Beyond The Veil Part 1 Novel Complete Hausa Novel
Reading file: Beyond The Veil Part 1 Complete Novel.docx
Chapter 65 of 79
Episode 65: Friends or More
Tana fito daga office É—in, har zata tafi ganin Mr. Alhassan yasa ta É—an tsaya, daya karaso wajenta ya ce
"Toh Miss Azrah sai gobe ko? Akwai rules and regulations zamu baki gobe In Shaa Allah, amma ba'a zuwa mana 8am" ta gyaÉ—a kai ta ce
"Okay, sir. Thank you"
Juyawa tayi ta nufa wajen stairs, takawa take a hankali harta sauka, bata yarda ta kalli secretary dake gefen stairs tana waya ba, Miss Safiyya ta ja tsaki ganin ta wuce, haka kawai taji ta tsana wannan sabuwar ma'aikaciya É—in nan, daga haka ta wuce sama
Azrah tana fita, tayi sallama wa security personnel dake zaune bakin gate, a hankali ta fara tafi, wani mota ya tsaya gefenta, ta É—an kara sauri, taga motar ma ya tsake gaba, É—an tsayawa tayi ta juya taga waye ne, sauke glass É—in yayi yana mata murmushi ya ce
"Sister" ganin bata gane sa ba ta É—an yi jimm, murmushi ya sakar mata ya ce
"Naga kamar ke sabuwar ma'aikaciya ce a wajen mu" kai ta gyaÉ—a masa, ya ce
"Toh shigo na rage miki hanya, dan nan arean ba lallai ki samu abun hawa da wuri ba" ta girgiza masa kai ta ce
"No need sir, thank you" ganin ba zata shige yace "Alright, good night" daga haka ya kara gaba, Allah ya taimake ta taga wani Napep yazo wuce wa tayi saurin tsayar dashi.
Tana sauka a Napep É—in ta shige cikin gidan da É—an saurinta, Umma ta samu ta idar da Sallah ta zauna tana mikawa Umma appointment letter É—inta, Zahra ta shigo da gudu ta faÉ—a kanta ta ce
"Yeeeee, my sister" dariya tayi, Umma bayan ta gama karantawa tana kallon Azrah tana kokarin mayar da hawayenta ta ce
"Allah mun gode maka, Allah ka mana komai" Zahra tana kallon Umma ta ce
"Umma menene?" Umma ta girgiza mata kai ta ce "Babu" Azrah ta karbi papern ta mikama Zahra
Zahra ta buÉ—e baki da sauri tana kallon Yayar nata ta ce "Ni fah dan Allah Yaya ki tsiya mana mota, ai ko kuÉ—in account É—inki ya kare naga na aikin ki zai taru" Umma ta ce
"Ke baki da damuwa sai asiya mota Zahra?" Zahra ta ce
"Eh mana Umma, wlh so nake ina shiga idan zan tafi wani wajen" Azrah ta ce
"Zamu tsiya kuma ki shiga Zahra, amma ba yanzu ba, yanzu maganar makarantar ki ne a gaba"...
Bayan ta idar da Sallah Zahra ta kawo mata abinci, tana ci tana basu labarin yadda wajen yake, wayanta ne yake ringing, É—auka tayi ganin Suhaila yasa tayi receiving takai kunne tare da cewa
"Hello.. Anty Suhaila". Bayan sun gama wayan tana kallon Umma ta ce
"Umma Anty Suhaila ce 'yar Mummy, wai idan bana wani abu dan Allah na tafi gobe gidansu" Umma ta ce
"Allah sarki, Toh ya zaki yi da aikin naki kuma?" Ta ce
"Idan na taso daga aikin sai na tafi Umma, ko?" Umma ta ce "Toh Allah kai mu"...
Ita kaÉ—ai take zaune cikin Maza uku dake zaune a cikin parlorn nata, hira suke cike da nishaÉ—i, banda dariya ba abinda suke, kana ganinsu kasan suna enjoying moment É—insu, ga abinci da su drinks da suke ci suke sha,Farouk ya ce
"Kai Samira, kice kina kashe mijinki da girki masu daÉ—i haka?" dariya tayi ta ce
"Wai kai baka taɓa cin girki na bane sai yau? Kai Farouk fear Allah" duk dariya suka yi, Ahmad ya ce
"Kila dai bai taɓa bane, ko kuma tsanti yake yi, amma girki kam sai dai mijinki yayi hakuri haka wata rana zamu kwashe jiki muzo muci" suka sake dariya ta ce
"Ai sai ka biya Ni, amma haka kawai ba zaku sakani wahala ba, shima mijin nawa wata rana fita muke mu ci" Ahmad ya ce
"Kai Samira, amma ance baƙon ka annabinka fah" ta ce
"Sai ka kawo matarka na koya mata idan har da gaske kake" karan buÉ—e gate suka ji, Aliyu da tun É—azu bai ce komai ba ya É—ago yana kallonta ya ce
"Kee Samira kar dai mijinki ne yazo?" Ta gyaÉ—a masa kai ta ce
"Shine" ya ce "ina ba zai yi maganar ya ganmu anan ba?" Ta ce
"Toh me a ciki idan ya shigo ya ganmu hakan? What is it? Ai friends dina ne kuma bashi da say" Umar ya ce
"Ahtoh, kuma tare ya ganmu, sannan mu ba other room muke shiga ba balle yaji kishi ko ya raba tsakanin" sallamar Deen yasa duk suka yi shiru
Ya karasa cikin parlorn yana binsu da kallo, Samira ta miƙe ta karasa ta yi hugging ɗinsa ta ce
"Welcome back, Deen" murmushi yayi mata ya ce "thank you" duk da yadda yaga dressing ɗinta kuma ba mayafi amma ya daure, karasa cikin parlorn yayi suka fara gaggaisawa da shi, ya miƙe yayi hanyar ɗakinsa, Samira dake binsa a baya tana kallonsu ta ce
"Besties bari ina zuwa" sai da Deen ya tsaya babu shiri ita kuma ta kusan buge shi dama dab da shi take bin sa a baya, kallonta yayi sannan ya kalli mutanen dake parlon sai kuma ya wuce corridor tana binsa, yana shiga É—akinsa tana masa maga kawai ya buge kofar nasa ta karfi, É—an tsayawa tayi tana mamakin reaction É—insa sai kuma taja tsaki ta fasa shiga cikin É—akin ta koma parlorn, samun su tayi already sunma fara fita tana murmushi ta ce
"Okayy, tafiya ba sallama?" Farouk yace
"Nope, ai mijinki ya zo kuma Kinsan zai bukaci kulawar ki" ta ce
"Alright! Sai munyi magana" ta koma parlorn ta kwanta kan kujera ta É—auki wayarta ta fara Game, sai ga Deen ya fito kamar zai tashi sama ko da wasa bata kalli direction É—insa ba
"Uban me waÉ—annan kattin suke min a gida?" Ta tsinkayi muryan sa, ba tare da ko ta Kallesa ko ta bar abinda take yi ba ta ce
"Kamar ya kenan? Abokai na ne kuma sun zo tayani murna ne, sai me kake son ka sani?" Da wani irin expression Deen yake kallon Samira ya ce
"What?! Your friends kike faÉ—a min?" Kara volume É—in game É—inta tayi sannan ta ce masa
"Nace friends ai kaji Ni? Wait... Dan na bika a baya zan haÉ—a maka ruwan wanka shine zaka wani bugomin kofa?" Sai kuma ta tashi ta zauna ta ajiye wayan nata a gefe tana Kallonsa, kamar yadda yake kallonta
Ya ce "Friends fah kika ce min Samira? All my thoughts cousins dinki ne harda tsayawa mu gaisa ba tare da komai a raina ba but Besties da kika ce ya tsaya min and now... Kina faÉ—a min cewa Friends É—inki ne?" Ta ce
"And so what Dan nace maka friends É—ina ne? Karya kake so na maka? Ko wani abu ne dan friends É—ina sun zo gidana dan taya Ni murna" wani tsawa Deen ya mata wanda sai data É—an rikice tana kallonsa a tsorace ta ce
"Deen? Yau Ni zaka ma ihuu?" Ya ce
"Nayin Samira, don't tell me duk mazajen da suke zuwa gidan nan Are all your male friends?" Sai ya kama kansa ya fara nanata innalillahi wa'inna ilahi raji'un
Tsaki taja ta ce "Ji yadda kake magana? Yanzu idan wasu suka ji a waje É—auka zasu yi na kawo kwarto ne" ya ce
"Idan suka É—auka hakan karya ne? Ai kwarata ma kike kawo, kalli dressing É—in jikinki kuma kina zaune comfortable a cikin su"
Samira ta ce "Enough Malam! Ba zaka zageni na ɗauka ba, karka sake cewa na kawo kwarto, da wannan rayuwar ka ganni kuma ka yarda zaka aure Ni a haka, kai baka taɓa bina India bane har kawata ta bar mana ɗakin, kwanaki nawa kayi? Abu ta taɓa shiga tsakanin mu ne? Kai ma kasan wacece Samira, bana iskanci, amma ina da Male friends shine yanzu zaka fara min ihuu akan wani abu da bakomai bane" tana kaiwa nan ta barsa tsaye ta wuce ciki abinta kamar zata tashi sama, tana shiga daki ta faɗa kan gadonta ta fashe da kuka sosai....
Dada tana zaune da yaran kwabta da suke shigo mata ta miƙawa ɗayan yarinyar da take da wayo ta ce
"Ke, danna min lambar Azrah, jikata na india in nan ne" yarinyar ta karɓa tana murmushi ta nemo numbern Azrah ta ce
"Laaa, Dada ashe ma dazu ta kira" Dada ta ce
"Allah sarki, Ni nasan zata kira ai" daga haka ta kai wayan kunnenta ganin ya fara ringing
Azrah da har sannan tana basu Umma labari wayanta ya fara ringing, ganin Dada yasa tana murmushi ta ce
"Umma surukarkice" daga haka ta É—aga tana sallama
Dariya Azrah tayi jin abin da Dada tace, ta ce
"Fatan kin isa lafiya?" Dada ta amsa da "Lafiya Klau, gobe zani wancan kauyen idan Allah ya kaimu neman maganin nan, Bappahn naku bayan tahowata ya shigo ko ya muku magana?" Zahra takarɓe wayan dan duk suna ji, ta ce
"Chap, Dada wai yanzu ke dauka kika yi zai shigo ko ya mana magana? Sai dai idan wancan matar nasa bata nan" Dada ta ce
"Shikenan, ai idan tasan wata bata san wata ba, Ni dai Karku ƙullace mahaifinku dan Allah" Zahra ta ce
"Toh shikenan" daga haka suka yi sallama..
Washe gari tun asuban fari Mama ta gama duk wani abu da zata yi, tana kallon Habibah ta ce
"Dan Allah kiyi da jiki mana kije ki cewa zulai ta baki kuɗin Adashe na, jiya an wuni zuwa nemanta amma bata nan" Habibah ta miƙe tana guguni ta ce
"Haba Mama! Dan Allah bai yi safe ba?" Mama ta ce
"Dan ubanki tafiya zanyi kice min yayi safe" hakan yasa ta miƙe ta nufi kofar kamar mara laƙƙa, fitan Habibah nada wuya sai ga Sallaman Hajiya kaltume, Mama dake zaune kofar ɗakinta ta amsa, ta ɗaga kai tana kallonta ta gaisheta, bayan ta amsa ta ce
"Ta shi mu tafi, zama ai bai kama mu ba" ta ce
"Wai na kara kuÉ—in wajena yayi yawa dan kar ace ya gaza shine na aika Habibah ta karbo min É—aukan adashe na" Hajiya kaltume ta ce
"Matsala ta dake baki da planing ne, tun jiya me ya hana ki karɓa" ta ce
"Anje bata nan ne ai" Zahra data fito haÉ—a wuta, dan daura wa Azrah ruwan wanka kafin ta daura musu breakfast ko da wasa taki kallon direction É—in su, Hajiya kaltume ta ce
"Wancan ba ita bace shegiyar?" Mama ajiyar zuciya ta sauke ta ce
"Wannan kanwarta ce, ai duk sunyu tsayi, sai ma Kinga 'yar iskan zaki ga abinda nake magana, Uhmm ai ita da aure sai kuma lahira idan ana yi" Hajiya kaltume ta ce
"Ikon Allah, kice duk de da Uwar suke kama?" Ta ce "kwarai kuwa, barin 'yar iskan ba" daga haka sai ga Habibah ta shigo da sallama Mama ta mike ta ce
"Bani" mika mata kudin tayi ta ce
"Mama baki ga yadda ta dinga matsifa ba wai kamar tashin duniya na bita karban Kudi da sassafe" Mama ta ce
"Ita ta sani kuma, tunda ta bayar ai hikenan" daga haka su Mama suka fita.
Zahra na shiga daki ta ce
"Umma, Mama fah tafiya tayi ita da wancan Yayar nata" Umma ta ce
"Toh ina ruwanki" Zahra ta ce
"Ni a jikina nake ji ba Alkhairi bane tafiyar nan nasu, amma dai Shikenan" daga haka ta koma wajen girkin nata
Bayan Azrah tayi wanka tayi shirin ta cikin rigar Abaya tayi rolling, ta fito ta wuce É—akin Umma ta ce
"Umma zan tafi" Umma ta ce "Allah bada sa'a, ki kula da kanki, ki rike tarbiyyar da muka baki" Azrah ta ce "In Shaa Allah Umma" tana kallon Zahra ta ce
"Zahra ki É—auki ATM dina a pink handbag dina ki mana cefenan rana kar ki sake mana abinci ba nama" Zahra tayi salle ta ce
"Ai kuwa toh kaza zamu ci" Azrah ta mike ta ce
"Ke kika sani" Zahra na dariya ta ce
"Toh Ni dai zan saya harda shawarma" Azrah dai ta fita ba tare data kula ta ba.
Kamar jiya Azrah na shiga cikin kamfanin haka idanu suka bita har Office É—inta, tana haura sama ta ga Sakatariyar PA, hakan yasa ta ce "Good morning" ta yamutsa fuska ta ce "Fine" Azrah sai taga wani iri a fine a É—in data ce, kawai sai ta kama hanyar office dinta, haduwa tayi da Merry zata fito daga parlorn Office É—in hakan yasa ta gaida Azrah da ladabi,Azrah ta amsa mata da fara'a sannan ta shige ciki, cleanern daya gama aiki ya gaishe ta ta amsa masa shima da sakin fuska..
Merry ta shiga office É—in PA, Miss Safiyya ta ce
"Kin haÉ—u da wancan yarinyar?" Merry ta ce
"Yes Ma, she's so nice" tsaki Miss Safiyya tayi ta ce
"Fuck the Nice din, banza daga zuwanta baki ga an bata Office É—in MD ba, shekarunmu nawa anan? Sai ita za'a bawa, kalli yadda take wani jijji da kai irin gata Slay queen, sai wani dressing take kamar ba 'yar nan ba, ko yadda Mazan nan suke kallon mu a Mata yanzu zasu daina tunda suna kallon wannan fuskan nata data sha uwar bleaching"
Sauke ajiyar zuciya Miss Merry tayi, ta ce "Nikam gaskiya Banga wani abu game da ita ba, kuma ai dama daga ganinta kema kin san ba mate dinmu bane, Maybe she's from rich family ai ko daga kallonta ma, wata kila ma É—an uwan Mr. Alhassan ne dan naga jiya sau biyu tana office dinsa amma Banga wani abu bad ba, wanda ya fika ai dama ya fika " wani tsaki taja ta ce
"Dalla bar nan, Banga za'a yi wani abun arziki da ke ba" a ranta kuma ta kudurci niyyar shafawa Azrah bakin fenti a wajen, wanda har sai an korata, ko da sharri ne sai ta mata. Miss Merry tuni tayi gaba tana mamakin halin Miss Safiyya
Azrah kuwa a office ɗinta, bayan ta gama waya da PA daya faɗa mata wasu aiki da zata yi, hakan yasa taje ta karba, a zuwanta ta sake haduwa da Miss Safiyya, Miss Safiyya ta tamke fuskarta, abin ba kaɗan ba ya bawa Azrah mamaki, ta lura tunda tace mata zata zauna office ɗin MD na wucin gadi shikenan ta canza mata while da farko da fara'a ta karɓe ta...
Bayan ta gama aikinta, da aka tashi, ta tsari wani taxi ta faÉ—a masa address É—in gidan Mummy wanda Anty Suhaila ta turo mata not long ago
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.