Beyond The Veil Part 1 Novel Complete Hausa Novel
Reading file: Beyond The Veil Part 1 Complete Novel.docx
Chapter 52 of 79
Episode 52:Â The Day Before Convocation
Wani sanyi ne mai daɗin gaske ya yake sauka. Azrah ta gyara kwanciyarta amma jin surutun wasu a hostel ɗin yasa ta buɗe Idanunta wanda yake cike da bacci, Ta miƙe a hankali tana jan bargonta, karasa jikin window tayi, sannan ta ɗan yaye labulen taga. Rana ce ke shirin fito da sauri ta juya ta kalli agogo, tabbas yau sun makkara
"SubhanAllah," ta furta tana murza idanunta
"Ke Samira ta shi, mun makkara fah, almost 6am fah" ta faÉ—a tana hanyar ban É—akin, bayan ta fito ta hau kan sallayan. Bayan sun idar da sallan suka yi azkar É—insu na safe
Kamar karfe 7:10am... Samira ta ce "Azrah can't believe gobe ne fah..."
Azrah cikin murmushi "Gobe shine final show, Ni ba wannan bama muyi mu karya kar Sarah ta fara damun mu da kira ne"
Suka nufi kitchen É—in su, inda suka dafa tea da toasted bread. Duk da excitement É—in da ke zuciyarsu, amma sun san tabbas zasu yi missing juna"
8:30am..
Samira ta ce "Gaskiya ya kamata mu tafi yanzu, Sarah tace ta riga ta isa tun karfe shida..."
Azrah ta ce "Bari na É—auko card É—in SPA É—in daga drawer É—ina" daga haka ta nufi wajen drawern
Bayan sun gama shiryewa suka fita daga hostel ɗin. Suka kulle ƙofar ɗakin su. Tsayawa suka yi suka gaisa da wasu neighbors a corridor, sannan suka wuce.
Harabar hostel ɗin a cike yake da yan mata masu shiri especially grad students, Kowa a cikin wani yanayi ne na shauƙi da farinciki. Suna tafiya suna gaisawa da friends har suka fito bakin gate, inda suka kira bold, driver ɗin da zai kai su.
Bayan sun shiga motar suka kama hanyar Spa É—in. Samira ta ce
"I can't believe four years just flew like that" Azrah ta amsa da
"It's not just four years. It's four years of pain, growth, and strength" Samira cikin dariya ta ce
"Hmm... And friendship. Don't forget that" Azrah tayi dariya bata sake ce mata komai ba
Suna isa SPA É—in, suka fito daga mota suna murmushi. Cikin SPA É—in suka shiga, A can gefe suka hango Sarah ana mata foot massage.
Sarah ta daga kai tana dariya ta ce
"Sannu bestie! Kun jima wallahi, ku kara so nan" Azrah na Murmushi ta ja hannun Samira suka yi wajen tana cewa
"Mun makkarae ne fa. Kuma kar ki manta ni da Samira muna da salon delayed beauty"
Samira ta ce "kar ki min sharri Nikam" duk dariya suka yi
Staff É—in SPA É—in suka zo suka tarbe su da fara'a
"Sannu da zuwa Darlings. Ku biyo mu nan please"
Suka bi su ciki, inda aka nuna musu kujerun su, babu bata lokaci suma aka shiga musu gyaran fata
A cikin SPA, ana tsaka da scrubbing da body massage, bakinsu ya gagara shiru, kamar duk damuwar da suka sha na makaranta kamar basu yi ba
Tun kafin ayi nisa kowa sai kallon Azrah yake, su Sarah da Samira sun saka Azrah gaba da tsokana.
Sarah cikin dariya ta ce
"Toh wallahi Azrah ki fa shirya. Gobe kawai ki saka hulan grad sai kuma ki saka wedding gown a É—aura aure"
Samira ta ce "Khalil zai zo ya tafi dake kai tsaye gidansa kawai!"
Azrah ta tabe baki tana dariya
"Ku kuka sani, ko kuma Samira da ya rage 2 weeks bikinta ita ce za'a daura auren gobe ba"
Ana nan wasy ma'aikatan SPA É—in suka iso da wata body oil suka ce za su yi final moisturizing.Â
Dayar tana kallon Azrah ta ce "Wow! Your skin is so beautiful and clear!"
Wata kuma ta ce "Very soft! What do you use?"
Azrah ta kalli Sarah tana dariya ta ce "wlh babu komai daga Allah ne kawai"
Sarah ta kwafa ta ce "Mune fa da muke baki da kulawa" duk aka yi dariya
A haka har suka gama cikin annashuwa da dariya, suka wuce wani saloon dake kusa. Aka musu gyaran gashi, aka dora musu setting cap, gyara ba na wasa ba suka sha, Kowa na kallonsu kamar bride squad suka fito.
Bayan gyara, suka hau bold suka koma makaranta. Suka wuce students unit direct suka karÉ“i graduation gown É—insu wanda ke dauke da sunansu da logo na department.Â
On the way back to hostel
Suna tafiya suna hira sai wayar Sarah ta fara ringing. Tana dubawa taga "Mum Mie" ke kira. Ta É—aga cikin sauri.
Sarah cikin muryar farin ciki ta ce "Hello Mum…" bayan Mamanta ta faÉ—a mata wani magana sai Sarahn ta ce "What?? Already??â€
Ta kalli Azrah cikin farin ciki tana dariya sosai ta ce
"They said they've landed! Their flight just landed now at the airport!"
Azrah ta ce "Oh wow! That's amazing! Ma Shaa Allah"
Sarah tayi hugging Azrah tana dariya ta ce
"I'm off! I have to go and pick them up right now!"
Azrah ta rike hannunta ta ce "Please send my greetings to them. I can't wait to meet them again!"
Sarah na dariyar farin ciki ta ce "I will. Later today inshaAllah zan zo, ynx ki huta fa!"
Azrah tayi mata sallama, sannan ta juya ta ce
"Samira nagode sosai. Zan wuce sai anjima na shigo"
Â
Samira ta ce "Allah ya kaiki lafiya. See you later"
Daga haka ta juya su kuma suka cigaba da tafiyar su
Suna isa hostel din cikin gajiya da annashuwa, fuskokinsun nan ya kasa boye yanayin farin ciki da suke ciki, da jin dadin ganin sun kammala shirye-shiryen gobe.Â
Azrah da Samira suka shiga cikin dakinsu, suna dariya suna tunanin yadda gobe zata kasance.
Bayan sun cire kayan jikinsu suka saka kayan mai sauki, sannan suka tsaya gaban mirror.Â
Suka zuba ido suna kallon kansu, sabbin fuskoki, sabbin fata, sabbin kyawu.
Samira ta shafa fuskanta ta ce
"Azrah wlhi yau dai ace ki kai attending wedding sai dai a É—auka kece matsayin amarya"
Azrah ta tabe baki cikin dariya ta ce
"Haba Samira, ai gobe ma bikin ne amma bikin karatu, ba bikin aure ba"
Duk suka fashe da dariya
Azrah ta juyo ta kalli kanta a mirror sosai. Sai ta ji wani abu ya tokare mata zuciya a hankali ta zauna a bakin gado tayi tagumi sai kuma dan tayi distracting kanta ta janyo wayarta, ta danna video call wa Umma
Umma ce ta É—auka da murmushin da kullum ke kawo mata natsuwa.
Azrah ta ce "Assalamu Alaikum Umma...
Umma cikin fara'a ta ce
"Wa'alaikum salam diyata, yau kuma wannan farin cikin duk na gobe ne?
Azrah tace "Umma baki ga yadda na kara kyau bane ina shining?"
Umma ta ce "kin kara kyau fiye da kullum ma!"
Azrah ta murmusa
"Umma, wallahi yau mun gaji... Sai ki ga gyaran jiki da gyaran gashi da aka mana"
Umma ta ce "Allah sarki. Ina Samira?"
Azrah ta ce Gata nan…" ta matsa wayar a zuwa ga Samira, karɓa tayi suka gaisa da Umma sai kuma ta bawa Azrah wayan bayan sun gaisa
Sai ga Zahra ta leko daga gefe tana dariya ta ce
"Ahhhh! YaAzrah! What are you turning into like this? Wallahi you look like one Indian princess!"
Â
Azrah ta fashe da dariya ta ce
"Zahra dan Allah ki barni haka, har kin ga gyaran jikin kenan?"
Ta ajiye wayan tana nuna musu hannunta da fuskanta
Umma dai murmushi kawai take, zuciyarta na cike da alfahari
Ta ce "Wlhi da ace da hali ko muna da kuÉ—i, sai dai ki ganni a India yau. I swear I for wear sari mu haÉ—u mu É—auki hoto!"
Azrah na dariya ta ce "Ina kaunar ku sosai. InshaAllah gobe everything will go well"
Umma cikin taushin murya ta ce
"Allah ya sanya albarka Azrah a karatun ki, Allah ya cigaba da haskaka miki lamuranki kamar yadda yake haska miki ko da yaushe" Zahra ta turo baki ta ce
"Ni fah?" Umma na murmushi ta e "Duk kan ku nake nufi"
Azrah ta ajiye wayar a gefe, idonta ya kaɗa sosai. Gobe zata karɓi certificate na digiri… ta tsaya har zuwa wannan mataki.
Kwanciya tayi tana tunani, sai wayarta ta fara ringing. Tana dubawa taga Khalil ke kira.
Ta dan tsaya kafin ta dauka, zuciyarta na bugawa da sauri.Â
Tana daga wayar, muryarsa ta fito da saukin da ya saba dashi ya ce
"Princess fito waje…"
Azrah ta zaro ido
"Wani waje? Don't tell me ka zo India wai?"
Khalil da dariya ya ce
"Toh sai ki fito ki gani"
Kafin ta ce wani abu ya kashe kiran. Ta kasa motsawa na dan lokaci.
Samira wacce ke kwance a kan gadonta ta kalleta cikin mamaki ta ce
"Lafiya? Hope all is well?"
Azrah ta mike tsaye tana tabe baki ta ce
"Khalil yace yana waje…"
Samira ta fashe da dariya
"Wai, gsky yana da romantic touch Khalil din kin nan. Dama nima Deen dina ya zo mana! Amma yana can yana hidimar shirin bikinmu. Hmmm…" ta karasa da dariyar zolaya
Sai kuma ta ce "Toh bestie, tafiyarki lafiya!"
Azrah ta nufi wardrobe ta zaro wani vintage green veil, ta daura shi luff a kanta, cikin sanyi jiki ta fara tafiya, zuciyarta na bugawa da sauri, tanason ganin sa amma bata tsammanin yau yau ba
Tana karasa kofar hostel, sai tagan shi tsaye a can gefe, hannunsa a aljihunsa, yana kallon wasu students dake wucewa
Khalil ya juyo kamar ya ji fitowarta. Idon su ya hadu.
Ta karasa wajensa a hankali, murmushinta cike da jin dadi da hawayen da bata san na menene ba ta cs
"Assalamu Alaikum…"
Khalil ya murmusa yana kallonta cike da So ya ce
"Wa'alaikum Salam. Kinsan É—auka kamar karya nayi miki ko?"
Azrah ta girgiza kai tana dariya da hawaye ta ce
"Wallahi ban taba tunanin zaka zo yanzu bane…"
Khalil ya numfasa, yana kallo kamar yana jin tausayinta ya cw
"Bazan zo ba? Sai dai not your graduation. Na zo ne… tare da su Ammah da little sis dina. Da harda Grandma me kama dake amma bata jin daɗi ne yasa bata biyo mu ba"
Azrah ta zaro ido sosai tana kallonsa cike da dunbun mamaki ta ce
"You mean… your biological mother da sister?"
Khalil ya gyada kai
"Eh mana, Sun sauka a hotel yanzu. Na bar su can, nace let me come see your face first"
Azrah ta rasa me zata ce. Idonta ya cika da hawaye, ta lumshe su.Â
Khalil ya matso kusa kadan, ya ce
"Haba mana, common. Ki daina kuka, ba na so ki bata wannan glowing face dinki kafin graduation... "ya dan yi dariya
Ta daga kai ta kallesa, da murmushi mai cike da jin dadin kulawarsa.Â
Wannan mutumin... kullum yana shigowa rayuwarta a lokacin da take bukatar shi fiye da komai.
Bayan sun É—anyi hira na dan lokaci can ya kalleta da murmushi ya ce
"Yau da daddare, zan dawo… mu fita tare, just to refresh your mind before tomorrow. What do you think?"
Azrah ta tsaya, zuciyarta na bugawa. Ta rasa ko ta amince ko ta ki.Â
Sai dai kafin ta gama tunani, sai kawai ta samu kanta da gyada kai a hankali ta cd
"Toh... okay"
Khalil ya yi murmushi mai sauki ya ce "Good. Ki huta yanzu kafin Anjima na shigo"
Ya juya, ya bar wajen a hankali. Ta tsaya tana kallonsa har ya É“ace daga ganinta.Â
Zuciyarta cike da wani sabo daÉ—in da ba ta saba ji ba. Sai ta juya, ta koma hostel.
Tana shiga dakin, ta tsaya a bakin ƙofa tana kallon Samira wacce ke danna system
Azrah ta ce cikin mamaki da dariya
"Samira… can you imagine? Ammah da Intisar sun zo India! Purposely dan Ni?"Â
Samira ta juyo da sauri kamar wanda aka ce wani abu ta sake baki tana kallon ta sai kuma ta ce
"Kar dai ki cemin Maman khalil kike magana?"
Azrah ta jinjina kai, murmushinta na yawo a fuska ta ce
"Ita fa… ta zo. Intisar ma tana tare da ita, har yanzu na daina amsa mamaki"
Samira ta zare ido, tana kallonta ta ce
"Lallai… wannan matar tana sonki da gaske. Kuma ba ƙaramin so Khalil ke miki ba…" ta dan harare ta da wasa
"Gobe convocation, amma yanzu kam ya nuna miki ke ce First Class Heart Holder"
Azrah tana murmushi ta ce
"Hmm… ni dai kawai ina fatan Allah ya sa mu gama lafiya mu koma gida lafiya"
Samira ta ce ta janyo ta gefe ta ce
"Wlh ki rike sa hannu bibbiyu, dama ace nice uwar miji zata so Ni? Kalli yadda uwar Deen kwatakwata bata So na amma tana pretending sai kace Ni ban sani ba" Azraj ta ce "ki cigaba da addu'a komai zai wuce"
Bayan sallar Maghrib, Azrah ta jima tana addu'a da godiya ga Allah. Zuciyarta cike da nauyin farin ciki da sabuwar fargaba. Duk da gobe rana ce ta farin ciki, tana jin wani irin nauyi a ranta irin wanda ba komai ke kawo shi ba, sai deep emotions
Ta shige bathroom, tayi wanka cikin nutsuwa. Ruwa na sauka a jikinta kamar yana wanke damuwa da gajiya. Bayan ta fito, ta shafa lotion mai kamshi,
Sai ta ɗauko wani classy fitted gown mai hasken pastel pink, ta saka wanda ya lulluɓe jikinta cikin kyau. Sai ta ɗaura karamin veil mai ɗan shimmering simple but elegant.
Wayarta ta yi vibration. Khalil ne.
Â
"I'm outside" kawai ya rubuto.
Ta É—auki jakkan ta, ta juya tana kallon Samira tace
"Bye bye Samira, see you later
Samira ta É—aga hannu kawai tana kallonta da dariyar irin yau ga itama zata bi saurayi.
Azrah ta fita, heel É—inta na kara a corridor. Tana fita ta hangosa, tsaye a gefen mota, sanye da simple t-shirt da jacket, amma charming as always.
Idanunsu suka haÉ—u. Bayan ta karasa
Khalil yana buÉ—e mata mota ya ce
"Shiga My Queen"
Ta yi dariya, ta shige.
Shima shiga yayi ya tada motar suka bar makarantar. Babu wata hira mai yawa, amma every silence had meaning.
Azrah ta juya tana kallon sa ta ce "Toh dama ina za mu je ne?"
Khalil ya murmusa
"Wait and see"
Bayan dan tafiya, suka isa wani shahararren mall a cikin garin. Suna shiga ciki, ya nufa da ita wani luxurious gown store, Azrah ta juya kallonshi da mamaki. a ranta tana whispering ma kanta "Don't cry, please don't cry…"
Ya matso kusa da ita, muryarsa a hankali ya ce
"Pick any… I want you to look exactly like the Queen that you are tomorrow. You deserve nothing less"
Idanunta suka cika da hawaye. Ta mayar da kai gefe tana ƙoƙarin danne su. Ta zabi wani dark green long gown mai uban kyau, wanda ya bayyana simplicity na masu class.
Khalil ya É—auka mata gold heels da bag da suka dace da stones din kayan. Daga nan suka wuce Jewelry section, inda ya zabi mata wani slim gold necklace, light gold earrings da tiny gold wristwatch
Daga haka suka nufa wajan biyan kuÉ—i, bayan anyi clearing É—insu aka saka musu kayansu a wani designer bag, suka kai musu booth É—in mota.
#Jiddatulkhayr
08110615256
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.