Complete Hausa Novels

Beyond The Veil Part 1 Novel Complete Hausa Novel

Reading file: Beyond The Veil Part 1 Complete Novel.docx

Chapter 44 of 79

Episode 44: The Crossing Point

Cike da tashin hankalin Siyama ta ce "Mama! Mama ina kike ne wai?"

Ganin kamar Mama bata nan yasa Siyama ta zauna kamar wadda aka hankaÉ—ata ta ce

"Habibah kin ga wannan motar kuwa? Wannan ba irin motocin unguwar nan bane fah, ace Mama na raye wani ya zo ya tsaya wa Azrah fa!?" 

Habibah ta ce "Naga sanda yake miƙa mata abu fah, Tabbas akwai wani abu a kasa dan ba kowa ke zuwa wa yarinya gida a irin wannan unguwar da irin wannan mota ba kai tsaye ba, wani mai kuɗin ne zai kula 'yar talakawa idan ba wani abun yake kawo sa ba"

Mama ta shigo rike da kaya a hannunta, tana kallon su ta ce, "Lafiya Nagan ku haka ?"

Habibah tayi saurin cewa  "Mama wallahi akwai abin da muka gani zauna ki ji, Wani mutum ne ya zo a babban mota wajen Azrah"

Mama ta kafe su da ido, taji jinta da ganinta ya É—an dauke, can ta ce a hankali "Kun tabbatar?"

Siyama ta ce "Eh Mama, a layin nan fah ya parka motar, can kofar gidan Maman shafa'afu ya tsaya, harda mika mata wani abu, ta karɓa tana murmushi"

Mama ta ajiye kayan hannunta kamar an zuba mata ruwan sanyi, tayi tagumi sai kuma ta fara girgiza kai ta ce

"Ni Uwani ina da rai har wani zai sake zuwa wajen Azrah? Inaaa wannan sai dai a mafarki"....

Azrah ta gama saka kayanta cikin trolley, tana dubawa don tabbatar da babu abinda ta manta. Sai ga Umma ta shigo tana rike da leda a hannu, ta ajiye ta a gefe ta ce

"Gashi nan Azrah. Na san abubuwan nan zasu miki amfani a India kafin ki samu acan, Citta ce, yaji, kanwa, da kuka, sannan ga kaninfari da tafarnuwa ma a ciki"

Azrah ta rungume Umma da godiya a fuskarta "Nagode Umma, Allah ya saka da alkhairi."

Umma ta zauna a gefenta, ta dauki wasu kaya cikin trolley din, ta ce

"Amma har yanzu baki iya jera kaya ba Azrah. Duba yadda kike barin space kamar wanda zata dawo gobe. Ki bari na nuna miki yadda ake jera kaya irin na tafiyar nesa"

Suna cikin haka sai ga Zahra ta shigo tana kallon su da murmushi, ta rike ƙugu tana cewa

"Iyyyeee! Kayan tafiya ma sai Umma ce ke jera miki? To sannu yar gatan Umma"

Azrah tayi dariya "Ke ai kin sani, ko ban fada ba Ni 'yar gatan Umma ce"

Umma ta ce "Ina ruwanki da mu?

Dole na taimakawa É—iyata"

Suka yi dariya gaba É—aya, cike da annuri

Daga haka suka fita zuwa dafa abinci tare a kitchen, suna cikin girkin Azrah ta ce da Zahra cikin taushin murya

"Zahra wlhi duk da farin cikin tafiyar nan, gaba É—aya inajin wani irin a zuciyata, taya zan bar Umma cikin wannan sabon yanayin da Bappah ya tsiro da shi, Gaskiya ina jin tausayinta matuka"

Zahra ta tsaya tana kallonta, ta ce

"Kada ki damu Ya Azrah. Ki je ki yi karatunki. Kila Allah yasa in kika gama kika fara aiki Umma ta samu sassauci, Kuma kin san ni, baki na baya shiru. In shaa Allah ba wani abu zai kuma faruwa. Nayi niyyar tackling komai da kaina"

Azrah ta juyo tana kallon Zahra da murya kamar mai shirin kuka, "Nagode sosai Zahra. Allah ya miki Albarka, ya kuma cika mana burukanmu"

Bayan sun gama girki, suka shigar ɗaki suka zauna suna ci dukkansu a plate ɗaya suna ɗan hirar su gwanin sha'awa, Zahra ta dauko wayar Azrah wadda ke ta ƙara "Samira ce" ta faɗa mata tana miƙa wayar da murmushi a fuskarta

Azrah ta karɓa, tayi picking ta kai kunnen ta "Wallahi dazu nayi ta kiran ki baya shiga" ta faɗa

"Eh, dazu sun kashe WiFi ne" cewar Samira daga dayan bangaren na wayar, ana jin muryarta cikin nishadi "Yaushe ne zuwanki yanzu?"

"Gobe da safe zan tafi Abuja, da yamma kuma zamu tashi In Shaa Allah''

"Allah ya kawo ki lafiya kawata" Samira ta faÉ—a

"Amin, nagode"

Samira ta ce "Kin san an canza mana hostel?"

Azrah ta ce "Haba dai!"

"Wallahi, Na gama mana komai fa É—azu, sai kin zo dai zaki gani yafi namu na farko komai"

Azrah ta yi godiya sosai, sannan suka yi sallama, ta daura kanta a cinyar Umma tana jin sanyi a zuciyarta, duk da shirye-shiryen tafiya da excitement É—in shiga 200 Level ta ji wata damuwa ce ke danne zuciyarta

Duk suka yi shiru kowa da kalar tasa tunanin, Bappah ya turo ƙofar ɗakin, ya tsaya yana kallon Azrah ya ce

"Ke Azrah, tashi kije ki faÉ—a wa Mama tafiyar ki gobe ne, kar sai gobe kice zaki mata sallama"

Zahra ta ɓata fuska ta ce ƙasa ƙasa "Hmm tabdijam…"

Bappah ya fice daga É—akin, Umma tama Zahra wani kallo ta ce "Sannu mara kunya, itama ki zugata ki huta kawai"

Zahra ta kama bakinta "Nayi shiru" ta faÉ—a

Azrah ta miƙe jiki a sanyeye Zuciyarta cike da rashin kwarin gwiwa ta fita zuwa dakin Mama, da sallama ta shige, Mama na zaune da 'ya'yanta, Siyama da Habibah suna gefe suna hira da dariya

Azrah ta zauna da ladabi, ta gaishe ta Mama ta amsa da kyar tana kallon wani waje "Dama gobe zan tafi makaranta ne" Azrah ta faÉ—a a hankali

Mama ta yi kamar bata jita ba. Can kuwa ta miƙe ta shige ɗakinta kamar bata da buƙatar ci gaba da zama a wajen,  Siyama da Habibah suka cigaba da dariyarsu da hirarsu kamar Azrah ba ta wajen

Azrah tayi ta zama har kusan minti biyar kawai ta miƙe tana kallo Siyama ta ce "Sai da safe"

Siyama ta kalle ta da wani wulakantaccen kallo ta ce "Sai kace mayya, ki tafi mana"

Azrah bata ce komai ba duk da kalaman sun taɓa ta, ta juya ta fita, cikin zuciyarta tana ta addu'ar Allah ya karesu da kiyayyar mutane da hassadansu

Tana shiga É—aki, Umma ta kalleta ta ce "Kin mata É—in?"

Azrah ta zauna a ƙasa cikin sanyin murya tace "Hmm, ai ko kallona Mama bata yi ba"

Zahra ta kyalkyale da dariya ta ce "Madallah! Me ya kai ki tun farko?" Sai ta kalli Umma ta gumtse dariyarta

Umma ta mata wani kallon hakan yasa ta mike ta ce "sai da safen ku" Azrah ma ta miƙe tabi bayan Zahra tana ma Umman sai da safen ita ma

Washegari da safe, Umma da kanta ta daura girki. Kamshin abincin duk ya cika ko ina, Azrah na gama shiryawa, ta zaune tana gyara travelling document dinta a cikin jaka, Bappah ya shigo cikin É—akin yana kallon agogo ya ce

"Kiyi sauri ku gama breakfast kafin nan zan je na taho da mai taxi" daga haka ya juya ya fita ba tare da jiran amsar su ba

Umma ta kalli Azrah ta ce "Kiyi sauri ki samu ki yi breakfast kafin Bappah'n naku ya dawo"

Azrah ta zauna tana ci, duk taste ɗin abincin taji babu wani taste a bakin ta, gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi, sai ga Bappah ya dawo, ya turo ƙofar ɗakin yana kallo ta kai tsaye ya ce

"Fito mu tafi" sannan ya ƙara da cewa "kije kima Mama sallama"

Umma ta taɓe baki, tana kokarin danne damuwar da ke cike da zuciyarta. Azrah tayi shiru, sai ta mike jiki ba ƙwari ta nufi sashin Mama. Ko da ta shiga, ta tsuguna da sallama, Mama bata ko kalleta ba, tace a hankali "zan tafi Mama" a fusace Mama ta juyo tana mata wani kallon tsana ta ce

"Wai ni kam ba jiya kinmin sallama ba? Ko sau nawa ake yi ne?"

Azrah bata ce uffan ba ta juya ta fita, ta iske Bappah ya riga ya saka kayanta a cikin booth É—in taxin, ta tsaya ta kalli Umma da Zahra, tana jin kamar tayi kuka

Rungume Umma tayi da sauri, hawaye na gangarowa fuskarta. Zahra ta rungumeta itama, idonta cike da kwalla.

"Yanzu sai kawai na tafi na barku? Anya banso kai na daya wa ba?" ta faÉ—a da muryar kuka

Umma ta shafa bayanta tana faÉ—in "Haba Azrah, sai kace wannan ne tafiyar ki ta farko? Be strong, ko so kike ki hakura da karatun?"

Cikin tsawa Bappah yace "Ke! kizo mu tafi"

Azrah ta janye jikin ta daga jikin Umma da Zahra, tana share hawayen ta, ta shiga taxin babu shiri

A haka suka nufi hanyar airport, zuciyar Azrah na dukan uku uku, kuma har sannan tana share hawayen daya ki tsaya mata

Sun isa airport bayan tafiyar 40 mins, Bappah yana kallon agogo, sannan suka shiga cikin, sashin departure suka nufa, Azrah ta fito daga cikin motar tana jan trolley É—inta. Fuskar Bappah ta kalla wanda babu walwala ko kaÉ—an

"Ki bi layi nan ki fara clearing" ya faÉ—a mata yana nuna mata sashen, ta gyaÉ—a kai sannan ta nufi wajen

Clearing É—inta ya É—auki É—an lokaci kaÉ—an. An duba passport, visa, da takardun scholarship É—inta. Komai ya tafi daidai. Bayan ta gama, ta dawo wurin da Bappah ke tsaye yana waya. Sai da ya gama sannan ya kalleta ya ce, 'Zan wuce yanzu. Allah ya kiyaye hanya, kina isa kuma ki kira mu"

Kafin ta amsa, ya juya ya fara tafiya, tabi bayansa da kallo tana jin zuciyarta yana wani iri at least ai ko amsarta sai ya ji, taji hawaye na shirin zuba ta goge da sauri kafin mutane su fara ganin ta

Azrah ta zauna a waiting area tana jiran jirginsu ya tashi. Tana bin mutane da idanu

Kiran tafiyar su ya fito da ƙarfe tara da rabi, ta mike, ta tura trolley ɗinta a hankali, zuciyarta cike da rudani da fargaba. Bayan kammala bincike na tsaro, ta hau jirgin. Ta zauna a gefen window tana kallon window, Lokacin da jirgin ya tashi, kawai samun kanta tayi ta fashe da kuka

Sun sauka a Nnamdi Azikiwe International Airport, Abuja bayan kusan awa guda. Lokacin da suka sauka, ta fito da jakar hannunta tana dube-duben inda zata jira next flight É—insu zuwa India, tana kallon agogo dake nuni da karfe shaÉ—aya saura

"Flight É—in zuwa India karfe biyar ne" ta faÉ—a a ranta

Ta samu guri mai sanyi ta zauna, ta cire hijabinta kadan ta sake mayar da shi daidai. Wani sanyi na airport É—in yana sanya mata natsuwa, sai dai duk da haka, cikin zuciyarta tana tausayin Umma da Zahra, ga tunanin India, da Khalil ba zai kasance tare da ita ba

ita dai tana zaune tana ta tunani tunani, harda tunanin Future dinta da bata san ya zai kasance ba, kawai sai ga message É—in Samira ya shigo akan ta turo mata lokacin da zasu tashi saboda zata zo É—aukanta idan ta isa, murmushi tayi bayan ta gama karantawa

Yayinda agogo ya nuna ƙarfe 4:30pm, wata jami'ar jirgin sama ta fito tana sanar da fasinjojin da za su tafi India su fito domin a fara clearing. Azrah ta miƙe tana gyara hijabinta, ta janyo trolley ɗinta a hankali, zuciyarta cike da kaɗaici

Tana cikin tafiya zuwa layin clearing ne kawai idanunta suka sauka akan wata mata da ta taimaka mata tun ƙuruciya har zuwa girmanta

Mummy ce! Tana tare da Suhaila da Saif. Without second thought, Azrah ta saki trolley É—inta ta ruga da gudu taje ta rungumi Mummy tana dariya kamar karamar yarinya, Mummy ta kalle ta da mamaki kafin ta buÉ—e hannu ta rungumeta da kyau

"Azrah! Is that you?"

Azrah ta cire kanta daga jikinta tana gyaÉ—a mata kai da fara'a ta ce

"Eh Mummy, nice to see you!"

Suhaila ta nufi gareta da murmushi tana cewa

" My Azrah? Gaskiya kin canza sosai"

Azrah ta saki Mummy ta rungume Suhaila tana gaishe ta, sannan ta juya ta ga Saif da ke tsaye gefe yana danna waya kamar baya cikin duniyar nan. ta É—aure fuska ta ce masa

"Barka da warhaka, ina wuni"

Sai dai bai ko kalleta ba, sai dai ya É—an gyara tsayuwarsa yana murmushin gefen baki kamar wanda aka takura masa ya mata kallon sama da kasa sanna ya É—auke kansa

Mummy ta ce "Me kike yi a nan Azrah?"

Azrah ta ce "Mummy, ai na samu schoolarship a India yanzu haka zan shiga Level 2 ne ma"

Mummy da fara'a cike da murna ta ce

"Ma Shaa Allah! Congratulations dear, da fa har ina tunanin zuwa in nemi ki, ashe kin koma makaranta? I'm so proud of you!"

Suhaila ma tayi murna sosai, ta karɓa lambarta. Azrah ta ce

"Zan kira ku in shaa Allah idan na sauka"

Daga haka suka yi sallama, ita kuma ta wuce zuwa inda ake boarding

Clearing ya gudana cikin sauƙi. Tana shiga jirgin, ta samu kujerarta kusa da window ta zauna tana tura trolley ɗinta sama, tana gyara zamanta da takarda da passport a hannunta, ita bata san meyasa ba tafi enjoying jikin window

Ta kalli gefenta, wani matashi ne kallon farko zaka gane wayayye ne kuma ilimi ya zauna a jikinsa, yana sanye da farin t-shirt da jacket mai É—an tsawo, Kallon da yake mata kamar yana son mata magana ne, sai dai Azrah tayi kamar bata lura ba, ta gyara zamanta ta kalli window.

Bayan 'yan mintuna, wani flight attendant ya fara magana da microphone

"Ladies and gentlemen, welcome onboard flight 6E-211 to New Delhi. Our flying time will be approximately 9 hours. Please fasten your seat belts..."

Azrah ta ja numfashi, ta gyara belt É—inta kamar yadda aka umarta. Tana jin yadda idanun wannan ke yawo a kanta amma taki juyawa

Lokacin da jirgin ya daga sama, ta lumshe idanuwanta tana ɗora kanta jikin kujerar. A cikin zuciyarta, ta roƙi Allah ya sa tana gama wannan karatun ta samu aikin yi dan Zahra ma ta samu ta yi

Bayan tafiya mai tsawo suka sauka a airport É—in New Delhi

"India…" ta faɗa a hankali.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.