Complete Hausa Novels

Kuyanga Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: KUYANGA part 1 cmplt-1-1-4-1.txt

Chapter 13 of 23

Yadago da kansa ckn Qunar rai yace da Mahaifiyarsa "Amma sam abinda yarima yakeyi baya kyautawa kodayake UMMAH ta daure masa gindi kuma inada tabbacin shine ma zaiyi cikin Sharri kawai za.ayi mata

FAATU tace "Muma tunanin mu kenan Amma dai koma meye ai dole asiri zai tonu tunda Inta futo daga Asibitin zata fadi ko cikin waye kuma Takawa yace agayawa yarima yadawo da gaggawa

LAMIDO Yace "Insha Allahu saina taimaka mata Da jikina da abin hannuna.

FAATU tayi murmushi tace "Allah yabaka iko D'an Albarka

ACAN asibiti kuwa MAHBUB ne Shida Zulaihat suka kebe yana tambayarta shin abinda yaji ackn gidan sarki gaskene?

Zulaihat tarintse ido tana futarda kwallah tace "MAHBUB duk abinda kaji gaskiyane Likitocin sun tabbatar Zeenatu cikine da ita na Daya da satittika wanda yaso ya bare Allah baiyiba rabon dai ta wahala ne Nayi kuka sosai danaji hakan dama kuma nafara fahimtar hakan kafin rashin lfyr tata.

MAHBUB yarintse idanuwa yana hawaye kirjinsa zafi yake masa meyasa Zeenatu taci amanarsa?meyasa Zeenatu tacanza hali? Meyasa tabiyewa sharrin Shaidan da Namiji ta Amince da wani Alhalin Sunyi Alkawarin Aure ……?

Muje zuwa fans
[7/30, 2:25 PM] Ummi Tandama: 📿 *KUYANGA...* 📿

*_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*Nabilancy Luv* 💘
(Auntyn S&S)

50-55

Jakadiya ce Zaune agaban UMMAH tagama kawo mata tsegumin Matan Sarki wai da alamar sun hade mata kai sunaso asirinta yatonu agidan abata mata d'a

UMMAH ta furzar da iska abakinta kana tace "jakadiya nadade da sanin abinda suke ciki nasan basa sona dani da yarima Kuma walh sainayi maganinsu agidan nan daya bayan daya cikinsu

Jakadiya tace " nibakomai nakeji ba sai *KUYANGA* Kada tacewa sarki cikin na Yarima ne domin zata iya k'ak'aba masa don tagaji abin arxiki na gdn Sarauta

UMMAH ta quta kana tace "zankuwayi maganinta domin nagama yanke shawarar abinda zansaka kiyi mata Wanda inhar kikayi zanbaki makudan kudi da zinare da gida agefen gari ckn gidajen Yarima

Jakadiya tahau murmushi tace " fadi ko meye kikeso inyi zanyishi uwar dakina "yr sarki jikar sarki me babban daki uwar gidan Sarki Fulani uwar Yarima Wanda zaihaye karaga da yardar Allah

UMMAH tayi murmushi najin Dadin kambamawa tace " So nake dazarar ansallamo *KUYANGA* daga asibiti yazamo tadawo karkashin kulawarki koda ace ta fadi ckn Yarima ne ko bama nashin bane yazama tana tare dake kullum zansa ta dawo dakinki inyaso kafin ta haihu kisa mata guba a abinci ko kishaqeta da filo ta mutu kawai

Zabura jakadiya tayi kana tace "Ranki ya Dade bazai yiyu akasheta da gaggawa ba za.a fassara mu kokuma azo ayi nadama gara dai inta haihu inbi dare inkashe abinda ta Haifa

UMMAH tayi murmushi tace " Dakyau jakadiya kinada hangen nesa tabbas zama dake akwai riba hakan ma da kika tsara yayi don haka kizama ckn shiri

Koda jakadiya ta futa daga dakin UMMAH saita nufi Dakin MAMAH domin kai mata tsegumin UMMAN tayi sa,a kuwa ta tarar da FAATU atare da MAMAHn suna hira

Jakadiya takai gaisuwa garesu kana ta xauna gefe bakinta na motsawa irin na munafukai sunso tsegumin

MAMAH tace "ya akai jakadiya akwai wani abun ne?

Jakadiya tahau shafa hab'a tana fadin 'Dama wani Abu najiyo dayake damuna tunda naji nakasa fada muku

FAATU tace 'ikon Allah mene wannan Abu fadi muji shi

Jakadiya tayi kasa da murya tace " Ranki ya Dade Gimbiya FAATU zancen ma dai akan d'an kine domin FULANI tananan tana hakon tayi masa mugun Abu domin kada yagaji sarautar mahaifinsa kada ma yaji yanaso aransa sannan inada tabbacin Yarima ne yayiwa *KUYANGA* cikin nan amma naga tanaso adanne mata hakkinta don haka yakamata kuyi wani Abu akai

MAMAH Da FAATU suka kama baki suna mamaki domin kuwa basu zataba duk da sun Dora zarginsu akai

MAMAH tace "lallai jakadiya mungode munyarda ke me kaunarmuce don haka munbaki izini akan kiringa bibiyar lamarin don kar hakanta yacimma ruwa

Jakadiya tace " Angama ranki ya Dade Amaryar Sarki Dangwale shalele agun maimartaba Uwar Lamido me jiran gado

Koda jakadiya tafuta sai FAATU tacewa MAMAH "Nifa shiyasa bantabajin inason LAMIDO yahau kankaragar nan ba in maimartaba yayi murabus haka shima LAMIDON bashida ra,ayi Sam mulkin baya gabansa balle yadorawa ransa

MAAMAH tace " to duk da hakan dai saiki tashi tsaye kiringa addu.a ba dare ba rana kirage bacci kigayawa Allah akan yakawo muku agaji kada aje a cutar miki dashi

Nan dai MAMAH tayita bata addu,o,in na kariya domin sunfurgita da zancen da sukaji abakin Jakadiya

**********
A can Asibiti kuwa anbaiwa *KUYANGA* kulawa daidai gwargwado harta samu kanta

Zulaihat CE agunta kafin arubuta musu sallama

Domin sai data kwana daya a asibitin kana aka bata sallama

Suka dawo gida Zulai ita ta gaya mata duk abinda yafaru da ita tunda a sume aka debeta xuwa asibiti batasan me akai mata ba tundaga Karin jini da daukar jininta aka auna aka gano tanada shigar cikin

Hannu ta Dora aka taringa kuka tana fadin "Nashiga uku na cuci kaina da tun farko na aminta dakai ban bujire makaba.biyayya batayimin ranaba wayyo Rayuwata ta gurbata Allah kadauki Raina kona hu.... Zulaihat tayi saurin toshe mata baki

" kada kice haka Zeenatu Allah yajarabceki da hakan babu tsimi babu dabara sannan Ni bana zarginki sai tausayinki

"Inke bakya zargina Zulaihat MAHBUB fa ? Nasan kome zance baxai yardaba Allah ne kadai zaifutar ni ko a gidannan.

Zulaihat tace " Waye yayi miki cikin?

*KUYANGA* Tace "wakuwa zaimin inba Yarima ba cikin sane bantaba sanin wani namiji ba inba shiba harta dole yakemin....nan tahau baiwa zulaihat labarin yanda rayuwarta ta gudana a Turai tareda Yarima bata rage mata komai ba har taimakonta Da SAHABI yayi

Zulaihat tashare hawayen tausayin zeenatu tace " Zeenatu Yarima yacuce ki domin ayanda nafuskanci MAHBUB yaji ciwon abun yakuma zaci ko kinyi cikinne abisa sonki har kuka yayi yace yayi nadamar fara kaunarki yace kincuceshi yayi kuka sosai a asibiti

Kuka takara fashewa dashi jin yanda MAHBUB yadauki lamarin

Shikenan tafaru ta kare tasan ko a agidan bakowa zai yarda ba sai Wanda yasan halayyar Yariman

Zulaihat ita tayi ta dannarta tana bata baki Dan kwantar mata da zcy

Kwana tayi kuka duk tafuta hayyacinta ta rame

Ko futa dainawa tayi saidai Zulaihat ta karbo mata abincinta in an gama abangaren nasu dayake dakinsu daya da zulaihat din

Tayi zaton ko MAHBUB zaizo yadubata amma saitajishi shiru na wasu kwanaki baizoba

Sannan takara tabbatarwa lallai yadau zafi da ita

Sati Daya da maganar cikin da *KUYANGA* Tazo dashi daga turai YARIMA yadawo

Magana ta yada ko ina na cikin gidan sarki

Wasu suna yarda na yarimane wasu kuma suna ganin bazai zama nashiba tunda ance yawonta take da maza dataje turan

KARSHEN TIKA TIKI TIK!!

Dawowar yYarima yasa kowa agidan yashiga murna domin ansan tunda yadawo kasar za,a samo matsaya akan cikin *KUYANGA*

Tana Zaune adaki tana tunanin data sabayi Zulaihat ta shigo da Sauri tace mata

"Zeenatu yi sauri kidauko hijabi muje an aiko sanarwa daga Fada Sarki nabukatarki agun Yarima yana can fadar da Kaf Ahalin Gidan za,ayi Zubeben kwarya...

Gabantane yafadi tareda dafe kirji take hawaye suka hau zarya akuncinta

Zulaihat tajata jiki tace mata "daina kuka kwantar da hankalinki me gaskiya yana tare da Allah Abinda kika Sani shi zaki fada kada kiji tsoro kada kuma kirage komai

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.