Kuyanga Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: KUYANGA part 1 cmplt-1-1-4-1.txt
Chapter 11 of 23
*KUYANGA* Tazauna tana fadin "wash !barni na huta tukunna zulaihat saiki watson tambayar
Zulaihat ta janyo jakar da Zeenatun tashigo da ita takaya tace "lallai kyan tafiya dawowa ina yariman ko batare kuka dawo ba?
"Idan tare muka dawo zaki ganmu atarene?
Zulaihat Tahau murmushi tana fadin "inafa kawai dai tambayace
*KUYANGA* tace '"to batni nahuta tukunna sannan kibani labari akan MAHBUB dina.
Zulaihat tayi dariya tace "MAHBUB dinki yananan qalau.
"To masha Allahu.
******
Gari na wayewa aka aiko kiran *KUYANGA* labari yakaiwa UMMAH anga Zeenatu ta dawo gdn da daddare
Saida UMMAH ta tabbatar da lallai Zeenatun ce tunda tazo da gaggawa kiran tadurkusa agabanta
UMMAH tace "Meya dawo dake Gida yarima baisaniba?
Gaban *KUYANGA* Yafadi take dabara tazo mata
"Fita nayi don ganin gari shine na bace har wasu suka tsinceni suka tambayeni inda nake nikuma namanta inda zance musu bansan kwatancen mazaunin yarima shiyasa dasukace zasu dawo dani Nigeria ban musa musuba
UMMAH nagama ji tace "kodai yawon iskanci kika tafi Allah yakamaki aka dawo dake gidan?.
Da sauri tahau girgixa kai tana hawaye tabudi baki tace "walh ba haka bane waccen maganar danayi ce gaskiya.
UMMAH Tace ta tashi tabata guri tayiwa kanta rayuwar jin dadi wasu ma nema suke
Tana futa UMMAH takira Yarima tagaya masa komai
Yarima yasha mamakin dahar ta iya dawowa ita kadai yacewa UMMAN yana tunanin akwai wanda yataimaka mata ta gudo zaiyi bincike
UMMAH Tace "nidai kawai kadawo Yarima domin nafi son zamanka akusa da mahaifinka don inyana ganinka akusa dashi zaifi shakuwa dakai sannan Hakan ne zaisa sarauta ta dawo hannunka ta sauki tunda wancen Sahoramin yatafi Sudan karatu bazai dawo yanzuba
Yarima yace "Nima bana jin Zandawo Yanzun UMMAH saikamar nanda wata guda.
Tace "To kayi kokarin kadawo awata gudan kada ka kara fa.
Yace "angama UMMAH Na baxan karaba.
Sukai sallama
Saida Labari yakai kunnan sarki wai *KUYANGA*
Dasuka tafi Turai da Yarima ta gudo itakadai
Mamaki ya ishi sarki domin baisan anyi tafiya da mace ba da bazai bariba balle har ya yarda yabar yarima yatafi da mace
Aranar yasaka UMMAH agaba yace ban kanki in aske
Yaita mata fada harsaida tayi hawaye
Tana fadin "Ayi hkr Takawa ai anrigada anyi kure dahar aka tafi ba.a gaya makanba baza.a karaba
Ita kuwa *KUYANGA* tasake ackn "yan'uwanta Bayi bata nuna wata damuwa ba ko Wani abun
Haka suma basu gano komai ba saima yabon canxawarta dasuke tayi wai tayi kyau fatarta tayi kyau acan
Shiko MAHBUB kallonta yai tayi yana fara,a dajin dadi yana fadin '" kincanza dayawa Zeenah kinyi matuqar kyau fatarki sai sheki takeyi lallai kin huta acan kinbarmu ckn aikin wahal
Inafa Hutu tambayemu kasha labarin komai 😅
tayi fari 🙄 tace kaima ka kara kyau anya kayi kewata kamar yadda nayi taka kuwa?
Yace "sosai kuwa ko nan gurin damuke xama zaishedi hakan dafatan dai soyayyata batayi gibi ba tananan yanda nasanta da yawa?
Gibi kai😉😄 Amma injini ita cewa tayi
"Saima karuwa tayi ai aduk inda nake dana tafi ina tare da sonka da kaunarka
Yace "naji dadi soaai.
Dayake wayar da yarima yabata Boyeta tayi sam bazata bari MAHBUB yagani ba balle yayi mata fassara gara Zulaihat ta nuna mata amma tace kada tafada wa kowa
Zulaihat hartana tsokanart dacewa "Toko dai SAHABIN nan zaki Aurane komai kice SAHABI mudai kada kiyi mana sakiyar daba ruwa
*KUYANGA* tace "Banga abinda zaisa nabar MAHBUB ba kima bar wannan maganar SAHABI abokin shawara ne abokan taka ce atsakaninmu
Dariya kawai Zulaihat tayi tare dajan bakinta tayi gum
*****
Watan *KUYANGA* D'aya da dawowa yanayinta yacanxa domin wani laulayi taringayi ga yawan Zazzabin dare Da ciwon Ciki da bacci da kasala da kwadayi da take yawan yi
Zulaihat itace tajikinta ita tasan matsalarta na rashin lfyr saita samo mata magunguna taita bata na gargajiya tana jikawa tana bata tana sha
Kwana biyu tayi akwance MAHBUB yatada hankalinsa ganin ciwo yaki lafawa Kullum cikin Aikawa da Rubutu yake
Aranar data gama shanye jikon da Zulaihat tayi mata aranar tayita malelekuwa atsakar daki mararta na ciwo kamar ta mutu
Tana ihu tana kiran sunan Allah
Jini ne yaringa xuba ajikinta ta kasanta me yawa
Zulaihat ta tsorata ainun
Da gudu tagayowa manyansu tsoffin Bayin gidan
Da sukazo kanta sukaga ikon Allah abin yafi karfinsu sai suka baxama cikin gidan gun matan Sarki aka gayo musu
Mamah ta tsakiya da Amaryar Sarki Faatu mahaifiyar Lamido sune suka fara zuwa gunta kafin UMMAH Tazo
Likitansu na ckn gidan aka kira macece *DOCTOR HALIMA WASAI*
da kayan aikinta tazo taxaci abin karamine
Saida tazo taganta tace musu ai bari zatayi da alamar cikine da ita maza atafi da ita asibiti don inya bare ayo mata wankin cikin
Hankalin kowa na gidan yatashi ba,a bari sarki yajiba
UMMAH taringa fadin "shegiyar yarinya Me sifar munafukai ashe abinda tayo akasar ta gudo kenan lallai asirinki yatonu Yarima bashida Alhaki shiyasa baima saniba ta munafurceshi.
MAMAH tace "ai irin wannan ba,a aibunta mutum kuma bamu tabbatar ba likitanma zato takeyi dan haka muyi mata fatan Alkairi tunda D'a nakowane
UMMAH ta harari MAMAH dama haushinta takeji ganin ta rungumi FAATU sunhade mata kai
UMMAH ta watsowa MAMAH magana me zafi dan taji haushi tace "TO IN D'A NAKOWANE WANI MA YAYI D'AN MANA NAZACI TUN ZUWANKI GIDANNAN KATON KASHI KAWAI KIKEYI KOKIN TABA YIN BARIN MA?
MAMAH jarumar mace me tawakkali tayi murmushi tace "Bantabayi ba Amma nagodewa Allah yabani Taqwa da Sanin yakamta kuma ina dada gode masa nasn kuma bai manta daniba, na tabbatar kuma inhar yabani agaba inda yawan rai xanfiki iya yiwa yara tarbiyya....FAATU ce taja hannun MAMAH tana fadin "kibar maganar haka kiyi shiru ga mutane fa bayinku agun baikamata ba.
MAMAH da FAATU suka bar gurin
Ita UMMAH Data gwaba me zafi aka mayar mata tafi MAMAHn jin xafin maganar ma
Yawwa ai gara hakan dama inbaki yafadi son rai aibaisan me za,a mayar masa ba.
*Muje zuwa dai Auntyn Sayyadah da Shahidah*
😅😂🤣😀😃😄😆😇😉☺😊
[7/28, 9:09 PM] Ummi Tandama: 📿 *KUYANGA* 📿
*_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*WANNAN PAGE DIN SADAUKARWA CE GA KAWATA TAKAINA REAL UMMEEY ZEEY Marubuciyar "YAMMATA ALKAIRIN ALLAH YAKAI INDA KIKE INA FANS DINA KUNEMI BUK DIN "YAMMATA KADA KUBARI ABAKU LABARI*
*Nabilancy Luv* 💘
(Auntyn S&S)
45-50
ACAN Asibiti Likitoci sunata iya bakin kokarinsu domin Suga jinin dake zuba daga jikinta yatsaya don tafuta ahayyacinta
Saida Allah yataimaka jinin yatsaya kana sukai mata allurar bacci sannan aka nemi "yan uwanta domin suzo adebi jininsu akara mata
Likitocin kansu sunyi zaton cikin dake jikinta yazube to ajiyar Allah baifita ba sai wuya datasha
Iya Yabi wata tsohuwa cikin wadanda suka kawota tace musu su taimaka su karasa fitar da cikin ba Aurene da itaba Abin kunya taja musu
Dr Halima tace mata
"Gaskiya bama zubda ciki domin inmunyi hakan tamkar munyiwa ubangiji shishshigine domin bamusan nufinsa dayasa tasamu cikin ba alokacin da bai dace tasamu ba
Iya tace "Amma dai da kuntaimaka sbd idan labarin yaje kunnan sarki baxataji ta dadiba dan korarta ma zaiyi agidan kuma gashi bamusan cikin wayeba gata marainiya
Dr halima tace "koma dai meye ne iya saidai kuyi hkr mufa bama Abotion a asibitinnan sannan kusani wannan ciki bame futa bane inhar kuma kukayi kokarin yi masa dole to tabbas zaku iya rasa ranta awajen zubarwa
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.