Kuyanga Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: KUYANGA part 1 cmplt-1-1-4-1.txt
Chapter 2 of 23
Yace "kada kidamu da Wannan Ummah na wataran ai dole inxauna din nidai yanzu kiyimin kokari intafi
Tace "kada kadamu kamar katafi kagama zanyiwa TAKAWA maganar ayau.
Yayi murmushi yace "Yawwa nagode Ummah saidai kuma.……
yai shiru yana sosa keya
Tace "ehe!fadi mana yakai shiru kafadi komeye in akwai bazai gagara ba zanmaka.
Yace ckn rage murya "Saidai naga wata yarinya awaje ackn KUYANGU zanso mutafi da ita tayimin Rakiya domin ta hidimta mini acan.
Murmushi tayi tace "bakada wannan matsalar kowannensu akarkashinka suke kanada ikon kowanne bawa agidannan ko kuyangu dan haka kasa aranka kamar ka tafi da ita kagama yatake yarinyar?
Take yahau kwatantata
Tagano ko wa yake nufi domin KUYANGA Zeenatu tafi kaf kuyangun gidan Nutsuwa dakyawun yanayi tanada kyau nagani afurta
Jin mahaifiyar tasa ta Amince masa yasa yaita xuba mata godiya
Shiyasa yake matuqar son mahaifiyar tasa baitaba neman abu ta bangarenta yarasaba tana son akullum tafaranta masa bata son laifinsa
Koda yafuto farfajiyar gidan baza ido yaitayi ko zai sake ganinta
Amma baiyi sa.ar ganin kome kamartaba
Tsaki yaja Aransa yace "to meye nawa nadamuwa da son ganinta Alhalin ita zata zamo gadon baccina ita xata xamo jin dadina ita zata zamo komai nawa sai yadda nayi da ita..……
_Tabdijan muje zuwa_
[7/23, 10:28 AM] Ummi Tandama: 📿 *KUYANGA....* 📿
*_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)
5-10
mai Martaba Sarki Abdallah yayi shiru bayan gama jin Bayanan da Ummah Tazo masa dashi natafiyar Anwar Turai
Yakalleta yana murmushi yace "Naga alamar yaronnan inmuka ta tashi bazai gyara halin saba Nikam bana sonsa da zaman wajen nan nafisonsa akusa damu domin Aure nake so yayi tunda yakai munzalin Aure ko Lamido yanzun ya isa Aure barantana shi
Ummah tace " Aure ai nufin Allah ne baisamu wacce tayi masa bane shiyasa saimu tayashi da Addu,a kada mutakura masa Tunda can din yafi jindadi gara kabarshin yaje aidebe kewa yakeso yayi
"Kina baiwa yaronnan gudummawa naga alamar bakya son yagyaru shiyasa kike daure masa gindi
Ta dafe kirji tacanza fuska
"Kamar yaya? Nikam walh babu wani daure masa gindi danakeyi kawai bana son yashiga takurane da damuwa Tunda shi bayaro bane da hankalinsa ai ko yana nesa damu bazai lalace ba shiriya fa ta Allah ce Addu.a kawai yadace muringa binsa dashi.
Mai martaba yace "Amma dai kinsan bazaki hada halinsa dana Lamido bako? Lamido yafishi nutsuwa da hankali harma biyayya da ace Lamidon ne babba dana more....
Ta katseshi tana kuka "Kawai dai kace kafison Lamido akan shi nikam walh banajin Dadi sai inga kamar kana nunan banbancine kuma komai lalacewar Yarima ai dai shine babba kuma dole shizai zama sarki acan gaba....
Yakatseta dacewa "Saurara Fulani kinsan dacewa Adalin Sarki me kamun kai shike cancanta da yin sarauta akowace masarauta dan haka dole sai inyarima yakasance da hakan sannan zai mulki garin nan inko bai canzaba to Al,umma bazasu soshiba Tunda ko a yanzun sunfara farga da banbancin halayyarsu
Tace "To walh koma meye Nikam Bazan taba barin Wani bayan Yarima ya mulki garinnan ba inba shiba dan haka koma meye za,a yi masa shine dai gaba
Yadaga mata hannu "ya isa meye na tada hankali da kuka indai wannan maganar mulki ce Allah ketsara komai bamu zamu tsara ba tafiya turai kuma Yaje yaita tafiya Nadaina hanashi tunda bakya so inhana din duk randa yagaji da zuwa yadaina Amma kusan da sani zanbashi mata nan ba dadewa ba
Har zatayi magana kuma saita fasa tunda bazata ari bakin yariman ba tasan halinsa sarai shima bazai so Auran hadiba.
Ta mike tafuce batareda ta gaya masa cewar da "yar rakiya zai tafiba wannan tafiyar tasan Sarkin bazai bariba
*****
Ana gobe zai tafin Ummah tasa aka kira mata *KUYANGA*
Koda tazo ckn biyayya ta durkusa gabanta tana jiran umarni domin tayi tsammanin aiki aka kirata tayi
Ummah tace mata "Kuyanga Zeenatu ko?
Ta daga kai sama
"To kifara shiri daga yau gobe zaku tafi turai keda yarima zakijene domin kiringa hidimta masa komai nashi kece basai yace ba indai aikin wahalane kada kibari yayi Har sai ranar da yaga damar dawowa zaku dawo tashi kije.
*KUYANGA* Tace "Angama Ranki yadade.
Ta mike tafuce daga dakin fulanin
Koda takoma sashinsu zama tayi a inda suke zama da MAHBUB Ta zabga tagumi tashiga tunanin wai itace zataje turai tabdijan lallai zataji dadin Rayuwa zata canza tawaye tunda tashigo gidan sarki tun tana karama bata taba futa wajen gari ba sai gashi abin farin ciki zata keta hazo
TO ABIN BAKIN CIKIN FA? wata xuciyar ta tambayeta tare dayi mata tunin abinda zatajeyi turai dakuma tuni da wanda zataje din
Take fuskarta tacanza daga walwala zuwa Damuwa
Zuciyarta tahau bugawa to shin wane irin zama zasuyi Alhalin halinsa bame kyau bane?ance yana shan giya ance yana neman mata zance ya yadu agidan dan dai ana boyewane kada aji abakin mutum a hukuntashi.
Jitayi antabata afurgice tadago kanta saitaga ashe MAHBUB ne abokinta abokin sha,awararta
Takalleshi kawai yau babu dariyar datakeyi masa
Yazauna kusa da ita yafahimci akwai damuwa yau kenan
Yacire mata tagumin da tayi yace " *ZEENAH*! Haka yake ce mata
Takalleshi akaro na biyu tasunkui dakai
Yace mata "meya faru naganki ckn damuwa anyi miki wani abin ne bayan nabarki anan din?
Ta dago ahankali tace "Bayan barinka nan gurin aka aiko kirana daga Fulani
Koda naje kiran saitake gayamin wai infara shiri gobe Yarima zaiyi koma Turai dani xai tafi domin hidimta masa da koma kuma inmun tafi ba ranar dawowa harsai inyagaji yadawo dankansa
MAHBUB yadafe kirjinsa tareda Rintse idanu yana kiran sunan Allah
Tabbas yashiga tashin hankali domin ayau yashiga halin dabai taba shiga ba arayuwarsa tunda yazo duniya
Yana bude idonsa kwalla nabiyo baya yace mata "ZEENAH tafiyarki Turai tana daidai da tafiyar farin cikina nackn gidannan Domin kece me deban kewa akoyaushe kuma ke nake kallo nake jin dadi koda ina ckn jin Yunwa ke nake kallo naji nakoshi kinsan da cewa Nadade ina son.....
Yayi shiru yana goge kwallar datake gudu akuncinsa
Yakalleta ido da ido yace "ZEENAH bantaba gaya miki Sirrin zuciyata ba saiyau, yauma dole ce zata saka domin naga zakiyi nisa dani Walh ZEENAH zaman da nake dake bana abokantaka bace Na SO Ne zallah dan Allah kisoni koda bazamui Aure ba kice kema kina sona ko naringa tuno kalmar inajin Dadi
*KUYANGA* Taji wani yarrr!ajikinta taringajin shigar wani abu tundaga tafin kafarta har zuwa kwanyarta tabbas Tafahimci wannan abun dayake shigarta bakomai bane illah Son MAHBUB ada itakam tadaukeshi aboki amini amma ayau saitaji yanayin yajuye mata da So
Tabbas tana sonsa itama bayama data tuno zasuyiwa juna nisa saitaji xcyrta ta karye hawayen da basu zubo ba saigashi sunxubo ganin nasa ma sunzubo din
Tace ahankali " MAHBUB meyasa baka gaya min tuntuniba meyasa kaboye sai yau da muka makarowa juna zaka fada yanzu gashi zanyi maka nisa
Yace "Duk nisan da zakiyi indai kina sona to tamkar muna tare ne kedai kitaimaka ki furta min ko naji dadi.
Takalleshi tayi murmushi tasadda kanta akasa tace
"INA SONKA MAHBUB."!
yai ajiyar zuciya tareda yin hamdala ga Allah yace "nagode naji dadi ki rikemin Alkawari ki rike amana kikuma kula inkun tafi bamu da ikon kanmu ZEENATU akarkashin ikon Sarki da Matansa da "YA"YANSA muke bamu isa muyi musu da Umarninsu ba sai yadda sukayi damu amma kada kiyi biyayya da aikin zalinci kada kisake acuceki kikasance me addu,a aduk inda kike kikuma zamo me kamun kai aduk inda kika tsinci kanki domin kada ayi miki cutar da zata karya miki Lagon Rayuwarki.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.