Beyond The Veil Part 1 Novel Complete Hausa Novel
Reading file: Beyond The Veil Part 1 Complete Novel.docx
Chapter 40 of 79
Episode 40: The Shout That Shook The House
Washe gari, Gidan yayi É—an nisa da hayaniya, kowa na harkar gaban sa ne, Zahra na wanke wanke, Azrah kuma tana jefa É—an wanke, Habiba da Siyama suna can suma suna aikin su, Mama na aikin kwashe alalen siyarwa, sallama suka ji daga bakin kofar gidan duk suka É—aga kai da mamaki suna Kallonsa, ya shigo gidan kamar wanda aka koro sa, Habibah ta ce
"Laaa Yaya ne ashe" Siyama ta taɓe bakin tana cigaba da aikin da take yi ta ce
"Sai sanda yaga dama yake zuwa kuma banga alamar kuɗi yake zuwa nema ba tunda ko sisin sa ban taɓa ci ba"
Ya shiga gidan har zai karasa part É—insu sai kuma ya tsaya yana kallon Azrah dake jefa É—an wanke, zuba mata ido yayi wanda ita kuwa tana kokarin kaucewa daga É—aga kai amma ta gagara har sai data É—aga kai ta kalle sa, Mama da ganin haka yasa ta ce
"Kai Abdul, ko ka manta É—akin ku ne ban sani ba?" hakan yasa ya juya ya nufe su, yana mita ya ce
"Ai naga kamar basu iya gaisuwa bane" Mama ta ce
"To kai yanzu kaga alamar tarbiyya tattare da su ne?
gaishe da Mama yayi yana kallon kannan sa sannan ya kunduma musu zagi ya ce
"baku iya gaisuwa bane ku É—in ma?"
Duk suka Gaishe sa a takaice, ko amsa musu bai yi ba ya wuce ciki
Bayan su Azrah sun gama girkin su suka kai É—aki, suka yi breakfast É—insu duk tare, Umma na kallonsu ta ce
"Ina son magana da ku?" Duk suka tsaya da abin da suke suna kallon Umma da mamaki dan sun san ba karamin magana bane tunda har tayi sounding so serious, Azrah ta ce
"Yanzu Umma?" Umma ta ce
"Eh, amma ku kai plates É—in kitchen sannan" bayan sun yi haka duk suka zo suka zauna a gaban Umma, Umma ta É—auke idonta akan su tana kallon wani wajan ta ce
"Kuyi hakuri da abubuwan da nake boye muku, nasan baku jin daÉ—i, nima ko kaÉ—an bana jin daÉ—i" duk kallonta suke da mamaki, Umma ta cigaba ta ce
"Tabbas akwai abin dana ke ɓoye muku tun kuna kanana, akwai wani sirrin daya kamata Ku sani, amma bana jin zan iya faɗa muku yanzu.. amma zan faɗa muku ranar da zuciyata ta shirya, sannan ranar da zata bukaci gaskiyar, kawai ku sani, akwai abubuwan da baku sani ba game da Ni.. da kuma dangina, ina me baku hakuri ku daina damun kanku akan haka, Nima tunanin hakan yana saka Ni cikin kunci, kuma shine babban dalilin daya sa sometimes zaku kamani ina kuka a ɓoye" Umma ta karasa maganar cikin rauni wanda har kana iya ji daga muryanta
Duk kallon Umman suke cike da tausayinta, kamar zasu yi kuka haka suke ji, dan dagaske Umma na cikin rashin nutsuwa, Azrah ta ce
"Toh Umma kiyi hakuri yanzu kar ki kuma shiga damuwa, everything will be alright In Shaa Allah then'' Umma ta gyaÉ—a musu kai ta ce
"Ku yafe min ba zan iya faÉ—a muku yanzu bane, amma ranar da lokaci yayi zan buÉ—e muku komai, zaku san komai a ranar" Zahra ta ce
"Toh Allah ya kaimu lokacin Umma" Umma ta amsa da Amin tana kallon 'ya'yan nata cike da tausayinsu
Azrah ta miƙe ta fita dan zuwa tayi wanka, bata dade sosai ba ta shirya cikin atamfa da kuma hijab ɗinta, ɗakin Umma ta nufa tana kallon Umma tace
"Umma idan baki bukatar komai yanzu zamu iya tafiya kasuwar?" Umma tace
"A'a ban jin akwai abin da zan bukata, inma akwai ai zan yi" Azrah ta ce
"Toh ai bana son kina yawan fita ne saboda yadda Mama ke behaving, amma idan baki fita ba bata kalle ki ba balle ta gaya miki magaan" Umma tayi murmushi kawai, Azrah kuma tana kallon Zahra ta ce
"Ahm, Zahra tashi mu tafi" Zahra ta miƙe suka ma Umma sallama daga haka suka nufi kofa
Haka suka É—auki hours a kasuwa, suka nufi ainahin shop da Azrah ke siyayyar ta, suka masa list É—in abin da suke so, ya juya ya fara É—auko musu, Azrah kuma na faÉ—awa Zahra yadda zata yi da kayan, Mai shagon yayi dariya ya ce
"Yarinyar nan ke da azama kamar ba mace ba"
Azrah tayi dariya ta ce
"Neman halak da wuya ne dan haka nake yi da kwazo'' ya ce
"Gaskiyar ki ne, toh Allah ya saka ma neman mu albarka" suka amsa da Amin
Bayan sun gama siyayyar su, suka tare adaidaita saho suka yi ciniki sannan suka shiga, har kofar gida ya kai su
Bayan su shiga suka samu tashin Umma kenan daga bacci zata fita dan yin alwalar Zuhur, Umma na kallonsu ta ce
"Sannunku da zuwa" suka amsa mata, zama suka yi suka fara nuna mata kayan da suka tsiro, Umma ta ce
"Ma Shaa Allah, Allah sanya albarka a ciki" suka amsa da Amin daga haka Umma ta fita
Can yamma bayan sun kulla kayan da zasu kulla idan na yi ne kuma duk sunyi, suna zaune suna hira kawai suka jiyo murya ana sallama
"Assalamu Alaikum! Wai Akwai mutane kuwa a gidan nan?"
Zahra ta É—aga kai tana kallon Azrah tace
"Ya Fatima ce fah" sai kuma ta miƙe da sauri ta fita tana amsa sallamarta ta ce
"Ki karaso mana" Azrah ta bi bayan Zahra tana murmushi
"Ohh Fatima.. I missed you, ki karaso mana" ta faÉ—a cike da zumuÉ—in ganinta
Fatima ta harareta ta ce
"Sai kace da gaske kike toh Ni dai wajan Umma na zo" daga haka ta shiga cikin dakin
Gaishe da Umma tayi, Umma ta amsa cike da fara'a tana tambayar ta ya gida, bayan sun gaisa, Azrah ta ce
"Haba mana yanzu fushi kike da Ni?" Fatima ta ce "ai mutuncin ki yayi yawa ne Azrah"
Azrah tayi dariya ta ce
"Yauzu dai na baki hakuri toh" Fatima na Murmushi ta ce
"Nayi hakuri ba dan halinki ba sai dan kinci albarkacin Umma" duk suka yi dariya...
Bayan sun É—anyi hira Azrah da Zahra suka raka ta har kusa da gidan su sannan suka juyo
Bayan Magrib... bayan sun idar da sallan Magrib, suna zaune suna karatun Alkur'ani harda Umma, wani yaro ne yayi sallama hakan yasa suka É—an yi shiru Zahra ta ce
"Wa'alaikumus Salaam, me kake so?" Ya ce
"Wani ne yake sallama da Azrah a kofar gida" Zahra ta kalli Azrah da sauri, Azrah ta É—auke kai ta ce
"Kace bata nan" Umma tayi saurin cewa
"Kace tana zuwa" ya ce "toh" daga haka ya juya
Azrah tace "Umma Ni fah ban san shi ba" Umma ta ce "Eh ai idan kika fita zaki san sa, amma kawai daga magana sai kice baki nan" Zahra ta kama ta ce
"Ah tho, kika san waye ne? Kika san me ya kawo sa? Kila ma sako ne" Azrah tana turo baki haka ta miƙe ta ɗauki hijab dinta ta saka sannan ta fita
Bayan ta buÉ—e kofar gidan ta É—an leka sai kuma ta ga Mutumin yana tsaya, É—an calming kanta tayi tun kafin tayi magana yace
"Assalamu alaikum" ya É—an kalle sa sannan ta É—auke kanta zuwa wani wajan ta ce
"Wa'alaikumus Salaam" ya ce
"I'm sorry nasa kin fito ba tare da shiri ba ko?" Azrah ta ce masa "Uhmm" a takaice
Ya ce "Sunana Muhammad, tun kwanaki wajan shekara guda kenan yanzu na ganki amma ban samu damar miki magana ba sai yanzu da nake jin cewa nan ne gidan ku" Azrah without interest ta ce
"Ok, akwai wani abu ne?" Ya ɗan ƙalleta sai kuma ya ce
"Dama ina so ki bani dama ne if possible" Azrah ta ce
"I'm sorry to say already akwai sadaki a kaina, thank you" ya ce
"Kash.. but please can I get your number ko da gaisuwa ce sai muna É—anyi" tana murmushi ta ce
"Ai banda waya yanzu ne, thank you" yana kallonta ya ce
"Toh shikenan, Thank you too, sai na sake zuwa please" daga haka ya juya ya tafi ita kuma ta juya zata karasa cikin gidan, dama bata wani fita ba a bakin kofar ta tsaya, tana shiga cikin zauren kawai taji an rungumota ta baya, da sauri ta juyo kanta tana kallon Abdul da mugun mamaki, nan take ya toshe mata baki, kokuwa ta fara da shi zata kwace kanta amma ya jata zuwa backyard É—insu, har sannan Azrah na kokuwa da shi, tana samu ta É—an sauke hannunsa daga bakinta ta zunduma wani ihuuu wanda kusan kowa yaji ihun nata a gidan ta ce
"Waaaalllllll!!!"
Umma ta miƙe wanda da sauri wanda kusan tare suka mike da Zahra
Bappah daya shigo gidan kenan ba shiri yayi inda yaji muryan azrah
Kamar a mafarki Bappah ya Gwale ido yana kallonta a hannun Abdul baiyi wata wata ba yayi kansa a mugun guje ya fincikota sannan ya sauke wa Abdul wata a zaɓaɓɓen mari, bai bari ya dawo daga processing ba ya sake wanke sa da mari, Azrah data ja gefe tana kuka, sai ga Umma da Zahra suma sun yi wajan, tsayawa suka yi suna kallon ikon Allah, Mama da karasowarta kenan tayi sauri ta tare Bappah, Bappah bai san sanda ya jefar da ita gefe guda ba
Umma na kallon Azrah ta ce
"Meya faru?" Zahra sai huci take kamar zata caƙumosa dan yadda zuciyarta ke tafarfasa ita kaɗai tasan me take ji, a rayuwarta ta tsana taga an taɓo Azrah, a hankali Azrah ta ce
"Nima bansan me ke faruwa ba kawai ya toshemin baki yana laluba na ne" Bappah sai huci yake yana ma Abdul wani kallo
Mama ta fara salati ta ce "ji wata sharri? Yanzu ke ko kunyar mu baki ji zaki buÉ—e baki kiyi irin wannan sharrin?"
Bappah yana pointing É—inta yace "kina wajen ne abun ya faru? Kin lalata tarbiyyar yaro sai sanda yaga dama yake zuwa gida ana magana kice yana legas yana tara kuÉ—i ko? Ki jira Kiga hukuncin da zan É—auka akan sa wannan lokacin" daga haka Bappah ya juya zai bar wajan, da sauri Mama tasha gabansa ta ce
"Yanzu har ka yarda da abinda tace kenan?, bayan kasan yarinyar nan ba kunya gareta ba, ta tafi waje ta buÉ—e ido tazo ta kamasa shine har zata masa sharri kai kuma sai ka hau kai ka zauna"
Umma tayi wani murmushi ta kama hannun Azrah, Zahra ta ce
"Ihun ta aka ji ko nasa? Sannan tayaya za'a ce ita ta kama sa idan banda sharrin" sauke mata mari Mama tayi, Umma da har tayi gaba riƙe da hannun Azrah ta jiyo tana ma Mama wani kallo ta ce
"Karki kuskura ki sake É—aura hannunki a jikin 'yarta, dan ko Ni bana daura musu hannu balle wacca bata san wahalan su ba tace zata mare min su" zata yi magana strictly Bappah ya nuna Mama cikin ido ya ce
"Karda ki kuskura ki sake É—aura mata hannu" with shock Mama ke kallon Bappah, ya juya ya bar wajan, Umma ta kama hannun Azrah tayi gaba, Zahra ta fara tafiya ta ce "kuma Allah saiya saka min" tana kaiwa nan ta falfala a guje tayi gaba
Mama ta juya ta kalli Abdul da ko a jikinsa kuma babu alamun shi aka mara ta ce
"Uban mayasa ba zaka buɗe baki kama Bappahn naku magana ka ce ba kai bane itace ta fara kama ka? Sai kuma ka tsaya kamar saɓalota" ya ɗan taɓe baki ya ce
"Toh ai ba karya bane, tsaya ma tukun nan taya za'a ce zan buÉ—e baki nace wai itace ta kamani tayaya ma abin zai bada hankali" Mama ta sake baki tana kallon sa, ya mike ya karkaÉ—e rigar jikinsa ya ce
"Da kin wuce da tsayuwar da kika tsaya kika yi" daga haka ya ratsa ta ya wuce ta bisa da kallo har sannan kuma mamaki bai barta ba
Bayan Umma ta shiga É—aki da Yaranta har sannan kuma Azrah na sheshekan kuka, Umma ta ce
"Kuyi hakuri daÉ—in abun Bappahn ku bai goyi bayan su ba, ai Shikenan" Azrah ta share hawayenta ta ce
"Umma Kinga yadda yake taɓani ne? Yanzu ace babu kowa kuma fa?" Umma ta ce
"Æai isa ba kuwa, dan Allah ba zai basa sa'a ba" Zahra dake huci tace "Allah ya taimake sa da ace Bappah da wancar Matar basu kusa zai sha mamaki na wallahi" Umma dai bata ce komai ba
Can Zahra ta sake cewa ai
"Ni dake yasan bana masa wasa kuma ina da baki ai koda wasa baya min magana dan yanzu zan gwada banma gane sa ba, tunda bawai a gidan yake da zama ba
Wayan Azrah ne ya fara ringing, duk zaton ta Khalil ne sai kuma zarah ta miƙa mata ta ce
"Karɓa Dada ne ke kiran ki" karɓan wayan tayi ta kai kunne....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.