Complete Hausa Novels

Kuyanga Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: KUYANGA part 1 cmplt-1-1-4-1.txt

Chapter 3 of 23

Taja ajiyar zuciyar Zuciyar xuciya tace "Naji na amince nakuma gode da Shawararka ya masoyina .

.

Ya mike yace mata "maza tashi kije kifara shiri indare yayi kizo muhadu anan dan muyi sallamar karshe

Tayi murmushi tace " sallamar karshe kamar wanda xan mutu inmunje can

Yayi murmushi yace " ba haka nake nufiba, nasan wataqila da sassafe zaku tafi kinga ai zaifi kyau mukadaita mu dade tare mukara yin wata hirar soyayyar ko?

Tagyada kai tana dariya

Ya daga mata gira tareda kanne ido yana kallonta

Harya tafi yabar gun bata daina kallon saba tabbas MAHBUB yahadu rashin gata ne da yanayi yasa cikar kamalarsa bata fito ba harsai ankura ido ake hanga atattare dashi

Ta girgiza kai kawai takara gaba tabar gun tayi dakinsu

Tana shiga Taga Aminiyarta ZULAI

Zulaihat tace "Hhhmmm inata nemanki ai saikuma nahangoki acan lambun soyayya.

*KUYANGA* Tayi dariya tareda dukan kafadar Zulai tace "harkin sakawa gurin zaman namu lambun soyayya lallai Zulaihat ke "yar sa ido ce.

"Ba wani sa,ido gaskiyace ba lambun soyayyar bane?

"Eh bashi bane, to ai ba soyayyar akeba.

Cewar *KUYANGA* Tana dariya

Zulaihat tace "kifadawa keya yarinya kowa yafahimceku ingaya miki duk wanda yaga yanda kuke tabbas zaigano ckn mintina batareda yasha wuya ba.

"Hhhmmm to inma soyayyar akeyi saime? Ko bamu daceba.

Zulai takama baki tace "ho! Ni na isa ince baku daceba aji haushina to walh bari kiji kundace da MAHBUB tamkar danjunanku akayoku ina kuma Son tarayyarku.

Zama *KUYANGA* Tayi kusa da ita tace " Zulai gobe zanketa hazo fa.

Da sauri Zulaihat takalleta da alamar tambaya tace "hazo kuma?kamar yaya?

Nan Ta zayyano mata komai nagame da Rakiyar da Zatai wa Yarima Turai

Zulaihat tace "wayyo Allah na inama ni aka zaba.

*KUYANGA* Tace "tabdijan !kenan har wani son tarayya kike yi da Yarima?mutumin dakowa yasan halinsa marasa kyau. To walh ni ckn bakin ciki nake ahalin yanzu da har aka zabeni

Zulai tace "Dan dai zakiyiwa MAHBUB nisa ne amma aikinsan zaki huta zakuma kisami hutu da Aikin gidannan ZEENATU kifa tuna mubayine bayinma kaskantattu wadanda ba,a san inda iyayanmu sukeba ko suna raye?ko sun mace Allah shiyasani mudai muntsinci kanmune agidan nan

Dan Allah kikwantar da hankalinki inkinje domin Allah ne yazabeki domin kihuta kedai kiyi biyayya dama ke me biyayyarce kowa yasani bakida surutu magana bata dame kiba inba sabo kikayi da mutum ba basawa ba hanawa dan haka ki ajiye soyayyar MAHBUB anan zuwa sanda zaki dawo kwacigaba

*KUYANGA* Tace "to inma ban ajiyeba yazanyi bayan askiyazo gaban goshi gobe nefa zantafin dole inyi hkr da komai dama saiyau yabayyana min abinda ke ransa

Zulai tace "hhhmmm keda bakida gano abu da wuri aisaiyau kika ji kika gane amma ai kowa yagane manufarku tabbas muna muku fatan Alkairi kedashi.

*KUYANGA* Tace "mungode.

Nan *KUYANGA* Tahau shirya kayanta ckn wani Dan akwatin karfe me kyau dashi tana Ninka kaya tana sakawa tana ayyanota A turai shin ko wane Zama zasuyi insunje……… ???

*muje zuwa fans*
[7/23, 10:28 AM] Ummi Tandama: 📿 *KUYANGA* 📿

*_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*Dis Page i Dedicated to My Best friend Hauwa,u* *(UMMU ALEESHA wa WALEED)*

*Nabilancy Luv* 💘
(Auntyn S&S)

10-15

Da Sassafe tagama kintsawa misalin Bakwai na safiya Aka aiko kiranta daga Fulani

Tana shiga Sashin Fulanin ta tararta atsaye Yarima na kusa da ita da akwatinsa babba guda daya da alamar zai dade din domin fam yacika akwatin da duk abinda yasan zai bukata duk da acan gidan nasa akwai kayansa na sawa

UMMAH Ta daka masa Yaji ta sa anyo masa dambun nama ta soya masa gyada me gishiri duk abinda tasan dai yana matuqar So ta tanadar masa taxuba masa ckn Akwatin

Yana ganin *KUYANGA* Da akwatin yahau kallonta fuska ba fara,a yace "ke wannan akwatin irin na mutanen da kumafa? Kina nufin dashi zaki bini? Kinsan kuwa Turai ?Bafa Me dile bace, maza jeki canzoshi kokuma kitafi ba kaya inmunje xan nasiya miki wasu kawai

UMMAH tayi murmushi tace "Yi mata hakuri Yarima ta canzo kasan sai ahankali kayi mata uzuri taje ta canzo kayan kokuma inshiga innema mata cikin akwatina na

Yahau girgiza kai yana duba agogon hannunsa

"Barshi UMMAH saura mintina Jirginmu yatashi saima munyi wuta ahanyar zuwa Airport din don karmu makara

Yakalli *KUYANGA* Yace "ke ajiye kayanki anan muje da najikinki inmunje zansai miki wasu kiringa sanyawa.

Ckn ladabi tace "to shikenan.

Ta ajiye akwatin karfen nata agefe tabi bayansa UMMAH tana musu Addu,u,a da fatan Alkairi

Wasu bayi maza ne suka kai masa akwatin nasa har ckn mota aka zura a boot *KUYANGA* Ta shige gidan baya

Motar natafiya zata fuce agidan Sarautar saitaji wani iri aranta tabbas zatayi kewar MAHBUB yau ranar zata zamo mata ranar bakin ciki tunda ta taso kullum suna tare gashi yau zasuyiwa juna nisa kamar ance ta dago kanta kuwa tana dagowa takalli bayanta saita hangoshi ta glass yana dago mata hannu

Ta zura hannunta tahau daga masa itama

Ashe Yarima yana hangosu ta mirro amma baiyi maganaba yai shiru

a Airport kuwa da sukaje Dakyar ta iya daga kafa tahau matattakalar jirgi saida ta rintse idonta

Jirine ma yaso kadata Allah yaso ya kula yai saurin rikota tayo luuu jikinsa yatarota yamannata ajikinsa yahau da ita ahankali

Yasan arina tunda yasan ba taba hawa tayiba

Koda suka shiga ckn jirgi akusa da juna suka zauna

Kujerarsa na kusa da tata

Idonta akasa bata iya hada ido dashi don kunyar abinda yafaru da kuma biyayya

Yakalleta yadauke kai yana so yai mata magana amma yarasa me zaice mata don baya son tana jin kunyar nan tasa shikam tana burgeshi amma baya son kunya shi faranse ne wayyayye

Gani yake duk kauyancin nan da zatayi masa bazasu shiryaba domin saiya wayarta kada tabashi kunya irin nayau

Da aka kawo musu abinsha kin dauka tayi saida yadaka mata tsawa

"Ke Dauki mana meye na kunyar!

Tasa hannu ahankali tadauki lemon taja ta rike takasa budewa

Yana kallonta tagefe taki budewa kanta akas!

Saida yashanye kana yakalleta yace "kawo inbude miki.

Ta mika masa ahankali

Yabude mata na gongwanine me gas

Taringasha ahankali kusan awa guda kafin tagama

Anyi rabin tafiya Tafara bacci takwanto da kanta kan hannun kujera yatsura mata idanu yana kallon kyakykyawar fuskarta da dan bakinta yaji kamar yakai hannunsa yashafata saidai yana gudun kada tafarka

Can bacci yai mata dadi saiga kanta ajikinsa

Yarasa yazaiyi da ita saboda mutane nakusa dasu suna kallonsu

Haka yabasar bai motsaba gudun kada ta farka takasa komawa

*******

Koda suka Sauka a England Kaitsaye suka hau mota ta haya har gidansa

Tamfatsetsen gidane da maimartaba yasiya don kawai insunzo karatu suzo suzauna ackn sa

Daki guda mekyau da tsari yakaita yace mata nanne inda zata ringa kwana

Dayake kayan jikinta riga da zanine tasanya hijabinta hannunta rike da carbi

Tazauna zagwade abakin gado tana so tayi sallah gashi bata san yazatayiba nafarko bata san inane gabas ba gashi Bandakin yawuce tunaninta batasan yanda zata sarrafa ruwa yazubo ba gashi ba agogo adakin

Data gaji da zama saita futo falon domin tambayarsa

Ta dade afalon azaune bayanan yana ciki tajiyoshi yafito daga wanka

Tananan zaune harya kintsa yafito

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.