Complete Hausa Novels

Beyond The Veil Part 1 Novel Complete Hausa Novel

Reading file: Beyond The Veil Part 1 Complete Novel.docx

Chapter 48 of 79

Episode 48: Turbulence

Sadeeq na fita daga lecture hall bai tsaya ko ina ba sai parking lot. Zuciyarsa banda ta farfarsa babu abinda yake yi. Ya buÉ—e motarsa da karfi, ya shiga, ya rufe kofar, ikon Allah ne kawai yasa bai fasa glass É—in ba.

Zuciyarsa na bugawa, numfashinsa yana seizing. Ya dafe steering yana fidda hucin ɓacin rai

"Wannan yirinyar… wannan jakar yarinyar! What the hell is she doing here?" Ya furta da ƙarfi, yana jin bakinsa na ɗaci

"Bayan wannan many incident, I still hate her. Still!" Ya danna horn da karfi kamar yana sauke haushinsa ne akan akan motar.

Bai san how long yake wannan wajen ba, sai kawai jin Sagir ya buÉ—e motar ya shiga yayi. Sagir bai ce komai ba har sai da ya zauna for some minutes sannan ya juya yana kallon Sadeeq É—in ya ce

"You good?"

Sadeeq ya juya ya zuba masa idanunsa da baka gane menene a cikinsu ya ce "Do I look good to you? You saw her right there, right in our class!"

Sagir ya gyara zamansa yana kokarin natsar da Sadeeq ya ce

" saw her, yes. But why are you reacting like this? That was days ago, bro"

"Days ago? Days ago she made me look like a fool! She made me feel like I was chasing after trash!"

Yayi ƙasa da murya da haushi mai tarin yawa ya ce

"And now she's here… in my space"

Sagir ya ja numfashi ya ce "Wannan makarantar ba taka ba ce kai kaÉ—ai Sadeeq. She didnlt beg to be here, infact naga ita tama riga mu farawa"

Sadeeq wani kallon yake masa ya ce "I swear, idan har zata zo ta raina min hankali kamar da… I won't take it this time, Dan ba karamin bata mamaki zan yi ba"

Sagir ya juyar da kansa gefe yana kallon waje ya ce da sassauƙar murya

"Let it go Man. You're better than this"

Sadeeq ya dafe kansa, yana jin kamar zuciyarsa na masa nauyi sbd har sannan duk abin daya faru na masa flashing, Ganinta, jin muryarta, yadda class É—in ya yi shiru tana magana ya hana shi sukuni

Sai ya furta a hankali

"She still gets to me… and I hate it"

__________

Azrah da Sarah suka karasa cafeteria suna tafiya a hankali, amma Azrah hankalinta baya tare da ita, tunaninta yana can a kan Sadeeq, Tana jin kamar zuciyarta tana saukowa da wani nauyi daban "Toh amma anya wannan shi ne? Da wannan jiji da kai, da wannan girman kai, har yanzu bai gama degree ba? Taɓe baki tayi tunawa yanzu suna same level

Duk da kasancewar abinci a gabanta, bata iya ci sosai ba. Sarah na kokarin sata dariya amma Azrah tana nan cikin tunanin da ta gagara gane kansa, a haka dai suka wuce lecture hall suka yi last lecture É—insu kafin duk suka wuce hostel.

______

Azrah tana isa hostel ta bude kofar É—akin su da key, ta tura kofar a hankali ta shiga, kamshin turaren Samira ya buge ta, fitowarta kenan daga toilet, tana goge gashinta da tawul.

Samira ta É—an É—aga kanta tana kallonta ta ce, 'Welcome back Azrah. Hope lectures sunyi kyau?"

Azrah ta zare takalmin ta, ta ajiye jakar ta sannan ta zauna a bakin gado tana kallon Samira har sai da ta ƙarasa goge jikinta sannan ta ce a hankali

'Samira... kin san wanene yazo class É—inmu yau? Ko kuma nace wa nagani a class É—in mu?"

Samira ta É—an tsayar da shafa man data Fara ta ce

"Wayee? Malami kuka yi É—an Nigeria?"

Azrah ta girgiza kai ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta "Sadeeq ne"

"Wait... Sadeeq? Which Sadeeq?! Samira ta tambaya da sauri tana dafe kirjinta

Azrah ta gyaÉ—a kai a hankali, "Wannan arrogant guy É—in da na faÉ—a masa jiki, Ashe ajin mu daya ne. Yana cikin sabbin DE students É—inmu... ashe degree ma bai gama ba, a haka yake wulakanta mutane kamar wani Acting President"

Samira ta zaro idanu ta ce "You're kidding me!"

Azrah ta yi tagumi ta ce "I wish I was, Gashi kwatakwata bayi da wani good mu'amalat da mutane, Kuma yanzu... guess what? Na fara jin kamar tsoronsa nake yi wllh"

Samira ta fara tafe hannu cike da al'ajabi ta ce "Matsala ta dake kenan, shiyasa ko wani banza yake taka ki mana, tsoron sa akan uban kine shi?"

Azrah ta gyara pillow ta kwanta da murmushi ta ce

"Wlh bansa meke damu na ba Nima Samira, ina son canza kai na sbd wannan eran da muke ciki, amma na komai"

Samira ta tsare ta da ido can ta ce "I know what's wrong. You're beginning to catch feelings shiyasa kike jin tsoron nasa"

Azrah bata san sanda ta miƙe zaune ba tana kallon Samira ta ce "haba Samira me kike faɗa ne haka? Imagine fah"

Azrah ta dafe kanta ta cigaba "Duk duniya babu wanda nake jin tsana irin wannan mutumin. And now I have to sit in the same lecture hall with him, mu fuskanci juna kullum, Samira I don't know how I'm going to cop"

Samira ta ce "You will cope. Saboda ba shi bane future É—inki, Education É—inki ne future, Idan ya sake miki wani abu, we report. Amma kar ki zubar da self-worth É—inki saboda irin halin sa"

Azrah ta zuba mata ido, cikin shiru mai zurfi Zata iya? Gashi ba wanda ta tsana kamar shi yanzu kuma tsoron sa ne take yi

_______

Sadeeq na zaune a kan gado, file É—insa a cinyarsa, yana cire wasu takardu daga cikin file É—in yana wurgi gefe da su kamar wanda amfanin su ya kare, wasu kuma yana zubawa idanu kamar dai yana son su karanta kansu ne, Sagir na tsaye a bakin kofar É—akin yana kallonsa, yana dai binsa da idanune yana kallon ikon Allah, shi dai yasa son ya gama waÉ—annan abubuwan ya tmby sa dalilin da yasa ya bar lecture hall kuma ya ki yin attending last lecture É—in

Yana gama ɗaukan wanda zai yi amfani da su ya saka wasu papers ɗin cikin envelope, ya rufe shi da sauri sai kuma ya miƙe tsaye, ba tare da ya kalli Sagir ya kama hanyar fita

Sagir ya daure fuska ya ce a hankali "Where are you going?"

Sadeeq ya juyo da wani kallo mai kaifi, idonsa sunyi ja dan ɓacin rai ya ce da tsawa "Department"

Sagir ya matsa gefe yana kallonsa, har ya fita Sagir bai ce uffan ba. sannan ya dawo ya zauna a gefen gadon, yana kallon envelope É—in da Sadeeq ya bata

"Me zai je department yi yanzu? Bayan pass 4 ne, lecturers duk yanzu sun fara tafiya" Sagir ya furta a hankali, yana jefa kansa cikin tunani

A bangaren Sadeeq kuwa, wani irin driving yake na marasa hankali a haka harya isa cikin school yayi parking sannan ya sauka ya shiga cikin department É—in wanda har ya fara shiru saboda rashin students dayawa a wajen, kallo É—aya zaka masa ka san cewa ba lafiya bane.

Yana isa department, sai ya tarar da yawancin lecturers É—in sun tashi. A haka dai a hankali ya karasa har gaba office É—in HODn su, yana gwaÉ—a buÉ—ewa yaji a kulle

Cikin takaici, ya juyo yana barin wajen ba tare da ya ce da kowa komai ba duk da yadda wasu suka bisa da kallo

_______

Daddare Samira ta fito daga bathroom daure da towel a jikinta tana goge sumar kanta da tawul, tana humming wata sabuwar wakar India. Azrah dake kwance a gadonta tana karanta wani PDF, ta É—aga kai da murmushi tana kallon ta.

Bata jima ba bayan ta gama shafe shafenta ta buɗe wardrobe tana bi da ido sai kuma ta zaro wata riga da wando crop top fitted da high waist trouser, tana jan zip ɗin sa a hankali, a haka ta saka, Sai kuma ta yi light makeup, ta sa turare me ƙamshi mai kama da vanilla flavor sannan ta gyara gashin kanta ta buɗe shi ya zubo akan kafadunta

Azrah ta tsaya kallon ta, fuska cike da mamaki da rashin yarda dan yanzu tasan dai dare ne

"Ina zaki haka Samira?" Ta tambaya a hankali.

Samira ta dan juyo da murmushi ta ce "Wani birthday party ne zamu je, it's just for tonight. Zasu yi celebration a Westrend Club ne"

Azrah ta zaro ido "Wai Club? Samira, da kin hakura kawai. Babu kyau ki fita da irin wannan shigar... kalli yadda kika yi fa, wannan ba dressing ba ne da ya dace da ke! Infact har a addininki"

Samira ta kalli kanta a mirror, sai ta É—an murmusa, ta matsa gaban Azrah ta zauna gefen gadon.

"Haba mana Azrah, it's only for today. You know I don't do this always… and besides, I need a little fun, wallahi semester ɗin nan ya fara damuna da pressure ne"

Azrah ta numfasa, tana kallon samira ta na girgiza mata kai ita dai bata son ta tafi

Samira ta miƙe, ta ɗauki small clutch bag ɗinta, ta ɗauki wayarta sannan ta saka a cikin Jakkan, ta wuce wajen takalma ta ɗauki wedge heels. Tana gab da fita ta tsaya ta kalli Azrah tace, "Ki rufe kofar idan na fita ta ciki... and don't worry, I'll be fine''

Azrah ba tace komai ba, tana kallon ta har ta fice. Azrah ta koma ta jingina da bango tana sauke numfashi. Sai kuma ta tashi a hankali ta nufi bathroom. Ta yi wanka sannan ta fito daure da tawul, ta zauna bakin gado ta shafa lotion duk wannan abun daga ke yi jikinta babu ƙwari

Bayan ta gama, ta saka modest pyjamas nata long-sleeved top da dogon wando. Sai ta kwanta kan gado, amma bacci yaƙi zuwa. Zuciyarta na ɗauke da nauyin tunani da damuwar Samira. Wani murya a zuciyarta na cewa

"It's her life, Amma ba zata iya barinta ba, Allah ka tsare mana zuciyarmu da abokananmu"

Washegari da asuba wajajan karfe 4 Sadeeq ya farka da wani irin nauyin zuciya da bai saba ji ba. Tunanin azabar yadda ganin Azrah kullum cikin class ɗaya yana masa nauyi, zuciyarsa cike da ƙiyayya da takaici, yana jin kamar yana shirin kamuwa da ciwon zuciya. A haka ya dinga sallah har asuba tayi. Ko breakfast bai yi ba, ya zare wata envelope daga drawer, yana rike da shi a haka har ya kai bakin kofa ya fita

Ba tare da sun gaisa da Sagir É—in ba

Ya isa department É—insu, ya tarar lokacin ne ma cleaners ke aikinsu, ya tsaya a bakin kofar yana kallon agogon hannunsa lokaci zuwa lokaci, zuciyarsa cike da fushi da tsoro, tsoron abin da zai fuskanta idan har aka ce babu mafita.

Bayan kusan minti talatin, aka buɗe Office ɗin, wajan da students zasu shiga su jira, kai tsaye ya nufi office ɗin HODn ganin an ajiye tag ɗin yana nan hakan ya fahimci ya shiga ta baya kenan, Ya tsaya gaban ƙofar ya kwankwasa a hankali, daga ciki aka ce "Come in."

Ya shiga cikin office É—in, yana dan lumshe idanu saboda AC É—in da ke kaÉ—awa da sanyi. HOD É—in yana zaune yana duba wasu files ya ce

"Yes, Mr. Sadeeq, what can I do for you this early?"

Sadeeq ya ƙara matso kusa, ya ajiye envelope ɗin a gaban sa. “

"Sir, I want to request for a departmental transfer"

HOD É—in ya É—ago kai da mamaki, "Transfer? At this time of the semester? Are you sure of what you're saying?"

Sadeeq ya dan gyaÉ—a kai, fuskarsa daure ya ce "Yes sir. I don't think I can cope in this department anymore"

HOD ya É—an janye files É—insa, ya juyo da kyau yana kallon Sadeeq ya ce

"Mr. Sadeeq, you are already registered, your Previous results, your class attendance, your course forms, all are already in the system. The only way you can change department now is to start afresh from 100 level. And that will be next academic year, not this one"

Cikin sauri Sadeeq yace "Sir, there must be a way, even if I lose some credit hours"

"No way" HOD ya katse shi. "System É—in nan rigid ne. Any attempt now is like starting over again completely. My advice? Stay, finish this semester. Next session you can apply early and get approval in time"

Sadeeq ya tsaya yana kallon HOD kamar wanda aka watsa ma ruwan sanyi. Bakinsa a rufe, zuciyarsa na bugawa. Bai sake cewa komai ba, ya É—auki envelope É—in shi a hankali ya juya ya fita daga office É—in kamar wanda ya rasa last hope É—ina.

Yana fita daga department É—in, lokacin an fara morning lectures ko nufar class É—in bai yi ba. Sai hanya ya bi da sauri ya koma gida, zuciyarsa cike da takaici. Yana shiga parlour ya jefa envelope É—in gefe ya zauna ya jingina da kujera, yana jin numfashinsa na tafiya da sauri. Kamar mai shirin fashewa da kuka amma haushinsa ya hana shi yin komai.

Jiddatulkhayr

08110615256

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.