Complete Hausa Novels

Kuyanga Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: KUYANGA part 1 cmplt-1-1-4-1.txt

Chapter 23 of 23

" Allah nagode maka.cewar *KUYANGA*

Zulaihat tace "Ga magunguna can inji Iya Sha,awa tace kada kiyi sake da kowanne masu kyaune akwai nasha da nono dakuma nasha da Zuma anjima zata kawo miki na tsugunno

*KUYANGA* takama baki " oh maganin mata kuma tun yanzun?

Zulaihat tace "Eh aishine daidai hakan kinga abin xaifi kamaki Sosai

" Hhhmmm Allah dai yasa ba daci

Zulaita tace "koma me gareshi haka zakisha tunda kinsan Halin tsoffin nan insuka bada Abu ba,ashaba fada zasuyi suce suna mana gata muna gocewa

*KUYANGA* Tayi murmushi tadauki magungunan tafara hada wa xatasha

******
Yarima yadauki wayarsa yalalubo nambar abokinsa SAHABI da suka Dade basuyi wayaba

Acan bangaren SAHABI yana ganin kiran Yariman yayi murmushi yadaga yana fadin" Dama kana da nambata kamance dani

Yarima yace "inada ita mana fushi nayi dakai na abinda kayimin amma yanzu na huce Dan haka Ina gayyatarka Aurena karshen wata

SAHABI yayi murmushi yace " Allah yasanya Alkairi nima Auren zanyi nanda sati mezuwa kafin nakama

Yarima yace "Shegen kaya wato banda nakira bazanjiba kenan ?lallai na yarda karikeni aranka SAHABI

SAHABI yace " ba haka bane yarima Aurenne ba Wanda nakeso ba Hadani akai da yarinyar diyar kanin mahaifina ce ita ke sona

Dariya yarima yabushe masa yace "sunmin daidai walh domin insun kyaleka " yar talakawa zaka dauko musu banza me sakaran ra,ayi

Sahabi yace "kai " yar INA zaka aura?

Yarima yabashi labarin Hindu da yanda suka hadu a Airport a England

SAHABI yace "Hhhmmm to bagiringirin ba dai tayi mai

Yarima yace " oho dai nafika tunda ni Auran Soyayya zamuyi

"Nima bawai kinta nakeba tunda yar 'uwa tace

Ina Zeenatu naji ance abinda ta Haifa yarasu

Yarima yace " Eh, Sunkusa Aure da LAMIDO...

SAHABI yakatseshi da sauri "ya akai hakan dama soyayya sukeyi?

Nan yarima yazayyane masa komai

SAHABI yace " Gud ammafa naji dadi LAMIDO yaburgeni Allah yasanya Alheri

Yarima baikulaba yai masa sallama

Acan kasan ransa soyayyar Zeenatu na nan baxai mantawa

******
Anata shirye shiryen biki akowane bangaren

Shi yarima agidansa na cikin gari zai zauna baiyda ra,ayin zama acikin gidansu wai kada atakura masa shida amaryarsa

Shiko LAMIDO sashi guda aka gyara masa agidan me dauke da dakuna agidan gidan yasha gyara babbane dama ba kowa ciki

Aka zuba komai na alfarma agidan

Lefe yazo daga Dubai akwatuna goma Sha biyu cike fal da kaya tsadaddu

Komai dozinne ciki koina acikin gidan da wajen gidan zancen kayan lefensa akeyi domin sunhadu sunburge kowa

Saida aka kaiwa takawa yagani yace sunyi yasa albarka kana mata suka hadu suka dauka bayan Su MAMAH DA FAATU sun gani aka kaiwa KUYANGA

Tsoffinsu sunsaka albarka sunyaba Angyagije Zeenatu anfiddata kunya dukda sunsan arina

Shiko Yarima karya yahada ackn kayan duk don ace nashi sunfi na LAMIDO

Harda key din mota yasaka akan lefen mahaifiyarsa ta saka takardun gida duk akan lefen gudummawarta duk don mutane suga na LAMIDO lami ne sannan su burge mutan Kaduna

Amarya anata rawar kai anatashan magungunan karin Ni,IMA da tsukewa sbd gurin anshigeshi

Tun fara karatunta a Abroad tayi soyayya da wani Anwar yamaisheta tamkar mata ta amince masa daga baya ya yaudareta yana gama karatu yakoma kasarsu yamance da ita

Shiyasa data hadu da yarima takasa ta tsare saida taga natsaida lokacin Aure sannan hankalinta yakwanta

Duk kashe kudin da akai alefenta baisa sunyi rawar jiki ko an yababa tunda su ba farin shigar komai bane ita kanta motocinta biyu na hawa tanada gidaje kuma

Aiko dai yan kawo kaya suka koma jiki asanyaye danma anbasu tukuici me tsoka

Rana bata karya saidai uwar diya taji kunya

Allah yakawomu wannan rana

Ranar Asabar takama ranar daurin Auren da nadin sarautar

Ancika agdn sarki anata kade kade da bushe Bushe da algaita LAMIDO yasha kwalliyar sarakai

Yayinda yarima yai tashi ta angwaye daidai misali ba yabo ba fallasa yasha tsadaddiyar shadda babbar Riga d yar ciki

Saida akayi nadi LAMIDO yazama sarki sannan aka daura auransa da KUYANGA kana akayi shagulgula sannan wasu suka dunguma da angoma Yarima suka tafi daurin Aurensa Kaduna

Andauro Aure antaho da Amarya a ranar domin sai dare suka iso aka ajiyeta a gidansa dake GRA

Itako KUYANGA data tashi daga wannan suna daga yau ta tare ackn gidan sarkin A gidan mijinta LAMIDO daya zamo sarki ayau

To fans saimu Tara a page din gaba *GIMBIYA ZEENATU* Cigaban KUYANGA

Wanda zakuji badaqala da cakwakiya ackn Wanda nake muku zaton yafi wannan Dan haka kada kubari abaku labari

Taku har kullum Auntyn Sayyada da Shahida

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.