Kuyanga Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: KUYANGA part 1 cmplt-1-1-4-1.txt
Chapter 19 of 23
Amma dai wannan jakadiya duk randa aka karya miki kafar dama baxamuzo cetoba kuma ko jaje bamuzuwa🙄😆
Muje zuwa
[8/5, 11:13 AM] Ummi Tandama: 📿 *KUYANGA...* 📿
*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION_*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*Nabilancy Luv* 💘
(Auntyn S&S)
80-85
YAU jakadiya bata samu damar yin tsegumin ba tana shiga sashen nasu ta tararsu Da Baki ga LAMIDO yana nan
Dole tayi kwana takoma da baya
*KUYANGA* Tasa jaririn agaba tana kallo Abu biyu takeji akansa na farko Tsanarsa adalilin Haushin Ubansa da ta hanyar da akasameshi tunda takasa manta yanda YARIMA yaringa mata karfa karfa akan saiya Santa a "Ya mace Ashe duk rabone Ke kira tabbas Banda ba,a Tara Sani ga Allah da tanada masaniyar samun ciki dashi da saita bujire masa bazatayi masa biyayya ba koda zai kasheta ko yaumata korar kare
Awani bangaren kuma tanajin Tausayin Yaron ta irin hanyar da yazo
Yanzu da ace ta hanyar sunna yazo da tuni gidan yacika da yan zaryar yiwa mutan gidan barka na xuwan jikan fari garesu
Wani makokon bakin cikine yatsaye mata ganin Yaron yana kama da yarima futuk yanda tatsani yarima bataso zata ringa kallon photography dinsa akusa da itaba
Kafin rasuwar MAHBUB ta tsara idan ta haihu in namiji ta haifa tasakawa Yaron SAHABI ta dalilin taimakon da yayi mata arayuwa takasa mantawa dashi akullum saita tunoshi inama zata Ganshi
Amma yanzu data haihu babu MAHBUB aduniya saita canza tunani inhar za,a bata dama sunansa zatasaka
Tasan dakyar in yarima zaiyarda tunda tasan ba kaunar sa yakeba
Da SAHABIN nema ya iya bari tunda Abokin sane
Ta goge wasu hawaye masu zafi akuncinta Adaidai lokacin da Zulaihat tashigo dakinta da Leda ahannunta
Zulaihat tazauna kusa da ita kan katifar tareda ajiye ledar tana fadin
"Kintisa yaro agaba sai kallo kike ko kunya bakyaji na D'an fari
Yanzu idansu iya Sha,awa sukashigo suka ganki kina masa qurillar nan aikin kade da magana bayama inna Dije taji labari uwar karadi da gyani bakyalewa cewa zasuyi Ma kinata masa wasa
*KUYANGA* Tayi gajeran murmushi tace " hhmmm Zulaihat walh banajin kaunar Yaron nan araina ko kusa dakinsan tsanar Dana masa da bazakice komai akai ba adole nake bashi NoNo nasan inban bashiba baida abinda xaisha kuma hakkin ne akaina kuma madara ba dauwwama zatayi gunsaba ba za tayi masa amfani kamar nononba sannan Za,a tuhumeni ackn gidan nan
Zulaihat tace "hhhuuimm Zeenatu kenan kifa godewa Allah ma da kaddararki tazo da sauki gashi Allah yasa kinyi arxikin da yaro yasami gata ackn gidan kowafa sonsa yakeyi
Nifa ji nakeyi inama niceke inama nice na haihun nan...
" amma dai Zulaihat kina da son duniya shiyasa kike wannan tunanin meye abin so ga haihuwa irin wannan nifa bana kwadayin sarauta ballantana arxiki kenifa da ayanzu LAMIDO zaidawo yace yafasa Aurena ko ajikina tunda dama bansaka akaba
Kuma da kike cewa yaron nan Dan gatana ta INA yazama Dan gatana tunda har yanzu Wanda yake amatsayin mahaifinsa baileko shiba balle mahaifiyarsa da bata kaunar Yaron
Zulaihat tace "barfadin haka kadama suzo din aikowa dai yasan nasune kuma ko tasoshi ko kada tasoshi yarodai jinintane kowa yashaida tunda d'anta yadawo yafadi gaskiya anji
Sannan inbasu so shiba dubunsu agidan sunsoshi koina fa kikayi zancen kyan yaron nan akeyi da kamarsa da ubansa ni tunani ma ko kunyace ta hanashi zuwa suda uwar
HhhhmM " kawai *KUYANGA* Tace tana fadin "me kika kawo aledar ne ?
" magungunan da akasiyo mk ne gashinan hardana Karin jini aciki
Tahau budewa tana nunnuna mata
*********
Da daddare bayan Sallar ishsha 'i saiga sakon kiran *KUYANGA* daga fada sarki ya aika mata
Zulaihat ce "yar Rakiya tadauki jaririn ta goya abayanta
Koda sukaje bayan sungaida mai martaba yace mata " kiyi hakuri Zeenatu natasoki da dare ga jego
Kanta akasa tana murmusawa tace
"Bakomai "
Yaci gaba "To dalilin kiran dama akan sunan da za,a sakawa Yaron ne daga bakinki nakeso ba daga bakin yarima ba domin bai isa komai ba aguna kenafiso kixaba domin ranar suna arada masa
Sai taji inama ta hanyar sunna aka samoshi da kawai cewa xatayi SUNANKA ME MARTABA
To amma yata iya daidai ruwa daidai tsaki takada baki tace " sunan margayi MAHBUB nakeso asaka masa Ranka yadade
Ya gyada kai yagamsu yaga kuma kyautawar ta duk da baisan tsakanin suba amma dai yasan Dan UWA yake gareta kamar yadda yake matsayin bawa haka take itama
Sarki yace "to jeki abinki za,a saka masa akwai wani Abu da kike bukatane?
Ta girgiza kai tace " Babu.
Yabasu umarnin tafiya tunda babu
Suka mike suka futa ko Dan. Bai Tambaya ba (amma bawai Dan baya son saba shikansa yanajin ba dadi inya tuna yanada jikan da aka haifa ba Aure ack)
Bayan kwana biyu ana gobe Za,a rada masa sunan saiga kaya daga UMMAH akwati guda kayan jarirai manya masu tsada ga kudi ackin akwatin dubu hamsin (Dan ma mekawowar jakadiya ta dauke hamsin din kai yarima me yasako dama)
Iya Sha,awa da inna Dije da sauran tsaoffin gidan nasu *KUYANGA* Sukaita murna ana guda
Jakadiya ta dauki Dan tana yabashi azahiri azuci kuwa kiyasta yanda zata kasheshi takeyi
Tun daganan jakadiya take kawo musu kafa sashen nasu duk don su saki jiki da ita tana nuna soyyyarta ga jaririn
Aranar ma agunsu ta wuni harda tayasu yiwa yaro wanka
Da dare ana gobe suna saiga Yarima yazo shima ganin yaro domin yanada labarin yanda aketa fadin kyansa da kamar da sukayi shiyasa yazo dai yaganewa idonsa yakuma gaya mata sunan dayakeso yasakawa Yaron
😏😇ka makaro
Ajikin katangar dakin *KUYANGA* yaja yatsaya ta farfajiyar tsakar gidan bai shigaba
Ta aika aka kai masa farar kujera ta roba
Ta aika masa da Yaron duk Zulaihat CE yar Aiken
Yakurawa Yaron idon akwai hasken tsakar gida nafitilu
Yaji kaunar yaron tashigeshi tabbas ko bai Aure taba zai karbi kayansa inyayi Aure yarike kayansa
Tafito gurinsa tana taku ahankali
Ya amsa sallamar da tayi
Bayan tagaidashi tanemi ta juya takoma
Yace mata "Dakata tukunna daga zuwa saiki tafi banga kyakykyawar fuskar kiba sannan banyi miki godiyar Haifar me kama dani da kikai ba
Tayi masa banza
Yace " Zeenatu INA matuqar sonki nasan kingane hakan walh nakasa sakat araina INA so tunda kin haihu lfy inkinyi arba,in Adaura mana Aure...
Tadago da sauri takalleshi "anya yarima ba kwaya yashaba kuwa tunda tasan yana korawa
To ita kuwa me zatayi dashi ga LAMIDO mutumin Kirki Allah yai mata tsari aiko babu LAMIDO bazata Aureshiba
Yakatseta da cewa " kin amince ?
Ta girgiza kai tace "LAMIDO shine mijin da zan Aura ayanzu haka ina ganin Allah ne yadubi abinda kayimin shiyasa yabani shi amatsayin miji dan hakama kacire batun wai zamuyi Aure dakai
Yace mata " kina nufin bakya sona?
Tace "babu sonka araina kam! Waima kamanta wata rana daka so kwanciya dani naki kacimin zarafi kace mezakayi dani bawai sona kakeba me zakayi da BAIWA maqasqanciya...
Yadaga mata hannu don borin kunya yace " ya isa bance kiyimin tuniba yadade da wucewa yanzu dai gonb suna na zabi insaka masa SAFWAN
Tayi murmushi tace "to saikaje kasanar dame martaba yacanza Wanda zaisaka
Yace " me kike nufi? Yaxabi wanine bansaniba?
Tace "tun jiyama yakirani fada yabukaci zabina akai nagaya masa MAHBUB nakeso asaka
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.