu galelen lalai,gawnin kyau ba kamar su da suke farare,kuma sunfi kowa kyau da d'aukan Ido,hata kawayen su sha'awa suke basu.
Khalissa tace"gaskiya Yaya yayi asara,anan,harar A'indo ta gala ma khalissa sai tayi saurin yin shiru,babu Wanda yaji ta.
A ranar a Salon suka wuni,sai k'arfe bakway na dare suka dawo gida yayyin da dinner party zai fara k'arfe takwas da Rabi na dare.......
Alhassan ma yaji dan sauki,dan haka hajiya tace ya shirya in anjima yaje dinner shima,tunda babu uwaye,su kadai ne yaja Matar sa su tafi.
Ba yanda beyi da Hajiya ba akan bazai je ba ,ta bata rai tare da cewar matsawar basuje ba zaiga bacin ranta,dan haka yace tayi hakuri zaije.........
K'arfe takwas dai-dai tuni anyima kawaye da amarya make-up Wanda kuma duka A'indo tayi musu,sunyi bala'in kyau,yayyin da yan matan amarya suka dinka suit na mata riga da wondo,dinkin jan yadi ne na maza, riga da wondo,sai sukasa farar riga daga ciki,yar saman kuma a bud'e take,gyaran gashin su iri daya ne kuma yayi kyau,a tsakiya aka kame musu gashin, jelar ta fado har a kafada,sauran da yake basuda gashi kamar nasu A'INDO da Husseina saida aka Kara musu gashin doki lol😝.
Sanan sukasa takama masu rufewa daga sama, masu tsini suma farare,sai karamar sarka a wuya,sanan sukasa fulla fara mai gashi mai dankaran kyau,duk iri daya ,sanan suka d'auki farar karamar jaka itama,waw yan matan sunyi bala'in haduwa,harda khalissa ma harda ita cik'in Yan matan amarya su shida kenan hadi da A'indo.
Salma ta juya ga A'INDO tace"keko yaushe zaki shirya kowa ya shirya,mu tafiya zamuyi tunda kinga mu ya kamata mu fara zuwa mu tarbi mutane, amarya da ango sai gaba zasu zo ."
"Ai kunce haka tunda kun samu nayi muku abinda kuke so,shine ni sai nabar fuska ta haka ba kwaliya.
Mimi tace"ai ke ba sai kinyi kwaliya ba domin kuwa bazaki hada kyanki da namu ba ."
"Hummmmm naji dai ku zage ni yanda kukaga dama.
Tafiya sukayi,dan abokan ango wajen mota bakway sukazo d'aukan kawayen amarya da ita kuma motoci masu kyau da tsada.
Nan aka d'auke su,gidan yayi dan shiru,amarya A'indo ta shirya ta da doguwar rigar ta fara,Mai kyau,irin ta turawa ,anma kuma batayi tsiraici ba,sai daga baya A'INDO ta shirya,tayi Make up simple ,tasa kayanta,sunyi bala'in yi mata kyau,domin tafi duka yan matan haduwa,,kayan sun kamata, kasancewar tanada hips,ga boobs,kirar Coca-Cola itama tasa fara riga daga cik'in wondon,sanan ta aza rigar ja daga sama,waw suit din sunyi bala'in amsar ta,kamar wata ba'indiya,sai kace zata zaben saurauniyar kyau.takalma tasa farare masu tsini,sanan tasa sarka fara ta roba mai kyau,tasa wani dan hannu fari shima na roba mai kyau,ga jan zanan lalen ta ya fito ram,yayi mata bala'in kyau....
Sanan tasa farin karamin gilashi,ga jan baki da ya zauna ram a bakin ta ,gwanin kyau da sha'awa.
Husseina da ke zaune tana kallon ikon Allah sai tashi tayi ta zaga ihu,A'indo ta juyo da sauri tana tambayar ta lfy , Husseina tace"wallahi sis kinfi duk yan matan nan haduwa,kayan sunfi kama ki,kinga kuwa yanda kikayi bala'in yin
Kyau ,wallahi kin hadu,ke kinganki kuwa iyeee🥰."
"Mtsss ni wly kin bani tsoro nayi tunanin wani abun ne ma."
"To anma ke kadai zaki tafi a motar ki dan naga duk sun tafi ko,Bash kuma yace sai wajen k'arfe goma jirgin sa zai sauka,kuma yace miki direct zai huce wajen dinner din."
"Eh na sani,a mota ta zanje dama."
"Ok"
Turare tasa bayan ta gama shirin,ta fesa turare masu kamshi,sanan tasa hular ta,ta d'auki karamar farar jakarta da key na mota,tayima Husseina kiss a goshi tace"bye sai kunzo"!
"Ok bye."
Fitowa A'indo tayi cik'in takun ta na kasaita da yanga,irin na yan mata masu aji, dai-dai fitowar Alhassan da Mina wanda shima yasa fararen kaya suit da bakaken takalma,yayi bala'in yin kyau shima tamkar ba'indiye,duk da ya rame,Mina kam yanda kasan figagiyar kazar da akasa ma ruwa ba'a fige ba a kusa dashi,dan wata doguwar fara riga tasa,ta tarkata abubuwa kamar mahaukaciya ,wai anan sytil🤔ne,abun ban dariya, Al'Hassan gaba-daya haushin ta yake ji,yanda yaga tayi wanan shigar,zuwa yayi wajen motar sa da take kusa da ta A'indo,juyowa A'indo tayi,suka hada idanu carab dashi,ji Yayi kamar sa masa lantarki,cak ya tsaya wuri daya ,tare da d',auke numfashi ya d'auke wuta,tare da gwalo idanu waje,a matukar razane. Ita Kam bata gansa ba,tayi shigewar ta a mota ta tada ta jata ta fita daga gidan a matukar mamaki yake kallon yanda take tuki,sanan shigar da tayi tayi bala'in tafiya da imanin sa,nandanan ransa ya baci da ya tuna cewar maza keda koi a gurin. Da sauri ya shiga motar,Mina ta tsaya gyare gyare rai a bace ya daka mata tsawa tare da fadin dan ubanki ki shiga muje."
Waro idanu Mina tayi tace "wallahi ba ubana ba,shiga tayi motar ya tada da gudu yabar harabar gidan ko gards dinsa baibi takan su ba,bisa titi ya taikayo yanda A'indo ke tuki cik'in kwarewa ,ba karamin mamaki ta shayar dashi ba......
Aci gaba da gashi 🍇
Maimou love😘
[26/10 à 18:50] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨
✨
*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋
*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚
*DAGA ALKALAMIN MARUBUCIYAR*
👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
_and Now_👇
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*
_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.