Complete Hausa Novels

Kuyanga Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: KUYANGA part 1 cmplt-1-1-4-1.txt

Chapter 18 of 23

Sukace "to shikenan Ranka yadade.

Suka tafi shima yajuya yashige ciki

Itama Jakadiya dataji komai akan kunnenta tajuya koma inda tafuto tana gyada kai mamakin abin fal ranta lallai Yarima yazama Takaddari acikin gidan Sarki......

To fans mujira zuwa safe muga ikon Allah mukasa mutsare mujira

Auntyn Sayyada da Shahida CE 👌🏻
[8/4, 11:18 AM] Ummi Tandama: 📿 *KUYANGA...* 📿

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION_*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*Nabilancy Luv* 💘
(Auntyn S&S)

75-80

Kwana Jakadiya tayi tana Tunanin abinda kunnenta yajiye mata akan Abinda YARIMA yasa ayiwa MAHBUB tabbas indai suka aikata hakan Sai ta tona asirinsu

Da gaggawa wata zuciyar ta kwabeta

"Ke kinsan ko abinda kk fada?yariman zaki tonawa asiri toki tabbatar indai kika fada sunanki matacciya kema kokuma korarriya a gidan Sarki domin yarima da mahaifiyarsa babarinki zasuyiba

Ta tuno yanda mahaifiyarsa keji dashi da sangartashi da gudun Bacin ransa

Ta tuno rashin mutuncin Yariman

Sannan ta tuno Yanda za.aita bibiyarta ana Neman cikakkiyar sheda daga gareta dazarar ta tona asiri domin dolene saita kawo shaida inko bata kawoba za,a hukunta akuma koreta agidan dama UMMAH ce ta daukaketa agidan

Dataga jan bakinta tayi shiru yafiye mata alkairi saitaja komai tasa agefe Dan yafiye mata kwanciyar hankali

********
Tashin hankali Wanda ba,asa masa rana domin abangaren bayi suntashi dashi

*KUYANGA* Da zulaihat suna kwance da Sassafe ihun da suka ringa jiyowa da koke koke agidan shiya tashesu afurgice

Zulaihat tace da ita " munshiga uku wannan ihun kuwa na lafiyane.

*KUYANGA* Tace "Ba lafiyaba gaskiya tashi muleko

Suna futowa bakin kofarsu sai suka hango dandazon mutane Asashin maza

Suntaru gefensu kuma mata ne tsoffi da yaran mata sunata kuka

Zulaihat ta yafito wata yarinya Laminde da batafi shekara gomaba yar Aiken Uztaz MAHBUB

Laminde tana goge hawaye ta iso garesu

Zulaihat tace mata " Ke laminde meyake faruwa agidanne?

Cikin kuka laminde tace "Tashi kawai akayi akaga wai UZTAZ ya mutu kuma ance kasheshi akayi da fullo....

" me!? Afirgice *KUYANGA* ta riketa tana tambayarta "waye yakashemin MAHBUB wayyo nashiga uku in Zeenatu

Ta Dora hannu aka tana kuka

Zulaihat da jikinta yayi sanyi takamo Zeenatu ajikinta tana fadin

" kada kidaga hankalinki muje mutabbatar dai

Tajata suka karasa gurin tsoffin

Lantana wata sa,arsu ta matso da sauri garesu tana kuka tana fadin "shikenan Ankashe uztaz Ya mutu ancucemu munyi rashin mallam

Zulaihat ta kara yadda sai kuka itama

Wata tsohuwa Iya Sha,awa mutuniyar Kirki tana son *KUYANGAR* ta maso da sauri gunsu ta janyo *KUYANGA* da taketa rufza kuka hannu aka tace mata " yi shiru Zeenatu kiyi masa addu,a Wanda kuma duk yayi wannan Abun Allah yatoni asirinsa

Zulaihat tace "wai iya me akayi masane?

Iya sha,awa tace " antashi dai anganshi yana kwance ayashe akasan katifarsa ga filo akan fuskarsa

Awuyansa da alamar shaqeshi akayi yajigata ma kafin sukasheshin ba,a gano kosuwaye suka aikataba

Kuka sosai suka ringayi dagama jin wannan mummunan labarin

Kaf kafatanin gidan sarki sun shiga tu,ajjibun abun

Banda wadanda suka aikata da yarima

Itako jakadiya ackn bakin ciki ta wuni

Gashidai tasan kosu waye amma badamar bayyanawa tana tsoro

Taji mutuwar MAHBUB sosai har kuka tayi itama

Yo muma munji mutuwarsa 😭 fans kutaho muje gaisuwa gidan sarki

Matan Sarki kaf sun halacci bangaren Bayi domin yi musu gaisuwa Mai martaba yazo gun ansallaci mamaci amma sai yakoma fada akaci gaba da karbar gaisuwa acan

Suma bangaren bayi mata a bangaren Tsoffin gidan suka taru ake zaman makokin *KUYANGA* Tafi kowa agun damuwa domin jiyan sun Dade tare suna hira me dadi yana bata shawara na yanda zata zauna da rayuwarta tayi kyau inta Auri LAMIDO

sosai yaita kwantar mata da hankali yana gaya mata irin son da yake mata

Ko zuwa kiran da yariman yai mata suna taren shiya takura mata saida taje ajiyan

Kwana tayi baci basha saida iya sha,awa ta takura mata

Sai aranar sadakar ukun MAHBUB sannan LAMIDO yazo bangaren Bayi ya aika tazo domin yai mata gaisuwa

Ta iso cikin hijab har kasa kanta akasa

Tagaidashi ckn sanyin murya

Idonsa akan fuskarta yana murmushi ya amsa tareda yi mata gaisuwa

Ta amsa tana yi masa godiya

Yace "Allah yajikansa yabaku hakuri da juriyar rashinsa

Ta dago da kanta takalleshi tace " Amin ngd

Yana murmushi yace "bakomai yiwa Kaine bari nakoma.

Yakawo kudi masu yawa yamika mata

" gashi kibada Sadaka

Takarba tana fadin "Allah yakarba.

Tajuya ta tafi tana zancen zuci " wato shi wannan nafahimci yana matuqar son yaga ya aikata aikin lada.

Tayi murmushi "yanada hali me kyau ga yawan fara,a

😆😮🙄🙄 *KUYANGA* kodai kin yaba ne...??

*********
Sai ranar sadakar bakwai Yarima yazo mata shikuma Gaisuwa

Fuskarta babu annuri tafuto gurinsa tagaidashi tayi shiru agefe guda kanta akasa

Yace mata " nasan kina cikin damuwa na rashin masoyi to amma yakamata ace kinsa hkr aranki domin Allah yafimu sonsa shiyasa yakarbi kayansa

Tayi masa banza don ba burgeta kalaminsa yayiba

Yaci gaba da fadin "duk kinrame Zeenatu Saikace Wanda mijinta yarasu

Bata dago takalleshiba balle tabashi amsa

Dayaga batada niyyar magana saiyayi mata sallama yatafi kawai yanajin farin ciki aransa

Yasan gaba dole zata soshi inta zama mallakinsa domin Saiya kauda LAMIDO shima inyaso ahakura abashi ita don bazai juri yaga tazama mallakin waniba alhalin ayanzu yana mata mugun so

Bayan wata biyar Cikin *KUYANGA* yana wata Takwas alokacin Yarima yazo mata da Kudi wai tayi sayayya na kayan jarirai

Taso taki karba saikuma taga dacewar karbar dazatayi domin Allah ma take godewa da har Ya karkato da hankalin yariman kan cikin tunda wasu sunshiga zarginta afarko tunda yariman yace bacikinsa bane ake tunanin cikin wani ne

YARIMA yazo da Sati biyu *KUYANGA* ta haihu ta haifo D'anta Zankadede kyakykyawa Wanda tsananin kyansa yasa aketa zuzutashi agidan tamkar balarabe

Saidai kuma yadauko wasu abubuwan na yarima afuskarsa kamar kwayar idonsa da habarsa sannan wani ikon Allah saiga cindo ahannunsa na hagu

Haka yarima yanada wannan cindo ahannun hagu

Wannan shiya kara tabbatarwa Al,ummar gidan lallai wannan yaro mallakin Yariman jinin sane ba haufi

Mai martaba ya Dade yana kallon Yaron

Yatabbatar da wasu abubuwan na yarima ajikin Yaron saiyaga tamkar yarima yana Yaro

Wata kaunar yaronce taringa shigar Sarki yaji inama tahanyar sunna aka haifoshi

Koda yakebe shikadai kuka yaringayi waiyau shine da jikan dayazo bata hanyar Aureba yarima yacuceshi yabata masa suna

Yarima baidauko halinsa ba baiyi shashanci ba yana saurayi Komai nasa da nutsuwa da kamun kai yayishi harsaida yayi Aure yasan mace to amma gashi Allah yajarabceshi da abubuwan tir agidansa

Munjajanta maka Sarki Abdallah 😭

Abin arxiki FAATU da MAMAH suka hada sosai na kayan jariri aka kaiwa *KUYANGA*

Jakadiya tabazama ta gayowa UMMAH

Fulani tahau gyada kai tana fadin "munafukai nagama ganosu sunayine badan Allah ba saidon Neman suna da kuma Neman duniya agun Sarki

Kinaji ko Jakadiya nima zanhada kayan inbaki kikai badan Allah zanyiba saidan wadancan munafukan Dan aga banyiba sukayi tunda za.ace niya kamata nayi ko

To zan yi nima Wanda yafi nasuma yawa sannan ke zanbawa kikai harkudi zandora amma inaso kiyawaita kai kafa don hidimtawa mejego dakuma duba yaro inaso kinuna musu soyayya tayanda inkin kashe Yaron baza,a zargekiba

Jakadiya tahau gyada kai

" angama ranki Dade.

Jakadiya nafuta ta wuce sashen su FAATU dontakai musu tsegumin abinda UMMAH tace na kayan da zata hada itama

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.