Complete Hausa Novels

Beyond The Veil Part 1 Novel Complete Hausa Novel

Reading file: Beyond The Veil Part 1 Complete Novel.docx

Chapter 47 of 79

Episode 47: Echoes of Resentment

Azrah ta share hawayenta, ta ce

I was shocked... and honestly, the worst part is... I've heard that before, Sai na tuna Saif ma ya taɓa ce min haka wai I'm attention seeker Kuma... it hurts more when it starts to feel true"

Samira ta girgiza kai cike da ɓacin rai ta ce

"Wait... shine kika tsaya kika yi shiru? Ko kuka? Like... after all the insults?"

Azrah ta É—an share fuskarta tana cewa a hankali

"I think... maganar da yayi... gaskiya ce somehow"

Samira ta sake baki da mamaki ta ce

"Wait... what?? Wani irin magana ne haka?"

Azrah ta numfasa da ƙyar ta ce

"He said I'm just looking for attention"

Idonta ya cika da hawaye, zuciyarta na ƙuna, ta ce

"And it's not even the first time I'm hearing that fah nace miki, Even Saif once said same thing... Shiyasa nace haka"

Samira ta dafe goshi da takaici, ta ce

"No way. wlh Azrah, there's no Nigerian guy that has the guts to say you're seeking his attention. Sai dai he is the one chasing yours. And if he's not it's his loss, not yours!"

Azrah ba ta ce komai ba, tana kallon wani waje

Samira ta ja tsaki ta ce

"Ke kuma, sai kika tsaya ya gama fadin duk abin daya zo bakinsa just like that? You should've opened your mouth and taken your respect back!"

Azrah ta ce da sanyi

"Wallahi nama rasa how to react. You know yadda ake kallon mu ai... Kowa attention É—insa fa ya koma kanmu ne"

Da ƙyar ta miƙe, ta nufi toilet ba tare da ta sake cewa komai ba zuciyarta na ci gaba da kuna, da kalmomin da har yanzu ba su dena damunta ba.

Da daddare, har lokacin Sadeeq ya kasa samun nutsuwa. Komai na ranar ya tsaya masa a rai kamar a jikin sa har sannan Azrah na nan, yadda ta faÉ—o kansa, yadda kallon ta ya tsaya masa da abinda ta faÉ—a. Komai yana dawowa masa tamkar a lokacin abin ya faru

Zaune yake akan kujerar parlon su, ya kunna TV yana kallon wrestling amma hankalinsa ba ya kan kallon, hannunsa riƙe da cup ɗin coffee amma shima bai kai bakinsa ba. Ya rasa me yake damunsa, tunanin incident ɗinma ya daina ya kasa, sai faman jan tsaki yake

Sagir ya buɗe kofar ya shigo cikin parlor da sallama.  ya jefa ma Sadeeq kallo ɗaya ya ɗauke kai. Sai kuma ya karasa ya zauna a gefensa ya ce

"How's the night, Sadeeq?"

Sadeeq ya yi banza da shi, Sai can kuma ya É—an kalli Sagir daya ke danna wayansa ya ce

"Duk Abbah ne ya jawo min. Da ya barni a Nigeria... yaushe hakan zai faru pls? Yaushe zan haÉ—u da wannan yarinyar ma dan Allah?"

Sagir ya juyo da mamaki yana kallonsa ya ce

"Wait... har yanzu kana thinking about that girl ne? You're not serious wallahi"

Sadeeq bai ce komai ba sai ya miƙe, ya nufi bedroom ɗinsa ba tare da ya ce uffan ba. Sagir ya bi shi da kallon gefen ido, ya girgiza kai a hankali, ya kwanta akan kujerar parlon yana kallon ceiling"

A bangaren Azrah kuwa, itama hakan ne, ta kasa mance komai gani take kamar kowa yasan da zagin daya mata, ji take ta tsane sa, tsaki tayi ta miƙe ta nufi toilet don yin wankan bacci, da ta yi wanka, ta sanya sleepwear dinta sannan ta kwanta, amma zuciyarta bata daina mata zafi ba balle ta manta, Sai gashi wayarta tayi ringing Khalil

Cikin sauri ta ɗaga kiran kamar dama jiran kiran nasa take. 

"Hello..." ta ce da wata kasalalliyar murya

Bayan sun gaisa, Khalil yayi shiru kamar mai nazari

"Azrah, what happened?"

ya yi tambayar da damuwa

Azrah ta É—an yi shiru, sai ta ce

"Me ka gani da zaka ce haka?"

"Seriously? You think I won't know when something is wrong with you? That means I don't really care, huh?"

Yace da murmushi dan karfafa mata gwiwa tayi trusting É—insa

Azrah ta sauke ajiyar zuciya "Okay…" ta ce a hankali.

Ta fara ba shi labarin duk yadda abun ya faru, tana faÉ—a tana jin ciwon abun na sake tashi, kamar yanzu abin ke faruwa

Khalil yayi wani irin shiru, shi kaÉ—ai yasan yadda yake boiling inside, dakyar ya buÉ—e baki cikin tsananin fushi ya ce

"Who the f** is this guy? Waye shi har zai ce kina neman attention dinsa? Yaushe kika zama mace mara daraja har wani zai zo ya wulaƙanta ki haka?, shi har ya isa ya Kalle ki balle yace kina neman attention ɗinsa?"

Yadda yake maganar da karfin gaske kuma cikin tsananin fushi, Azrah dai tayi shiru, tana mamakin yadda zafin maganar ke fita daga bakinsa, tone É—insa kaÉ—ai ya isa ya nuna mata cewa ya fita jin zafin abu, amma lokaci guda zaka fahimci cewa tsansan kishine

"I'm not in the mood now" ya ce daga ƙarshe

"Let's talk tomorrow. Sleep tight, dear"

Ya katse kiran ba tare da ya jira me zata ce bama

Samira dake gefe tana game, ta É—ago tana dariya

"An taɓo miki sarkin kishi, baby girl"

Azrah ta juya da kai tana kallonta ta ce

"Waye yace miki kishi yake yi?"

Samira ta kyalkyale da dariya ta ce

"Ke baki ji yadda yake magana ba? The tone alone was jealous enough. Wallahi yana kishi"

Azrah ta mayar da kanta ta rufe idonta, bata ce komai ba

Sai dai wani sanyi ya ratsa zuciyarta dan yanzu ji take kamar duk damuwarta ma an yaye mata shi ne tass daga zuciyar

Washegari kamar yadda ta saba, Azrah ta farka da wuri. Bayan sun isar da sallar asuba, tayi azkar É—inta cikin nutsuwa. Daga nan ta kwashe kayan wanke-wanke da basu yi jinya da daddare ba ta fita dasu zuwa kitchen ta soma wankewa, bayan ta gama wanke wa ta dawo É—akin da su sai taga Samira already ta daura musu breakfast tana mopping É—akin

Hakan yasa Azrah ta wuce toilet bayan ta ajiye plates É—in, ta yi wanka. Bayan ta fito, Samira har ta gama komai, ta zuba musu breakfast a plate, tana cikin zuba tea a cup

"Zauna mu yi breakfast kafin na wuce nayi wanka" Samira ta ce tana matsowa kusa da gadon

Dukkansu suka zauna suna breakfast dinsu, bayan sun gama, Samira ta wuce toilet, Azrah kuwa ta gyara wajen sannan ta zauna gaban mirror

A hankali ta shafa lotion É—inta, ta kama gashin kanta da kyau ta taje shi, ta kama da ribon fari wanda ya haÉ—u da fresh complexion dinta, Daga nan ta fito da kayan da zata sa, straight jeans mai light blue, tare da white short-sleeve shirt da tiny embroidery a chest É—inta, tayi tucking neatly, sannan ta É—aura open Abaya akai, ta saka flat black shoes da matching handbag. Kallon kanta tayi a mirror ta É—an murmusa, tana jin kamar zata iya fuskantar komai yau.

Ta zauna bakin gado kenan tana duba time, sai Samira ta fito daga toilet tana goge fuskanta, Bats ɓata lokaci ba ta gama shiryawa

fita daga hostel É—in suka yi, suna hira irin na safe cikin raha da dariya. A hanya suka rabu bayan sun iso faculty, Azrah ta shige department É—inta Samira kuma ta karasa

Yayin da take tafiya cikin corridor na department É—insu, ta ci karo da wasu daga cikin classmates É—inta, ta tsaya suna gaisawa da ita cike da annashuwa. Bata bar wajen ba sai Sarah ta iso, tana dariya da sauri ta rungume Azrah

"Good morning bestie!"

Azrah ta amsa da murmushi, "Morning, hope you had a restful night"

Sarah ta gyada kai da fara'a "Let's go to the lecture hall yanzu, mu samu front seat please"

Azrah ta ce "Yes, let's"

Kamar an ce ta kalli gefe, sai idonta ya faÉ—a cikin na Sadeeq, wanda ke tsaye a gefe da hannayensa cikin aljihun wandonsa, sanye da fitted black T-shirt da dark jeans. Yayi mugun kyau irin wanda idan ka kalle sa sai ka sake kallonsa, sai wani cold expression a fuskarsa.

Itama Azrah tana kallonsa kenan, shima ya É—ago kai... ido ya faÉ—a cikin na juna, wani tsinkewar zuciya suka ji a lokaci guda

Ba tare da ta ɓata lokaci ba Azrah ta ɗauke kai da sauri, fuska a ɓace kamar wanda taga abu mara kyau. Shima Sadeeq ya ɗauke kansa cikin sauri yana jin wani haushin sake ganin ta da yayi, me take yi a department ɗinsu? Abin da ya ayyana a zuciyarsa kenan

Azrah da Sarah suka zauna a front seat cikin hall É—in, amma zuciyar Azrah ta nemi nutsuwarta ta rasa

Yayin da lokacin lecture ya yi, lecturer É—insu ya tunkaro hall É—in. Wannan yasa students É—in dake waje suka fara shigowa cikin hanzari, kowanne yana neman kujerar da zai zauna

A ƙarshe, su biyu suka shigo cikin tafiyar kasaita da kuma jiji da kai,

dake duk yawancin ma sun girmi students ɗin tunda su karin karatu suka zo not as fresh student, hakan yasa babu wata alaƙa ko gaisawa da su. Ko fuska basu sake wa kamar ba su da sha'awar zama da kowa ballai har a saba

Sadeeq yana kallon gabansa ne, har sai da ya karasa seat É—insa, Sagir dake binsa a baya kawai idonsa ya sauka kan Azrah, Kallo É—aya ya mata sannan ya É—aga kansa akanta, kana kallon fuskarsa zaka gane akwai tsananin mamaki da É—an wani abu dabam a idonsa

Ya zauna a seat É—in da Sadeeq ya zauna, daidai lokacin da lecturer É—in ya shigo, sake kallon direction dinta yayi sannan ya É—auke kansa.

Sai kuma ya É—an kalli Sadeeq ta gefen ido ganin ko Sadeeq ya lura da ita, sai dai kamar baisan da zaman Azrah a ajin ba, ya cigaba da duba laptop dinsa yana gyara glasses É—in idon sa

Sagir ya ja numfashi bai san sanda ɗan murmushi ya kuɓuce masa ba, A ransa kuwa ya ce "Let’s see what happens when Sadeeq finds out…"

Lecturer É—in yana tsaye gaban class É—in yana scanning É—in students É—in da suka zauna da nutsuwa. Ya É—an É—aga murya cikin seriousness ya ce

"Before we start today's topic, let me ask a question from the last reading"

Zuciyar kowa ta fara bugawa wasu suna sunkuyar da kai, wasu na duba note kamar suna son sake kallon abinda aka musu a previous class din, Aji ya dauki shiru, tamkar babu kowa

"Anyone?" ya ƙara tambaya, idonsa na yawo cikin ajin.

Sai ya É—an tsaya, yana kallon list na attendance. Ya É—aga kai cikin authority

"You… Miss Azrah"

Zuciyar Azrah ta ɗan tsinke, Bata yi expecting ba. Ta kalli Sarah, wacce ta ɗaga mata gira kamar irin you got this. A hankali, Azrah ta miƙe tsaye, tana gyara hijab dinta, ta ɗan natsu kafin ta fara magana

"Sir, The reading focused on the structure of Indian public administration and how it evolved post-independence. It highlighted how the British legacy influenced centralized control, and how the democratic system later reshaped the bureaucracy. The chapter also discussed the roles of civil services, particularly the IAS, and how federal and state governments share administrative responsibilities"

Muryarta ta kasance cikin nutsuwa da ladabi, tana faÉ—in bayanan kamar mai karatu, duk da slight tension a zuciyarta. Amma yadda take articulate ideas É—inta ya janyo hankali duk wanda ma baya sauraronta ma, sosai kowa yayi shiru yana sauraron ta

Sai a sannan Sadeeq, wanda tun farko bai ɗago kansa ba balle yasan wake magana sannan ya ɗaga kai da mamaki wannan yarinyar

Eyes met

He froze Idanunsa suka tsaya a kanta The girl? Aji É—aya da shi? Kuma har tana iya magana haka? A take zuciyarsa ta fara bugawa da sauri, kamar ba shi da control.

Ya kasa ɓoye shock ɗin da ke bayyane a fuskarsa. Zuciyarsa na bugawa da irin "Why ita kuma again?"

Sagir dake gefe ya kalle shi sideways, ya lura da reaction É—insa, ya É—an murmusa a ransa yana ayyana yadda Sadeeq yake feeling ynz

Azrah kuwa ta gama bayani, ta tsaya daidai inda ya kamata, bata ja maganar ba. Lecturer É—in ya É—an gyada kai da gamsuwa ya ce

"Well done, Miss Azrah. You're absolutely right"

Ta murmusa kaÉ—an ta zauna. Sarah ta bubbuga kafadarta da jin daÉ—i.

Sadeeq yaji kamar ya yi yaya ne, bai taɓa jin abu ya dame sa ba sai wannan karan, wani irin zuciyar sa ke tafarfasa, imagine taya zai zauna aji ɗaya da wancan 'yar gidan ba kowa ba

Ana gama lectures, kafin lecturer ya kai ga rufe laptop ɗinsa gaba ɗaya, Sadeeq ya miƙe tsaye tamkar wanda aka yiwa allura. Ba tare da kallon kowa ba, ya nufi kofa kai tsaye, shi kaɗai yasan meyake ji, Sagir ya juyo ya bishi da kallo, ya girgiza kai kawai.

"What the hell is she doing here?" Sadeeq ya furta da haushi a ransa

"Of all places, why this school, why this department… why my class?" Yana jin kamar duniya na kokarin yi masa dariya ne, Yarinyar data gama raina sa huh?

Azrah da kanta ke ƙasa tana shirin tashi, sai idonta ya sauka a jikin mutumin da ya fice kamar wanda ke shirin tashi sama. Tsayawa tayi cak, zuciyarta na bugawa. Tana kallon bayan Sadeeq da sauri da mamaki wani abu na ratsa ta, tsinkewar zuciya da tsoro da rudani a lokaci guda.

"Anya kuwa? Shine ne?" Ta tambayi zuciyarta. 

"Amma ai India muke... Ba yanda za'a yi naga Nigerian na É—auka É—an India ne"

Tana kokarin ɗauke kai, suka haɗa ido da Sagir wanda ya juyo ya kalleta. A nan ne ta tabbatar cewa shine, Sai ta sauke ajiyar zuciya a hankali, ta ɗan taɓe baki da mamaki da ɗan fargaba.

"So, it's really him"

Sarah ta miƙe tana fuskantar Azrah, ta ce da murmushi, "Let's go, sweetheart"

Azrah ta gyaɗa kai ba tare da ta ce komai ba. Tana ƙoƙarin boye rudanin da zuciyarta ke ciki. Duk da hakan, zuciyarta na ta faman tambayoyi da bata da amsarsu.

Daga haka suka nufi kofa, suka fice daga lecture hall É—in cikin natsuwa

#Jiddatulkhayr

08110615256

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.