Beyond The Veil Part 1 Novel Complete Hausa Novel
Reading file: Beyond The Veil Part 1 Complete Novel.docx
Chapter 32 of 79
Episode 32: The Unfamiliar Voice
Ranar wata Juma'a bayan azahar, Azrah ta dawo ɗaki a matuƙar gajiye, tana shiga ta fara buɗe warmers ɗin ɗakinsu amma bata samu abinci ba, kanta na sarawa kawai taje ta zube a gadonta da hijabinta har sannan a jikinta. Kallon Samira da take dariya ga waya ƙare a kunnenta tayi, taɓe baki tayi dan sana'ar Samira kenan, ji tayi tana cewa
"Baby wallahi ka raina ni" Samira ta faÉ—a tana dariya sosai
Sai kuma ta juyo tana kallon Azrah ta ce
"Ga Deen ɗina" ta kare maganar tana dariya "ku gaisa mana, ko da yake kina yawan ƙin yarda in baki labarinsa''
Azrah ta ɗan ware ido sosai tana kallonta ta ce "No need…"
"Come on!" Samira ta ce tana miƙa mata wayan nata, "he asked to say hi, Just for a second mn"
Cikin murmushi da rashin kuzari, Azrah ta karɓi wayar, ta kai kunnen ta sannan cikin nutsuwa ta ce
"Hello, sir! good evening''
A can É—ayan bangaren kuwa, muryar saurayin ya amsa da very calm voice É—insa ya ce
''Peace be upon you, kawar Samira, Ni dai na gaji da yawan jin sunanki kullum a gun Samira, Finally yau dai, na samu zan gaisa da ke"
Azrah ta tsinkayi zuciyarta ta buga 'dimmm' Muryar… kamar ta ta san sa, tabbas tasan me wannan muryan, tunanin me murya ta fara tana son figure it out ne amma ta kasa, Muryar ba sabuwa bace a kunnenta, itakam har tama manta cewa waya take yi kuma har sannan zuciyar nata bai daina tsinkewa ba, muryansa taji wanda ya dawo da ita daga duniyar tunanin data faɗa, murmushi kawai tayi, tana kokarin ɓoye rikicewarta
Deen ya ci gaba da cewa
"By the way, kina huta wa ko? Samira ta ce min kina stressing kanki sosai, Please, don't do that, You won't help anyone if you break down''
Azrah ta ce a hankali ''Thank you. I'll try''
"But… muryarki tana da daɗi sosai har yafi na kawarki'' Azrah ta juya ta saci sallon Samira dake shirin fara haɗa musu lunch, sai kuma ta ɗauke kai bata san sanda ta kirkiri murmushin ba
Kafin ya ƙara wani abu, Azrah tayi saurin katse shi da ɗan dariya marar kuzari
''No, thank you''
Yayi dariya a can bangaren ya ce
''Ko dai wayar a handsfree take ne? Naga kamar baki son magana sosai''
Sake Satan kallon Samira tayi sannan tayi kasa da murya ta ce
"Please stop, ba zata ji daÉ—i ba"
Wani murmushin yayi ya ce
"Okay, dole zan zo ko saboda ke Azrah"
Azrah da zuciyarta ke bugawa tayi saurin cewa "No... Thank you" daga haka ta cire wayan daga kunnenta ba tare da taji me zai sake cewa ba ta karasa wajan da Samira take zaune ta miƙa mata ta ce
"Samira, gashi mun gaisa" Samira na Murmushi ta karɓi wayan daga hannun Azrah
Azrah ta zauna bakin gado tayi tagumi ''Where have I heard that voice before?'' Ta fada cikin zuciyarta, tana bin kowane kusurwa na memories dinta da tunanin inda wannan muryar ta shiga rayuwarta a da
Samira kuwa ta cigaba da dariyarta kamar ba ta lura da halin da Azrah ta shiga ba, Amma Azrah… zuciyarta tuni ta dau wani sabon nauyi, Kuma bazata iya bayyana shi ba
Bayan fitar Samira, Azrah ta kwanta. Amma a zuciyarta tana nan 'taɗaɗɗen tunani' tana ƙoƙarin tunawa inda ta tsɓa jin wannan murya... amma ta rasa.
Lumshe idonta tayi, zuciyarta na bugawa da ƙarfin da bata san dalilinsa ba
*****
Wani babban parlour ne mai É—auke da duk wani kayan more rayuwa ta duniya, yalwa da kuma peace, Fentin bangon cikin parlorn launin cream, sannan gefe guda kuwa wall paper ne, kujeru masu launin fara kal sai wasu kuma Black, da agogon zinariya dake manne a bangon É—akin, ana hango manyan framed photos na iyalin a bango tun daga bakin kofa, A tsakiyar parlorn kuwa wani dattijo ne zaune a kan wani resting chair, yana sanye da farar jallabiya da hula, yana lumshe ido lokaci zuwa lokaci wanda hakan yasa baka gane wani yanayi yake ciki, hannunsa da yake saka wa lokacin zuwa lokaci yana É—iban fruit salad daga cikin glass bowl da ke gefensa
A gefe guda kuma matar sa ce wanda ake kira da Ummi, mace mai kamewa da natsuwa, tana zaune a kan sofa tana kallon su cike da kauna. A gaban dattijon kuwa, akwai samari biyu da suke suna zaune a kan carpet, duk da girman su, alamun cewa suna gaban mahaifinsu da girmamawa
Abbah ya gyara zama, muryarsa ya fito da karfi amma cike da kulawa dan hakan ma alamune na ransa ya fara ɓaci ne dan jayayyan da suke son masa
''Ku saurara Ni da kyau, dole ne ku koma makaranta na ce, Ku maza ne, ba za ku zauna da tunanin cewa yanzu komai ya ishe ku ba a rayuwa ba ko baku bukatar komai, A'a, Ilimi ba ya ƙarewa''
Wanda yake zaune kusa da Abba ne ya ɗago kai, yana mai cike da rashin jin daɗi amma yana ƙoƙarin bayyana ra'ayinsa cikin mutunci da kuma girmama Mahaifin nasa, baya so ya buɗe wani door da abokinsa ma zai samu har yayi jayayya da mahaifinsa, ya ce
"I'm sorry to say this Abbah… amma yanzu fa, ba lallai sai mun koma physical school ba, Zamu iya yin online classes, kuma we'll still graduate successfully''
Abbah ya masa wani kallo yana mai harararsa, sannan ya girgiza kai ya ce
"You're very stupid for even thinking like that! Makaranta nace, kuma sai kun koma da ƙafafunku, Ya zaku ce kuna da kamfani da zaku jagoranci amma diploma kawai ke hannunku? Is that what you'll present to the board? Ko dan kuna ganin kuna da gadon dukiya shiyasa baku ganin bukatar ƙarin ilimi, ba certificate kaɗai nake so daga gare ku ba harta ilimin ina so ku samu?"
Sagir wanda tun farko bai É—ago ba ya É—an gyara zama, sannan da ladabi ya ce
"Toh Abbah… zamu koma, ee understand"
Ummi ta ajiye bowl É—in hannunta a gefe, ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce cikin natsuwa
"This is for your own good ne Ilimin shine zai sake baki daman shiga cikin manyan masu companies kuna represent mahaifinku, ba zai É—auke muku matsayi ba sai ma ya kafa muku daraja da kuma karfafa ku a gaban duniya, Hakuri za ku yi, ku je ku kammala karatun ku akan fannin da ya dace da ku sannan ku samu certificate É—in degree"
É—ayan saurayin ya ce "In Shaa Allah Ummu zamu koma, hakan gaskiya ne kam"
Ummi ta juya tana kallon kofar É—akin Hajara tana kwala mata kira "Hajara!"
Sai ga wata yarinya mai kimanin shekara 20 ta fito da sauri, tana sanye da apron tana
"Na'am Ummi'
Ummi ta ce "Ashe ma kina kitchen, toh je ki haÉ—awa 'yayanki lunch, kinji ko?"
"Toh Ummi" ta amsa cikin sauri
Tana wucewa sai saurayin ya tashi yana kallon mahaifinsa da girmamawa ya ce
"Abbah zamu iya tafiya ?" Kai ya gyaÉ—a musu ya ce "Eh zaku iya"
Ummi ta ce "Ina kuma zaka bayan Hajara zata saka muku abinci" É—an murmushi yayi yace
"Abu zan karɓa yanzu zan dawo"
kafin ya fice daga parlorn yayin da abokinsa ya biyi bayansa, zuciyarsu cike da tunani… amma sun san wannan shawarar da Abbah ya kawo yayi daidai dan suma jin daɗin rayuwa ne ke mantar da su.
Yayin da kwanaki ke tafiya, test da assignments na ƙaruwa, amma hakan bai hana occasional calm moments tsakanin Azrah da Khalil ba
Kamar kullum har lecture hall ya raka ta sannan ya zauna a cool down dake gaban hall É—in har sai da suka gama lectures suka fito, Azrah da murmushi ta karasa inda yake zaune ta zauna tana maida numfashi ta ce
''Exams mutum zai fara Monday amma su wani takura sa da lectures ko ya suke so muyi copping"
Sake baki Khalil yayi yana kallonta cike da mugun mamaki sai kuma yayi murmushi bai ce komai ba, duk shiru suka yi suna shan iskan wajan can Khalil ya ce
"You always act like you have 10 children to feed back home''
Azrah bata san sanda ta fashe da dariya ba, ta ce
''I'm feeding more than that dreams, expectations, and fear of failure''
Khalil yayi shiru yana kallon ta, kullum yana son tambayar ta game da tarihinta amma sai ya ƙasa, yanzu ma yaji yana son sanin komai akanta sai kuma yaji ba zai iya tambayarta ba
***
Kwance take a kan gado tana bacci irin na gajiya, dan har zazzaɓi ta fara ji bata ma san sanda baccin ya ɗauke ta ba, sai ƙarar wayarta da ke ta ruri kamar zata fashe ya farkar da ita, ta jayo wayar a hankali, har sannan kuma idonta a lumshe yake, tayi receiving call ɗin Khalil, ta gyara kwanciyar ta tana kokarin maidawa jikinta kuzari kafin ta ce
"Hello" muryarta na nuna alamun daga bacci ta tashi
"Are you okay?" Khalil ya tambaya, muryarsa cike da damuwa
"I'm fine… just tired, still studying'' ta amsa a hankali
''Azrah… you need rest, You've been pushing yourself too hard, Exams ba sa bukatar ki rasa lafiyar ki pls*
Ta ɗan murmusa, da wani ƙarfi da bata san ina ya fito ba ta ce "I'll rest after the exams, I promise''
"You always say that'' ya faɗa ƙasa ƙasa, amma cike da kulawa ''Anyway, I brought some food, I'm coming to the usual spot ki fito ki same Ni a wajanll
Bata ce komai ba, kawai ta sauke ajiyar zuciya. Bayan mintuna kaÉ—an, ta yaye duvet É—in sannan ta buÉ—e idonta cike da karfin hali,
toilet ta wuce ta wasa ruwa sannan ta fito ta sanya Abaya, Studying bag ɗinta ta ɗauka sannan isa inda ya ce mata, ganin baya Nana ta buɗe littafi ta fara karatu, can taga Khalil ya nufo ta da leda a hannu, yana karasowa ya durƙusa a gabanta ya ajiye mata abincin yana mata murmushi meanwhile yana leƙa idonta
"You skipped lunch again, right?"
Ta É—an yi murmushi ba tare da ta amsa ba, ya ce
"Azrah... please, just eat something"
Da kyar ta É—auki spoon ta fara ci, tana ci tana duba nots dinta Khalil ya girgiza kai kawai yana kallonta cike da mamaki
*****
Zahra da ta shigo cikin gidan da sallama ta samu Bappah yana alwala anan compound, turo baki tayi dan bata É—auka ma zata gansa ba tana karasa inda ya ke, ta ce
"Bappah ina wuni" a dakile ya amsa mata da lafiya, babu ya school ko ya hanya nothing more, kuma ya bata amsar ma ba tare da ya kalleta ba, Zahra ta ce
"Bappah ko dai laifi na maka ne da har baka son gani na ballai ka tambaye ni ya school da kuma tests tunda test week muke kuma ka sani" Bappah ya É—an kalle ta sai kuma ya É—auke kansa ya ce
"Dan Allah tashi ki wuce ɗaki kina cika min kunne kuma hakan ciwon kai kike saka min" with shock Azrah take kallon Bappah, iya saninta Bappah koda wasa baya ƙaunan ɓacin ranta amma ji abin da yake ce mata
Mama ce ta fito daga É—akinta tana É—an wake wake da alama dai ko ta fahimci me ke faruwa ko kuma kawai dai tana son maida magana ne, kallo É—aya tayi wa Zahra ta ce
"Kema ai Kinsan ba'a shiga gonan mai unguwa ko?" Zahra bata sake kallon direction É—in Mama ba kawai ta shiga É—akin Umma bayan sun gaisa ta ce
"Umma Nikam ko Bappah aljanun garesa ne? Umma ta dinga kallon ta da mamaki can ta ce
"Zahra amma tafiyarki kuwa? Toh ai kece ma wanda ya kamata ayi wa wannan tambayar?" Zahra ta ce
"Allah kuwa Umma, Ni abun Bappahn ne yake bani mamaki, wani lokaci Kiga yadda yake damuwa da damu abin ban sha'awa amma tunda Dada ta koma shikenan kuma halinsa na da ya dawo sabo fil fah" Umma ta ce
"Toh bana son na sake jin wani magana daga bakinki kwatankwacin wannan ya fito, kinji?" Zahra ta miƙe tana turo baki ta nufi ɗakin su tabar Umma a ɗakinta
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.