Complete Hausa Novels

Kuyanga Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: KUYANGA part 1 cmplt-1-1-4-1.txt

Chapter 17 of 23

FAATU DA MAMAH sunyi mamakin wannan Abu sunkuma Daukeshi arainin hankali yariman yazo dashi sunsan kuma TAKAWA bazai daukaba

Yo muma ba dauka zamuyi ba 😡

Muje zuwa
[8/3, 11:13 AM] Ummi Tandama: 📿 *KUYANGA* 📿

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION_*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*Nabilancy Luv* 💘
(Auntyn S&S)

*wannan shafin Sadaukarwace ga Binta kabir Auntyn Yasmin Mrs ibrahim R/k quarters* 👍🏼👍🏼 Kawata inayinki Ina godiya da tayani posting a grps

70-75

JAKADIYA tana isa cikin Dajin tayita shiga cikin Ko tsoro babu atare da ita haka har tazo gindin wani tsauni ta haye daf !daf!!daf!!! Ta nufi wata babbar bishiyar Kuka dake kan katon Dutsen

Tana isa ga bishiyar saita cire takalmanta ta tsaya gaban bishiyar tana fadin "Gafaranku dai manya da kanana na fadar GOGAL ga jaririya tazo tazo Neman taimako da cin Albarkaci ayi min iso gurin Hakima mandiya shugabar matsafa

Wani kuka taji yana tashi na muryoyin yara daga ckn bishiyar taitaji harna tsahon minti talatin can kuma taji shiru sai kuma ga amsa kuwwar Babbar murya tana fadin

" SANNUNKI DA ZUWA HATSABIBIYAR JAKADIYA GAMANDI ME HADA WANDA TASO

Jakadiya ta hadiyi yawu domin kirarin nan bai mataba tasaba yi matashi

,"Barkanki da isowa GOGAL

Cewar Jakadiya

GOGAL da ba,a ganinta saijin muryarta ta jikin bishiyar tace da jakadiya

"NAji zuwanki angayamin tunkina afarkon daji nasan meke tafe Uwar Dakinki ta aikoki akan Acirewa D'anta son da yakewa *KUYANGA* Daga zuciyar sa ko?

Jakadiya tace " E kwarai hakan yake.

Jakadiya taci gaba da cewa "Hakan data tsara nikuma incanza salon abun yazamo amaimakon ancire masa son yarinyar saidai ma akara masa don ya axabtu sosai

Yakasa sakat yashiga damuwa akanta sakamakon yanda yasaka yarinyar adamuwa

Wata bunsurar dariya aka sheke da ita dg jikin bishiyar kukar

Daga can kuma akace da jakadiya " ko baki fadaba hakan za,ayi domin Baxan iya cire wannan soyayyar dake ransaba na duba naga ajiyar Allah ce ban isa in girgizata ba Dan haka zankara da Dora aikinki da kika bukata domin nima ayaune zanrama abinda YARIMA yataba yiwa Jikana yafita rangadi suka hadu ahanya YARIMA yabuge minshi da doki yafadi ko kulaminshi YARIMA baiyiba harya suma agun

Jakadiya tahau gyada kanta

Tana mamakin jin wannan labari na GOGAL duk da tasan zai aikata din

Jakadiya tahau godiya tareda ajiye kudin da uwar dakinta tabata agindin bishiyar ta mike da niyyar tafiya

Sai taji ana mata magana da muryar tsohuwa ta jikin bishiyar

"Kema kibi lamuranki na gidan nan a sannu domin a irin zaqewar da kikeyi wataran zaki girbi kashinki ahannu domin akwai abinda zaki aikata zaija miki babban aiki da kuma danasani HAHAHAHA

Aka rufe da katuwar dariya

Jakadiya na kyarma tace " Ataimaka agayamin ko mene wannan Abu da zaijamin danasani don inkiyaye

Dariyar dai akaci gaba dayi mata babu wani Karin bayani

Tana kallo kudin data ajiye yabace sundauke

Difff! Taji anmata tasan bakuma xasu karace mata kanxil ba shiyasa ta tafi da baya kamar yadda ta saba

*******

Yarima Yana kwance akan makeken Gadonsa yanata juyi yakasa controlling din kansa akan soyayyar *KUYANGA* Da take azabtar dashi arai

Hotonta ke masa gixo alokacin dayake kanta a time din suna Turai

Tabbas Yanda takeda tarin baiwa bazai iya barin taba saiyayi yanda yayi ya mallaketa baxai taba barin LAMIDO ya Aure taba

Can kuma saiya mike da sauri ayau saiya ganta kota halin kakane koda zai karya billensa yashiga ckn gidan bayin bazaiji wani Abu aransaba Sontane yaja

Yazira kaya ajikinsa dama dagashi sai gajeran wando da singilet

Yafito farfajiyar gidan yatsaya yana karewa kowa dake wucewa kallo duk Wanda zai wuce ta kusa dashi saiya kawo masa gaisuwa

Da ka kawai yake amsawa

Sarkin gida ya hango agurin ajiyar dokuna yana baiwa wani farin doki da LAMIDO kefuta dashi abinci

Matsawa yayi kusa da Sarkin gidan tareda kwalla masa kira

Da sauri yabar abinda yakeyi yataho gurin Yariman

Ya mika gaisuwa tareda tsayawa ckn ladabi agefen yarima yanajiran abinda zaice masa

Yarima yace "Sarkin gida Inaso kaje ka kiramin *KUYANGA* Zeenatu

Sarkin gida yace " Tana tareda MAHBUB acan bayan Gamji da suka saba zama

Yarima yadaka masa tsawa yace "To intana tareda wani bazatazo ba ko Yaya?shi wanin yafinine ?mijin tane ko waye dinta?

Sarkin gida yahau fadin " kayi hkr ba nufina kenan ba sanar maka nayi dai bata gida agarceni bari aje can akirata

Yatafi da sauri inda yasan zaisametan

Yarima yahau cizar yatsa jin wai tana can tareda MAHBUB tabbas dole yadau mataki akan wannan Bawan dazai kawo masa tsaiko

Yananan har lokacin da Sarkin gida yadawo tareda ita tana biye dashi sanye take da zurmemen hijab harkasa

Yaringa kare mata kallo na yanda take tafiya anutse kanta akasa

Gabantane yake faduwa domin batasan dame yazo mataba

Tana ZUWA gareshi tagaidashi tareda tsayawa gefe kanta akasa

Yana murmushi yace

"Zeenatu dago kai kikalleni gani agabanki da kokon barata

Nazo Neman yafiyar kine
Akan laifin dana aikata miki nayi nadama nakuma karbi cikin jikinki domin tabbas D'ana ne ko "yata zaki Haifa jininane inason abuna ki kwantar da hankalinki kisaki kowa ki kamani domin rufuwar asirinki

Ta dago da sauri takalleshi ido cikin ido ayau Allah yadauke mata shakkarsa tace masa " Ai asirina yagama rufuwa atun lokacin daka budeshi Allah yanufi Dan uwanka da rufeshi kuma abinda yaimin bazan taba mantawa dashiba bakuma zankishiba na aminta shi zan Aura....dasauri yakatseta

"Kina nufin kice Kinason LAMIDO?

Ta girgiza kanta
" zan Auri LAMIDO sbd halaccinsa agareni da muhimmancinsa aguna da gun abinda zan Haifa sannan bazan bijireba INA ganin kima da daraja ta me martaba amma SO d'aya tak! MAHBUB nabaiwa shi

Kamar ta watsa masa wuta amakoshi yaji jinta Ambaci MAHBUB take so

Tabbas Zeenatu tacanxa yaushe tayi baki haka yaushe tasan tagaya masa magana tsararo babu taunawa tabbas babu musu MAHBUB ne zai kintsa mata komai akansa tunda suna tare yasan gunsa ta taho kuma saiyayi maganinsa

Yadubeta duba na tsanaki yace "Nayi alqawarin saina raba zuciyarki da soyayyar bawa Mara amfani

Tace " agunkane baida amfani amma aguna yana da amfani

Tana gama fadin haka tajuya tatafi abinta

Ayanxu ji take komai zata iya gaya masa tunda yazubda mutuncinsa agunta

Yadade tsaye yana kallonta harta qule zancenta na masa yawo azuci kamar tadaba masa wuqa haka yaji tabbas ayau ba sai gobe zaiyi maganin MAHBUB shine sila nakomai datayi masa ayau

Kafin yabar gurin saida ya yanke shawarar abinda zaiyiwa MAHBUB

wasu fadawa Yasamu guda biyu dasuke girmamashi ya yafito su suka taho da sauri suna zuwa yace musu

"Wani aiki zanbaku me tattare da hatsari amma zaku samu abin alheri me tsoka

Sukai farat sukace " indai zamu samu matsayi agunka da kuma abin duniya kowane irine zamuyi

Yarima yaji dadi yagyara tsaiwa yace "nasan zaku iya daganinku anga jarumai Wani bawa nakeso kukashe adaren yau...

Yayi shiru yana so yaga wane action zasuyi ko zasu firgita saiyaga sabanin hakan ko gezau basuyiba da alamun zasu iya abinda yafi hakanma dama da ganinsu tantiraine

Yaci gaba dafadin " dazarar kunkasheshi zanbaku gida ackn gari zanbaku kudi har naira Miliyan daya duk kuraba amma kuxama masu sirri so nake dasafe atashi da kukan mutuwarsa

Sukace atare "angama ranka yadade.

Yace " kutafi kujira zuwa dare da zaku aikata hakan saikunyi natabbatar zanbaku abinda na alqawarta muku

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.