Kuyanga Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: KUYANGA part 1 cmplt-1-1-4-1.txt
Chapter 21 of 23
Yace " ZEENATU ya hakuri kuma?
Ckn sanyin muryarta tace "Da Godiya
Yace " Allah yajikansa yabaki hakurin rashinsa
Ahankali tace "Amin nagode"
Yaso yafurta mata wata kalma saikuma yafasa
Yaimata sallama yatafi
Yauma binshi tayi da kallo
Yanda yake takunsa na kasaita da iya tafiya ta sarakai abin birgewane kokusa Yarima baikamoshi akomai ba Tabbas LAMIDO na daban ne
Ayau tayiwa Allah godiya dayasa zata zamo mallakinsa donta farajin wani Abu akansa
Abin mamaki ma da dare kasa bacci tayi tayita juyi akatifa tana tuno irin yanda yake maganarsa da tsari da tausasawa ga iya kallo kodon idanunsa Sexy eyes ne gashi da kyau da tausayi
Tabbas Samun Namiji irin LAMIDO sai antona
Tooo🙄😳fans *KUYANGA* me kuka fuskanta ne a Heart din KUYANGA
To kodai ta kamu ne ???
Muje zuwa
[8/8, 8:11 PM] Ummi Tandama: 📿 *KUYANGA...* 📿
*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION_*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*Nabilancy Luv* 💘
(Auntyn S&S)
90-95
FAATU ce A zaune aturakar mai martaba bayan yagama cin abinci yadubeta yace "Kince kinada magana inajinki meke tafe dake akwai damuwane?
Ta gyara zama tace "Dama maganar LAMIDO ne Naga tunda har anyi sadakar arbain din jaririn Zeenatu nace to me zai hana atsaida ranar Auransu da LAMIDON ba tunda har ya amince kuma naga kamar yafara sonta
Murmushi Sarki yayi yace "To babu komai sai a tsaida Wata daya mai zuwa sai adaura Auran nasu bamusan me Allah ya ajiyeba kuma Inaso aranar da za,a daura Auran ayi bikin dorashi Kan karagar mulki natsufa yakamata nayi murabus nadorashi akai duk abinda nakeyi wanda yakamata yake kaina zai iya sannan ya cancanta don haka zansa ayi shela agari kowa yasanda wannan rana
FAATU tace "To amma Takawa kana ganin wannan abun dakayi bazai kawo rabuwar kai atsakaninsa da Dan,uwansa yarima ba mahaifiyar safa ta kudurci dantane zai zama sarki natabbata zataji ba dadi koma tayi bore
Sarki yace "Nike da iko da komai daga kan mutan gari da bayi da ku kanku iyalaina da dukuma Sarautar kanta Dan haka babu me canzamin zabin da nayiwa Garina
Ckn biyayya FAATU tace " angama ranka ya Dade Allah yaja kwana yakara lfy
Yace "Amin Fatima. Inkin futa kituromin LAMIDO
tace "To.
Bayan futarta tazarce Dakin MAMAH domin takai mata wannan batu sbd duk abinda take ciki saita sanarta kuma bata zartar da komai saida izininta
Jakadiya na zaune kusa da MAMAH tana mata hira
Shigowar FAATU yasa ta tsahirta tareda gaisata
FAATU ta amsa tareda zama kusada MAMAH
Ta zayyanewa MAMAH komai na abinda Mai martaba yatsara na bikin LAMIDO da *KUYANGA* Da kuma bikin nada LAMIDO Sarki da za,ayi
Jakadiya na qunsa tafuce da rawar jiki ta nufi dakin UMMAH Donkai mata Rahoto
UMMAH taga shigowar Jakadiya hankali atashe
Ranta yai matuqar baci dajin wannan kalami daga bakin Jakadiya kamar ta Dora hannu aka tayi kuka taji
Inama tana da damar da zata hana wannan Nadi
Jakadiya tace "Kibar komai ahannuna domin nima bazanso adora Lamido INA gani ba zanso ace Yarima ne zaizama sarkinmu
UMMAH ta gyada kanta tana fadin "Nagode jakadiya nasan ke me qaunata CE
Jakadiya taxo futa adakin kenan sukai kicibus da Yarima shima yashigo dakin UMMAH
Kallon kallo sukaiwa juna ko gaidashi Jakadiya ba tayiba kowa aransa akwai abinda yake ayyanawa akansu
Yaxauna akan kushin yana fadin "UMMAH naxo gaya mikine zantafi turai nan da kwana biyu nagaji da zama agarinnan babu masu sona
Tace "Kamar yaya babu masu sonka baya gamu nida mahaifinka
Yace "Hhhmmm adane kike sona amma ayanzu kam dagake har TAKAWA babu me kaunata kinrabani da gudan jinina kinkuma ki sanyawa Takawa ya yafemin yafaina fushi dani
Tace "YARIMA kai kake janyo komai gashi yanzuma zaka tafi kuma kasan bason tafiyarka yakeyiba Danhaka tafiyarka daidai take da karin wani laifin kanka sannan kuma abinda nayi daidaine agunmu nidakai domin inhar Yaron ya girma xai iya tasowa ackn wani yanaya na mugayen halayya ko kuma muzama abin kwatance
Inaso kacireshi aranka kafuskanci abinda ke shirin Kasantomu na Nadin Sarauta da mai martaba zaiyi akan kaninka LAMIDO
Yarima ya gyara zama da firgici akan fuskarsa yace "Da gaske UMMAH yanzu haka Takawa zaimini SBD yabakanta min rai. Tabbas saina dauki mataki sosai akai
Waye ya kawo miki wannan labarin?
Tace "JAKADIYA CE
yace "shikenan.
Yafuta yanufi Dakinsa yadebo kudi masu yawa aljihunsa yafito yanufi sashin da Jakadiya take
Cikin ikon Allah Yatararta Ita kadai kuwa
Tanaganinsa gabanta yafadi ganin irin kallon da yayi mata dazu tana ganin ko akwai manufarsa ta hakan
Yakalleta ba fara,a afuskarsa ya mika mata kudi ahannunsa yace "Karbi wannan !
Jiki na tsuma ta karba
Tace "na menene wannan?
Yace "Nakine aiki zansaki
Tace '"aikin meye hakan? Wannan uban kudi yafi karfina
Yace "Yanda kika zama makisiya shine nakeso ki kashemin wani nima
Ta zabura "Baxan iya ba walh
Yadaka mata tsawa "zaki iya !! Waishinma kinji kowaye?
Tace "waxan kashe?
Kaitsaye yace mata "LAMIDO!!
taji dirar Kalmar akunnenta tadira gefe tana miko masa kudin "karbi kudinka bazan iya kashe LAMIDO ba ka kaiwa wadanda sukai maka aiki akan MAHBUB suyi walh bazan iyaba
Yadaka mata harara yace "babu Wanda zansa yayi saike don haka kisani k'in yinki yana daidai da tonuwar asirinki
Yana gama fadin haka yajuya yabar ta tsaye atsorace take da wannan lamari ina ita ina iya kashe LAMIDO to yanzu yazatayi gashi tana bukatar kudin sbd yawansu yakai ace tagina kanta da rayuwarta na wasu shekaru toshin yanzu Yaya zatayi ? Rana zafi inuwa Quna!!
Mafita ce tazo mata arai gara taraba kudin biyu taje tasami Fadawan da taga yasa su kashe MAHBUB tabasu sutayata aikin
******
Abin Duniya yadami Yarima gashi da gasken Gaske Mai martaba yajuya masa baya ko gaisuwarsa baya amsa masa don hakan ma ya qudiri niyyar kawar da LAMIDO domin yazamo dolen sarki yanad'ashi agaba yakuma Auri *KUYANGA*
Shawara ya yanke natafiya Turai tun agobe domin in aka kashe LAMIDO kada adora zargi akansa gara ayi bayanan
Da safiyar Lahadi ya daga ko sallama da Mahaifinsa baije yayiba yabarwa UMMAH sallahun tagaya masa
Itako dama ranta baiso ba
Da kuwa taje ga sarki tagaya masa ko uffan baice mataba shiru yayi mata dole tabar maganar yariman ta tafi
Amma ta qudurci yin aikin Asiri atsakaninsu domin janyo soyayyar yariman azuciyar sarkin
Yarima Yana dira akasar waje Allah yahadashi da wata bakar fata Ta nuna tana muradinsa azahiri bama tasan shidin Dan sarki bane saida taga alamomi a Dan zaman da sukayi na mintina a Airport
Hindu "Yar Minister ce a jahar Kaduna mahaifinta me kudine sananne Alh Khalid Baffanyo
"Yar boko ce gata da jijji da kai da dagawa Amma yau sai Allah ya damketa duk yanda take wulakanta samari a garinsu sai gashi ayau Allah yasa mata Soyayyar Saurayin da batasan asalin saba tashi guda
Dayake yariman ma na mamajo ne tuni ya afka cikin sonta shima taringa kanainaya da kissa don yasota takuma yi sa,a
Har rakiyarta yanema gidansa takuma bishi
Saidataje gidansa ta tabbatar shidin Dan babban gidane ta gane dawa take tare Domin tafahimci da alamar Dan gatane kamar yadda take yar gatan babanta
Saida suka kadaita sannan yahau tambayarta meya kawota England ?
Tace masa tazo Hutu ne gun kawunta Wanda shiya riketa alokacin datayi karatunta acan
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.