Complete Hausa Novels

Beyond The Veil Part 1 Novel Complete Hausa Novel

Reading file: Beyond The Veil Part 1 Complete Novel.docx

Chapter 77 of 79

Episode 79: Whispers of power, and Hidden Games

Ɗaga kanta tayi jin an buɗe ƙofar office ɗin da sauri

Turus!!! Sadeeq ne tsaye a ƙofar, yana kallonta da mugun mamaki

a kan kujerar Mr. Alhassan? wanda tana zaune comfortable abinta

Idanunsa cike da astonishment, ya shigo cikin office É—in, sai kuma ta É—auke kanta cikin rashin shiri fuskarsa kaÉ—ai ya isheta da tsoro

Ta fiye yake yi zai ɗauki abu, da sauri ta miƙe tsaye

"Get out!" ta faɗa da ƙarfi

Ya tsaya yana kallonta, sai kuma yayi murmushi irin murmushin muguntan nan

Direction É—in da ya nufa ne kawai sai ya fasa ya nufe ta, da sauri ta ce

"Nace get out!" ta kara maimaitawa.

Ta kalli gefenta, ta danna security alert button

Yana kallonta, har yanzu da mamaki a fuskansa sai ya ce cikin husky voice É—insa

"Really? Well, who are you? And what gave you the audacity to sit on that seat?"

Cikin some seconds, securities uku suka buɗe ƙofar suka shigo

Azrah ta ce da su

"Ku fitar min da shi daga office É—in nan!"

Sadeeq ya gyara tsayuwarsa yayi folding hannayensa yana kallon ta da mugun mamaki

Suka tsaya suna kallon juna, É—aya daga cikinsu ya ce a hankali

"But Miss Azrah, it's MD Sadeeq"

"And so?!" ta ce da ƙarfi

"Nace ku fitar min da shi! Ko baku ji nane?"

Ƙofar aka buɗe

Mr. Alhassan ya shigo

Duk suka juya suna kallonsa, shima su yake kallo ya ce

"What is it?" Azrah ta tsaya ta faÉ—a masa abin da ya faru

Sai ya kalli securities É—in, sannan ya kalli MD Sadeeq

Har yanzu Sadeeq bai iya magana ba, yana kallon ikon Allah ne kawai, dan wannan ya wuce tunaninsa

Mr. Alhassan calmly ya ce

"Meyasa zata saka ku aiki kuma ku ƙi yi? Ku aiwatar da abinda ta ce!"

Sadeeq ya tsaya yana kallon Babansa, Securities dinma sun kasa zuwa kusa da shi

Da suka fara zuwa toward him kawai ya É—aga musu hannu sama, sai kuma ya fice cikin fushi kamar zai tashi sama

Securities É—in suka bi bayansa suna girgiza kai, suna mamakin audacity da capacity na Azrah.

Azrah ta sauke ajiyar zuciya, ta ce

"I'm sorry sir. Wannan ba zai kuma faruwa ba"

Mr. Alhassan ya murmusa ya ce

"It's okay, Miss. Amma kina kai zuciya nesa pls"

Ya É—auki briefcase dinsa da ya manta, sannan ya fita...

Sadeeq ya É—auki makullin motarsa, ba ya jin zai iya ci gaba da zama a wurin nan yau, dan zai iya illata Azrah,

Yana shirin fita sai ga Safiyya ta sha gabansa. 

Duk da cewa gabanta na dukan uku-uku, sai ta fara murmushi da wani dirty look da take masa

ta ce da marairaiciyar murya

"Sir... kamar ranka a bace fah? Ina zaka je haka?"

Wani kallo mai cike da ƙiyayya ya jefa mata

Shi a cikin ransa babu wata halitta da ya tsana kamar Safiyya, rashin kamun kanta ya fi komai bata masa rai

Ya ce da murya mai cike da ɓacin rai

"Zaki tashi gaba na, ko sai na hankade ki!"

Sai ta ja da baya sum-sum, ta ba shi hanya

Yayi tafiyarsa kamar zai tashi sama har ya isa wurin motarsa, ya shiga. Kai tsaye gida ya wuce

Yana isa, yayi parking da hanzari, ya fito cikin É—acin rai

A hanyar entrance ya haÉ—u da wata cousin É—insa ta karasa da sauri tana shirin magana masa magana

Ya kafe ta da ido, ya tamke fuska bai ce komai ba, sai kuma ya wuce ta tamkar bai santa bama

ÆŠakinsa kai tsaye ya nufa

Yana shiga ya rufe ƙofa, ya saka mata key

A gefe guda kuma, Mr. Alhassan ya shigo gida

Yayi mamakin ganin motar Sadeeq a harabar gidan yayi parking, ya sauka cikin mamaki..

Mr Alhassan ya tura ƙofar parlour ɗin a hankali, fuskarsa ɗauke da damuwa. Matarsa da ke zaune tana duba waya ta ɗago kai da murmushi

"Barka da zuwa Alhaji, fatan ka wuni lafiya?" Ya ce

"Lafiya kalau Sadeeq yazo gida ne?"

"A'a ban ganshi ba gaskiya"

Mr Alhassan ya É—an gyaÉ—a kai cikin mamaki ya ce

"Na ga motarsa a waje ne... Kuma kin tabbata bai shigo ba?"

Cousin É—in Sadeeq, da ke kan shiga parlour, ta karasa ta ce

"Eh ya shigo sir, amma kai tsaye ya wuce dakinsa"

Fuskar Mr Alhassan ta cika da damuwa 'Hmm… me ke damunsa kuma?' Ya juya ya nufi ɗakin Sadeeq, yana knocking har sau uku kafin daga baya ya buɗe ƙofar da ƙyar.

"Ina wuni sir" Sadeeq ya furta da ƙarfin hali

"Me ya hana ka zama a office? Me ya kawo ka gida a wannan lokaci?"

Sadeeq ya kawar da kai, "Nothing sir"

"No, ka faÉ—a min gaskiya. Wani abu ya faru ne? Ko dai maganar É—azu ne?"

Sadeeq ya ja numfashi ya ce

"Haba sir, duk Kai kake sa yarinyar nan ta raina ni? Taya zaka bata kujerarka, kuma duk yadda ta wulakanta ni, sai ka goya mata baya?"

Mr Alhassan ya karasa shiga cikin É—akin ya zauna a gefen gado ya ce

"Haba Son. Idan na tsaya maka za'a É—auka dan kai É—a bane, gaskiya kawai nake bi. Kuma kaima kayi hakuri ka rage wannan rainin hankalin da kake nuna mata, ka duba fa da kai kaÉ—ai take samun issues fah, kuma kai ma kasani tun kafin ma na bata kujerar ta riga ta cancanta, kuma harsh da kake mata ba zai sa ta girmama ka ba"

Sadeeq ya yi shiru, ya lumshe ido

Mr Alhassan ya miƙe ya ce

"Idan na isa da kai, ka koma office yanzu, bana don shiririta"

Sadeeq ya dan jinjina kai, "Okay sir"..

Oga Mahmoud yana kallon Abubakar ya ce

"Bana son wannan aikin ya kwana, ka tabbatar ka gama su yau É—in nan?" Sai kuma ya maida kallonsa ga Safiyya ya ce

"Kema make sure kin karasa" Oga Abubakar zai yi magana ya É—aga masa hannun alamar baya son jin komai daga garesu, ya ce

"Ina son idan kun gama da wannan ne na baku sabon aikin kafin Mr Alhassan ya dawo daga trip" da mamaki Abubakar ya ce

"Wai dama baya nan ne? Office dinsa kuma haka zai zauna a kulle kenan? Toh ai no need mu wahalar da kan mu muce sai mun gama aikin yau" wani kallo Oga Mahmoud ya masa ya ce

"Toh office ɗinsa a buɗe yake, Azrah ce ke office ɗin kafin ya dawo, kuma kasan bata wasa da aiki" saura kiris Miss Safiyya ta faɗi sabar razana sai kuma tayi saurin kama kanta tana kallonsa sai kuma ta miƙe ta ce

"I'm coming, sir" daga haka ta fita

Office É—in Mr Alhassan ta wuce direct, da shige ciki without permission sannan ta buÉ—e ainihin inda yake zama, turus ta tsaya ganin Azrah akan seat É—insa, Azrah ta É—aga kai tana kallonta, mamaki ne ya kamata ganin idanun Safiyya ya cika da hawaye, kafin tayi magana Safiyya ta juya ta fita da sauri har tana buge Merry da zata zo submitting wani file, office É—inta ta wuce ta É—auki jakkanta a ranta tana rantsuwar a satin nan sai ta saka abun da sai an Kore Azrah, a haka har ta bar harabar wajen..

Azrah ta fito a office É—in hannunta rike da handbag da kuma keyn motar ta, tana shirin sauka ganin Sadeeq yasa tayi saurin komawa baya sai ta wayence cewa waya take yi, ganin ya shiga office É—insa kawai ta sauka, parking space ta wuce sai kuma ta shiga..

Horon tayi a kofar gidan su, almajirin su ya buÉ—e mata gate ta shiga da motar tayi parking, hankalin ta duk na kan Bappah, a haka ta wuce parlorn su da sallama, Umma ta amsa mata, bayan ta shiga ta gaida Umma sannan ta wuce ciki, bayan taci abinci tayi sallah tana kallon Zahra ta ce

"Zahra ki tashi ki shirya mana, ko kin manta zamu asibiti duba Bappah ne?" Zahra ta ce

"Amma dai kin san cewa karatun medicine nake yi ko? Tun É—azu sai maganar fita kike yi, toh Ni ya kike so nayi da karatun ne wai?" Azrah ta sake baki tana kallonta sai kuma ta ce

"Banyi tunanin zanji wannan maganar daga bakin ki ba, kaff 'ya'yan Bappah akwai wanda yake gudun ɓacin ransa ne idan ba ke ba Zahra?" Zahra ta miƙe ta nufi wajen wardrobe ɗinta tace

"Ni karki wani fassara Ni, ba gashi zan sa kaya ba? Ai shikena" basu wani daÉ—e sosai ba suka nufi asibiti a hanya suka saya suka tsiya masa abinci, yoghurt sai fruits

Suna isa ward ɗin da Bappah yake suka karasa ɗakin, da Sallama suka shiga, daga Mama har yaran nata babu wanda ya amsa, Zahra ta wuce ciki ba tare data Kalle su ba, Azrah ta gaisheta amma kamar bata san tana yi ba, sai Bappah dake zaune hannunsa riƙe da plate ɗin shinkafa fari da manja, kai ma kana gani kasan ba abincin mara lafiya bane, suka karasa jikin gadon nasa, Mama kuwa ta kura musu ido, tama daina jin taɗin da take yi da yaran nata, Zahra ta karɓe plate na hannun Bappah ta saka masa wanda suka tsiyo a cinyarsa, duk wannan abun tun data gaishe sa taki kara cewa komai balle ta yi magana da shi, hakan da take yi ma dan ta kona wa su Mama rai ne, Azrah ta ce

"Amma yanzu ya jikin dai ? Akwai improvement ina?" Bappah ya gyaÉ—a kai ya ce

"Anjima ma za'a sallame mu", Azrah ta ce

"Toh sai mu jira mu tafi tare kawai tunda da mota muka zo"

Zahra ta mata wani kallo ta ce

"Amma kin san cewa karatu nake yi ko? Ni da zan koma yanzu shine zaki wani ce sai Anjima" Azrah ta Ciro kuɗi a jakka ta miƙa mata ta ce

"Gashi sai ki hau keke" Zahra ta tsaya kallon Azrah da mugun mamaki, sai kawai ta share hawayen daya gangaro mata ta miƙe ta ɗauki jakkanta, Bappah yayi saurin cewa

"No Azrah, ki tashi ku tafi, Kinga kar dare yayi" Azrah bata so ba amma kawai ta Ciro kuÉ—aÉ—en dake cikin jakkanta ta saka ma Bappah a aljihun sa ta ce

"Toh Bappah sai kun dawo, In Shaa Allah anjima zan shigo na duba ka" ya ce

"Allah miki, Albarka" ta amsa da Amin, ya ce

"Inaa...." Sai kuma yayi shiru ya kasa karasawa Azrah ta kura masa ido, sai kuma ya gyaÉ—a mata kai, hakan yasa tayi hanyar kofar tana wa su Mama sallama duk da tasan ba amsawa zata yi ba, Mama ta ce

"Dan Allah tunda kun gama da abin da ya kawo ku, ku tsaya a matsayin ku" Azrah bata jiyo ba tayi wacewarta

Tana karasa jikin motar ta taga Zahra harta kusa bakin gate, hakan yasa ta shiga motar, ta isa inda take tana mata horn amma Zahra ko da wasa bata jiyo ba, Azrah tayi gaba sannan tayi parking ta sauka ta karasa wajenta da sauri ta ce

"Zahra baki jin ina miji horn ne?" Zahra ta ce

"Ina bukata ne nace miki? Ai da kin tsaya kin taho da su tunda su ne naki, sune dolenki" Azrah ta tsaya kallonta, Zahra zata yi gaba Azrah ta jawota ta ce

"Me haka Zahra? Akan wannan abun ne ranki sai ya ɓaci? Toh I'm sorry" dakyar dai ta shawo kan Zahra har ta yarda ta shiga motar daga haka suka isa gida, tun da suka shigo layin take kallon motar dake parke a kofar gidan Bappah, mutumin yana tsaye a jikin motar kamar yana jiran wani, bayan ta isa kofar gidan su, Zahra ta sauka ta shiga da niyyar buɗe mata gate, Azrah ta juya tana kallon mutumin, sai da gabanta yayi mummunan faduwa ganin fuskansa wani yaro daga cikin gidan nasu ya fito yana masa magana, sai kuma ya juya ya karasa jikin motar sa ya shiga, harya tada motar Azrah bata ɗauke kanta daga kansa ba, tabi motar da kallo a hankali ta furta

"Toh me Saif yake yi a nan? Idan aika Samira ta mata ai ba can gidan zai tafi ba ai, tunda nan din yake kawo ta" haka kawai taji bata yarda da zuwansa ba, taja motar ta ta shiga cikin gidan..

Safiyya ta shigo cikin gidan nasu pass 9pm, da sanÉ—a sanÉ—a take tafiya harya ta samu ta shige É—akinta without letting anyone notice her, tana shiga ta sauke ajiyar zuciya, ta zauna bakin gadonta ta fito da abin jakkan tana kallon, lokaci É—aya ta fara dariya Mugunta ta ce

"Azrah naki ya kare, ba sai gona ta zaki shiga ba? Hmm, kinyi saurin trusting É—ina, but dole na É—au mata ki dan ba zaki cigaba da hanani baccin dare ba" buÉ—e kofar É—akin aka yi, da sauri ta mayar da abin bayanta, Mama ta karasa shiga cikin É—akin tana kallonta ta ce

"Ina kika tafi da daddaren nan?" Safiyya ta rike kanta ta ce

"Kai na ke ciwo, da magrib na shigo naga kina sallah shine kawai na É—an fita tsiyan magana" tana kallonta ta ce

"Kin ci abinci kuwa?" Kai ta girgiza mata, ta ce

"Toh tashi kije ki É—iba" da sauri ta ce

"Zan É—iba dama amma sai nayi sallah fah Mama" ta gyada mata kai ta mike ta ce

"Good night, Allah ya kara sauki" kai kawai gyada mata daga haka ta fita...

Umma ta ce

"Azrah tashi ki fita Kiga ko wane ne mana, amma ai hakan babu kyau zai zama kamar wulakanci ne" Azrah na ɓata rai ta miƙe, Zahra sai dariya take yi

Azrah ta fita, ta tsaya jikin gate É—in su tana jiran wanda yazo wajen nata ya sauko yazo, ai kuwa bata wani daÉ—e ba sai gashi ya sauko, da mamaki ta juya da sauri tana kallon sa, ya karasa yana kallonta ya ce

"Barkan ki da warhaka, idan babu damuwa zamu iya samun wajen mu zauna? magana nake son muyi me muhimmanci" Azrah tana kallonsa cike da mamaki ta ce

"But... Are you really okay?" Sai kuma ta juya zata shiga gidansu, yayi saurin shan gabanta, rai bace da kuma É—an sawa ta ce

"Saif ka fice min a hanya, kar na maka abin da zaka kasa yarda cewa Ni ne" yaja da baya yana kallon ta, ta wuce cikin gidan su rai ɓace...

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.