Kuyanga Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: KUYANGA part 1 cmplt-1-1-4-1.txt
Chapter 16 of 23
Adaidai lokacin da *KUYANGA* Ke furtawa MAHBUB wannan daddad'an kalma ar daidai lokacinne Allah yakawo yarima yazo xai girfta ta gun yahangosu yabiyo ta jikin katangar da suke tsaye kunnansa yadebo masa wannan kalami da muryarta yawatso akunnansa
Yaja da sauri yatsaya baya so su ganshi domin dan ita kawai yabiyo ta gurin
Rintse idanunsa yayi wani abu yaji yana masa yawo akirjinsa
Tabbas yau yakara aminta da zargin dayake mata na soyayya da MAHBUB duk da ta taba tabbatar masa amma kalaminta na yau yakara bashi haske
Ya dafe kansa domin Wani hali yashiga Akanta yadawo adalilinta tun daya hada kayansa yabr kasr yakoma turai yakas sakat Allah yajarabceahi da azababbiyar kaunarta dayaji batun da mahaifiyarsa ta gaya masa na LAMIDO zai Aureta bakaramin tashin hankali yashiga ba domin yasan shirinsa yagama baci
Nemanta yakeyi ido arufe ruwa ajallo Donsu keb'e yanuna mata nadamarsa ya amshi cikin nasa domin ta yarda dashi yakuma roki alfarmar tarakashi gun Sarki Ta tayashi neman yafiya
Yasan ita din me hkr ce da biyayya bazaisha wahalar taba
Waishin ma tawace hanyar zaisamu hakan? Anya bai makaro ba kuwa hhhhhh fans kufito ku gaya masa 😆😅😂🤣
Muje zuwa
[8/2, 5:04 PM] Ummi Tandama: 📿 *KUYANGA..* 📿
🌈 *KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION*
{United We Stand and succeed;Our Ambition is to entertain & motivate the mind of reader's}
*Nabilancy Luv* 💘
(Auntyn S&S)
*KAFIN AYI NISA KAI TSAYE INA MIKO GAISUWA DA GODIYA GA D'AUKACIN "YAN CIKIN GIDAN NABILA'S ONLY 4 STARS WRITERS MA,ABOTA KARANTA KUYANGA MUSAMMAN MASU COMMENT*
65-70
A SANYAYE Yarima yajuya da baya don gara yakoma kada wani cikinsu yaganshi su rainashi
Yakoma sashen mahaifiyarsa ya tararta tana Safa da marwa atsakar dakinta tana buga hannunta daya cikin daya tana kwafa da alamar har yanzun ranta abace yake tana kuma ckn halin damuwa
Tana ganinsa tahau fadin "Ya Akai yarima kasame tane?
Yazauna akan kushin yana fadin "Bansami ganawa da itaba UMMAH natarta ne da wani Kazamin bawa da take so..,UMMAH Takatse shi da sauri
"Au dama ackn gidan nanma akwai wanda take soyayya dashi ? Ashe haka tazama yarinyar to da alama ma cikin agida tayishi kenan
Yarima yadago da sauri yadubi mahaifiyarsa da jajayen ido yace "A,a UMMAH tunjiya Dana dawo nagaya miki cewar Wannan cikin fa nawa ne kada ki kakabawa wani makaskanci mana jini na karba.... " Dakata!
Ta dakatar dashi da daga murya ranta abace
"Wai bazaka daina kiran cikin jikin *KUYANGA* da sunan mallakin kaba,walh inkai ka karba to ni ban karb'aba domin bazan yarda da shege ace shine jikanaba jikanma ajikin baiwa Allah yakiyaye dama ajikin wata baturiyar ne ko " yar sarauta da sauki
Yarima yace " Amma ai u UMMAH shi .mahaifina
yakarba ballantana ke da kike mace kikafi sona.
Tace "Dan babanka yakarba be dameniba domin yakarbane da wata manufa aransa tunda bayason azageshi bakuma yaso Dan daza,a haifa yatashi yarasa madafa amma nasan ba har zuci yakarba
" kidaina fadar haka UMMAH.
"Saina fada din kaida bakasan inda yake mk ciwo ba baka ma damu da kyautar kujerar sarauta da Aka baiwa LAMIDO ba
Yarima yace "Ni wannan kam baya gabana fatana dai ayanzu *KUYANGA* zeenatu ta Amince da abinda nazo dashi sbd Allah yajabceni da kaunarta UMMAH kitaimaka kiyi wani Abun walh sonta nakeyi sosai har cikin raina
UMMAH ta maka masa wata harara tace "Shima LAMIDOn daya Amsa yana sonta zai Auretan nasan badan Allah yayiba a to.
Yarima ya shiga tunani
Kai Yadafe don kan nasa ke bugawa dolene yasamo mafita akan MAHBUB Domin irin kalamin dayaji tana watsa masa na soyayya tabbas su yake muradin yaji wataran tagaya masa
Toshin ta wace hanyar? Ta Yaya?
Yakasa samo amsar tambayar domin kansa yakulle Dole saiya nutsu
UMMAH bacin ran abinda Yarima yaxo mata dashi baisa tasami nutsuwa ckn rantaba tabbas dolene tasami mafita akai rana zafi inuwa quna knn domin wannan shine ana wata ga wata can Hukuncin da sarki ya yanke nabaiwa LAMIDO sarauta nacinta arai saigashi Yarima yazo mata da wani batu wai yana son *KUYANGA* to tawace hanyar ma zaisameta Alhalin LAMIDO yakarba kowa yashaida hakan lokaci kawai ake jira
Yarima yadago dakansa yaga mahaifiyarsa ta hada kai da guiwa
.yasauko kasa Yakama kafafunta yana fadin
"UMMAH kitaimaka mini kije ga mai martaba kinemamin yafiya sannan kifada masa batuna na karbar cikin *KUYANGA* da zanyi kice nayi nadama sharrin shaidanne inasonta yadaina fushi dani
Wani dunqulelen abune yatsayewa UMMAH a maqoshi na takaici da bakin ciki
Taki jinin jin Kalmar nan dayake furtawa na son *KUYANGA* dayake fada mata yanayi domin ita ji takeyi tana kara tsanarta ma tunda itace tazamo silar rushewar Burinta ayau,tayi nadamar amincewa da tayi tun farko daya yatafi da ita kasar waje tasan da bata yarda sun tafin ba da tuni hakan bata faruba tunda gashi akan Yariman yak'ita yaki cikin ne LAMIDO yashirya manaqisa yakarba don abashi sarauta kuma anbashin kamar yadda sukeso kuma bazata taba bari suji Dadin yin mulkinba indai daranta saita zame musu masifa a ckn gidan
Wannan tunanin tane
UMMAH dai taga Yarima da Gaske yakeyi domin shirin kuka yake mata akan bukatarsa
Dabara ce tafado mata tace masa "kwantar da hankalinka shalele zansan abinyi agun Takawa
Yace " to agun ZEENATUN fa?
Tahade rai
Yamarairaice mata Taga dai da Gaske ne lamarin nasa saitahau tunanin anya kuwa ba Wani abun akaiwa D'an nataba mutumin dayaqi Abu futuk kuma cikin "yan kwanaki saiya haukace akai
Lamarin Allah nefa UMMAH 😃Allah yakara inji fans 😂
Takama hannayensa itama ckn marairaita tace masa "YARIMA kai D'ane D'an fari abin so aduk wani gidan sarauta baikamata ka lanjare a son BAIWA ba kafi karfin Auren *KUYANGA* ajinka da kimarka da izzarka na Dan sarki zai ragu inhar ka Auri *KUYANGA* inaso kayi hakuri kabarta ni dakaina zansamo maka ko ackn gidan sarautar mune akwai mata masu kyau adangina mahaifina kafin ya mutu yayi sarki yanzu babban yayana shine sarkin garinmu kasan da haka Babbar masarautace datafi wannan munada mata kyawawa yan boko wayayyu sai wacce kazaba babu me kinka walh kanada cikar da namiji kaidin gwarzone me tattare da mazan taka gaka kyakkyawa kafi LAMIDO kyau da kwarjini Meye naka na damuwa da Baiwa Alhalin kafi karfinta shi din dayace abashi ita ya Aura kabarsu dama da ita yadace
Yarima yakyabe fuska yace " UMMAH bazaki ganebane
Tace "tayakuwa zangane kaki amsar batuna
Dayaga da Gaske takeyi baxata sakkoba saiya rushe mata da kuka yasan lagontane bata son damuwarsa balle ganin hawayensa
Nan take kuwa ta rude tace masa yayi shiru zata duba lamarin yaje zuwa gobe kafin tasan abinyi
Yana Fita ta aika aka nemo mata jakadiya
Jakadiya na zuwa tagurfana gabanta
" gaisuwa nakeyi Uwar dakina barka da warhaka gani ckn ladabi mezan miki ?nasan bukatace babba tasa kk kirani
UMMAH tagyada kai tace "tabbas kuwa jakadiya domin Yarima yaxo min da banzan zance wai yanzu shi *KUYANGA* yakeso kuma ya amince da cikin jikinta nasane
Jakadiya tadafe kirji tace " wannan Abu bai Dadin jiba kamar Wanda akai masa surkulle
UMMAH TACE "Maza kije kishirya kije min gurin GOGAL matsafiya kice inaso acire masa son yarinyar ckn kwana daya
Da sauri jakadiya tace " angama uwar dakina.
UMMAH takawo kudi tabata jakadiya tafuce da sauri
Amma kafin ta tafi gurin matsafiyar tasu dake bayan gari saida tafaki ido tashige Sashin MAMAH Takai musu Gulmar wai ga Yarima can yarikicewa Mahaifiyarsa waishikam yanzun *KUYANGA* Yakeso kuma ya amince cikin jikinta nasane
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.