Beyond The Veil Part 1 Novel Complete Hausa Novel
Reading file: Beyond The Veil Part 1 Complete Novel.docx
Chapter 56 of 79
Episode 56: Homecoming
Umma da Zahra suna zaune suna ta hirarsu, Azrah ta fito daga É—aki ta wuce zuwa compound É—in gidan dan yin alwala, Umma ta bita da kallo sai kuma ta kalli Zahra ta ce
"Nikam baki ga yadda Azrah ta canza ba?" Zahra tayi dariya ta ce
"Wlh Umma Nima naga ta kara girma sosai kamar ba ita ba".
Azrah ta shiga É—akinta tayi sallar la'asar cikin nutsuwa. Tana idarwa ta kwanta cinyar Umma. A lokacin ne ta fara jin gajiya sosai bayan dogon tafiya, nan da nan kuwa bacci mai daÉ—i ya É—auke ta
An fara kiraye kirayen Magrib ta farka. Ta miƙe zaune tana murza idanunta wanda yake cike da bacci, mamakin yadda tayi bacci a cinyar Umman tayi, ta juya ta kalli Zahra na kwance kan darduma tana kallon hotunanta na a wayanta data buɗe mata kafin tayi bacci, yayin da Umma tana ƙara bin ta da kallo cike da farin ciki ganin yarda 'yar nata ta girma
Azrah ta É—an yamutsa fuska da wasa, ta ce
"Toh! Gaskiya yanzu zaki fara gani da idon k, bari na baku album gift da aka bani nan zaki fi gani…"
Ta mike, ta nufi wajen akwatin ta wanda ke cikin ɗakin su. Babban jakkan da Samira ta tara mata gifts a cikin ta ɗauka, komawa ɗakin Umman tayi, ta zauna zata buɗe jakkar, Umma ta miƙe ta ce
"Mu je muyi sallah kafin nan" daga haka suka wuce zuwa É—auro alwala wanda gidan shiru dan babu Mama balle Yaranta
Bayan sun idar Azrah ta buÉ—e jakkan tana kallon Umma ta ce
"Ga certificate ɗina nan first class, da awards ɗin nan... Best in CGPA, Best Student of the Year…" ta miƙawa Umma Zahra ta sake baki tana ware idanu
Ta mika musu Result ɗinta. Umma ta karɓa tana murmushi, tana kallon certificate ɗin tana hawaye. Zahra kuwa ta miƙa hannu tana kwasar envelopes ɗin tana karanta sunan Yayarta da ke ji kin.
Umma ta ce "Allah Sarki… Azrah kin cika mana burinmu, Allah ya yasa ki samu aiki, ya baki miji na gari" Azrah sai murmushi take ta gagara cewa komai
Zahra ta ce "Antyyyy… ke ce fa Most Talented kuma! Harda Best Student? A wata kasa? Kai Allah mun gode maka"
Suka yi dariya gaba É—ayansu, sai Azrah ta ce
"Zaki iya fiye da hakan ma Zahra"
Ta juya ta fito da wani ƙaramar bag wanda Intisar ta bata. A ciki akwai gift packs da gold jewelry da ta bata a wajen small party da suka yi, sai kayan da Ammah ta mata wanda ta raba wa colleagues ɗinta mugs da hotonta a jiki, memo pads, cards, sannan wasu envelopes na kuɗi daga wasu VIPs da suka ji labarinta. Daga Umma har Zahra buɗe baki suka yi dan suma sun gagara magana
Ta jawo wayarta, ta bude banking app É—inta, ta nuna musu alert na credit transfer
Ta ce "Wannan kuwa… kuɗin governor of New Delhi ne. Check ya bani shine tun acan aka mayar min acc din, Nace sai na dawo gida zan muku bayani"
Zahra ta rufe baki ta ce "Kiiiiiiiii... Allah ya ga wahalar mu, Shikenan yanzu munbar talauci knn! Gobe gobe kuma sai ki sayi mota ki bani ki ce nice driver"
Azrah ta harareta ta ce "Shikenan sai kawai na tsiya mota? Sannu Zahra" dariya Zahra tayi
Umma na murmushi mai hawaye ta ce "Wannan kenan Azrah. Wannan ba kawai ilimi bane, soyayyar Allah ce. Allah ya dube wahalar ki shiyasa ya mayar miki cikin ruwan sanyi"
Azrah ta ce "Na san babu inda zani sai da yardarku. Wallahi duk inda na kai, addu'ar ku ce"
A haka suka ci gaba da hira, suna duban gifts É—inta, certificates da hotuna. Zahra ta É—auki gift mug daya ta ce
"Wannan mug É—in kuwa tuni zan fara amfani da shi. Yau dai ga cup É—in 'yan gayu da hoton Yayata, ni zanna shan koko dashi kullum"
Banda farin ciki babu abin da suke ciki, har ba zasu iya misaltawa ba, Umma da Zahra na jin kamar suna mafarki da yadda Azrah ta dawo ba kawai da certificate ba, amma da wani irin nasara da ba'a iya auna ta. Kuma har a zahiri, sun gane Azrah ta canza ta girma, ta natsu, ta ƙara haske da wayewa.
Jin karan shigowar su Mama da Yaranta yasa Umma ta kalleta cikin murmushi ta ce
"Azrah tashi kije ki nuna wa Mama dan kar Bappah'n ku ya dawo tace ai bata san da zuwan ki ba irin na wancan lokacin''
Azrah ta gyada kai, duk da bata ji wani murnan zuwa ba, tayi murmushin dole, ta miƙe, ta ɗauki graduation gift packs guda biyu, mug cup guda biyu ɗin da aka buga hotonta da sunanta, da kuma memo hardcopy ɗin da aka rubuta Congratulations, Azrah Muhammad Class of Excellence Ta daure vintage a kanta sannan ta miƙe tana kallon Umma ta ce
"Ai wannan É—in sun yi ko?" Umma ta ce "Eh, amma ki dauki harda result dinki mana" Zahra ta kyalkyale da dariya tana tafe hannu ta ce
"Toh me amfanin nuna mata bayan ko sanin muhimmancin sa bata yi ba balle tasan me abin yake nufi" Azrah bata san sanda tayi murmushi ba kawai ta fita..
A sashin Mama, sun cika dakinta da ihu, Mama na zaune gefenta kuma Siyama, Habibah kuma tana gefen Abdul. Hirarsu suke yi amma babu nutsuwa, ana dariya da shewa
Amma da Azrah ta shiga, duk cikin É—an lokaci suka yi shiru,
duk Idanu suka zuba mata dan yadda canjin da ya bayyana gareta ya tsorata su ba kaÉ—an ba
Fuskarta ciƙe da fara'a, dressing dinta simple amma classy. Idon Mama ya sauka a kanta tun daga kai har ƙafa, a zuciyarta tace 'Ita ce wannan matsiyaciyar? Sai kace wata ‘yar minister hmm zama bai kamani ba
Azrah ta zauna a kasa tana kallon Mama, sannan ta ce
"Ina wuni Mama"
Mama ta É—an gyara zama tana É—auke kai, ta amsa da,Â
"Uhm. Yauwa"
Siyama ta taɓe baki tana kallon gefen, Habibah kuma kamar ta fi kowa ɓacin rai. dan miƙewa tayi ga bar dakin. Azrah bata kulasu ba. Ta miƙa gift ɗin da murmushi ta ce
"Ga wannan Mama, daga makarantar ce, saboda graduation É—ina, É—azu na dawo"
Mama ta karɓa ba tare da godiya ba ta ce
"Toh"
Shiru ya biyo bayan hakan. Azrah ta miƙe cike da nutsuwa, ta kalli Mama ta ce
"Zan tafi Mama, sai anjima"
"Toh" inji Mama ba tare da ta kalleta ba.
Ta juya ta fice cikin natsuwa ta saka a ranta like wannan normal ne a wajenta dan da sabo ta saba da rashin kirkin Mama
Da ta shiga É—akin Umma, ta zauna, tana kallon su Zahra da murmushi. Umma ta ce
"Ya kuka yi da ita?"Â
Azrah ta gyara zama ta ce "Na je Umma, na gaishe ta, na kuma bata gift ɗinta"
Kafin Umma ta ce wani abu, sai suka ji muryar Bappah daga compound ɗin yana magana da wani. Azrah ta miƙe da sauri, zuciyarta cike da farin ciki ta karasa bakin kofar ta daga labule, idanunta suka sauka a kansa, da sauri ta sauka har kasa tana dariya, ta tafi da gudu ta rungume shi ta ce
"Bappah na!"Â
Bappah ya saki murmushi yana shafa kanta ya ce
"Iyyee… yarinyar Bappah ta girma! Toh yaushe kika iso?"Â
"ÆŠazu ne fah Bappah. Bappah ka zo na nuna maka certificate dina da awards!"Â
"Toh muje mana. Yar bappah ta gama degree" inji Bappah yana dariya
Suka shiga ciki, Umma da Zahra suna zaune, Zahra ta tamke fuskarta kamar bata san me dariya ba
"Toh yarinyata, nuna min certificate É—in" cewar Bappah bayan ya zauna
Azrah ta ɗauki jakar certificate dinta, ta fiddo manyan awards, da plaque trophy. Ta miƙa masa certificate ɗin, album da dai komai. Bappah yana karantawa yana girgiza kai cike da alfahari
"First Class? Sai wannan 'yar Baba. Most Decent Student? Best in Business Skill? Haba sai Azrah É—ina!"Â Ya rungume ta ya manna mata kisa a forehead dinta ya ce
"Allah miki albarka, Allah yasa wannan shine mafarin nasara"
Azrah ta kuma fito masa da wasu kyaututtuka da aka bata, ta jawo wayanta zata nuna masa alert É—in, Zahra ta mata wani kallo ta fake idon Bappah ta kwashe wayan ta ce
"Bappah kuma an bata kyautar 10 Million" Azrah ta dinga kallon Zahra ganin ta rage wajen 30 mil a kuÉ—in
Bappah ya kasa boye mamaki
"Azrah nikam ma bansan me zance ba, harda 10 mil kuma?
Umma ta zuba mata ido tana murmushi ta ce
"Allah Ya saka musu da alheri. Allah Ya kare ki daga idon hassada, mu de mun gode"
Azrah de tagumi tayi ta rasa me zata ce jin Zahra ta rage amount din....
Bappah na fita Azrah ta kalli Zahra tun kafin tayi magana Zahra ta riga ta "Toh so kike a faɗa masa dukkan kuɗi yaje ya faɗawa Matarsa tazo ta samu a gaba ko kuma ya karɓi some amounts yace zata ja jari"
Washegari da safe, bayan sun kammala breakfast, Azrah na zaune gefen Umma tana duba wayarta. Ta juya tana fuskantar Umma da murmushi ta ce
"Umma ai jiya da daddare wani kamfani ya sake turo min sako suna so suyi hira dani. Na ce musu zan je yau"
Umma ta kalleta da ƙwarin gwiwa ta ce
"Toh mana tashi ki shirya. Ai irin wannan dama ba'a watsar da ita ba"
Azrah ta gyada kai, ta miƙe cikin nutsuwa, ta fita compound ta shiga bayi, tayi wanka, ta fito ta wuce ɗakin su, bayan ta gama shafe shafenta tasa wata light brown abaya mai kyau. Tayi kwalliya light, sannan ta ɗauki jakarta da mayafinta. Ta wuce zuwa ɗakin Umma tana kallon ta ta ce
"Umma sai na dawo"Â
"Allah Ya kiyaye hanya" inji Umma tana kallonta da kulawa.
Tun data fita daga gida 'yan layinsu, duk wanda ta hadu da shi sai ya gaishe ta Manya da yara har hakan yaso ya fara bata kunya, kowa da abin da yake faÉ—i
"Yarinyar Bappah kin dawo lfy?"Â
"Masha Allah, muna taya ki murna"
"Wannan ce 'yar India din nan ko?"Â Irin maganar da ake ta yi kenan
A haka har ta isa event center É—in da ake shirin yin interview É—in. Kamfanin "SheLeads Africa" ne suka gayyace ta. Bayan an kammala shiri, aka fara gabatar da ita ga jama,'a.
Tambayoyin da suka mata sun haÉ—a da
1. "Za mu so ki faÉ—a mana, me ya ja hankalin ki zuwa business administration?"
  Azrah ta ce "Tun tasowa ta na taso ne cikin sana'o'i wanda a lokacin Umma na kanyi min faɗa dana bari amma kuma ban hakura ba, sannan duk abin dana saka a gaba idan har na sana'ace ina samun cigaba, shiyasa naji kawai na karanci course ɗin dan aiki a Manyan companies"
2. "Wane challenges kika fuskanta a wajen karatu da kuma yanda kika shawo kansu?"
  "Rashin sanin yare da sabon yanayi ya sha banban, amma da addu'a da support daga gida da friends na, na tsallake komai"
3. "Me zaki iya cewa matasa musamman mata masu burin yin karatu a waje?"
  "Su daure, su kasance da kyakkyawan niyya da tsari. Kuma su kasance masu kima da mutunci, domin shine darajar su, ba wai suje da niyyar sharholiya ba"
4. "Me kike shirin yi yanzu da kika dawo gida?"
  "A halin yanzu, ina shirin fara NYSC da kuma kafa small business da ya shafi skin care products ne"
Anan aka rufe interview É—in da kyaututtuka, aka bata branded gift box, certificate of appearance, da wata brown envelope. Tayi godiya sosai sannan ta fito da murmushi a fuska.
Yana zaune a Babban Office ɗinsa, yana kallon TVCnews da suke hasko ta a masayi live video, ganin kamar yasan fuskar sai kuma ya dauki wayar sa ya shiga IG nan ya dinga kallon post din da aka dinga yi akanta, ba shiri yabi ya duba history dinta kamar yadda aka bayar, abin daya fi connecting da heart ɗinsa shine ganin yadda aka bata awards na best a bangaren business skills lumshe idonsa yayi yana nazari sai kuma ya miƙe zaune yayi dialing wani number....
Azrah ta fito a wajen tana kokarin tsayar da keke-Napep kenan, sai ga wayar Samira ya shigo
"Hello Samira!"Â ta faÉ—a bayan tayi receiving call É—in
Samira ta ce "Baby Girl! Kin ji labari kuwa? NYSC portal an buÉ—e fah yanzu yanzu!"
Azrah ta ce da mamaki
"Serious? Toh ai tunda har na fita, zan tsaya a café yanzu kawai in cika komai, kafin na koma gida"
Suna dariya suka yi sallama.
Azrah ta karasa wani café, ta shiga, shiga tayi da sallama bayan sun amsa tace zato registration ne na service, ai kuwa cikin sauri suka taimaka mata aka yi mata registration, aka duba requirements, aka shirya, sannan aka tura. Tayi godiya ta fito da murmushi a fuskarta
Ta É—auki hanya zuwa gida, zuciyarta cike da natsuwa da kwanciyar hankali, tana tunanin yanda komai ke sauka a bisa hanya. ..
Bayan kwana biyu da dawowar Azrah gida, gidan ya sake samun É—an sauyi. Wata rana da safe, aka ji karar horn a kofar gida. Sai ga Dada. Duk suka fita da murna don tarbar ta.
Zahra da Azrah suka fi nuna excitement, akan su Habibah da Siyama, suka shiga mata da jakunkunanta, suna mamakin bazatan zuwa da tayi.
Bayan kwana biyu da zuwan Dada, wata rana tana zaune da Bappah a dakin sa, ta kallesa cike da damuwa tace
"ÆŠan nan, gaskiya wannan lokacin ne daya dace, ya kamata kowa daga cikin yaran nan su fito da wanda suke so idan suna da shi, a samu a aurar da su"
Bappah ya gyara zamansa yana nazari, sai ya ce
"Ai wlhi Dada wannan abin kullum na cikin raina. Wani lokacin idan na kalle su, ina ganin yanzu ne lokacin da ya dace ace sun fara barin gida" a haka dai Dadda da Bappah suka yake hukunci.
Washegari da rana, Bappah ya tara duka 'ya'yansa harda Dada dake gefe ga Mama ma data zauna wai tana jiran saƙo ne, a filin gidan. Yana kallon su cikin natsuwa ya ce
"Na kira ku ne dan muyi magana mai muhimmanci. Lokaci ya yi da kowannen ku ya kamata ta fito da wanda take so na aurar da ku nima na huta"
#Jiddatulkhayr
08110615256
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.