Complete Hausa Novels

Beyond The Veil Part 1 Novel Complete Hausa Novel

Reading file: Beyond The Veil Part 1 Complete Novel.docx

Chapter 43 of 79

Episode 43: Between Paths and Promises

Bayan wasu kwanaki...

Kamar yadda suka saba kowa na harkar sa ne a gidan tun faruwan wannan incident ɗin Azrah da Abdul, yau Laraba saura kwanaki Azrah ta koma India saboda week din da zasu shiga za'a yi resuming. buɗe idonta tayi ta jawo wayanta ta kunna, kallon lokacin da tayi pass 9am yasa ta miƙe zaune, bayan ta gama tattaro nutsuwarta sannan ta miƙe ta nufi ɗakin Umma

Zahra ta ɗaga kai tana kallonta ta ce "Ya Azrah ke da zaki yi resuming next week ai kamata yayi da safe zaki tafi dan ayi clearing dinki da wuri kar a samu wasu issues" 

Azrah na murmushi ta zauna gefenta tana kallon ta, ta ce

"Gaskiya dai, yau nake son zuwa Scholarship Board don karɓar final clearance dina, da zarar sun sa hannu, shikenan na gama komai sai tafiya idan Allah ya yarda"

Umma ta shigo daga waje da veil dinta a kafaɗarta tana kallon Azrah da har sannan idanuwanta bai game washewa daga bacci ba  ta ce

"Ki tabbatar komai na cikin file É—in ki Azrah, Passport É—inki, admission letter, medicals, da sauran takardu, ban son sai kin tafi kuma kice baki dau kaza ba"

Azrah ta ce "Toh Umma, na haÉ—a komai tun jiya, sai dai na shirya yanzu kawai na tafi"

Umma ta ce "Kiyi sauri ki je saboda ki samu ki dawo da wuri dan ganin yaushe ne tafiyar naki kar kuma ace available flight jibi ne"..

A cikin dogon wata Maroon Abaya da ta amshe fatar jikinta tayi mugun kyau Azrah ta shiga harabar Scholarship Board Office, Bayan ta cike wasu forms, ta miƙa takardunta ga jami'in da ke duba su.

Officer É—in ya ce "You've been cleared already for departure. Your documents are intact. Just make sure to report to the embassy before Friday for your visa stamping"

Azrah da murmushi É—auke a fuskarta ta ce "Thank you so much sir. I appreciate it"

 

Officer É—in ya ce "Safe trip ahead. You've made the country proud, keep it up Miss Azrah"

 

Azrah na murmushi ta ce "In Shaa Allah, sir"

Tana fita daga ofishin, ta sauke ajiyar zuciya tana jin wani sabo yana yi, buÉ—e handbag É—inta tayi ta Ciro wayarta ta kira Bappah don shaida masa cewa ta gama komai

Bappah na ɗagawa Azrah ta ce "Bappah na gama clearance, Zasu aika da report din zuwa Embassy, yanzu sai dai na shirya dan kai musu sumin signing" 

Bappah ya ce "Alhamdulillah, Amma dole sai an kai can Embassy É—in kenan?"

Azrah ta ce "Eh haka dai suka ce"

Bappah "Toh shikenan, bari muga yadda abin zai kasance" daga haka ya katse kiran

Azrah ta fito daga cikin harabar scholarship board hannunta rike da takardun clearance da suka tabbatar da tafiyar nata nan kusa ne, Duk da rana bawai yayi bane amma hasken rana ya ɗan dusashe kamar za a yi ruwan sama, iska mai ɗauke da ƙamshin kasa yana kaɗawa, alamar dai ruwan zai sauko anytime

Haka kawai ta tsinci kanta tana farin ciki atleast zata koma India as Level 2 students, wani murmushin ne ya sake kubucewa a fuskantar tana gyara veil É—in kanta saboda iskan da ake yi, wani abu ne yayi flashing a kwakwalwarta nan take taji zuciyarta ya buga, tafiyar nata ma taji bata wani dauki, yanzu haka zata koma can baya nan? Taya zata fara copping, hawaye taji amma bata bari ya zubo ba

A haka take tafiya a hankali harta isa bakin titi. Ta nufi inda za ta tare adaidaita, tana tsaye tana ganin duk Napep ɗinda zai wuce da mutane a ciki, wata mota ta yi parking a gabanta. Bata buƙatar

kallon wanda yake ciki domin ta riga da ta san motar, Motar Honorable ce

Duk da yadda zuciyar ta ke bugawa da sauri da sauri amma haka ta dake taki kallon direction É—in motar, Ji tayi kamar ta juya ta bar gurin amma wata murya cikin zuciyarta tace mata kar tayi hakan dan duk walwala da suke ciki tsilansa ne ko ba komai bayi deserving haka daga gareta ba

Kawai samun kanta tayi ta karasa jikin motar a hankali kamar wacce aka ma dole, Ya sauke glass É—in gefe yana murmushi

"Assalamu Alaikum Azrah," ya ce da wata very calm voice dinsa

"Wa'alaikum salam, Ina wuni, Sir?" Ta amsa cikin ladabi, kanta a kasa as usual

"Alhamdulillah, Ya karatu? Yaushe zaki koma kuma?" Ya tambaya yana kallon ta da kyau

"Alhamdulillah, Insha Allah jibi zan tafi, abinda ya kawo ni nan dinma yanzu dan clearance din ne" Ta amsa, tana ƙoƙarin kin kallonsa dan tana jin idanuwansa akanta

Ya kai hannunsa cikin dashboard ɗin motar ya ciro wani bundle na kudi, yana miƙa mata ya ce

"Karɓi wannan ba yawa dai, ko ruwa kya siya da shi"

Azrah ta ja baya da sauri ta ce "Nagode sosai, Sir, amma…"

Ya yamutsa fuska, yayi saurin katse ta yana fadin

"Ke yanzu har kin fara jin girma ko? Naga ba roka kika yi ba kawai naji na baki kyauta ne"

tayi shiru tama rasa tunanin da zata yi, har sannan kuma bai sauke hannunsa daga mika matan ba, ta miƙa hannu a hankali ta karɓa, ta ce

"Thank you sir, Allah ya saka da alkhairi" ta faɗa ƙasa ƙasa

"May Allah be with you, Azrah" ya faÉ—a yana kallon ta kamar yana da wata tambaya a zuciyarsa amma ya rasa ta ina zai fara, sai kallonta daya zuba mata ido yake yi, ita kuma ganin kallon ya fara yawa yasa ta ce

"Amin" a takaice dan yanzu babu abinda take so kamar ya bar wajan, kawai ya ja glass É—in motar sama a hankali, sannan ya ja motarsa ya tafi

Azrah ta tsaya na Æ´an dakiku kafin ta nufi gefen titi, ta tare adaidaita saho, zuciyarta cike da abubuwa masu nauyi da babu wanda take da damar faÉ—a musu su kuma fahimce ta.

Azrah na shiga gida bayan dawowarta daga scholarship board, ta samu Umma a É—aki tana kulla kanwar sayarwa, ta zauna kusa da ita cikin natsuwa, tana fuskantar ta da murmushin data kirkira ta ce

"Umma na dawo…"

"Umma ta ce "Sannu da zuwa 'yata, ya abin naku ya kasance?"

Azrah ta ce "An gama komai, sai dai sun ce dole ne na tafi embassy a Abuja nayi signing kafin a bani visa"

Umma ta kalli Azrah da mamaki ta ce

"Me ya sa ba za su aika irin wancan tafiyar naku ba? Naga ai wancan haka suka yi babu wani signing da kika je yi ko?

Azrah ta ce "Wallahi ni ma ban sani ba, haka kawai aka ce za a je wannan karan ban san kuma menene yasa su fadan hakan ba Nima Umma"

Umma ta sauke ajiyar zuciya, nan da nan har fuskarta ya cika da damuwa ta ce "Toh yanzu kenan zaki tafi Abuja?"

Azrah ta ce "Haka suka ce Umma"

Umma ta ce "Amma fah ace kawai kije kiyi signing ki dawo naga za'a kashe kudi ga kuma tafiya a gabanki kina bukatar wasu abubuwa naga ai"

Azrah tayi shiru tana nazarin maganar Umma, tasan Umma tayi gaskiya dan yanzu ace taje ta dawo ma, babu wani lokaci kuma dole zasu kashe kuÉ—i, kawai ta jawo wayanta ta shiga text na Honorable without second thought ta fara typing...

FaÉ—a masa cewa ance sai ta tafi tayi, sannan ta danna send message É—in ya tafi

Bayan mintoci kaÉ—an sai ga message dinsa shima ya reply dinga back

"Ki haɗa Everything yanzu za'a zo a karɓa za'a tafi dashi yanzu idan ya so a dawo miki da shi gobe tunda flights zasu bi"

Azrah ta ji dadi sosai da wannan sakon nasa, ta juya tana kallon Umma sannan ta shiga narrating mata...

Da Daddare bayan sallar Magrib

Honorable ya aiko mata da saƙo

"Ina waje zaki iya bada wa a kawo min"

Azrah ta É—an tsaya tana kallon message É—in sai kuma ta wuce daki da sauri ta fito da komai na takardar signing É—inta ta fita zuwa waje..

A hanya zuciyarta cike da nauyi, da kunya, ta fita bata ga motarsa a kofar gidan nasu ba sai ta hango motarsa daga nesa, ya tsaya houses away from their home, Ashe yayi hakan ne saboda mugun kunyar Bappah daya ke ji yasa ba zai iya karasowa ba

Ta karasa har inda yake, bayan sun gaisa ta miƙa masa takardar, buɗe motar yayi ya karɓa, yana kallonta cike da regret da kuma tausayinta ya ce

"Na karɓa, In Shaa Allah idan suka isa bayan Isha'i gobe za'a miki signing"

Ta gyada kai kawai, sannan ta juya ba tare da ta kalli fuskansa ba ta fara tafiya tana jin wata irin sanyi a zuciyarta, cike da godiya da kuma tambaya Me yasa ta kirasa har ta basa? Me yasa yake damuwa da damuwarta har kulawa da ita haka?

Habibah da Siyama da suka shigo layin nasu a gajiye ashe tun daga nesa suke kallonsu, bakin ciki ƙarara ya bayyana a fuskokinsu su, suna shiga ko Bappah dake compound basu lura ba suka wuce dakin Mama dan kai mata gulma, da rahoto

Azrah ta karasa cikin gidan nasu tana shiga taga Bappah tsaye a tsakar gida, hannunsa goye a bayansa yana kallon ya dakatar da ita ya ce

"Ke Azrah... da wa nagani kina magana a jikin mota?"

Azrah ta tsaye cak, ta sauke idanunta kasa ta ce

"Eh... Honorable ne Bappah"

Bappah da wani expression ya ce "Honorable? Me kike yi da shi a wannan lokaci toh?"

Azrah ta ce "Bappah… ai Umma ce naga maganar kai takaddun Embassy ya dame ta shine na tura masa text akan dole sai na tafi Abuja signing shine yazo ya karba yace akwai masu zuwa Abuja a daren nan, gobe sai kawai a min signing a turo mana"

Bappah ya ce "Toh kenan shine ba zaki sanar dani ba?"

Azrah ta sauke idanu ƙasa, muryarta na rawa ta ce

"Ai baka gida ne Bappah, kuma naga kar ayi wasting time ne tunda tafiyar yazo ne akan idan ka dawo zan maka baya Ni"

Bappah yayi shiru, yana kallon ta, sai can ya É—an gyara tsayuwarsa ya ce

"Next time duk wani abu da ya shafi tafiyarki ko wani abu ki sanar dani farko, uwarki mace ce, ni nake da alhakin ki, kinji ko?"

Azrah ta gyada kai da ladabi ta ce

"Na fahimta Bappah, in sha Allah bazan sake ba"

Bappah ya ce "Ki je kiyi sallah lokaci yayi"....

Azrah na kwance a kan katifarta, tayi nisa cikin tunanin da take yi, yanzu ga maganar Umma da Bappah wanda bata san yadda zata yi ba, ga maganar idan ta tafi Khalil baya nan,rabon data shiga damuwa kila tun lokacin da take neman kudin Waec, wayanta dake gefenta ta jawo tayi dialing numbern khalil

Khalil bugun farko ya É—aga ya ce

"Hello my Azrah…Muryarsa cike da natsuwa

Azrah ta É—anyi shiru jin My daya ce, sai kuma ta dake ta ce

"Hey... Khalil, how was your trip?

Khalil ya ce "Alhamdulillah. I just landed safely in Egypt this morning. I've been trying to reach you"

Azrah ta ce "I know…"

Khalil ya ce "Hmm, it's okay. I missed your voice"

Azrah tayi shiru, tana kallon ceiling kamar tana kokarin danne wani abu a zuciyarta, ita dai yau bata fahimce sa ba, sai jin muryan sa tayi ya katse mata tunaninta ya ce

"Are you okay?"

Azrah ya ce "I don't know... I was really looking forward to this India trip, but now that you're gone back to Egypt, it doesn't feel the same"

Khalil Softly "Azrah your journey is still valid, Our dreams don't pause just because we're far apart"

Azrah at this point ya sake daure ta ne da maganganun sa, kawai samun kanta tayi da ce masa

"I guess... I just wish you were still around" sai kuma ta rufe Fuskarta da sauri kamar yana ganin ta

Khalil ya ce "Don't worry, I'll be back before you even realize it And besides, I want you to talk to someone... my mom"

Azrah da mamaki ta ce "Your... mom?"

Khalil ya ce "Yes. She's here with me, She keeps asking about you. Let me put her on"

Azrah ta ji gabanta ya fadi, murya wata Mata ne, with very calm voice tayi mata sallama

"Salam Alaikum dear Azrah"

Azrah tana murmushi ta ce "Wa'alaikum salam Ma..."

Mama Khalil ta ce Khalil talks about you all the time. You must be special. May Allah bless your journey and protect you always deat"

Azrah na Murmushi haka kawai taji wani farin ciki ya mamayeta ta ce "Amin... Thank you so much Ma"

Mama Khalil ta ce "In shaa Allah we'll meet someday, Stay strong and stay focused. Good night, sweetheart"

Ta mayar da wayar ga Khalil. Sallama suka yi sannan ya katse kiran. Azrah ta sa wayar a gefenta, ta lumshe ido bata san ma tana murmushin dake kubuce mata ba.

Washegari... Azrah na zaune a dakinsu tana gyaran kayanta, wani ya leko yace ana sallama da ita a wajen, hakan yasa Umma ta shiga ciki dan sanar mata

Umma ta ce "Azrah ki je ki, ana neman ki wai a waje nace ko honorable ne"

Azrah ta mike da mamaki, ta fita zuwa kofar gida sai taga

Honorable tsaye da takardu a hannunsa, ta karasa inda yake tsaye a jikin motar sa, tun kafin tace komai ya ce

"Good evening, Azrah"

Azrah ta dan sunkuyar da kai ta ce "Afternoon sir"

Honorable yana mik'a mata takardun ya ce "Gashi har an samu an gama, sai tafiya ta rage yanzu Jin Shaa Allah"

Azrah ta karba da ladabi tana murmushi ta ce

"Thank you so much sir. Allah ya saka da alheri"

Honorable ya ce "Ameen. Make sure you go through them idan da matsala sai kiyi magana"

Azrah ta ce "In shaa Allah. Nagode sosai"

Ya juya ya shiga motar sa, Azrah kuma ta tsaya kallon takardun a hannunta Sai kuma ta juya a hankali ta nufi hanyar shiga gida

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.