Beyond The Veil Part 1 Novel Complete Hausa Novel
Reading file: Beyond The Veil Part 1 Complete Novel.docx
Chapter 73 of 79
Episode 75: The Company's Betrayal
Abdul na zaune ga ƙwanon tuwa a gabansa yana ci, Siyama da Habibah suka shigo gidan a guje suna kwala wa Mama kira, kallonsu yayi ya daka musu tsawa, cike da magana irin ta 'ya'ya marasa tarbiyya ya ce
"Ubanku aka muku a wajen da zaku wani shigo mana gida haka?" Ko kallonsa basu yi ba, Mama ta fito daga dakin hankali tashe tana kallon su ta ce
"Uban me ya faru kuma? Tunda na lura banda son ku saka min ciwon zuciya baku da wani buri"
Siyama ta fashe da kuka ta ce
"Mama kina ji fah É—azu aka kawo wa Azrah motar har kofar gidan su" É—abas Mama ta zauna a kasa tana kallonsu, Habiba ta É—aura
"Mama ko mu marasa sa'a ne? Komai ace can gidan" tana kai wa nan ta fashe da kuka, Mama ta ce
"Bakin ku kullum banda tsiya babu abin da kuke fata wa kan ku, yanzu inji ubanwa ya ce muku an tsiya mata mota?" Sallamar wata makwabciyarsu suka ji, takara so cikin gidan, Siyama da Habibah suka wuce ciki, tana murmushi ta ce
"Akwai alale ne?" Mama na mata wani kallo ta ce
"Dama na taɓa yin alale warhaka ne?" Ta ce
"Ayyah ashe ya kare, kwaÉ—ayi nake ji Shiyasa na ce bari na shigo ko zan samu saura ne" Mama ta tamke fuska, har zata fita sai kuma ta dawo tana murmushi ta ce
"Ashe abun alkhairin ya faru? Mantawa nayi ban miki murna ba" Mama ta ce
"Aina abun alherin ya same Ni?" Ta ce
"Kawai sai muka ji 'yarki Azrah tayi mota ba?" Zuciyar Mama da É—azu bai samu ya tsinke ya faÉ—i ba shine yanzu yayi skipping na wasu dakiku tana kallon Matan wanda har ta soma jin dishi dishi, ta dake ta ce
"Toh yanzu ke uban me ya kawo ki? Gulma ko jin kwakwaf?" Abdul ya miƙe yana kallon matar ya ce
"Kee dalla wuce ki tafi" sakeke take kallon Abdul sai kuma tayi murmushin takaici ta juya ta ce
"Allah baku hakuri" daga haka ta fita, Mama tayi tsuka ta ce
"Wallahi duk gulma ce ke kawo su" tana kai wa nan ta fara share hawayen fuskanta, a tare Habiba da Siyama suka fito, Siyama ta ce
"Ai gashi kinji da kunnenki, da gaske yanzu mota gare su" Mama duk da damuwar da take ciki ganin damuwar yaranta yasa ta dake ta ce
"Ku dallah ku share hawayenku, ai na faÉ—a muku mutumin ya ce maza zasu fara sintiri kofar gidan, yanzu kar ku sha mamaki wani daga cikin 'yan iskan nata ne ya tsiya mata, toh me abun damuwa" Siyama ta sake fashewa da kuka ta ce
"Ai haka zaki ce dama, kullum ma banda hakan babu wani abun cigaba, dan ba ke bace kike fita ake gaya wa magana shiyasa, ina yanzu a hanyar mu ta dawowa wannan tsohuwar bakin hanyar ta ce mana mu banda tallah da yawo babu abin da muka yi, ko kunya bamu ji ne ace 'yan-uwan mu suke nan a nutse kuma kullum ci gaba suke yi, kiji fah abin da ta faÉ—a mana" Mama ta sauke ajiyar zuciya
Abdul ya ce "tun ba yau ba haka Mama take lafta mana magana kuma yaki yiwa, kuma maganinku ai da kuka yarda" Mama ta masa wani kallo ta ce
"Ubanka shegen yaro Ni zaka karyata kenan?" ÆŠaga hannun sa bibbiyu yayi ya ce
"Mijinki kenan! Ai yana ɗaki" Mama ta sake baki tana kallon sa, ta lura tun daya dawo ya sake ɓantarewa, Siyama ta ce
"Mama Ni kam na yarda ko 'yan iskan ne suna zuwa waje na Nima" Mama ta ce
"Amma baki da hankali yarinyar nan" Habiba ta daura
"Gaskiya Nima Mama ina so, ina ga idan zaki koma ma Malamin kice ya haɗa harda mu" daga haka ta miƙe tayi ciki, Mama ta rabka uban tagumi tana tunanin wata mafitan kuma, Siyama ta miƙe ta bi bayan 'yar uwanta...
Dariya tayi ta ce
"Kai Samira! Toh yanzu yaushe zaki zo gani?" Samira a ɗayan ɓangaren ta ce
"Ai dole nazo gani, dan ma yanzu Deen na lallaɓa Ni idan nace ya kawo Ni nasan zai kawo Ni" Azrah tayi dariya ta ce
"Toh yanzu bai fi muku ba akan wanan faÉ—an naku?" Samira ta ce
"Dama can shi ya É—aura Ni akan wannan yanayin fah, shi a dole rayuwar turawa, wayayyar mace, amma yanzu ai idonsa yayi clear, ya gane Allah É—aya ne, Nima nagane kuskuren hakan musamman yadda kike nutsar da Ni" Azrah ta ce
"Ma sha Allah, Allah kara haÉ—a kawunan ku, yanzu yaushe kenan zaki zo" ta ce
"In shaa Allah gobe zan sa ya kawo Ni" Azrah ta ce
"Toh Allah kaimu" daga haka suka yi sallama ta kashe wayar...
Da sauri ta fito a office É—in, duk da cewa babu ko wani maaikaci saboda tun tuni aka tashi, kalle kalle take dan sake tabbatar da cewa babu wani cctv a wajen sannan ta sauko a hankali, bayan ta karasa bakin gate, tana murmushi masu gadi suka tambaye ta
"Kin ga wayar naki? Ta gyaÉ—a kai ta ce
"Ai dama nasan anan na bari, ina haurawa kuwa na gani" suka ce
"Toh Alhamdulillah" fita tafi, ta shiga motarta ta kunna motar sannan ta bar layin
Daya daga cikin gateman ya ce
"Kalli dama matar nan na saka hijabi ne?" Yayi dariya ya ce
"Baka ganta duk a birkice ba? Har wani jaa idonta yayi ina ga duk ta ruÉ—e ne akan neman wayar nata" dariya yayi ya ce
"Ashe dai duk burgane idan har akan ɓatan wayanta zata yi haka, ita ai kullum ji take da kanta ita wata siyar ce kamar tafi kowa da munin fuskanta a wajen" dariya sosai ɗayan yayi ya ce
"Ga uban girman kai, gashi a Gaishe ta taki amsawa, amma yau harda fara'a dake abun ta take nema" duk dariya suka yi...
Maman Amira ta shiga É—akin Dada da sallama ta ajiye mata plate É—in abincin ta ce
"Dan Allah Dada ki samu ki É—an ci abinci ko da kadan ne, zama da yunwar ma zai kara miki wani ciwon ne" Dada ta ce
"Zan ci Maman Amira, amma yanzu kam ki tashi ki tafi gidanki Kinga har Magrib yayi" ta gyada mata kai ta ce
"Amma Dada wannan ciwon naki Allah na tuba bada saka hannu ba kuwa? Dan na lura tunda kika dawo fah kullum kike kwance" Dada tayi murmushi ta ce
"Ke ma ai kinsan wannan ciwon bana Allah bane, ace jiki baya tashi sai na shiga Mota zani cikin Katsina? Yau sati nawa ana fama da abu É—aya" Maman Amira ta ce
"Toh nikam Ina ga ko zanma Maman Amira magana idan abokinsa dake jan keke Napep a cikin garin Katsina sai a basa maganin ya tafi da shi ko?" Dada ta gyada kai tana hawaye ta ce
"Ai da hakan ma zai fi, amma matar nan ta cuce Ni da ɗana da kuma jikoki na, gashi suma yanzu basu kira na wanda ba halin su bane kila har su bata barsu ba, Uwarsu da bata da kowa ne abin tausayi" Dada ta miƙe dakyar tana hawayen bakin ciki, ita da garin ɗanta amma bata isa zuwa ba, Maman Amira data yi tagumi ta ce
"Toh nikam anya ba kai ki gun masu magani zamu yi ba? Ai su zasu gano bakin matsalar" kai kawai Dada ta gyada mata...
Washe gari Azrah ta tashi da cramps, sosai yake galabaitar da ita, hakan yasa tayi ta shan bacci da safe, wanda Umma ta hana Zahra tashin ta, tuni Zahra ta gama nata shirin ta saka wani Abaya daga cikin uban kayan da Azrah ta musu shopping last week, ba kaÉ—an ba tayi wani sihirtatcen kyau, ta maka face mask dan ta tsane takuri gashi harta Lecturers É—insu ba barinta suke ba, sallama tama Umma sannan ta fita. Can wajajan karfe goma Azrah ta farka, Umma ne ta shigo É—akin tana kallonta ta ce
"Ya jikin naki kuma?" Azrah dake riƙe da cikinta tana juye juye ta ce
"Ya ɗan sauka, amai nake ji kuma yanzu" Umma ta miƙe ta ce
"Ina zuwa" daga haka ta nufi kitchen bata wani daɗe ba ta dawo ɗakin, ta ajiye kayan hannunta sannan ta ɗaga Azrah zaune, cup ɗin ruwan zafi data tafasa mata da Habbatus sauda ta miƙa mata, Azrah ta karɓi kaɗan tasha, Umma ta saka towel a ruwan zafin tana matse ruwan tana ɗaura mata a mararta a haka wani baccin ya sake ɗaukarta, hakan yasa Umma kwantar da ita, ta ɗauki roban ta fita da shi
Yau tun da safe da suka shigo Companyn kananun maganganu ne ke tashi, Mr Alhassan ya kasa zaune sabar asarar kuÉ—in da yake fuskanta wanda zai yi, PA ma ya girgiza ba kaÉ—an ba da jin wannan lamarin
2nd floor É—in companyn ya cike da hayaniya, a reception har zuwa gaban HR, ana jita-jitar wani 'matsanancin bincike da ake yi da wasu masu knowledge a harkar cyber security, kowa na jiran su san me ke faruwa.
Sadeeq ya shigo cikin hanzari yana yamutsa fuska kowa basa hanya yake yi a haka har ya nufi office dinsa kai tsaye yana mamakin abin daya ji, baya kuma kaunar yayi zargin kowa, har lokacin ba a ga Azrah ba kuma a office, wanda hakan ya sa tambayoyi suka ƙaru.
Miss Merry data shiga cikin Office É—in PA wanda su suna can sun haÉ—a zufa, tana kallon Miss Safiyya ta ce
"Yau banga Miss Azrah ba, ko lafiya amma? Dan wannan ba halinta bane na rashin zuwa"
Safiyya ta harareta ta ce
"Haba mana Miss Merry, ke baki ji kamar wani abu ya faru bane kuma ana zargi a cikin staff ne sai kuma yau bata zo ba, toh Allah da dai lafiya"
Miss Merry ta ce
"Ban gane ba? Wai wani maganar kuma kike yi haka? Dama an san abin daya faru ne? Tou Ni a bakin ki na fara ji ma" jin me ta ce yasa miss Safiyya ta yi saurin cewa
"Noo! Nima hakan naji fah amma kasa kasa ne, I'm not sure"...
Mr Alhassan ransa a mugun ɓace yana kallon PA ɗinsa ya ce
"Ka yi calling meeting cikin gaggawa" hakan kuwa akayi
Kowa ya taru daga Mr Mahmoud, Oga Abubakar, Safiyya, Sagir, Merry har ma da kananun staff
Tension ya cika conference room din
Mr. Alhassan ya kalli su gaba É—aya sannan ya ce
Â
"Mun samu matsala da confidential document da aka tura jiya ga wani babban investor. Bayanai sun nuna akwai sauyi da aka yi a cikin file É—in. And this could cost us a major deal, waya ke son ganin bayan mu har haka?"
Dakin ya É—auki shiru kowa da tunanin da yake yi
Ya kalli IT manager ya ce
"Malam Haruna, ka faÉ—i mana abin da ka gano"
Haruna ya buÉ—e system, ya haÉ—a projector a hankali ya soma magana
"An yi login daga account din Miss Azrah Muhammad, IP ɗin kuma ya fito ne daga system ɗinta, timestamp ɗin da kuma files sun nuna changes da password dinta aka yi, duk wadannan abubuwa sun faru ne misalin ƙarfe biyar na yamman jiya"
Gaba É—aya cike da tsananin mamaki suka ce
"Subhanallah!"Â
Wani staff ya ce
"No wonder bata zo aiki yau ba!" Wannan ai cin amanar kamfani ne!" Duk hall din suka fara reasoning da maganar sa na yau bata zo aiki ba
Sagir ya ce
"Dama ai kun san ita ce ta fi shige da fice da investors. Maybe ta fara amfani da damar data samu ne"
Oga Abubakar ya harare shi,Â
"Ka rufe mana baki Sagir! Bincike ake, ba ka yanke hukunci ba, We're not sure yet, unless an ji daga gareta"
Sadeeq wanda tun farko yake gefe amma bai tanka ba, ya É—an gyara zama, ya ce cikin taushin muryansa
"Maybe system É—inta ne aka yi hacking, ba lallai ba ne ita da kanta, hakan zai kuma iya faruwa, for now kada a yi saurin yanke hukunci"
Sai kawai Miss Merry ta ce tan dariya
"To ai ko hakan ne, ita ce ke da alhakin password dinta. Komai ya faru daga bangarenta ne, Sir"
Miss Safiyya na kaɗa jiki ta miƙe cike da jan hankali ta ce
"Amma idan ba ita bane mayasa yau taki zuwa?"....
Tension ya kara tashi sosai a Companyn lokacin da zancen ya kareÉ—e ko ina, wasu ma daga junior staff na waje sun fara cece-kuce
"Ni na farka da mugun mafarki yau, ashe dama wata fitina zata tashi anan ne" inji Ishaq
"Tunda ta fi kowa shahara, ta fi kowa da kusanci da manya, maybe ta samu chance ne da Company" Adam ya ce
Wani ya ce "Hmmm! Ai wallahi dama bana jin daÉ—in irin shigar data ke yi. Wata kila ai da kuÉ—in Company tun da can take kamfalawa, amma ai wannan rashin godiya ne, ina anan aka bata kyautar mota shine kuma zata aikata haka wa Mr Alhassan?".
Yadda hayaniyar yayi yawa yasa Mr. Alhassan ya sake komawa cikin su ya dakatar da hayaniya,
"Ba wanda zai yanke hukunci kafin mu ji daga gareta, sai ta dawo gobe, za mu ji bayani cikakke daga bakinta, amma yanzu investigation zai ci gaba"
Sadeeq ya miƙe a fusace ya bar conference room ɗin, har zai shiga office ɗinsa kuma sai kawai ya fasa ya fita gaba ɗaya daga Companyn.....
#Jiddatulkhayr
08110615256
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.