Kuyanga Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: KUYANGA part 1 cmplt-1-1-4-1.txt
Chapter 12 of 23
Iya Yabi ta tsorata matuqa gaya jiki na rawa tace "to abar maganar Allah yabata lfy yarufa Asiri
Acan gida Da labarin neman jini yazowa kowa sai akaita nokewa MAHBUB kuwa da rawar jiki yanufi asibitin sbd yabada jininsa ga masoyiyarsa
Shi atunaninsa ko wata lalaurar ce tadaban take wahalar da ita
*********
Dayake aranar LAMIDO yadawo yanufi daga SUDAN yagama karatunsa wanda yayi na shekara 5
Rangadi suka futa shida maimartaba domin Sarki yana son LAMIDO kwarai. can bayan gari yajashi wai suyi hirar yaushe gamo anitse kada atakura musu
LAMIDO yaji dadin wannan zaman da mahaifin nasa domin sunsa hira tun da sukazo wajen sha daya nasafe sai yamma suka fara haramar komawa gida dayake dirar sassafe yayi Nigeriyar
Jakadiya tana gaban UMMAH tana fadin "Ranki yadade naje cikin azama fada domin insanarwa sarki labarin irin abin kunyar da *KUYANGA* ta hada mana ayau sainatarar bayanan natambayi Dogari wai yafuta shida LAMIDO dakuma fadawa Rangadi
Lallai nayarda Sarki yana son LAMIDO domin namanta rabon dana ganshi yafuta ran gadi balle bai taba zuwa da YARIMA ba anya kuwa ranki yadade ba asiri Matar can tayiwa Sarki da Yarima ba kuwa?
UMMAH ta hau gyada kai ckn takaici tana fadin "Ai walh jakadiya matar can burinta ackn gidan nan baxai taba cikaba domin D'ana shine sarkin gobe da yardar Allah kuma Duk me binsa Da sharri sai nayi maganinsa muxuba mugani
Har dare da Sarki yadawo shida LAMIDO labari baije kunnan saba
Sai da Sassafe Jakadiya ta bazama taje takai gaisuwa tagurfana agabansa don takware a munafurci da gulma
Saida tagama banbadan cinta dayi masa kirari kana ta zayyano masa komai duk abinda tasani daya faru
Sarki yayi Shiru kirjinsa na dukan uku uku dan fargaba
Yanzu cikin KUYANGUNsa akaiwa 1 ciki?me hankalin ciki da yasanta farin sani sbd yawan Ayyukanta ackn gidanba da ladabinta
Yadafe kai yai tsahon minti biyar ahakan kana yadago ya kalli jakadiya yace
"maza kije ki kira min matan gidannan su ukun
Su UMMAH Da FAATU Da MAMAH yake nufi
Dakin fulani tafara isa tagaya mata kana tawuce dakin MAMAH
Bayan tasanarta kiran sarki saita wuce Dakin FAATU Tana shiga ta tararta da LAMIDO Suna hira tadurkusa takai gaisuwarta garesu kana ta isar da sako tafuta
Koda suka hadu gaban Sarki UMMAH tafisu faduwar gaba sbd tasan kaf dinsu itace me laifi tunda itace silar samuwar cikin *KUYANGA* dan dabata turata kasar wajeba da yarimanba da batasa samuba
Bayan Shiru na wasu mintina Sarki yayi gyaran murya kana yakallesu d'aya bayan d'aya yace "Kunada masaniyar Abinda yake faruwa agidannan?
Suka hau gyada kai
Yace "to ya akai har hakan tafaru ?ya akai *KUYANGA* Tasami ciki a ina akai hakan meyasa kukai wannan saken...?
MAMAH ta budi baki ahankali ckn ladabi tace "Ranka yadade Takawa banida laifi ciki
FATUU ma tace "Nima dai banida laifi…
UMMAH ckn jin haushinsu tace "to tunda bakuda laifi ciki saiku gaya masa me laifin naga alamar dai so kuke kununa masa karara nice da laifi ack
Mai martaba yadaga mata hannu yace "ya isa bana son daga murya domin zcy ta tafasa takeyi raina abace yake tambaya kawai nayi ba neman jin fitina ba ya akai hakan tafaru agayamin.
MAMAH Tace "Ranka yadade cikin nanfa tun daga turai aka sameshi domin da alamar dashi ta dawo domin YARIMAN ma da suka tafi dashi can tabaroshi baisaniba ta dawo.
Sarki Abdallah ya furgita da jin wannan maganar yace "TURAI!? ya akai har *KUYANGA* taje turai batareda sanina ba meyasa yarima yatafi da ita ba,a gayamin ba tabbas FULANI kece da laifi tunda kinsan da tafiyar tasu kika boyemin kinkuma san halina akan in aka munafurceni a abu
UMMAH tayi kasa da kanta
Yaci gaba da cewa "To shi yariman ne yayi mata cikin ko wa?
Da sauri tadago tana fadin "ba cikin yarima bane baima san ta taho ba Yace min ta dade bata gidansa tun zuwanta kasar idonta yabude take bin maza farkan natane yasata ajirgi ta taho ahalin yanzuma yarima baisan tanada cikiba
Mai Martaba yace "Koma dai menene laifin na yarima ne ko ba cikinsa bane to kune sila sannan Alhakin yana kanku meyasa Da hankalinki xaki hada mace da namiji suje su zauna agida daya ba matar saba bakomai ba Alhalin kinsan halayyar d'anKi munada masaniyar yana bin matan turawan nan acan
Maimartaba yaja ajiyar zuciya yace "Yarima baidauko halin kirki na gidan sarauta ba domin babu me munin halinsa adangina banyi fasikanci ba banyi shaye shaye ba amma gashi Allah yajarabceni da yaron dakeyi Allah nagode maka Allah kashirya minshi
UMMAH tahau zubda hawaye tana fadin "Amma dai kasan akwai mahassada na agun baidace karinga aibunta min Da suna gunba.,
Tsawa yadaka mata "yimin shiru fulani ko ranki yabaci banasan zancen banza wadannan abokan zaman kine ba mahassadan kiba Kuma ki gaggauta kiran yarima awaya kigaya masa maza injini yadawo gida
Tahau gyada kai tana goge hawaye
Yace duk sutashi sutafi
Sun mike kenan zasu futa saiga Jakadiya ta shigo da sauri tadurkusa tace "Anzo da babban batu daga asibitin da aka kwantar da *KUYANGA* Ana bukatar jini ackn gidannan za,a kara mata domin tana cikin wani hali.
UMMAH taharari Jakadiya
Yayinda FAATU taji wani tausayin *KUYANGAR* Yashigeta tace da jakadiya "Maza Ki kiramin Ladimo A bangarensa kisanar masa yafito yaje asibitin adebi nasa.…
Mai martaba najin tafadi hakan yai mata magana "akan wane dalili zaki bashi wannan umarnin Alhalin jiya-jiya yadawo baigama hutawa ba zaki sashi wahala babu nasiyane da baxamu siyaba.?
FAATU tace "Ranka yadade dazu muna hira dashi yagama fadamin an auna jininsa anga Group O" ne yace kuma yana son yaga yabaiwa mai bukata domin yasami lada natabbata kuma inyaji ackn gidannan ne zaije da gaggawa
Mai martaba yagyada kansa yace "To ace masa yabayar din nima na Amince tunda ladan yake nema.
Jakadiya tace "angama zanje yanzu ko ingaya masa.
Duka suka fucedaga Turakar Sarkin
Koda jakadiya tajewa da Lamido wannan magana ta umarnin yaje yabadajini inji mahaifiyarsa bashiri yahau shiryawa zuwa Asibitin
Direbansa na gidan da aka ware masa yanema yace maza yakaishi Asibitin da suke ganin likitansu
Zuwansu keda wuya suka tarar ana Auna jinin MAHBUB
Likitan daya gama awon jinin yadawo yatarar dasu duka azaune yace "jinin MAHBUB baiyiba damar diba shima yana bukata sannan yanada Typhoid
Nan LAMIDO yamike yace da likitan shi aje a debi nasa yanada tabbacin nasa zaiyi tunda group O ' Ne dashi zai iya baiwa kowa jini
Likitan daya Auna yagani yatabbatar saiyace da LAMIDO "jininka yayi saidai ba leda daya take bukata ba adebi biyun ba matsala ko adebi daya su sai dayan?
LAMIDO yace "Debi biyun na amince lada nake nema bawani abuba
Take yakwanta aka debi leda biyu
Saida yahuta agadon sannan yafuta daga asibitin ko *KUYANGAR* bai nemi inda takeba don hankalinsa ba,a gunta yakeba bukatarsa dai ta biya yataimaka mata don baiwaye taba ma.
Koda yakoma gida mahaifiyarsa taringa masa godiya da addu,a gareshi takuma bashi labarin yarinyar da abinda yafaru da ita
LAMIDO yadade yanajin ciwon abin aransa meyasa akaiwa baiwar Allah haka meyasa don anga batada gata aka danne mata hakki?
Dayake shi mutum ne mejinkai da tausan bayi sannan gashi da ilimin Addinin domin acan din dayaje karatu Islamic yakaranta yanada sani sosai
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.