Complete Hausa Novels

Beyond The Veil Part 1 Novel Complete Hausa Novel

Reading file: Beyond The Veil Part 1 Complete Novel.docx

Chapter 23 of 79

Episode 23: The Hardest Goodbye Begins

Yau gaba ki É—aya a gajiye Bappah da Azrah suka dawo gida, nan ma yamma lis sai da yayi, sai da Bappah ya tabbatar an buÉ—e ma Azarh account, sannan suka bi duk wajajen da ake neman su dan karasa abinda ba za'a rasa ba, shiyasa ana idar da Isha'i Azrah ta kama bacci

Bayan dawowan Bappah daga sallahn Isha'i harya shiga É—akinsa sai kuma ya dawo É—akin Umma ya ce

"Ki sanar da Azarh ta shirya gobe zamu gidan Dada dan ba lallai daga baya ta samu daman mata sallama ma" Umma ta gyaÉ—a kai ta ce

"Kamar ka shiga zuciya ta nima abinda nake tunani kenan" Bappah ya ce

"Gobe da safe sai ta shirya" daga haka yama Umma sai da safe.

Washe gari kamar yadda Umma suka yi magana da Bappah, bayan sun idar da Sallah Umma tana kallon Azrah ta ce

"Azrah kije ki shirya kayan ki, Bappahn ku ya ce zaku gidan Dada tunda Kinga maganar naku kamar yanzu zaku tafi" Azrah ta gÆ´aÉ—a ma Umma kai a hankali tayi shiru tana kallon waje guda, Umma ta ce

"Lafiya dai ina?" Azrah ta kirkiri murmushi ta ce

"Babu komai Umma" Zahra ta ce

"Nima dai naga tun jiya kin wani canza" Azrah ta harareta ta miƙe zuwa ɗakinsu yin yadda Umma ta ce mata.

Kafin karfe takwas na safe Azrah ta gama shiryawa tana zaune suna hira da Umma tana jiran zuwan Bappah dan lokacin Zahra na makaranta, Bappah ya buÉ—e labulen É—akin yana kallon ciki ya ce

"Fito mu tafi idan kin gama shiri" Azrah ta miƙe ta ɗauki ɗan jakkanta, tana kallon Umma ta ce

"Umma zanyi missing É—inki" Umma tayi murmushi ta ce

"Ya kamata ki fara sabawa tun daga yanzu kafin ki tafi India, yanzu dai ki gaida min Dada" Azrah ta gÆ´aÉ—a mata kai, Umma ta musu Allah kiyaye hanya sannan ta koma ta zauna a É—akinta

Bappah da Azarh suka nufa compound É—in Mama dake zaune har ta fara tara nata jama'an tana kallon Bappah Zuciyarta na bugawa ta ce

"Malam ina zuwa kuma?" Ba tare da Bappah ya Kalleta ba ya ce

"Gidan Dada zamu" Mama ta taɓe baki ta ce

"Toh ai Shikenan, amma dole sai ka tafi da itane ba zata iya zuwa da kanta bane" sai kuma ta sake taɓe baki dan bata kaunar ko kaɗan Bappah ya tafi garin da Dada take gudun karta ce zata biyo sa dan ta tsana matar nan kamar mutuwa

Ba tare da Bappah ya kara kallon direction dinta ba ya fita, Azrah ta gaisheta wani kallon banza ta aika mata kafin ta cigaba da aikin gabanta tana kallon customers É—inta.

Bappah na fita ya tsare musu adaidaita ya kaisu har tashan da zasu shiga mutane garin, suna zuwa kuwa wajan mutane biyu ya rage hakan yasa suna shiga Mota ta tashi, basu suka isa ba sai wajajan 11:30am

A kofar gidan suka samu yara na wasa ganinsu yasa yaran suka zo da gudu suna ma Bappah oyoyo, Azrah sai murmushi take wa yaran a haka suka nufa cikin gidan wanda babu laifi gidan da É—an kayunsa dan duk layin gidan yafi su kyau

Dada tada fito daga É—akinta zata sauke abincin kan wuta ta sake baki tana kallon Bappah da Azarh cike da mamaki ta ce

"Dama kuna tafe ne?" Bappah ya ce

"Eh Dada" Azrah ta karasa ta rungume Dada cike da farin cikin ganinta ta ce

"Kakana nayi missing É—inki fah" Dada ta ture ta tana hararanta ta ce

"Eh amma ai baki san hanyar zuwa ki ganni ba" Azrah ta fara dariya, Dada ta bawa wata 'yar makwabciyarsu kulan hannunta ta ce

"Ke Zainabu, kwashe min abincin nan" sai kuma ta maida kallon ta ga Bappah da Azarh ta ce mu shiga ciki, daga haka suka nufi É—akinta

Dada na kallonsu ta ce

"Ina fatan lafiya dai?" Bappah ya ce

"Lafiya kalau Dada, dama akan maganar da muka fara ne" ta ce

"Oh' okay".

Kwana É—aya suka yi a gidan Dada sannan suka mata sallama suka dawo cikin garin Katsina, a gajiye suka shiga gida da yamma, Mama suka samu a tsakar gidan tare da wasu mata amma ko kallon direction É—in Bappah bata yi ba Matan ne ma suka gaishe sa ya amsa musu a takaice ya wuce ciki, Azrah ta gaishe su in jam'i ta wuce abinta ganin irin kallon tsana da Mama ke wasa mata.

Washe gari tun da sassafe Azrah ta kalli message É—in honorable ta zura wa wayan ido, Zahra ta ce

"Menene?" Azrah ta ce

"Honorable ne wai na tura masa account details É—ina, yau kwana biyu kenan yake damuna" Zahra ta wani Kalleta ta ce

"Okay... You mean ba zaki basa bane kenan or what? Ai wanda ya fika ya fika ne, sannan ai ba roka kika yi ba shine yaga dama" Azrah ta ce

"Toh sai na tura masa kenan kike nufi?" Zahra ta ce

"A'a karni tura masa, amma muga yadda ya ce miki a message ɗin" ta kare maganar tana miƙa mata hannu, Zahra ta karɓi wayan da Azrahn ke miƙa mata, contact ta shiga tayi typing 'my acc no' nan sabon account details ɗin da Azrah tayi ya bayyana, copying acc details ɗin tayi, ta fita a contact ta shiga message ɗin honorable sannan tayi pasting ta danna sent, message ɗin na tafiya nan take ta goge, tayi minimizing ta goge komai sannan ta mika wa Azrah wayanta duk within short secs ta yi hakan wanda yasa ko kaɗan Azrah bata kawo komai a ranta ba ta ce

"Kin gani ba? Ni kuma gaskiya bana jin zan tura masa, baya min magana amma kuma sai ya wani ce zai tura kuɗi? Is like ni kaɗai nake neman taimako" Zahra ta taɓe baki ta miƙe ta fita daga ɗaki ta barta.

Azrah bayan sun gama lunch taji karan message a wayanta, Zahra ta kalli wayan Azrahn da sauri, ko kaÉ—an Azrahn bata ma É—auka wani abu ba dan ita gaba É—aya ta É—auka mssg É—in MTN ne, Zahra ta ce

"Yaya Azrah baki ji wayanki yayi karan message bane ?" Azrah ta ce

"Ya wuce message É—in mtn ne" Zahra ta girgiza kai ta ce

"A haka sai Alkhairi ya wuce ki yanzu idan kuma daga banki ne ko kuma daga inda kika je suka tura miki wani important abu fa?" Umma na kallon Azrah ta ce

"Eh Azrah Kanwar ki tayi magana yanzu ba lokacin da zaki na ignoring messages bane, maybe zai iya zama something important ne ko kuma urgent" Azrah ta jawo wayarta tayi unlocking passcode ɗin, with shock take kallon message ɗin sai kuma ta miƙawa Umma without saying anything

Umma ta karɓa itama with shock take kallo alert ɗin sai kuma ta kalli Azrahn, tama rasa me zata ce, Zahra ta karɓi wayan a hannun Umma tana kallo sai kuma ta gwalo ido ta ce

"Allah sarki honorable, wallahi Allah ne ya turo mana shi dan ya taimaka mana" daga Umma har Azrah kallonta suke sai yanzu Umma ta tuna Azrah ta nuna mata message É—in daya mata wanda bata masa replying ba, Azrah ma mamaki take toh ya akayi yasan account details É—in da ko ita bata haddace ba sai Umma data saka ta tayi saying a wayarta

Umma na kallon Zahra ta ce

"Kuma shine ko? Zahra ta gÆ´aÉ—a kai ta ce

"Sure! Umma shi'ne, kuma ko hour banyi da tura masa acc details É—in ba fah" sai kuma ta rufe bakinta da sauri jin me ta gama faÉ—a

Daga Umma har Azrah kallon Zahra suke da mamaki....

Matan honorable ne ke zaune a katafaran parlorn Uwargidansa, tana shan fruits salad É—in gabata wanda kwatakwata bata jin taste É—in saboda rashin appetite, Allah kaÉ—ai yasan yadda zuciyarta ke tafarfasa da wani abu data ji ya tokare ta a throat É—inta

"Shikenan kenan, yanzu ba iya mukaminsa bane kaÉ—ai yake amfani da shi wajan taimaka mata? Bayan saka sunanta sai kuma yayi amfani da dukiyarsa ne don faranta ran matsiyaciyar yarinyar?" ta furta a hankali, tana cije lebenta

Hajiya Rabi tayi shiru tana kallon Hajiya Maryam da mamaki ta ce

"Amma ya akayi kika san ya tura mata waÉ—annan huge amount É—in bayan kince babu wani communication tsakanin su?"

Hajiya Maryam ta ce "kina wasa da Ni kenan, na kuma sake duba transactions É—insa na yau sannan naga sunanta, ko ba ita bace Azrah?" Ta karasa tambayar tana mata wani banzan kallon

Hajiya Rabi ta ce

"Ikon Allah, amma malam ya ce ba a cire asirin bafa, Ni har yanzu abun na ɗaure min kai, kai gaskiya na yarda Wannan Yarinyar idan har bamu yi da gaske ba ta shigo gidan nan sunan mu sorry, yarinya kamar mayya asirin ma ba'a jikinta yake ba amma dake ta raɓe sa ji yadda take ɓata mana aiki"

Hajiya Maryam ta juya da sauri tana kallonta ta ce

"Me kike nufi?"

"Cewa yayi  idan muka sake ƙara kuɗi, zamu iya hana tafiyarta gaba ɗaya, sannan za a mantar da ita a zuciyar Honorable, kuma zata shiga kuncin rayuwa"

Hajiya Maryam ta lumshe ido

"Bana so ta samu nasara, bana so ta cigaba da bayyana kamar yadda naga yanzu duniya ta fara saninta balle har wani yaji zai taimaka mata, tabbas zamu ci gaba da plan B, Na shirya kashe ko nawa ne, zan je kauyen nan da kaina gobe da safe" daga haka ta miƙe ba tare data sake ko kallon inda take ba ta wuce ciki abin ta...

A bangaren Azrah kuwa komanta ya fito na tafiya, wanda jibi ne tafiyar na su, jikin Azrah yayi sanyi fiye da yadda take tunani, da yamma suna zaune sai ga Dada ta duro gidan

Mama dake tsakar gida tare da jama'arta ta É—aga kai jin muryan Dada nan da nan fuskarta ya canza dan ko kaÉ—an bata so ganinta ba, infact bata kaunar ko ziyara ce ta kawo gidan

Dada ta fara tafe hannu ganin yadda gidan ya cika da makwabta da yaransu duk suna zaune sai hira ake, Mama ta miƙe tsaye da sauri tana canza fuskanta zuwa murmushi, Dada ta ce

"Biki ake a gidan ne ban sani ba? Ko kuma Uwani haihuwa kika yi ne bani da labari irin wannan jama'ar da kika tara mana?" Mama ta fara murmushin dole, duk matan suka miƙe suna gaida Dada cike da ladabi, a dakile ta dinga amsa musu tana bin gidan da kallo, Mama ta karasa wajan zata karɓi jakkanta, Dada ta ɗaga mata hannu alamar ta barshi ganin yadda kayan jikin Maman yayi duku duku ta ce

"Wai har yanzu Uwani baki canza ba? Haka kike tara mutane a gidan ne ko kuma haihuwa akayi bani da labari" Mama ta mata wani kallo ganin bata kallonta da zata juyo tayi saurin É—auke kai tana bata hakuri, makwabta sanin halin Dada suka fara zame jiki suna fita É—aya bayan É—aya

Zahra ta fito a É—aki da mugun gudu taje ta rungume Dada cike da farin ciki

Nan da nan Dada ta washe baki ta ce

"Me suna kece kika kara girma har haka? Eh lallai dole na dage da taru" daga haka tama manta da sabgar su Mama ta wuce ciki da murnan ganin jikarta..

Washegari da safe, gidan su Azrah ya kara cika da mutane, wasu dan tafiyar Azrah wasu kuma dan Dada ta zo, Kusan kowa ya san gobe ne tafiyarta

Tun safe Zahra da Umma na lura da yanayinta dan gaba ki É—aya tayi wani Irin shiru wanda gana mata kallo É—aya zaka gane damuwa ce fal a ranta, Zahra ta ce

"Anty Azrah, menene?" Kamar jira take kawai ta fashe da kuka, jikin Zahra ne yayi sanyi ta karasa wajan da take zaune ta soma lallashinta, Umma ce ta buÉ—e É—akin ta shigo sai kuma ta tsaya tana kallonsu da mamaki ta ce

"Lafiya?" Zahra ta ce

"Kuka take Umma" Umma ma kawai daurewa take ta karasa shiga É—akin ta zauna kusa da Azarh sannan ta jawo ta jikinta

Umma ta soma rarrashinta without saying anything, Azrah ta ce

"Umma yanzu zan tafi in barku? Toh waye zai kula da ke duk da ba fata nake ba idan ciwon ki ya tashi fah? Maybe banyi tunani bane da farko, kuma Maybe naso kaina da yawa shiyasa naso tafiya" Umma ta girgiza mata kai ta ce

"Not at all, Nima ina son ki tafi ko zaki huta Azrah, idan baki tafin bama ba lallai ki cigaba da karatu anan ba, karshe zaki cigaba ne kawai da sana'arki kuma Kinga ina so kiyi karatu wata kila kina da rabon aiki sai kuma kiyi sponsoring kanwarki ko?" Azrah dai sheshekan kuka take wanda gaba ki É—aya sai yanzu take ganin wannan

Muryan Bappah da Dada suka ji a ɗakin Umma, Umma ta miƙe zata fita kuma sai ga Bappah ya buɗe kofar ɗakin yana kallon su sai kuma ya ce

"Menene kuma?" Umma ta masa bayani ya ce

"Dama ina so Ni da ke da azrah muyi magana kafin gobe" Umma ta bi bayan Bappah, Azrah ma ta miƙe ta bi bayan su, Zahra ta bita da kallo

Azrah ta samu already Bappah na zaune ga Umma sai kuma Dada, ta zauna bakin kofa tana jiran jin me zasu ce mata, nan kowa ya mata nasiha mai ratsa jiki akan karta je can ta canza hali ko ta bar ibadanta, wanda tun kafin a gama Azarh ta gama shan Kukanta...

This book costs 500. Make the payment to Hauwa Jibrin, Wema Bank account 0421255553, and send proof of payment to 08110615256.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.