Kuyanga Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: KUYANGA part 1 cmplt-1-1-4-1.txt
Chapter 14 of 23
*KUYANGA* Tahau gyada kanta taredajin karfin guiwa ajikinta
Zulaihat tace " muje inrakaki fadar......
🏃🏼♀🏃🏼👭🚶🏼♀🚶🏼🕴🏽👪👩❤💋👩👨❤👨👩❤👩 fans kutaho rakiya mana
Duk masoyin *KUYANGA* kada yasake abarshi abaya ataho arakata Fadar *SARKI ABDALLAH*
MUJE ZUWA FANS😅
[7/31, 11:29 AM] Ummi Tandama: 📿 *KUYANGA...* 📿
*_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*Nabilancy Luv* 💘
(Auntyn S&S)
55-60
CARBI ne ahannun *KUYANGA* datake ja ackn burmemen hijabin dayake jikinta Addua kawai takeyi Akan Allah yabata Nasara yashige mata gaba yakuma dorata akan maimartaba
Gaban tane yafadi ganin yanda fada ta cika da ahalin gidan daga matansa da yaransa YARIMA da LAMIDO da kuma fadawa da Galadima da sauran masu mukaman gidan Bayi ne kawai basa gurin
Kowa ita yake kallo itako kanta akasa tasami guri anesa dasu tazauna Zulaihat ma ta xauna kusa da ita
Maimartaba yana ganin shigowarta yayi Gyaran murya ganin tazauna nesa da mutane duk aka nutsu ana kallonsa
Yace " *KUYANGA ZEENATU* Ke muke jira kuma adalilinki muka taru anan Dan haka kidawo tsakiyar mutane kizauna domin ki amsa tambayoyi daga bakina
Tayi saurin tashi tabi umarni takoma tsakiyarsu inda fadawa suka bata guri akusa da Yarima dayake kusada Sarki LAMIDO na gefen yariman Wanda tunshigowar *KUYANGA* Yazuba mata idanu yana kare mata kallo
Bayan ta zauna Mai martaba yawatso mata tambayar data rikita mata kwanya
"Dawa kike tarayyar fasikanci a kasar waje ???
Ahankali tace " Bakowa,
Yace "To waye yayi miki ciki?
Hawaye na zuba a idonta tace " cikin jikina bana kowa bane illah na YARIMA!
fadawa suka hau salati
Yayinda Sarki ya rintse idanu jin yasami jika Dan gaba da fatiha a ckn gida
Suko matan kirji suka dafe alamun mamaki
Yarima kuwa fuskar sace ta nuna bacin rai tsababa ji yake tamkar yashaqeta ta mutu akan wannan tonon sililin datayi masa
LAMIDO kuwa girgiza kai kawai yk yi na al,ajab sannan yana mamakin yayan nasa da wannan hali
UMMAH mahaifiyar Yarima Ta dakawa *KUYANGA* Tsawa "karya takeyi munafuka saikin nemo Wanda yayi miki inma ackn turawan da kika barosu kika gudo
Sarki ne yatsawatar mata akan tayi shiru
Yajuya kan Yarima yace masa " YARIMA ya abin yake? kanada tabbacin naka ne ko ba nakaba?
Yarima yaji sassanyar Tambaya sai yahau gyada kai yana fadin "Ranka ya Dade bansan da maganar ba baninayi mata cikiba
Sarki yace " to wanene?
Yarima yayi shiru
Jin yayi masa shiru yasa yaci gaba da tambayarsa
"Sau nawa kataba Kusantar ta?
Nan ma yayi shiru kansa akasa yahau fidda xufa
Ganin haka sarki yace " tun anan alamu sun nuna cikin kane Dan haka bazaka wulakanta Rayuwar yarinya kaci riba ita ta wulakantaba Dolene ka Aureta....
"bazai yiyuba!
Cewar UMMAH tafada ranta abace
" don ci baya sai D'ana ya Auri KUYANGA gaskiya da sake
Mai marmataba yanunata da yatsa "kishiga taitayinki Fulani idan Dan kine nima nawane nama fiki iko dashi danhaka magana dole abita in anason zaman lfy dani
YARIMA yadukar dakansa yana magana ahankali " Ina Neman Alfarma ayimin rai walh bana sonta akwai wacce nakeso mun mayi alkawarin yin Aure atsakaninmu ayimin kowanne irin hukunci amma banda wannan
Galadima yayi Gyaran murya yace "kwantar da hankalinka Yarima Munanan ma baza.ai hakaba kaidai katsaya da gaskiyarka inhar bakai kayi cikin nan ba Ai jini zai nuna dazarar ta haihu za a auna jininka da abinda ta haifan agani
Galadima yadubi *KUYANGA* duk don yakamata da laifi sbd yana goyon bayan Yarima yace mata
" Ke Wanene shaidarki akan wannan lamari?
Tadago dakai ahankali tana tace "SAHABI shine Shaidata domin shine yadawo dani daga kasar waje
YARIMA yazaro idanu yana mamakin lafazinta wato Ashe SAHABI munafukin Sane?
Galadima yace mata " wanene kuma SAHABI?
Tace "Abokin Yarima tun acan yasan wasu abubuwan
Nan tahau bada labari tiryan tiryan Har takai karshe tana fidda kwalla a idonta
Kowa agun yaji labarin KUYANGA me taba zuciya Wanda masu tausayi agun harda hawayensu irinsu MAMAH da FAATU
Haka LAMIDO yacika da tausayinta zufa taringaa karyo masa agoshi yana gogewa
Sarki yakalli Yarima daya sunkui dakai alamun rashin gaskiya yace masa "Maza kira SAHABI awayarka kasaka handsfree kowa
Jiki asanyaye yakira wayar SAHABI yabarta a bude sunajin tana ring
Saida takusa katsewa kana Sahabin yadaga
Sarkine dakansa yahau masa magana
SAhABI yanutsu awaya jin martabane dakansa
Duk yanda ake ciki dai da mai martaba yazayyane masa kana yakara da koro masa Tambaya
SAHABI yakadu dajin hakan tabbas yasan abin babbane
Nan yagyara zama yafede masa biri hr wutsiya bai rage masa komai ba na abinda yasani duk domin yaga yafutar da *KUYANGA*
Yarima yaita mamakin SAHABI nayanda yake zayyano bayanai
Da sarki yagamaji yaiwa SAHABI godiya yakashe wayar
Ran sarki yagama baci akan musantawar da Yarima keyi
Yarima yahau sose sosen kai jin Sarki yace masa " kaji abinda abokinka yace anyi hakan?
Yagyada kansa
Sarki yace "Kasan da saninka Inta haihu zan daura muku Aure da ita sannan ayanzu Alhakin kulawarta yadawo kanta sbd abinda ke jikinta
YARIMA bai yi maganaba
UMMAH Ranta yabaci sosai da jin sannan hukunci
Take Sarki yasallami kowa aka watse
Kwana biyu da faruwar hakan YARIMA yabar gidan batareda Sanin kowaba ckn dare yagudu ko UMMAH bata saniba
Yahada kayansa yasilale cikin dare yatafi inda yafito
Da labarin yashiga ckn gidan ba karamin tashin hankali mahaifiyarsa tashiga ba Don hartahau zargin waiko Asiri akai masa dahar yabar gida
Abu kamar da wasa saida yakwana hudu labari ya isa fada
Tabbas Sarki ya guntsi bakin ciki awannan ranar yasan Yarima yanason yakun yatashine kawai tun aranar yakara tabbatarwa kansa cewar Yarima bai cancanci yaxama sarki ba
Tuni aka hadu kowa da kowa afadar Sarki domin shi yakira taron
Inda yabayyana musu bakin cikin dayake ciki
Yace da *KUYANGA* dafarko inaso kizama me daukar kaddararki haka Allah yatsara miki naso inga yarima ya aureki domin Asirinki yarufu kedashi dinma
To gashi Allah baiba yanunan ban isaba yawatsan kasa a ido yagudu yabar kasar
Dan haka inaso kikwantar da hankalinki da zarar kinhaihu zan karbi abinda kika Haifa hannu bibbiyu nayi miki Alqawarin baxaku wulakantaba ke dashi Dan haka wanene kike so ackn gidananna fadawa ko ckn BAYI xan muku Aure domin inwanke miki zuciya
*KUYANGA* tayi shiru kanta nakasa
Ayayinda MAHBUB dake ckn mutane nesa da ita yadago dakanta yana kallonta gashi dai har ynzu yana sonta to amma wani Abu ma sukar ransa inya tuna ta yaudareshi duk da azaman farko da akayi babushi ankawo masa Rahoton cewa Ba da saninta komai yawakamaba Yarimane ya cuceta
Yana so yafurta kalma abakinsa ya gagara jiyayi mai martaba yayi masa kwarjini bakinsa yayi masa nauyi
Yaso yafurta shine maaoyinta na asali na gaskiya da akai musu kutse arayuwa aka rushe musu farin ciki
Allah cikin ikonsa MAHBUB saiya kasa magana Allah yanufi LAMIDO Da maganar data furgita kowa harni
Hannu LAMIDON ya daga yana fadin "Ranka ya Dade ka Amince min Na Aureta domin inraya sunnar manzan Allah nakuma shiryi taimaka mata kota halin kaka domin naji zuciyata ta kwanta da ita....
Kallon kallo UMMAH suka hauyi da Jakadiya hakama MAMAH takalli FAATU yayinda FAATUN takalli Mai martaba domin jiran Abinda zai yanke akai....
To muma fans da writers sai mubi layi afada domin jiran tacewar Sarki Abdallah
🙇🙇🏼♀🧖🏼♂👩❤💋👩👨👨👦👦👩👧👦👩👧
Muje zuwa
[8/1, 3:17 PM] Ummi Tandama: 📿 *KUYANGA...* 📿
*_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.