Kuyanga Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: KUYANGA part 1 cmplt-1-1-4-1.txt
Chapter 5 of 23
Magana me tsayi bata hada su to me zatace masa ? Bayaga ina kwana ina wuni sai tambayar wani abun kuma
*******
Cikin Sati biyu yazamto tafara sabo da komai hatta kayan datake sawa matsatstsu yazame mata jiki tasaba dasu tunda yakaro mata wasu yakawo mata dayawa
Tun tana kunya inta sakasu harta daina
Yakawo mata manshawa masu kyau da man wanke kai da sabulai nagyaran fata dai
Tana tsafta sosai tana gyara kanta dayake tanada tsahon gashi da cika saidai kullum yasha gyara ko tayi masa manyan kalba ta bazo jelar kalbar baya aiko takanyi balain kyau dama ga fuska kamar ba india sosai kyanta yanata bayyana don hutu yanata shigarta ba koina take zuwa ba kullum bacci daga dakinta sai kicin sai falo
Sai intafuta kaiwa me gadi abinci ko aikin farfajiya
Zaman gidan yafara damunta to amma bayanda zatayi tunda baice tazo tafuta wajenba aibaxata iya futa batare da izinin saba
Yakan futa tun dare sai tsakar dare yadawo tarasa wane aikine haka kamar na barayi
Hhhh bakisan club yake zuwa ba kenan to zauna wataran zaki sani😅
wata ranar Lahadi tana Daki akwance tayi rub daciki tanata tunanin masoyinta MAHBUB Tasan akoina yake yanzun hakan yananan da kewarta
Kawai taji yashigo mata ba sallama
Ta tashi da sauri tace "Sannu dashigowa akwai abinda kake bukatane?
Yaja yatsaya yaruke murkar kofa yace "kitaso maza kidafa abinci ga bakina nan zuwa gidannan "yan Nigeriane amma anan suke karatu Abokina ne sosai Shi d'in Jinin Sarautane kitsaya kinitsu kiyi abinci me dadi bawai bamuda inda zamu ciyo bane akwai hotels kawai dai yafison abincin gidane nasan sa sarai
Ckn ladabi kai akasa tace "to angama.
Yajuya yafuta yana karewa "yar shimin dake jikinta kallo wanda agaban rigar aka rubuta *HOT KISS!* Da manyan Harufa
adaidai lokacin da bak'in nasa sukazo adaidai lokacin Allah yabata sa,a tagama komai
Har juice ta hada na mango da Banana da kayan fruit dai
dayake yakawo komai yasaka afurji
Itako akwai basirar iya yin komai wani abunma ba koya tayiba datayi nazari aranta tsaf zata hada
*Tab kaga KUYANGA "YAR Baiwa* ho Allah yabamu yataki zeenatu 👍
Tayi musu sallama falon yarimane sai bak'in su biyu kawai kallo suke suna hira
Bakin suka bita da kallo
Ta dire akan table tareda durkusawa tagaidasu
Yarima yana kallon yanda suketa kallonta
Saida takoma ciki Yarima yakaiwa nakusa dashi duka yana fadin "kai SAHABI kashiga hankalinka wannan kallo haka na miyene?
Wanda aka kira da SAHABIN yakyalkyale da dariya yace "yo mutumina ai abu nagani kamar Zinare agidanka tabbas inhar zai dauku saina daukeshi.
Yarima yasake kai masa bugu
"dan ubanka wannan ba kalar taku bace kafi karfinta *KUYANGA* Ce fa da ita nataho ita tadabance ackn BAYIN ma
SAHABI yace "kai anya kuwa zanyarda da batunka ace wannan *KUYANGA* CE tabbas ackn kuyangun ma ta dabance kaga halitta fa ga kyau ga cikar halitta Ga kuma………
Yarima yarufe masa baki yana fadin "basaika karasaba abar maganar akoma wata wannan munwuce ajinta.
SAHABI YACE "kaga yarima kabarni nikam wannan tayimin ta furgitani dayawa domin ko ackn KUYANGIN gidanmu bantaba ganin mekyau irinta ba
ASHRAF da sukazo tare ya bushe da dariya yace "Kai SAHABI kadai tafi dayawane Plz cool your mine kada kafara ma you are handsome and gentle fa karike girmanka dai.
Yarima yace "yama fara mana nikam dai bazan yardaba badani a wannan abin kunyarba domin yafi karfin ajinta shima yasani
SAHABI YACE "Kai! yarima bangane bafa kodai dama kaine aciki.?
Yarima yaja wani mugun tsaki yace "Allah yakiyaye niko mezan da wannan kamanta nine? ko a mata cikakku ba kowacce nake kulawa ba balle ackn Bayin gidanmu haba Abokina Me Yarima irina zaiyi da *KUYANGA*
Yahau bude abincin Duk Dan abar maganar yana fadin "Kufara cin abinci tukunna dai.
Anyi haka da kwana guda yacimmata har daki yace mata "Ke Daga yau inhar kinjini da baki kidaina Saka kananun kayan dana kawo miki
Tace "to, amma babu wasu dazansaka sai wanda mukazo dasu kuma sun tsufa
Yace "bakomai kisasu ahakan inzaki fito gun bak'ina kafin asan abinyi
Ckn ladabi ta gyada kanta alamun xatabi umarnin
Ammafa ta dade tana tambayar kanta shin ko meyasa yace mata hakan? Toko tayi ba daidaiba ko sunyi maganar dasu akanbai dace bane ? Dayake dai batada Amsar tambayar sai muje zuwa …………
*Auntyn Sayyada da Shahida ce* 👌🏼
[7/24, 8:15 PM] Ummi Tandama: 📿 *KUYANGA...* 📿
*_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*NABILANCY LUV* 💘
(Auntyn S&S)
20-25
Ranar wata lahadi Tana mopping a falo daga ita sai 3quater da body hug me karamin hannu kanta da kallabi bata taba yarda tabar kanta abude ba sbd akullum lokacin tana gida sai MAHBUB Yahaneta da hakan
Wakarta takeyi ahankali tana Dan motsa kafada
*SAI WATARANA MASOYI ZANBARKA SAI WATA RANA INA MAKA BANKWANA* _bankwana_ 💃🏼
*ASHE SABO YANADA DADI* *AMMA IN ZA.AI RABO DA ZAFI* 💃🏼 *MAHBUB NATAFI NABARKA...BANSAN HALIN DA KASHIGE CIKI BA.* _Bankwana_ 🎻🎧🎺🎸
😭😭 tahau goge hawaye domin wata kewar MAHBUB ce tazo mata shiyasa take masa waqa
Ashe duk abinda takeyi Yarima yashigo yana bayanta yajingina da bango yana kare mata kallo ga muryarta ta masa dadi ga shigar da tayi ta fusgeshi domin wata sha,awarta ne yashigeshi lokaci guda
Saida tagama tajuyo zata bar gurin da tsumma da mofa ahannunta kawai taja tunga kanta akasa tana masa barka da shigowa wata kunyace ta lullubeta domin tasan yaji irin waqar da takeyi
Yayi gyaran murya bayan amsa mata da yayi yace mata "kishirya anjima zaki rakani wata unguwa.
Ta gyada kai tana amsawa da "to.
Tagama shirinta ckin wata doguwar riga daya hado mata dasu ckn kaya da siririn mayafi
Tayi kyau ainun tamkar balarabiya tafuto sak
Yaleko yace ta futo sutafi
Takwas ta wuce alokacin
wani Store suka fara zuwa *ROYAL STAR*
Yajibgo kaya aleda yabata tarike suka fito
Yakarbi kayan yasaka a boot
Tashiga gidan gaba
Yaleka fuska ba fara.a yace mata futo kishiga gaba niba Drivern ki bane.
Ta futo sum sum tashige gaba domin itakam kunyar rabarsa takeji tanajin nauyinsa tafi son bayan domin tana shiga takura takuma fi son taringa nesanta dashi
Suna tafe suna saurarar wakar Nancy Ajram ackn motar daya kunna yana son wakokinta sosai
Yakatse shirun da watso mata tambaya
"Zeenatu! Wanene MAHBUB ne? Kuma meye alakarki dashi?
Tahau sinne kai ahannunta tana in inar magana
yace mata "alamu sun nuna masoyin kine kenan.?
tayi masa shiru fuskarta dauke da murmushi
Yace "Amatsayinki na *KUYANGA* Meye ribarki in kika Auri *BAWA* ?
ranta taji ba dadi kalmar batayi mata dadiba tunda aiduk mutanene kuma Allah ne yayo *KUYANGA* yayi *BAWAN*
Dayaga batada niyyar magana saiyaci gaba
"Wato nafuskanci kina cikin soyayya kuma kina ckn kewarsa ko? Inban mantaba naganki aranar da zamu baro gida kina daga masa hannu.
Anyi hakan?
Ta daga kanta
Ya d'aga kafad'a yace "Well Zancire miki kewarsa domin kiji farin ciki ayau.
Itakam bata ce kanzil ba domin bata fahimce shiba sam
Kaji sokuwa hhhmmm muko fans mungane 😅
dayaga taki cewa komai saiyace "Zan baki farin cikin da Saurayin naki yake baki domin farin cikinki....Ta dago da sauri tasadda kanta akasa ckn mintina kwakwalwarta tahau aiki to me yake nufi kenan soyayya zaiyi da ita?
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.