Aindo Part One Complete Hausa Novel
Reading file: Aindo Tantagariyar Yar Aiki Part One Complete Hausa Novel.txt
Chapter 31 of 44
*Page 61-62*
Hajiya takai kallon ta ga Alhassan,tace"ka gani ko?
Shi yasa akace dan Adam a kullum idan zaiyi abu ya dinga tuna gaba,share hawaye Hajiya tayi,tare da fadin kiyi hakuri Halissa kalar taki kaddarar kenan,tashi kije ki huta,zan kira doctor ya duba ki."
Tashi Halissa tayi tabar wurin tana share hawaye,shi kansa Al'Hassan share hawayen sa yayi,tare da dukawa ,ya kama hannuwan Hajiya,yana kuka yace"Hajiya dan Allah ki tayani neman gafara agun A'indo,nasan cewar a yanzu banida hurumin mata magana anma ke zaki iya,wallahi na sani cewar Alhakin ta ne ke bibiyata ,wallahi na tuba,ya Allah!😭"
Shafa kansa Hajiya tayi tace"karka damu kayi hakuri Allah dama maji rokon bayin sa ne ,ka dinga yin istigafari insha Allah komai mai hucewa ne,dama tun farko abinda nake gujewa kenan........
Da k'yar ya tashi ya nufi b'angaren sa ,haka ya dinga kuka har dare,Sallah kawai ke tada sa ba abinda yake bayan neman gafarar ubangiji.
Bayan sati biyu,ne Khalissa itama ta dawo gida sakamokon rashin lfy da take tayi acan,daddyn ta ma ya dawo da ita,anan hankula suka kara tashi.
ana kaita asibiti gwajin farko aka tabatar da karamin ciki ne da ita yake wahalar da ita .
Innalillahi wa'ina illaihi Raju'un ,fadar tashin hankalin da family Alhaji Sanmani suka shiga abin baya misaltuwa,domin Khalissa batada miji budurwa ce kuma gata d'auke da ciki ya salam.!
Wanan abun babu wanda yafi tabawa kamar Alhassan,domin kuwa duk gani yake abinda ya shuka ne yake girba,lokacin da yaji kanwar sa nada ciki ba karamin gigicewa yayi ba tare da fita hayacin sa,inda tun a gurin ya fara buga kansa a katanga,yana hawaye,akazo aka kakama sa anma ina yaki bari saida goshin sa ya fashe ya fara zubar da jini,daddyn sa ne bale sa da mari sanan ya dawo hayacin sa,anma yana dawowa ya fice daga asibitin,ya shiga mota da k'arfi yaja motar ya fita daga harabar asibitin,Hajiya duk da bata cikin hayacin ta,saida tayi magana cewa"
A tarbo sa,kar ya halaka kansa,nan idrissa ya biyo sa gudu sosai Alhassan keyi yana kuka,shi abin ya masa yawa,har ya fita wajen gari ya shiga daji baisan yana gudu ba,bai ankara ba yaje zaiyi karo da katuwar mota yayi saurin kauce mata,a garin kaucewar ne sitiyarin motar ya kufce masa ya kasa controlling din motar,aiko nan motar ta kife ta gangar cik'in wani rame tana wulitsawa gar saida ta shiga cik'in wani katon rame duk akan idannun Idrissa anan ya waro idanu cik'e da tsoro da firgici ya kwala kiran sunan Yaya! Da k'arfi,ya fito,Allah ya taimaka kusa da wani kauye ne kuma sunga abinda ya faru,Nan aka dunguma aka shiga ramin domin ceton ran Alhassan,ana zuwa aka iske motar ta tula sa can gefe,ya bugu da wani dutse, gaba-daya jikin sa jini ya bata, ba rai haka aka d'auko sa Idrissa na kuka ya kira Mahaifin su,nandanan sai gashi,shima yana hawaye aka d'auki Alhassan akayi asibiti dashi.......
A lokacin kuma A'indo ta fara fuskantar halaye irin na Bashir wanda ya boye mata, abun mamaki yanzu idan zai sadu da ita sai ya bata wata kwaya yace tasha,na Karin lfy ne,sanan in yahau kanta ya jima yakai minti biyar,daganan zai juya sai barci,sanan babu wani wasa kafin a gudanar da harka.
Duk wata kulawa da Bashir ke nuna nata kafin aure yanzu babu ita sai masifar kishi .
Hakan ko ya faru ne Lokacin da aka d'aura auren Bashir da A'INDO,inda Salman abokin sa suna zaune kafin suje wajen A'INDO,Bashir nata washe Baki da zumudi,Salma ya kalle sa tare da murmushi yace"hum nikam Bashir naga kanata rawar kai kadai bi a sannun."
Fuska Bashir yayi yace"ban gane ba Bashir me kake nufi?
"Hum ai bazaka gane bane kasan sarai tsohuwar Matata zuweira abinda tayi min,saboda na nuna mata so kaga abinda ta mayar dani,ta Raina ni,ta maida ni mijin tace,a ko ina zagi na take,abinda na lura da matan yanzu idan ka nuna kana son su,kana tatalin su sunfi raina ka,sanan basu ganin ka da daraja, dan Ina mai baka shawarar da kasan zaman da zakayi da matar ka,domin su mata mai kyautata musu sunfi gasa sa,anma mai kuntata musu sunfi son sa."
Tun daganan Bashir ya d'auki gurbataciyar shawarar abokin sa,tare da kara tuna irin zaman da mahaifiyar sa da kuma Mahaifin sa sukayi suna son junan su,sanan Mahaifin sa baya musa ma Mahaifiyar sa,ada Yana ganin soyaya ce sai yanzu da Salman ya ankarar dashi ya fara tunananin mahaifiyar sa ma dan mahaifin sa na sonta shi yasa sai abinda tace akeyi.
Wanan dalilin yasa yake ma A'indo wanan abubuwan da yake yi. duk da yanada wani burin da kuma banzan ra'ayin sa na daban,wanda shidai har ga Allah baya son haihuwa,a cewar sa yara basa bari aji dadin rayuwa,wanan dalilin yasa a dare na uku da zai sadu da A'INDO ya fara bata kwayoyin hana haihuwa.
Zaune suke suna kallon TV,A'indo takai duban ta ga Bashir tace"wai hubby me yasa ka canza min halin ka lokaci guda?
Kuma me yasa kake bani wanan kwayar kullum idan zamu kwanta."
Juyowa yayi ya kalleta da kyau,sanan ya bata fuska yace"anma dai kinsan ba kashe ki zanyi ba kuma ba cutar dake zanyi ba ko.?
"Wai meye ke damun ka ne Bashir,na fahimci tunda mukayi aure kake tsuro min da wasu banzayan halayan ka to ka sani ni bazan lamunci wanan abun ba .
Tassssss taji an kwashe ta da mari,ta dafe kumci yayin da hawaye suka zubo mata,tace"Bashir ni ka mara duka duka ko wata bamuyi ba da aure anma har ka fara duka na,ashe haka kaima kake."
Fauuuuuu yabar gurin ransa a bace,tabas yanzu ya kara gaskata maganar Salma mata idan ana sake musu raina maza suke yi.
Rai a bace ta nufi inda yake ta bisa tace"nace ka fada min kwayoyin meye kake bani kullum dadare,idan ba haka ba wallahi bazan kara shansu ba.
"Saboda a tsari na ni bana son haihuwa!!!."
Ya fada mata cik'in daka mata tsawa .
Waro idanu A'indo tayi cikin shok tace"Bashir baka me?
Baka son haihuwa ashe haka kake dama ban sani ba,ashe haka halin ka yake ka boye min."
"Ke dakata ya ishe ki hakanan meye na wani Ashe ashe,nida na taimaka miki har zaki dinga fadamin haka,karki manta kefa ba kowa bace,acan ma inda kike har kike jin ke wata ce kina takama da gidan Yar aiki ce ke,har kin samu kamar ni na auro ki,wa ya sani ma ko dama can tsohon mijin naki saboda wanan bakin halin naki ya rabu dake."
Tana hawaye na bakin ciki tace"Bashir ada ina tunanin nayi zabe,na cire tuta na samu mijin da ako ina zanyi tinkaho dashi,da ilimin sa da Addinin sa da kauce ma abinda Allah yayi hani dashi ashe abun ba haka yake ba....."
"🤣a gaskiya Aisha kinada abin dariya a ganin ki ku mata ku kadai ne kuka iya basaja ,to bara kiji tun lokacin da na fuskanci cewar dole sai na maida kaina mai tsoron Allah na koma ustaz na k'arfi da yaji ta haka kawai zan samu Zuciyar ki da ta wa'inda kike zaune a gidan su shi yasa nayi hakan,na maida kaina Ustaz ,dan haka ki share kawai tunda yanzu munyi aure ai an huce gurin.......
Tace"ka sani bazan kara Shan wanan maganin ba,domin da raina da lafiya ta bazan sha wasu kwayoyin hana haihuwa ba,idan kai baka son haihuwa ni ina so."
"Aiko baki isa ba,wallahi Allah kika yarda kika d'auki ciki hummmmm ni kadai nasan abinda zan miki."
Share hawaye A'indo tayi ,wanda take jin Zuciyar ta na bala'in yi mata zafi,zata yi magana kenan wayar ta tayi kara,dubawa tayi taga yar uwarta ce Husseina ke kira d'auka tayi ta daga nan Husseina na kuka take shaida ma A'indo abinda yake faruwa a gidan su Alhassan tun lokacin da ya kwanta asibiti, sakamokon jin da yayi ance tayi aure,duk abinda ya faru a gidan idrissa na fada mata,har ya zuwa yau da Khalissa ke d'auke da cik'in shege,da kuma Accident din da Alhassan yayi,wanda yana can tsaka tsakiya cik'in halin rai ko mutuwa ,Husseina tana gama fada mata tace"dan Allah A'indo kizo asibiti ko Hajiya ta samu sasaucin Zuciyar ta,ki yafe ma Alhassan ko ya samu sasauci shima, wallahi a yanzu na yarda da tuban sa ,tunda kinyi aure yanzu ki yafe masa,kinaga wanan abun da ya miki ne yake bibiyar sa,gashi Hajiya bai kamata ana hukunta ta ba bisa kan abinda batayi ba plz."
Share hawaye A'indo tayi tare da fadin "innalillahi wa'ina illaihi Raju'un,gani nan zuwa asibitin."
Tana gama wayar ta kashe,takai duban ta ga Bashir tace"dan Allah ka kaini Asibiti gidan Hajiya ba lafiya,hata danta baba Alhassan yayi accident,a yanzu Hajiya na bukatar wa'inda zasu kwantar mata da hankali ."
Murmushin gefen baki Bashir yayi yace"kin gama?
To ki sani ba inda zaki wallahi,munafuka,salon kije kiga tsohon mijin ki ko?
ai dama na sani kina son sa munafurci ne,tunda dai yanzu kin bar hannun su meye na wani shiga sabgar su,shishigi kawai,can ta matse musu idan ma mutuwa zaiyi da yafi masa wallahi mtssss.....
.aci gaba da gashi🍇
Maimou love😘
[30/10 à 20:48] MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE: https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*A'INDO*
_(Tantagariyar Yar Aiki_)
✨✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
✨✨✨✨✨
✨✨✨✨
✨✨✨
✨✨
✨
*NA*
*MAIMOUNA MATAR ABDOULAYE AM*💋
*🤝🏻ANA TARE WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_(We are the best Writers Among All writers_)📚
*DAGA ALKALAMIN MARUBUCIYAR*
👇
*YA MACE KOWACE DA IRIN NI'IMAR TA*,
*LABARIN MAIMOUNATOU*,
*KAICONA*,
*HASSADA GA MAI RABO*,
*YAN MATAN ZAMANI*,
*INA MATSALAR TAKE MAZAN KO MATAN*,
*MAKIRCI*,
*LATIFA*,
*CANJIN RUHI*,
*WACECE NI KAMRINA*,
*SO NE SILAR FARUWAN HAKAN*,
*LATIFA SABON SALO*,
*A'INDO (Tantagariyar Yar Aiki)*
_DEDICATED TO SADJIDA & UMMY ONTOP_
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.