Kuyanga Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: KUYANGA part 1 cmplt-1-1-4-1.txt
Chapter 10 of 23
Kayanki kaf bayardasu xanyi bazaki kara sakasuba domin kwata kwata babu na arxiki ack
Yanzu zanfita zansayo miki Dogayen riguna kala uku natabbatar baxa,a dara kwana uku biza bata samuba sannan zantaho miki da magani sbd ciwon kan naki zantaho miki da abinci ma kada kisawa kanki damuwa baxan cutar kiba ba halin na daya da yarima ba domin ni ina zuwa kasar nan ne don hutawa ba wai don lalata da mata ko yin mummunar dabi,a ba dai kiyi hkr da abinda yayi miki haka kaddarar ki take kijure kixama me tawakkali Zeenatu watarana sai labari zanje baxan dadeba
Tace ahankali "Nagode
Yace "ba damuwa kigodewa Allanki.
Yajuya xaitafi kenan tace masa "Dan Allah kada kanuna masa muna tare ina tsoron abinda xai faru tunda shike da iko da ni da kuma.…
SAHABI yakatseta da Cewa "kwantar da hankalinki nasan kina cikin tsoro kuma kina neman taimako bazan bari yasan kina guna ba zankoma gidan ma yanzun gun me gadi inja masa kunne akan kada yagaya masa
Tayi ajiyar zcy tareda kakaro murmushi tace
"To saika dawo.
Yasa kai yafice
Kai tsaye Gidan Abinci ya wuce yasiyo mata me tsadar gaske
Kana yashiga pharmacy yasiya mata magunguna hardana ciwon jiki dana zazzabi da ciwon kan
Sannan yawuce gidan Yarima yai sa,ar kuwa Baidawoba
Yakebe da Me gadin yabayyana masa komai tareda bashi kudi cinhanci
Me gadin musulmine dan kasar cameroon ne yanajin hausa sosai
Yahau gyada kai yace "bazan fadaba insha Allahu domin natausaya mata yarinyar tanada kirki tun zuwanta nadaina zama da yunwa wannan Yaro bashida kirki sam, baya ganin karama ce Amma dai kaima kayi taimako Allah yabiyaka.
SAHABI yaji dadi yayi murmushi yace "Amin ngd.suka karayin musabiha yatafi
******
Abangare guda da YARIMA ANwar yadawo gidan bai neme inda takeba ko kusa ko alama domin cikin fushi yake da ita
Kwana yayi yana tuna yanda takasance atsakaninsu domin ta bashi haushi sosai wato don yana jin dadi ajikinta shine tasami hanyar rainashi har tana iya musanta masa da sa,insa dashi lallai dolene yayi maganinta domin bazai zauna da *KUYANGAR* Da bata ganin darajar saba zai gyara mata zama
Abu daya yake masa yawo akwanyarsa Baiwarta da YANDA take wajen ni,ima tabbas awannan fage yasan ta ciri tuta ba karya yarinyar tacika mace baitabajin macen daya kusanta yajita zam -zam kamar taba
Aikoda zaiyi fushi da ita na lokaci kalilan ne bazai iya rabuwa da itaba tunda ya dan daneta yaji wani abu aransa akanta yazaune masa kamar super glu aransa
Yakwana yana tuno Dadin dayaji ajikin *KUYANGA*
Da Gari yawaye sai yashirya zaifuta gidan wani abokinsa zasu je wani shoping har ya futa kuma yai tunanin yacancanta yaganota tunda baiji motsin taba ko batada lafiya
Yana kuma son dai yaganta domin shap dinta na burgeshi da cikar kirjinta
Yana shiga abin mamaki baiganta ba baikuma ji motsinta a toilet ba har lekawa yayi
Saiyaja yatsaya a tsakiyar dakin yana tambayar kansa "to shin ina wannan yarinyar taje ne?
Yai sauri yafuta yaleka kicin namma bata nan
Yazaga bayan gidan shine har lambu yagama zagayensa yana neme nemensa amma shiru ba bayaninta balle ma wata alamar ko tana gidan
Nan kuma jikinsa yafara sanyi kada dai guduwa tayi? Yatambayi kansa
Gabansa yafadi alokaci guda
Domin yasan inhar ta gudu ba iya kai kanta gida xatayiba tunda batada kudin jirgi balle wata hanya agarin da xata iya guduwa gida
Yatafi da saurinsa yatambayi me gadi yace masa shin ko yaga fitowar Zeenatun?
Me gadin yahau girgixa kai yana nuna tu,ajjibinsa azahiri yana fadin "bangantaba tun jiya rabona da insata a ido
Yarima yace "azamanka nayau aget kamatsa na awa nawa ko minti nawa?
Me gadi yahau sosa keya yace
"Eh to dayake dai yau natashi da bacewar ciki inata shiga toilet shiyasa bana ce ko sau nawa ma nabar get ba kuma nakan dade kafin nadawo.
Yarima yadafe kai yace "Shikenan ta gudu! Nashiga uku.
Me gadi yazabura yace "ta gudu? Zeenatun innalillahi wa innailaihirrajiun.
To yanzu ina za.aje aganta wata sani a kasar nan?
Yarima yaharareshi yace "koma wata sani ko bata sanin ba ai kana da hannu aciki tunda kana wasa da aikinka baka rufe gidan yadda yakamata.
Yajuya yabar Megadi da atsaye saroro
Aifa aranar yarima yarasa tsugum yanata Faman xaryar gun jami,an tsaron garin yana basu bayanin B'atan *KUYANGA* waiko Allah zaisa aganta ahanya
Kwana biyu sukai suna checking akanta amma shiru dole yahakura yakira gida yana tambayar mahaifiyarsa
Koda UMMAH taji abinda yake faruwa daga bakinsa ta kidime tahau yi masa fada
"Yarima kodai akwai abinda kake matane?ko takura mata kayi da ayyuka da fadanka?
Yarima yace "To UMMAH inma nayi mata fadan saita gudu? Banida ikon dazan matane?kawai dai yawon bude ido nakejin ta tafi tunda idonta yabude dama bakiga yanda take shigar kananan kayaba tana son tafuta gari nahanata ashe dai xata shammaceni tagudu
Jin Hakan yasa UMMAH ta yarda tahau fada tana cewa "to ai da ba guduwa yakamata tayiba saita fada maka maza take bukata saika dawo da ita gida ayi mata Aure yanzu kaga hakan ai sharri zata jawo maka ace kai ka koreta ko cutarta kakeyi yasa ta gudu gani da mahassada ackn gida (kishiyoyi)
Kuma dole kasan TAKAWA zaiyi fada amma kabarni dashi zansan mezan fada masa
Yarima yahau godiya yanajin dadi aransa
******
Akwana na ukunta agidan SAHABI bizarta ta samu itadashi
Suka kamo hanyar dawowa Nigeria
Dayake tasaki jikinta dashi tunda taga ba cutarta xaiyiba sai suketa hirarsu ajirgi tana ta masa godiya da nuna masa farin cikinta azahiri
Shikam bakomai yake ce mata ba sai "nikam bazan daina gaya miki ina sonkiba kirike alkawari
Ta lumshe idanunta tabbas inda wanda zataso to abayan SAHABI yake amma ina yau data nufi kasarta ji take wata kaunar MAHBUB ta dawo mata sabuwa
Dayaga tashiga tunani saiyace mata "Zeenatu kada fa kisawa kanki damuwa kicire komai aranki domin ni da Aure nake sonki kuma bazan ringa miki kallon abinda yarima yai miki ba kimance da komai yadda nima zanmanta da komai haka kuma kija bakinki kiyi tsit kada kifadawa kowa abinda yasa kika dawo ko abinda yarima ke miki kimarki zata ragu agun mutane sannan za,aita yawo da maganar agidan.
Tagyada kanta tagamsu itanma ai zataso asirinta yarufu domin kada masoyinta yaji bazaiji dadiba sannan ga "yan uwanta KUYANGU abin xai iya zama abin surutu ayi mata wani kallo
Da dare suka diro kasar Nigeria bayan Ishsha'i
Har gidan sarki Abdallah yarima yadauki shatar mota aka kaisu amma shi bai bari anganshiba
Ita kadai aka sauke akodar gidan sarki aka tafi dashi zuwa hotel din dazai kama yakwana ingari yawaye ya wuce Daura garinsu
Kafin su rabu tun amota yabata waya karama kirar Tecno domin yace yana son yaringa jin muryarta akoyaushe sannan in tanada Damuwa ta sanar masa zai mata maganin damuwar
Tabbas SAHABI yagama mata komai
Shigarta gidan tun daga kofa aka fara mamakin dawowarta tunda ansan da Ita da yarima suka tafi kuma basuda labarin dawowar yariman
Kai tsaye bangarensu ta zarce bata bari kowa yagabta ba
Adakinsu mutum biyune basuyi bacci ba Zulaihat idonta biyu kawarta
Da zulaihat taganta kirji ta dafe tana fadin "wa nk gani kamar Zeenatu? Dama yau kuna tafe amma banji sanarwar ackn gidan ba
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.