Beyond The Veil Part 1 Novel Complete Hausa Novel
Reading file: Beyond The Veil Part 1 Complete Novel.docx
Chapter 76 of 79
Episode 78: The Beginning of the End
Mama na zaune can yamma tayi tagumi, Siyama ta zo ta zauna gefenta ta ce
"Mama kina jin likitan abin da ya ce yana damun Bappah?"
Mama ta ce "wai menene?" Ta ce
"Hmm wai damuwa da ciwon zuciya wanda mutum ke fuskanta bayan wata mummunar abu daya same sa, kamar tashin hankali, ko wani abu daya girgiza sa shine ya shiga wannan abun" Mama tayi shiru tana tunani sai kuma ta kalle ta da sauri ta ce
"Ai ya daɗe bai shiga ba, Ni sai yanzu ma nake kara tunawa, tun lokacin daya rabu da wancan kunamar shikenan yau lafiya gobe babu ai shikenan tunda haka ya zaɓa ma kansa ya je can ya karata yanzu da wanne zan ji? Da rashin abinci da bamu da shi ko da kuɗin jinyarsa?" Wata likita ta karasa tana kallon Mama ta ce
"Haba baiwar Allah, tun yaushe ake jiranki da ki kawo ko da wani abu ne a samu a fara basa kulawa amma har yanzu shiru.. kamar ma baki damu bane naga.. idan baku shirya bane É—auki mijinki ku tafi" Mama ta bi yarinyar da kallo, sai kuma ta kalli Siyama ta ce
"Gaskiya ba abin da zai sa naci bashi, idan kuma ta gagara sai dai yayi ta zama a haka, ai shi yaga daman shiga wannan halin" Siyama ta ce
"Uban me su Azrah suke da ba zasu bada kudin ba? Dole sai kin wani wahalar da kanki ne Mama? Kawai zan je na sanar da su nace su bada kuÉ—i mun kashe wanda zamu iya sauran kuma su cigaba" Mama ta ce
"Daya fi, idan kin sanar da su Ni zan koma gida dan banga zan iya zama a asibiti ba gaskiya".....
Karan shigowar message yasa ta dauki wayar tana buÉ—e sakon, sai kuma ta É—aga kai tana kallon Dada ta ce
"Dada ya shigo kuÉ—in, Allah ya saka musu" Dada da yanzu ta fara samun É—an karfi ta ce
"Har nawa ne ta turo?" Maman Amira ta ce
"Ai dubu É—ari ta turo" Dada ya fashe da kuka tana girgiza kai ta ce
"Allah musu albarka, ya nuna min aurensu, Allah basu maza wanda zasu kula da su harda mahaifiyar su" Maman Amira na Murmushi ta ce
"Amin Amin" Dada ta ce
"Idan kin huta sai ki tsiya min kayan abinci, wata satin kuma sai na sake komawa gun mai maganin nan, amma yanzu kira min Azrahn" Maman Amira na murmurshi ta shiga kiran layin Azrah, yana fara shiga ta miƙa wa Dada
"Hello Dadan mu" Azrah ta faÉ—a tana dariya, Dada ta amsa da
"Allah sarki 'yar albarka! Ke da kike fama da makarantar 'yar uwarki shine wannan watan zaki kara kuÉ—in da kike turowa?" Azrah ta ce
"Toh ai zaki yi magani Shiyasa, yanzu ya jikin naki kuma?"
Dada dake share hawayenta ta ce
"Alhamdulillah da sauki" Azrah ta miƙawa Umma, Umma bayan sun gaisa ta ce
"Ayyah Dada ina son na sake zuwa na duba jikin naki amma dake duk suna fita kuma nakanyi abinci kafin su dawo Shiyasa bana son mu bar gidan ba kowa sai Zahra tayi Hutu tukun nan" Dada ta ce
"A'a karki damu Bitti, yanzu ai jikin da sauki sosai ma, kawai kin san samun saukin ne sai a hankali" bayan sun yi sallama ta kashe wayan..
Almajirin su dake sakar gidan yana shara yaji ana knocking, ya ce
"Waye ne ? kofar a buɗe take" yau ne rana ta farko da Siyama ta fara shiga cikin gidan duk tsawon lokacin nan, ta karasa tsakiyar compound ɗin tana taɓe baki, Zahra da tun daga parlorn suka jiyo muryanta, wuff ta miƙe ta fita bakin kofar parlorn tana kallonta ta ce
"Ya aka yi?" Siyama ta ce
"Toh Ubanku ne bashi da lafiya kwance asibiti, mun kashe iya wanda muka ga zamu iya sauran idan kun ga zaku iya tohh, idan kuma ba zaku iya ba sai ku bari ya karasa mutuwan" Zahra tayi wani dariya ta ce
"Wato ubanmu ba naku ba? Well,sannan idan ya mutu kune ai abin kuka bamu ba tunda bamu sara ci, ko sha ko sutura ba" Siyama ta mata wani kallo tana jin yarda tafara boiling inside tace
"Idan kuka ga dama kar ku taimaka masa, ruwan ku" ta juya zata tafi, Zahra tayi saurin cewa
"Tunda har kuka zo neman taimako, ko nace bara ai shikenan za'a taimaka masa É—in ba dan halin ku ba" Siyama ko juyowa bata kuma yi ba ta fice daga gidan, dan ji take zata iya makure Zahra idan har ta tsaya É—in
Zahra na shiga parlorn Umma ta mata wani kallo ta ce
"Ke da waye?" Zahra ta turo baki tana kallon Umma sai kuma ta É—auke kai ta ce
"Wai ubanku ne bashi da lafiya yana asibiti sun kashe wanda zasu iya sai mu cigaba, haka ta faÉ—a min fa Umma, ai manners ne ta rasa" Umma ta ce
"Shine har hakan zai baki damar cecekuce da ita? Idan ke mai manner ne sai ki tura aniyarta tunda kuma Ubanku ne, ya shafe ku kuma"
Ta zauna tana kallon wani wajen ta ce
"Umma ai Ni komai nayi laifi ne a wajenki, baki ga laifin ta na yarda tayi magana ba sai nawa dana bata amsa daidai da tambayarta" Azrah data kasa É—auke kanta akan Zahra ta ce
"Bappahn ne bashi da lafiya?" Zahra ta ce
"Eh, kuma yanayin maganar inaga jikin ba wai da sauki bane" Azrah ta ce
"Wani asibitin kuma?" Ta ce
"Oho ai bata faÉ—a min ba" Azrah ta ce
"Matsalata da ke kenan, bansan yaushe zaki koyi tambayar mutum abu mai muhimmanci ba
Azrah ta kalli Umma ta ce
"Umma yaushe zamu je duba sa?" Umma ta mata wani kallo ta ce
"Ke da Zahra amma ko?" Zahra ta ce
"Ah toh, Amma banga dalilin daya sa zaki ce harda Umma ba, mune dai ya kamata" daga haka Azrah taja bakinta tayi shiru sai kuma ta miƙe ta ɗauki veil ɗinta tayi hanyar fita
Umma ta ce "Ina zaki kuma?" Ta ce
"Zan tambaye su ne, ai tunda suka mana magana kila abin yafi karfin su ne" Umma ta gyaÉ—a mata kai, daga haka ta yi hanyar waje..
Da sallama ta shiga cikin gidan nasu, Siyama da Habibah duk suna zaune, babu wanda ya amsa mata, ta ce
"Ai ko ba zaku kulani ba ai amsa sallar tawa wajibi ne akan ku ko?" Siyama ta ce
"Bayan maganar da Zahra ta gama gaya min, shine kike tunanin sake kula ku?" Azrah ta ce
"Toh ai naga ba Zahra ba ce anan, tunda na shigo nayi sallama ai sai kuji dame na zo" Siyama ta ce
"Toh muna dai ji ko?" Ta ce
"Ba komai bane sai dama ina so nasan wani asibiti aka kai sa sannan wani ward ne"
Siyama ta taɓe baki ta ce
"General Amadi Rimi specialist, wat kika ce ko me, Ni ban rike ba" Azrah ta juya ta ce
"Nagode" daga haka ta fita daga gidan, gidansu ta koma tana shiga ta samu Zahra ta daura girkin dare, ta shige dakinsu tana kallon Umma ta ce
"Umma bari inaga Ni zan tafi yanzu" Umma ta ce
"Zahra fah?" Zahra ta daga murya daga kitchen ta ce
"Ke kije amma Ni ina girki sai gobe In Shaa Allah" Azrah ta wuce dakin su ta É—auki jakkanta daga haka ta fita...
Azrah ta shiga cikin asibitin da saurinta kamar wadda ake turata, hannunta rike da jakarta, idonta cike da damuwa, tana isa bakin 1st ward kawai, ta hango Mama zaune akan kujera, suna haÉ—a ido ta É—auke kanta kamar bata son ganinta
Ta isa har inda Mama ke zaune, kafin ma ta samu damar gaishe ta
Mama ta tamke fuska ta ce
"Ki wuce can… likitan na jiranmu a office dinsa"
Bata ce komai ba, ta juya da sauri, zuciyarta na bugawa, ta nufi inda aka nuna mata, tana shiga ta zauna kan kujera jin ta gaji, bayan ta gaishe sa ta ce
"Ni ce 'yar malam Muhammadu… nazo ne dan biyan kudin asibitin"
Likitan bai É—ago ba har sannan ya ce
"Waye shi toh?" Ta ce
"Ga dai wanda suka zo tare tana can zaune"
Sai sannan likitan ya É—ago daga rubuce-rubucensa, yana kallonta da launin tambaya a idanunsa ya ce
"Dama kuna da kuÉ—in biyan ne kuka barshi yana galabaita?"
Azrah ta lumshe ido, wato ba'a ma fara ma bappah wani treatment ba? Ta daure ta ce
"A'a… ba tare muke zaune da shi ba, amma ni 'yarsa ce, don Allah likita… me ke damunsa ne amma?"
Likitan ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya daidaita muryarsa ya ce
"Patient É—in naku na fama ne da mental trauma"
"What!? Mental trauma kuma?" Azrah ta maimaita da fargaba, tamkar kamar bata ji ba
"Eh" ya ce, yana kallonta da tausayawa
"Wannan wata irin cuta ce da ke shafar tunani da yanayin hankali, mutum zai iya shiga wani hali na rashin gane inda yake, ko ya manta da abubuwan da suka gabata, wasu lokuta yakan rikice ne, ko ya zama mai shiru, zuciyarsa tana cikin firgici, kwakwalwarsa kuma ba ta iya daidaita tunani kamar da"
Hawaye Azrah ta fara sharewa, ta ce
"Amma likita meya ke haifar da hakan?" Ya ce
"Damuwa da shock, sai kuma yawan tunani" Azrah ta ce
"Don Allah likita… ku fara masa magani yanzu, ga ATM ɗina nan, ku ciro kuɗi ko nawa ne, kawai burina ya samu sauki"
likitan ya girgiza mata kai, ya ce
"A'a, zaki je unit É—in biyan kuÉ—i ne, su cire daga can"
Azrah ta miƙe, ta karbi bill papern a hannun likitan, ta fita da sauri ta nufi unit din, ta biya duk abin da ake buƙata, bayan ta gama, ta tsaya ta siya masa abinci, sannan ta dawo cikin asibitin..
Data isa ward É—in, wucewa tayi. ba tare da ta ko kalli Mama ba, ta buÉ—e É—akin da Bappahn yake ta shiga, lokacin har an É—aura sa kan medications, ta ajiye abincin a gefe, ta zauna kusa da Bappahn tana kallonsa da tausayi
Ba kaÉ—an ba Bapphan ya rame yayi baki, sai take jin bata kyauta masa ba, bata sauke hakkinta na 'ya akansa ba data bari har yayi going through, hawaye ta fara sharewa, a ranta tayi alkawarin komai tsadar kulawa, ba zata sake barinsa ya shiga haka ba
Motsin Bappah ya fara, ta kura masa idanu a hankali ya buÉ—e yana kallon saman É—akin, sai kuma taga yana motsa bakinsa, É—akin yake bi da kallo har idonsa ya sauka a kanta, ta karasa jikin gadon tana masa murmushi tare da ce masa Sannu, ya sauke idonsa kasa, yana kokarin tashi, ta taimaka masa harya tashi ya zauna, ta É—auki takeaway ta buÉ—e abincin ta ajiye masa akan cinyarsa, ta sake É—auko yoghurt É—inma ta ajiye masa ta ce
"Bappah ka ci, nasan kana jin yunwa" kallonta yayi sai kuma ya sake sauke kai, likita ne ya shigo hakan yasa ta mike ta fita
Ba Azrah ta bar asibitin nan ba sai pass 9pm, kafin ta karasa gida har 10pm yayi
Washe gari..
Azrah tana cikin tsaka da aiki a office ɗinta, duk tunaninta na wajen Bappah ne, tana Allah² ta gama aikin gabanta ta tafi asibitin yanzu, sai ga wani staff ya buɗe office ɗin, lokacin babu Sadeeq, yana kallonta ya ce
"Mr Alhassan yana kiranki, Miss Azrah"
Â
Tayi saurin gyara veil É—inta sannan ta miÆ™e tabi bayansa, ta nufi officen, tana shiga ta same shi tsaye, yana gyara takardu a saman desk.Â
"Sir, you called me?"Â ta tambaya
"Yes Azrah" ya ce, yana murmushi , ta gyaÉ—a masa kai, ya ce
"Zan tafi wani business trip na kwana biyu. And I want you to take over my position temporarily"
Azrah ta zaro ido sosai, bata ma san tayi hakan ba, sannan tace da sauri
"Okay sir… but I'm sorry to say why me, please? Ga MD Sadeeq, ga su Oga Mahmoud?"
Mr Alhassan ya yi murmushi, yana kallonta kai tsaye ya ce
"Saboda na yarda da ke, and I believe you'll handle things with sense and maturity"
Tayi shiru, zuciyarta cike da mamaki dan ita bata wani son fifitata da yake yi, sai kuma ta tuna zata samu hutu kwana biyu, kawai ta dan sunkuyar da kai ta ce
"Okay sir"
Sai kuma tayi saurin yin shiru dan bata so amsawa ba amma ya zata yi?, Hakan kuma in other hand ya mata, musamman ganin zata samu hutu daga matsin lambar da ke tsakaninta da Sadeeq kwana biyun nan, ta least dukkansu zasu huta
Mr Alhassan ya mike, ya kalleta cike da kwarin gwiwa
"You can take over, Miss" ya fada yana wucewa daga office É—in
"Okay sir" ta amsa, tana kokarin boye yadda take ji, sai kuma jiki ba ƙwari ta nufi kofa
Daga nan ta koma office dinta, ta tattara wasu takardu and other stuffs dinta, sannan ta koma zuwa office É—in nasa, tana shiga ta zauna, zuciyarta na dukan uku uku...
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.